Friday, 04 October 2024
Email
Make My Homepage
RSS
Register
Bayani kan ayyukan Sallah (2) Print E-mail
Written by administrator   
Sunday, 19 February 2017 21:09

A darasin da ya gabata mun tsaya ne a bayani kan Ruku’u, yanzu insha Allah zamu tashi ne kan Sujuda.

          6-Sujuda:Sujudai guda biyu na kowace raka’a suna matsayin rukuni ne,saboda haka duk wanda ya barsu da gangan ko da mantuwa ko kuma ya }ara su to duka sallar shi ta ~aci.To amma da a ce sujuda guda ]aya ce ya manta bai yi ba,ko kuma ya }ara sujuda guda ]aya da mantuwa to anan sallar shi ba ta ~aci ba,akwai hanyar da zai bi ya gyara sallarsa misali idan ya manta sujuda guda ]aya a cikin Sallah to idan ya sallame Sallar zai rama sujuda da ya manta wato zai yi niyyar ramuwar sujudar sai ya yi sujudar tare da yin tasbihin da ake yi cikinta amma ba wajibi ba ne bayan sujudar ya yi tahiya ko Sallama,bayan haka sai ya yi sujudar Rafkannuwa.Wata mas’ala kuma itace dangane da abubuwan da suke wajibi ne a sujuda yinsu wa]annan ababe ko sune: 

1-Wajibine ya zamanto in da mutum zai a za goshi a sallarsa ya kasance abinda ya inganta a yi sujuda akansa ne sai idan akwai lalura ta ta}iyya to anan mutum zai iya sujuda akan abinda bai inganta a yi sujudar a kai ba kuma sallarsa ta yi.Abubuwan da suka inganta a yi sujuda a kan su suna da yawa ga wasu daga ciki:{asa,Dutse,ganye na itatuwan da ba a ci,Takarda,Marmara,Gawayi,~awon }wallon itatuwan da ake ci misali }wallon Mangwaro wato idan an cinye jikin na sa to }wallonsa za a iya sujuda a kai,Katako,Ciyawa,Siminti,Tabarma ta ganyen itace,Turba Husainiyya da dai sauransu,wanda ya fi falala daga cikinsu baki ]aya shine Turba Husainiyya.Idan mutum bai samu abun da ya inganta ya yi sujuda a kai ba,ko kuma akwai amma saboda wani uzuri misali Ta}iyya ba zai iya yi ba,to sai ya yi sujuda akan tufafin Auduga ko kittani,idan kuma ya rasa wannan ]in ma,sai ya yi sujuda kan tufafinsa,wanda ba na Audugar ba ko kittani,idan ba wannan to sai ya yi sujudar a kan bayan hannunsa,idan hakan ma ba zai yi yu ba to ya yi akan wani Ma’adini-abin da aka tono daga }asa-Wata mas’ala kuma itace mutum ne yana sallah }ila ma ya kai tsakiyar Sallar sai ya rasa abun da ya inganta ya yi sujuda akai-misali yana cikin Sallah da Turba sai yaro ko yarinsa suka ]auki Turbar suka tafi to ya zai yi-To a nan abun da zai yi shine idan akwai yelwar lokaci zai yenke Sallarsa,in kuma lokacin Sallar ya }ure to sai ya yi Sujuda akan tufafinsa,idan ba zai yi yu ba to sai ya yi sujada akan bayan hannunsa..2-Wajibine ya kasance abin da mutum zai yi sujuda akai wato wanda ya iganta a yi sujudar to ya kasance yana da tsarki.3-Haka nan daga cikin wajibobin Sujuda wajibi ne ya kasance babu wani shamaki tsakanin fatar goshi da abun da za a yi sujuda a kai,misali ga namiji kamar hula a ce ta ]an gangaro gaban goshi ta yadda in ya yi sujuda to jikin hular ne ke kan Turbar ba goshin ba,haka nan ~angaren mata yana da muhimmanci suma su lura ka da ya kasance akwai shamaki tsakanin goshinsu da kuma abin da suke sujuda a kai saboda rashin kiyayewar na iya ~ata ma mutum Sallah,wata mas’ala da take da ala}a da wannan itace mutum yana sallah sai ya kasance da yayi sujuda misali a kan yashi ko tur~aya sai goshinsa ya kwaso yashin to a nan in zai koma sujuda ta biyu to sai ya gusar da yashin daga goshin nasa saboda ka da ya zama masa shamaki tsakanin goshin sa da kuma abun da zai yi sujuda a kai.3-Haka nan wajibi ne lokacin da mutum ya yi sujuda ya kasance ga~o~i guda bakwai suna kan }asa,wa]annan ga~o~i sune:Goshi.Tafin hannun dama dana hagu.Guywar }afar dama da hagu.Kan babban yatsa na }afar dama da hagu.Wanda ba zai iya sa goshinsa ba a }asa saboda rashin lafiya to abin da ya wajaba a kansa shine ya sunkuyar da kansa gwargwadon iko saannan ya aza turbarsa ko abin sujadarsa kan wani abu mai tudu sai ya yi sujudar a kai.

