Friday, 04 October 2024
Email
Make My Homepage
RSS
Register
Hadisai 40 na Imam Muhammad Jawad (AS) Print E-mail
Written by administrator   
Sunday, 22 January 2017 20:37

Imam Muhammad Jawad[AS] shine Imami na tara a jerin lissafi na Imamai 12.A cikin Imamai 12 shine mafi karancin shekaru saboda ya rasu yana da shekaru 25 a duniya.Ga wasu sassa na rayuwarsa mai albarka.

1-    Wiladarsa:An haifi Imam Jawad[AS] a madina,ranar 10 ga watanRajab shekara ta 195 bayan hijira.

2-    Nasabarsa:Sunan mahaifiyarsa Sabika.sunan mahaifinsa Imam Ali- Arrida[AS]

3-    Nash’a ]insa:Ya tashi a Madina,ya rayu tare da mahaifinsa shekara 18.Amma }arshen rayuwarsa ta kasancea Ira} ne.

4-    La}ubbansa da kuma kinayarsa:Yana da la}ubba masu yawa,amma wa]anda suka fi fice sune Al-Jawwad da kuma Atta}iy.Kuma anai masa kinaya da Abu Ja’afarus-sani.kuma yazo akan cewa Imam Ridha[AS] saboda Ta’aziminsa bai ambatonsa da sunansa sai dai da wannan kinaya ta Abu Ja’afar.

5-    Shekarunsa:Ya rayu a duniya shekaru 25.Wato shine mafi}arancin shekaru idan an kwatanta da Imaman da suka gabace shi da kuma wa]anda suka biyo bayansa.Kamar yadda Imam Sadi}[AS] shine mafi yawan shekaru,a cikin Aimma[AS] domin ya rasu yana da shekaru 65,a wata ruwaya 68.

6-    Muddan Imamancinsa:Shekaru 17 ne.

7-    ‘Ya’yansa:Yana da ‘ya’ya 4.maza biyu,mata biyu.

8-    Wafatinsa:Imam Jawad[AS] ya rasu ranar Asabar }arshen watan Zul-}ida,shekara ta 220 bayan Hijira.kuma ya rasu sakamakon guba da khalifan Abbasawa mai suna Mu’utasim yasa asa masa.wato kamar yadda aka sa guba ga Imaman da suka gabace shi da kuma wa]anda suka biyo bayansa,in ka ]ebe Imam Ali[AS] da kuma Imam Husain[AS] su da takobi ne aka aka kashe su.kamar dai yadda yazo daga Imam Sadik[AS] yace, “Babu wani daga cikinmu face wanda aka kashe da takobi ko aka sa mai guba.”

          9-Kabarinsa:}abarinsa yana a kazimiyyane wato a Ira}, kusa dana kakansa Imam Kazim[AS].

Sai kuma Hadisai 40 wa]anda aka ruwaito daga wajensa.

          1-Imam Jawad[AS] ya ce, “Duk wanda ya dogara ga Allah Ta’ala to zai taimake sa ga dukkan al’amuransa,dogara ga Allah kariya ne daga dukkan ma}iya kuma ku~uta ne daga dukkan sharrori.

            2-Imam Jawad[AS] ya ce, “Duk wanda ya kasance yana da si}a da Allah Ta’ala to zai kasance cikin farin ciki da natsuwa,si}}a da Allah Ta’ala wata garkuwa ce wacce ba wanda yake kasancewa a ciki face Mumini.”

            3-Imam Jawad[AS] ya ce, “Duk wanda ya ji tsoron Allah Ta’ala to Mutane za su soshi.”

            4-Imam Jawad[AS] ya ce, “Yana daga cikin kyawawan ]abi’u na mutum kamewa daga cutarwa.” Wato ga Mutane.

            5-Imam Jawad[AS] ya ce, “Yana daga cikin kamalar mutunci ga mutum ya amshi gaskiya idan ta bayyana masa,haka nan kuma kada yayi ma wani mutum abinda shi bai so.” Wato a yi masa.

            6-Imam Jawad[AS] ya ce, “Allah Ta’ala yana da wasu bayi wanda ya kan yi masu ni’ima koda wane lokaci,kuma ni’imar ba zata gushe a cikinsu ba matukar suna ba da ita-wato ga mutane misali ni’ima ta dukiya idan Allah ya ni’imata mutum da ita to matukar yana bayarwa to ko Allah Ta’ala zai cigaba da bashi-Idan kuma basu bada ita ba to sai Allah ya amshe ta ya ba wasu.”

