Bayani kan ayyuka na Sallah (1) |
Written by administrator | |||
Sunday, 19 February 2017 21:20 | |||
A darasin da ya gabata an yi bayani cewa za a shiga sashen mu’amaloli to kasantuwar yadda ‘yan uwa da yawa suka bu}ata na a maida wa]annan darussa da suka gabata zuwa ga littafi, na ga zai yi kyau wasu Babobi da suka gabata a da]a bayanin su a warware ta yadda in an maida su littafin zai ba da fa’idodi masu yawa.Saboda haka yanzu insha Allah zamu ]an koma baya mu ]auko wasu babobi a da]a bayanin su filla-filla da kuma kawo wasu babobi wa]anda da ba a yi bayani a kai ba misali jinin Haila,Nifasi,wankan janaba da dai sauransu.A wannan darasi bayani zai gudana ne a kan ayyukan Sallah. Ayyukan Sallah sun kasu kashi biyu:Akwai wa]anda suke wajibi akwai kuma wa]anda suke mustahabbi.Wajibobin Sallah guda goma sha-]aya ne sune: 1-Niyya. 2-Kabbarar Harama. 3-Tsayuwa. 4-Karatun Fatiha da sura. 5-Ruku’u. 6-Sujuda. 7-Tasbihi a ruku’u da sujuda. 8-Tasshahud-Tahiya- 9-Sallama. 10-Jerantawa. 11-Rashin ba da tazara a ayyukan Sallah. Bayan haka kuma akwai ababen da ake ce masu rukunan Sallah,su kuma guda biyar ne sune: 1-Niyya. 2-Kabbarar Harama. 3-Tsayuwa domin kabbarar Harama da kuma lokacin zuwa Ruku’u. 4-Ruku’u. 5-Sujuda guda biyu. Wani zai iya tambaya to minene banbanci tsakanin wajibin Sallah da kuma rukunin Sallah? Banbancin shine idan mutum ya }ara ko ya rage wani daga cikin rukunin Sallah ko da mantuwa ko da gangan to sallah ta ~aci wato sai dai mutum ya sake ta,amma da mutum zai }ara ko ya rage wani daga cikin wajibin sallah da mantuwa to sallah ba ta ~aci ba,in da kawai take ~aci sai in da gangan ya yi.A yanzu za a ]auki wa]annan wajibobi na sallah ]aya bayan ]aya a yi bayani a kai dai dai gwargwadon iko. 1-Niyya:Wato mutum ya yi nufin yin Sallah ayyananna misali Sallar Zuhur domin misaltuwa da umarnin Allah da kuma kusanci zuwa gareshi.Ba wajibi bane lokacin Niyya mutum ya yi lafazin ta da harshe misali ya ce- Nawaitu Salatu Zuhuri-ita Niyya al’amari ne na Zuciya ba harshe ba,amma da a ce zai yi lafazin Niyya da harshensa kamar yadda aka ba da misali to sallarsa ba ta ~aci ba.Haka nan shara]i ne mutum ya assasa niyyarsa akan asasin ikilasi ba akan asasin Riya ba.Saboda haka da mutum zai gina farkon Sallarsa ko tsakiyarta akan asasin Riya to sallarsa ta ~aci,wato saboda ganin mutane ba saboda Allah ba.Mas’ala:Idan mutum yana Sallah misali Sallar Asar sai Shakka ta bijiro masa kan Niyya cewa Niyar da ya yi ta Sallar Zuhur ya yi ko ta Asar ne to a nan sai ya tafi akan cewa Niyyar Asar ya yi.Haka nan idan mutum yana Sallah to akwai wani yanayi da wajibi ne ya canza Niyya akwai yanayin da Mustahabbi ne ya canza Niyya.Yanayin da wajibi ya canza Niyya misali yana Sallar Asar sai ya tuna ai bai yi sallar Azahar ba to anan sai ya canza Niyya daga Asar zuwa Zuhur,to amma da a ce sai bayan da ya gama sallar ya tuna to a nan sallar Asar ]in ta yi sai ya tashi ya kawo Sallar Zuhur.Wajajen da kuma yake mustahabbi ne mutum ya canza Niyya misalinsa shine mutum yana Sallah Azahar sai ya ga wasu za su yi Sallar Jama’a to a nan mustahabbi ne ya canza niyyar sallarsa zuwa ga niyyar sallar nafila saboda ya sallame ya shiga jam’i ]in domin samun ladar sallar jam’i. 2-Kabbarar Harama:Shine fa]in “Allahu Akbar” wato lokacin da mutum zai fara Sallah.Da mutum zai manta bai yi wannan kabbarar Harama ba a farkon sallarsa to sallar shi ta ~aci.Amma da a ce shakka yake