Thursday, 19 September 2024
Email
Make My Homepage
RSS
Register
Tambayoyi da Amsoshi kan Azumi. Print E-mail
Written by administrator   
Sunday, 04 June 2017 11:03

Kasantuwar wannan wata mai albarka da muke ciki wato watan Ramadan wanda a cikinsa muke Azumi da Allah Ta’ala ya wajabta mana domin mu samu Ta}awa.Insha Allah a wannan darasi za a kawo tambayoyi ne da kuma amsoshi kan sassa dabam dabam da suke da ala}a da Azumi wa]anda aka tambayi Ayatullahi Sayyid Khamna’i da kuma amsoshin da ya bayar a kai.

          Tambaya:Yarinya wanda ta kai shekarun taklif wato shekara tara,amma sai dai bata iya Azumin watan Ramadan saboda raunin jikinta,bayan watan Ramadan bata samu ikon rama wannan Azumin ba har wani watan Ramadan ya zagayo,to minene hukuncin ta?

          Amsa:Rashin iya yin Azumi ko rama shi saboda dalilin raunin jikinta bai wajabta fa]uwar ramakon Azumi akanta ba,a’a wajibi akanta ta rama Azumummuka da suka ku~uce mata na watan Ramadan.

          Tambaya:Yarinya wanda shekarun ta suka kai tara a saboda haka Azumi ya wajaba akanta,amma sai ta ci abinci saboda Azumin yana yi mata wahala,to shin wajibi ne ta rama Azumin?

          Amsa:Wajibi ne a gareta ta rama Azumin da tasha A watan Ramadan.

          Tambaya:Minene hukuncin wanda bai samu yin Azumin watan Ramadan ba saboda dalili na rashin lafiya,kuma bai samu sau}i na rashin lafiyar ba har wani wata na Ramadan ya zagayo?

          Amsa:Idan Azumin watan Ramadan dukkansa ko wani sashensa ya ku~uce ma mutum saboda rashin lafiya,kuma rashin lafiyar ya cigaba har wani watan Ramadan ya zagayo,to ba wajibi bane ya rama kwanukan da suka ku~uce masa,yanzu abinda zai yi shine ciyarwa,amma da ace uzurin da ya hana ci yin Azumin wani dalili ne ba rashin lafiya ba misali kamar tafiya,kuma ya cigaba da tafiyar har wani Ramadan ya zagayo,to anan wajibine ya rama Azumin wato ba ciyarwa zai yi ba.

          Tambaya:Minene hukuncin wanda akwai ramakon Azumin Ramadan akansa amma ba tare da wani dalili ba sai bai rama ba har wani watan Ramadan ya zagayo?

          Amsa:In dai babu wani uzuri da ya hana shi ramawa,to ramuwar da kuma kaffarar jinkiri ta hau kansa,wato wajibi ne ya rama Azumin da kuma ciyarwa.

          Tambaya:Minene hukuncin wanda mahaifinsa ko mahaifiyarsa suka rasu alhali akwai bashin Azumi ko ramakonsa akansu?

          Amsa:Wajibi ga babban ]a namiji shi }ashin kansa ya rama masu Azumin ko kuma ya yi jinga da wani wato ya biya shi akan ya rama masu.

          Tambaya:Minene hukuncin yin Azumi a tafiya cikin watan Ramadan?

          Amsa:Duk wanda yayi tafiya a cikin watan Ramadan in har tafiyar ta kai ga haddin yin }asaru to wajibi ne ya aje Azumi-Sai dai akwai wasu yanayoyi da koda mutum yayi tafiya ba zai aje Azumi ba misali mai kasuwanci daga wannan gari zuwa wannan gari,ko mai tu}in mota wato zuwa wasu garuruwa ko kuma ya je waje da nufin zai kwana goma ko sama da haka da dai sauransu.

          Tambaya:Minene hukuncin Azumin wanda yayi tafiya gabanin zawal ko kuma bayan zawal?

          Amsa:Wanda yayi tafiya gabanin zawal Azumin sa ya ~aci amma da ace zai yi tafiyar yaje har ya dawo zawal bai yi ba to Azuminsa na nan bai ~aci ba misli a ce shi mazaunin Kaduna ne sai yayi sammako ya tafi Kano yaje har ya dawo zawal bai yi ba.Idan bayan zawal ne yayi tafiyar to Azumin sa ya inganta wato wajibi ne ya kammala Azumin sa.

          Tambaya:Idan mutum zai yi tafiya gabanin zawal to ya halatta ya ci abinci daga gida?