          7-Tasbihin Ruku’u da Sujuda:Tasbihi ko zikiri na cikin Ruku’u da Sujuda akwai wanda yake matsayin wajibi akwai kuma wanda yake matsayin mustahabbi,Wanda yake matsayin wajibi a cikin Ruku’u shine(Subhana-Rabbiyal-Azim-wa-bi-hamdihi)Sau ]aya.Ko kuma fa]in(Sub-hana-llah)sau ukku,wato duk wanda mutum ya yi cikin wa]annan guda biyu ya yi,to }ari akan wancan adadi da aka ambata mustahabbi ne,wato yin wancan mai guda ]aya da yake matsayin wajibi mutum ya yi sau 3,5 ko 7 ko kuma in subhanallah ya ]auka bayan yayi ukku na wajibi sai ya }ara akan haka misali ya yi 5,7,ko 9 to duk yin haka yana matsayin mustahabbi.Shi kuma Tasbihi ko zikiri na Sujuda shine(Subhana-Rabbiyal-A’ala-wa-bi-hamdihi) shima fa]in haka sau ]aya yake matsayin wajibi }ari akan haka mustahabbi ne,in kuma ya za~i fa]in(Sub-hana-llah) shi kuma fa]in haka sau ukku a sujuda yake matsayin wajibi }ari akan haka mustahabbi ne.Wata mas’ala muhimmiya itace wajibi ne lokacin da mutum yake tasbihi na wajibi a cikin Ruku’u da Sujuda ya zamanto jikinsa na a natse,domin rashin yin haka da gangan yana iya ~ata ma mutum sallah.Haka nan kuma lokacin da mutum ya yi sujuda to wajibi ne ga mutum a yayin da yake Tasbihi na wajibi ya kasance wa]ancan ga~o~i guda bakwai da aka ambata duka suna }asa ne,saboda idan mutum ya ]aga wani daga cikin wa]annan ga~o~i misali tafin hannunsa ko kan ]an yatsansa na }afafuwa da gangan to sallar shi ta ~aci,shi yasa ko da mutum zai sosa jikinsa ko kuma sauro ya cije shi lokacin da yake wannan tasbihi na wajibi to ka da ya ]aga tafin hannunsa domin susar jikin sa ko kuma misali ya ]aga ]an yatsan }afarsa domin cizon sauro,mafita guda ]aya da in ta kama dole sai mutum ya sosa jikin nasa ko ya ]aga yatsan }afarsa lokacin da yake wannan tasbihi na wajibi shine ya yi shiru da yin tasbihin sai in mutum ya sosa jikin nasa ko ya ]aga }afar tasa ya dawo da ita }asa saannan ya yi tasbihi,to da a ce mutum zai yi wannan tasbihi na wajibi amma jikinsa ba a natse yake ba akan mantuwa wato ba da gangan ba,to anan zai sake tasbihin ne bayan ya natsar da jikinsa,in ko bayan ya wuce muhallin ne ya tuna ya yi haka misali bayan ya ]ago daga sujuda to a nan ba komi kansa kuma sallarsa ta inganta.Wata mas’ala kuma itace da mutum zai manta sai yazo da Tasbihin da ake yi cikin ruku’u a Sujuda ko kuma na Sujuda ya zo dashi cikin Ruku’u to wannan babu matsala a Sallarsa,amma da a ce da gangan ya yi haka to bai inganta ba.Haka nan kuma baya ga wannan tasbihi mustahabbi ne mutum ya yi ma Manzon Allah da Alayensa Salati a cikin Sujuda da kuma Ruku’u.Haka nan kuma mustahabbi ne lokacin da mutum ya ]ago daga Sujuda zai mi}e zuwa ga wata Raka’a ya ce, “Bi-hau-lillahi—wa-}uwwatihi-a-}umu-wa-a}-udu.Haka nan kuma mustahabbi ne tsakanin kowace sujuda ta ]aya da ta biyu mutum ya ce-Astagfurullah-wa-a tubu-ilaihi-Wa]annan tasbihohi da kuma Azkar mutum na da za~i ko ya yi a bayyane ko a ~oye a cikin dukkan sallolinsa wa]anda ake ~oye karatu da kuma wa]anda ake bayyanawa.