yi a kan ya yi kabbarar Harama ko bai yi ba to a nan idan shakkar ta bijiro masa ne gabanin ya soma karatun Fatiha to wajibi ne gareshi ya yi kabbarar Haramar.To amma da a ce shakkar ta bijiro masa ne bayan ya soma karatun Fatiha ko ya gama Fatihar ya ma shiga karanta Sura to a nan hukunci shine ya yi watsi da shakkar tasa ya kammala sallar sa kuma Sallar ta inganta.Wata mas’ala kuma ita ce ya yi kabbarar Harama amma daga baya sai shakka ta bijiro masa na tunanin shin kabbarar Harama da ya yi dai dai ya yi ta ko ba dai dai ba to a nan hukunci shine zai yi watsi da shakkar ya gina akan dai dai ya yi.Haka nan kuma wajibi ne lokacin da mutum yake kabbarar Harama ya kasance jikinsa a natse wato cikin natsuwa.[aukaka hannuwa zuwa kunnuwa ko fuska lokacin kabbarar Harama shi mustahabbi ne. 3-Tsayuwa:Akwai wajen da yake rukuni ne tsayuwar akwai kuma in da yake wajibi,in da yake rukuni shine tsayuwa lokacin kabbarar Harama da kuma tsayuwa lokacin tafiya zuwa ga ruku’u,in da kuma yake wajibi shine tsayuwa lokacin karatun fatiha da sura da kuma tsayuwa bayan Ruku’u.Mas’ala:Idan mutum ba zai iya yin Sallah a tsaye ba ko da ko ta hanyar jingina da bango ne ko kuma dogaro da sanda to abunda ya hau kansa shine yin sallah daga zaune yana mai fuskantar Al}ibla,idan kuma a zaunen ma ba zai iya yi ba to sai ya yi sallar a kwance amma a ta gefen jinsa na dama,in bai zai iya a haka ba to sai ya yi a gefen jikinsa na hagu,in shima ba zai iya ba to sai ya yi sallar a rigin-gine.Wata mas’ala kuma itace da zai iya yin sallah a tsaye amma kuma saboda wata lalura da yake fama da ita ba zai iya yin ruku’u ba,to a nan zai yi sallar a tsaye idan yazo yin ruku’u sai ya zauna ya yi shi a zaune,in kuma a zaunan ma ba zai iya ba to sai ya yi ima’i da rukun yana tsaye.Haka nan idan zai iya tsayuwa a wasu raka’oi a sallar tasa to wajibi ne ya yi sallar tsaye har ya zuwa lokacin da ya gajiya sai ya zauna,in kuma ya sake samun ikon tsayuwa sai ya tsaya haka-haka dai har ya kammala sallar. 4-Karatun Fatiha da Sura:Shima wajibi ne a salloli na wajibi amma a nafila mutum na iya ta}aitawa ga fatiha ba matsala.Haka nan a karatun sura na salloli wajibai to dole ne mutum ya karanta sura kamila wato cikakkiya ba wasu ayoyi daga cikinsu ba,a raka’oi biyu na }arshen sallar Zuhur, Asar,Isha’i da kuma raka’ar }arshe ta sallar Magariba mutum ya na da za~i ko ya karanta Fatiha ko kuma ya yi wannan tasbihi sau ]aya ko sau ukku (Subhanallah-walhamdu lillah-wala’ilaha illallah-wallahu Akbar) Mas’ala:Idan mutum ya rafkana sai ya fara karanta sura gabanin Fatiha to a nan idan har bai kai ga yin ruku’u ba ya farga misali yana cikin karatun surar to sai ya bar surar ya karanta Fatihar sai kuma ya sake karatun Sura.Wata mas’ala kuma ita ce da zai manta karatun sura ko fatiha har sai da ya je ruku’u ya farga to a nan ba zai ce ya dawo ba domin ya karanta surar ko fatihar a’a zai cigaba da sallarsa kuma ta inganta.Wata mas’ala kuma itace mutum yana karatun wata Sura a sallah sai ya kakare a karatun ta yadda ba zai iya kammala surar ba to a nan sai ya bar ita surar ya koma zuwa ga wata wadda ya san ya haddace da kyau.Wata mas’ala kuma itace a sallolin da ake bayyanar da karatu misali sallar Asuba,Magarib da kuma Isha’i ga mataye suna da za~i nasu bayyanar da karatu ko su ~oye,sai dai idan akwai aj-nabi kusa dasu to su ~oye karatu shi ya fi.Bayan haka akwai wasu ababe wa]anda suke mustahabbi ne yin