          Amsa:Bai halatta gareshi ba ya ci abinci daga gida har sai ya kai haddin da ake soma sallar }asaru-wato dai kamar yadda mutum ba zai soma sallar }asaru daga gida ba har sai ya kai haddinta to haka nan hukunci yake ga cin abinci,saboda haka da ace mutum zai ci abinci daga gida ko gabanin ya kai wannan haddi to kaffarar cin abinci da gangan a watan Ramadan ta hau kansa,amma da ace ya dawo daga tafiyar ne to anan dun ya ci abinci a gida ba komai akansa misali ace shi mazaunin Kaduna ne to ya tafi Kano gabanin zawal bai dawo ba sai bayan zawal to anan in ya dawo zai iya cin abinci a gida-

          Tambaya:Minene hukuncin wanda ya dawo garin da yake zaune gabanin zawal ko kuma bayan zawal?

          Amsa:Idan matafiyi ya dawo garinsu gabanin zawal ko kuma ya isa wajen da yake da niyyar yayi kwanaki goma gabanin zawal to in bai ci komi ba a hanya to wajibi ne yayi Azumi amma idan yaci abinci gabanin ya isa to ramuwa ne akansa.Idan kuma ya dawo garin da yake zaune bayan zawal to ba zai yiyu masa ba yin Azumi.

          Tambaya:Minene hukuncin tsoho ko tsohuwa wanda yin Azumi yana wahala garesu?

          Amsa:Azumi ya fa]i akan su abinda ya wajaba akan su shine ciyarwa-sai dai a lura anan ana nufin irin tsofaffin da suka tsufa sosai.

          Tambaya:Minene hukuncin Azumin Mace mai ciki ko kuma mai shayarwa?

          Amsa:Mace mai ciki wadda take tsoron idan ta yi Azumi abinda yake cikinta zai cutu to wajibi ne ta aje Azumi sai ta ciyar kowace rana saannan kuma daga baya sai ta rama Azumin.Haka nan hukuncin yake ga Mace mai shayarwa wanda in da zata yi Azumin ruwan nononta zai }aranta ko kuma ya bushe wato itama wajibine ta aje Azumi ta ciyar kowace rana daga baya kuma sai ta rama Azumin.

          Tambaya:Minene hukuncin wanda yana Azumi na wajibi ko na nafila sai ya manta ya ci abinci ko ya sha wani abin sha?

          Amsa:Azumin sa bai ~aci wato yana nan.Haka nan Azumi bai ~aci ba idan mutum ya ha]iye yawun bakinsa.

          Tambaya:Minene hukuncin Mace da take Azumi sai jinin Haila ya zo mata?

          Amsa:Idan jinin Haila ko Nifasi ya zo mata Azumin ta ya lalace ko da ko gab da fa]uwar rana ne abin ya faru.

          Tambaya:Minene hukuncin macen da tayi tsarki daga jinin Haila ko na Nifasi da daddare a watan Ramadan sai ta yi jinkirin wanka har Alfijir ya keto?

          Amsa:Idan ta yi jinkirin wanka har Alfijir ya keto to Azumin ta na wannan rana ya ~aci.

          Tambaya:A watan Ramadan Mace za ta iya amfani da magani da zai hana ta jinin Haila saboda gudun yenkewar Azumin ta?

          Amsa:Ba matsala zata iya yi.

          Tambaya:Minene hukuncin wanda janaba ta same shi a watan Ramadan?

          Amsa:Idan janaba ta samu mutum da daddare a watan Ramadan to wajibi ne akansa yayi wanka gabanin ketowar Alfijir,saboda da zai kasance bai yi wankan ba har Alfijir ya keto da gangan to Azuminsa na ranar ya ~aci.Amma da ace ba da gangan bane misali da janabar ta kama shi sai yayi barci bai farka ba sai bayan fitowar alfijir to anan Azuminsa ya inganta.Irin wannan hukunci haka yake a ramuwar Azumin watan Ramadan.Amma ga Azumi na nafila ko wa]anda ba na watan Ramadan ba ko ramuwarsa to su koda alfijir ya keto yana da janaba da gangan to Azuminsa ya inganta.

          Tambaya:Minene hukuncin wanda janabar ta kamashi amma sai ya manta bai yi wanka ba har alfijir ya keto?

          Amsa:Azuminsa na ranar ya lalace wato bai inganta ba.

          Tambaya:Minene hukuncin wanda yayi mafarki da rana a watan Ramadan-wato mafarkin da zai wajabta ma mutum wankan janaba-?

          Amsa:Azuminsa bai lalace ba abinda ya hau kansa shine yin wankan janaba.