          8-Tashahhud-tahiya-:Yin tahiya a cikin Sallah matsayin sa wajibi ne saboda haka da mutum zai bar ta da gangan bai yi ba to sallar sa ta ~aci,amma idan bai yi bane akan asasin mantuwa to zai rama ta bayan Sallah.Akwai abubuwa guda biyu da idan mutum ya manta su a cikin sallah to zai rama su bayan sallar sune:Sujuda guda ]aya da kuma tahiya.Wata mas’ala kuma itace mutum ne yana Sallah sai ya manta bai yi tahiya ba ya mi}e zuwa ga raka’a ta ukku,sai bayan ya mi}e ya tuna amma bai kai ga yin ruku’u ba to a nan wajibi ne ya dawo ya zauna ya yi tahiyar saannan ya mi}e ya zo da raka’a ta ukkun,bayan ya sallame sallah sai ya yi sujudar rafkannuwa saboda mi}ewa da ya yi ba a muhallinsa ba.To amma da a ce da ya mi}e bai tuna ba sai da ya yi ruku’u to a nan zai cigaba da sallarsa a haka bayan ya sallame sai ya ramka tahiyar, bayan haka kuma ya yi sujudar rafkannuwa,wato yana sallame sallah sai yayi niyyar ramka tahiyar in ya kammala ba zai yi sallama ba bayan haka sai ya yi sujudar rafkannuwa.Sigar yin tahiya da take matsayin wajibi itace, “Ash’hadu-anla-ilaha-illah-wahdahu-la-sharika-lah-wa-ash-hadu-anna-Muhammadan-Abduhu-wara-suluh-Allahumma-salli-ala-Muhammada-wa-ali-Muhammad.” Amma mustahabbi ne gabanin mutum ya fara tahiyar ya ce, “Al-hamdu-lillah” ko kuma ya ce, “Bismillahi-wa-billahi.” Haka nan kuma mustahabbi ne bayan mutum ya gama tahiyar ya ce, “Wata-}abbal-shafa’atuh-war-fa’a-darajatuh.”

          9-Sallama:Yin sallama bayan gama sallah matsayin sa wajibi ne,Sigar sallama ta wajibi shine(Assalamu-Alaikum) amma ana son }arawa da(Warah-matullah-wabara-katuh) Idan mutum ya manta bai yi sallama ba bayan sallarsa sai ya tuna to idan bai yi wani abu da yake ~ata sallah ba misali bai ba Al}ibla baya ba to sai nan take ya yi sallamar,to amma idan har ya yi wani abu da ke ~ata Sallar misali sai da ya bar wajen ya tuna aiko bai yi sallama cikin sallar nan tashi ba to a nan sai dai ya sake Sallah.

          10-{unuti:Shi yin }inuti a cikin Sallah matsayinsa mustahabbi ne ba wajibi ba saboda haka da mutum zai sallah sai bai yi }unutin ba sallarsa ta yi wato babu wani matsala a kan sa,kuma shi }unuti a kan yi shine a dukkan salloli na wajibi da kuma salloli na nafiloli,kuma shi }unuti bai da wata siga ayyanan na wato wadda dole ita mutum zai karanta,A’a mutum zai iya biya kowace addu’a ko kowane irin zikiri ko ya biya wata aya ta Al}ur’ani mai girma wadda take da ala}a da addu’a kamar Rabbana-Atina-fidduniya-hasana.........amma addu’oin da aka fiso a }unuti sune wa]anda aka ruwaito daga Manzon Allah[S] da kuma Aimma na Ahlul-bayt[AS] musamman ma wannan addu’a ta farj wadda Sayyid Zakzaky[H] ya kan karanta ta ko da wane lokaci cikin }unutin Sallolinsa wato “La’ilaha-illahul-Halimul-karim..............” Insha a darasi na gaba bayani zai gudana kan mas’aloli na bayan kammala Sallah kamar Ta’a}ibat,sujudu-shukur da dai sauransu.

 
Home Darusan Fiqh Bayani kan ayyukan Sallah (2)
Copyright © 2024. www.tambihin.net. Designed by KH