su a cikin karatun Sallah ga wasu daga ciki:Mustahabbine a raka’a ta farko gabanin mutum ya soma karatun Fatiha a cikin Sallah ya fara da Ta’awwuz wato-Auzu billahi-minashai]anir-rajim-Haka nan kuma mustahabbi ne a Sallar Zuhur da Asar a raka’oi biyu na farko mutum ya bayanar da karatun Bisimillahir-Rahmanir-Rahim.Haka nan kuma mustahabbi ne a cikin sallah bayan mutum ya karanta Fatiha idan ya kammalata ya ce-Alhamdu-lillahi-Rabbil-Alamin.wato maimakon fa]in-Amin-A fi}hun Ja’afariyya in mutum ya fa]e ta da gangan a cikin sallah bayan Fatiha to sallar sa ta ~aci sai dai idan ya fa]e ne akan asasin Ta}iyya ko mantuwa wannan ba komai.Haka nan mustahabbine bayan mutum ya kammala karatun {ulhuwallahu Ahad..... a sallah ya ce-Kazalikallahu-Rabbiy sau ]aya ko biyu ko ukku.Haka nan kuma mustahabbine a raka’oi biyu na }arshe in mutum ya za~i ya yi Tasbihi maimakon Fatiha to idan ya kammala tasbihohin ya ce-Astagfirullah-Rabbiy-wa’atubu-ilaihi- ko kuma ya ce-Allahumma-igfirliy-Akwai kuma wasu ababe da suke makruhi ne a cikin karatun Sallah daga ciki akwai:Makruhi ne maimaita karatun Sura a sallah guda misali mutum ya karanta Inna-Anzalnahu----a raka’a ta farko ya kuma maimaita a raka’a ta biyu wato ana so ya samu wata sura ya karanta,amma ya zo a kan cewa idan {ulhuwallahu ne ba matsala idan ya karantata a raka’a ta farko da ta biyu.Ya ma zo a kan cewa Makruhi ne a salloli na wajibai guda biyar na kowace rana mutum ya zamanto bai karanta {ulhullahu ba a cikin su. 5-Ruku’u:Wanda ba zai iya yin ruku’i ba kamar yadda ya kamata a yi shi,sai ya yi ruku’in yadda ya sau}a}a masa misali ta hanyar dogara da wani abu,in kuma kwatata ba zai iya du}awa ba ne to sai ya yi ruku’in a zaune,in kuma a zaunen ba zai iya ba to sai ya yi ima’i da kansa yana tsaye wato ya ]an sunkuyar da kansa a matsayin ruku’u bayan haka kuma ya ]ago kansa matsayin kamar ya ]ago daga ruku’in kenan,in kuma ma haka ba zai yi yu masa ba to sai ya yi ruku’in da idanuwansa,yadda zai yi shine ya kulle idonsa bayan haka kuma sai ya bu]e idanuwansa,kullewar tana matsayin ya du}a zuwa ruku’u bu]ewar kuma yana matsayin ]aukakowa daga ruku’u.Mu duba mu gani yadda muhimmancin Sallah yake a ce duk halin da mutum yake ciki matu}ar dai yana cikin hankalinsa to shari’a ta koyar da yadda zai sallar.Mas’ala:Idan mutum ya manta bai yi Ruku’u ba sai ya zarce zuwa sujuda bai tuna ba sai gab da zai sa goshinsa a kan }asa to a nan abun da zai shine zai mi}e tsaye }yam sai ya yi ruku’un,haka nan zai yi ko da a ce sai da ya yi sujuda guda ]aya ne ko kuma ya ]ago daga gareta sai ya tuna,to amma da a ce sai bayan da ya kai ga yin sujuda ta biyu sai ya tuna to a nan sallah ta ~aci saboda sujuda guda biyu suna matsayin rukuni ne,shi kuma rukuni idan mutum ya }ara shi ko da mantuwa ko da gangan to sallah ta ~aci, sa~anin wajibi in mutum ya }ara da mantuwa sallah bata ~aci ba,shi yasa in muka duba a sujuda ta farko da ya yi in ya tuna a lokacin ga abunda zai yi wato sallar bata ~aci ba,amma bayyan sallama zai yi sujudar Ba’adiyya ne wato saboda }arin sujuda da ya yi.Wata mas’ala kuma itace wajibi ne bayan mutum ya gama tasbihin Ruku’u ya mi}e tsaye }yam jikinsa ya kuma natsu kafin ya du}a zuwa ga sujuda saboda da a ce zai tafi zuwa ga sujuda gabanin mi}ewar sa tsaye sosai ko gabanin natsuwar jikinsa da gangan to sallar sa ta ~aci.Insha Allah a darasi na gaba zamu kammala bayani kan wa]annan wajibobi na Sallah.
|