          Tambaya:Minene hukuncin wanda janaba ta kama shi a watan Ramadan sai ya kasance bai da ruwan da zai yi wanka ko kuma yana dashi amma in yayi wankan ruwan zai cutar dashi?

          Amsa:Anan Taimama ne ta wajaba akansa wato maimakon wankan.

                   Tambaya:Minene hukuncin wanda ya ci abinci a lokacin sahur amma ba tare da ya duba lokaci ba ko fitowar alfijir?

          Amsa:Duk wanda ya ci abinci a lokacin sahur a watan Ramadan ba tare da ya duba lokaci ba ko fitowar alfijir sai daga baya ta bayyana masa ai alfijir ya fito ko lokaci ya wuce to Azuminsa ya lalace saboda haka wajibi ne ya rama Azumin wato bayan sallah,amma da ace ya duba lokaci ko kuma yana da ya}ini cewa alfijir bai keto ba sai ta bayyana masa daga baya ashe ya keto to anan Azuminsa bai lalace saboda haka babu wani ramuwa akansa.

          Tambaya:Minene hukuncin wanda yayi bu]e baki da tsammanin cewa lokaci yayi sai daga baya ta bayyana masa cewa ashe lokacin bai yi ba?

          Amsa:Azuminsa na ranar ya ~aci saboda haka wajibi ne ya rama shi wato bayan sallah-Tambihi anan yana da gayar muhimmanci lura da kuma kiyaye lokaci na sahur da kuma bu]e baki saboda gudun ~acin Azumi.

          Tambaya:Minene hukuncin mai Azumi da yayi bu]e baki a }asar da yake sai ya tashi ya tafi wata }asa wadda su rana bata fa]i ba wato lokacin bu]e baki bai yi ba?

          Amsa:To a wannan mas’ala Azuminsa ya inganta kuma ya halatta masa ya cigaba da cin abinci a }asar duk da cewa su lokaci bai yi ba,sai dai bai halatta gareshi ba ya ci abinci gaban mutane ba wato gabanin fa]uwar rana.

          Daga }arshe yana da gayar muhimmanci ga kowannenmu mu yi amfani da wannan dama da kuma fursa da Allah Ta’ala ya ni’imta mu da ita wato na raya mu da yayi ya kawo mu wannan wata mai albarka,mutum yayi tunani ga wasu wa]anda ya sani wa]anda suka rasu a cikin shekarar wato su wannan damar ta ku~uce masu,saboda haka mutum ya yi tunani shima bai sani ba ko wannan shine watan Ramadan na }arshe a rayuwarsa,akan asasin haka ya yi mujahada wajen ganin cewa ya tsayu da dukkan ibadodi na watan Ramadan misali Salloli,karatun Al-}ur’ani,Azkar,Addu’oi,ciyarwa da kuma infa}i ta fuskoki dabam dabam wato ga ‘yan uwa na jini da na addini da kuma ma}wabtan da dai sauran ayyuka na ]a’a,bayan haka kuma yana da gaya-gayar muhimmanci kowannenmu yaga cewa ya nisanci aikata duk wani zunubi wato dai ya tsare dukkan ga~o~insa misali ya tsare harshensa daga giba ko }arya,idanuwansa daga kallon abinda ya haramta ya kalla,haka nan jinsa shima daga jin abubuwa na haram ko makruhi,haka nan }afafauwansa daga zuwa wajaje da basu dace ba,haka nan hannuwasa daga ta~a abinda bai dace ba,haka nan cikinsa lokacin bu]e baki ko sahur ya kasance abinda zai ci ya same shine ta hanyar halal ba ta hanyar haram ba ko shubuha,haka nan kuma lokacin bu]e baki mutum ya guji take ciki da abinci,domin yin haka zai kasalantar mai da jiki wanda haka zai hana shi tsayuwa da ibadodi da daddare,in kuma har ya iya yin ibadodin to zai kasance babu kushu’i a ciki,a ta}aice dai kamar yadda Allah Ta’ala ya wajabta mana wannan Azumi a cikin wannan watan domin mu samu Ta}awa to kowannenmu yayi mujahada da taimakon Allah Ta’ala ya ga cewa ya fita wannan wata na Ramadan da satifiket na Ta}awa.Allah Ta’ala ya kar~a mana ibadodi da kuma Addu’oi da muka yi a wannan wata mai albarka ya kuma bamu fiye da abunda muka ro}a ya kuma tsare mu da fiye da abunda muka nemi ya tsare mu,ya kuma gaggauta bamu faraj na wannan wa}i’a da muke a ciki.

                            

 
Home Darusan Fiqh Tambayoyi da Amsoshi kan Azumi.
Copyright © 2024. www.tambihin.net. Designed by KH