            7-Imam Jawad[AS] ya ce, “Babu wanda ni’imar Allah zata yawaita gareshi-misali ni’imar dukiya ko ta ilimi-fa ce ya samu yawaitar mutane da suke da bukatuwa zuwa gareshi,to duk wanda bai iya jure hidima ga mutane da ni’imar ba to haka yana iya zama sanadiyyar gushewar ni’imar.”

            8-Imam Jawad[AS] ya ce, “Halaye guda ukku suna janyo so da kuma }auna:Kyakkyawan mu’amala,taimako lokacin da wani yake cikin tsanani da kuma tsarkin zuciya-wato ya kasance tsakanin ka da mutane ba hassada ko gaba da dai sauransu.”

            9-Imam Jawad[AS] ya ce, “Abu ukku duk wanda ya kasance yana dasu to ba zai yi nadama ba:Dogara ga Allah ga dukkan al’amuransa da suka taso,yin shawara da kuma rashin yin gaggawa.”

            10-Imam Jawad[AS] ya ce, “Duk wanda yayi ma ]an uwansa nasiha a ke~ance to ha}i}a ya kyauta,wanda kuma yayi masa nasiha a bayyane-wato cikin mutane-to ha}i}a ya munana.”

          11-Imam Jawad[AS] ya ce, “Bayyanar da matsayi a cikin al’amari gabanin ya bayyana to ~arna ce gareshi.”

            12-Imam Jawad[AS] ya ce, “Duk wanda aka yi wani mummunan abu a gabansa sai bai so abun ba-misali aka zalunci wani a gabansa-to kamar wanda bai wajen ne.Duk wanda bai nan aka aikata wani mummunan abu sai yaji ya kuma yarda ko yaso abunda aka yi to kamar yana nan aka yi-wato sun yi musharaka wajen laifi da wadanda suka aikata misali kamar masu murna da jin da]i na zaluncin da aka yi ma yan uwa.”

          13-Imam Jawad ya ce, Mumini yana bu}atuwa ga muwafa}a daga wajen Allah Ta’ala ga dukkan al’amuransa.”

          14-Imam Jawad ya ce, “Izzar Muumini itace wadatuwarsa daga Mutane da kuma kar~ar nasiha ga wanda yayi masa.”

          15-Imam Jawad ya ce, “Abubuwa ukku suna kai mutum ga samun yardar Allah Ta’ala sune:Yawan Istigfari,yawan sadaka da kuma Tawali’u.”

          16-Imam Jawad ya ce, “Ta yaya wanda Allah Ta’ala shine maji~incinsa zai tozarta.Haka nan kuma ta yaya wanda Allah Ta’ala yake nemansa zai ku~uta.”

          17-Imam Jawad ya ce, “Babu abinda yake rusa addini kamar bidi’a.”

          18-Imam Jawad ya ce, “Da addu’oi ne ake gusar da bala’oi.”

          19-Imam Jawad ya ce, “Kusani Ta}awa tana janyo ma mutum izza.”

          20-Imam Jawad ya ce, “Ilimi taska ne,shiru kuma haske ne.”

          21-Imam Jawad ya ce, “Mutane biyu ba zasu kasance dai-dai wa dai-da ba a fagen addini da kuma nasaba face wanda ya fisu a wajen Allah shine wanda yafi Ladabi.”

          22-Imam Jawad ya ce, “Malamai Ba}i ne saboda yawan jahilai da ke a tsakaninsu.”

          23-Imam Jawad ya ce, “Duk wanda aka yi abu ba dai-dai ba sai ya yaba ma abun to yayi tarayya cikin zunubin wanda ya aikata abun.”

          24-Imam Jawad ya ce, “Dauriya akan musiba to musiba ne ga ma}iyi-wato bisa ]abi’ar ma}iyi kullum so yake wata musiba ta sami mutum ya ji da]i,misali da musibar zata bijiro sai kuma mutum ya daure to shi ba zai ji da]i ba.”

          25-Imam Jawad ya ce, “Da jahilai zasu yi shiru a fagen Addini to da ba za a dunga samun sa~ani tsakan-kanin mutane ba-wato mafi yawan sa~anin da ake samu a fagen addini dalilinsa shine jahilci misali wasu al’amura tsakanin Sunna da Shi’a,in mutum ya duba zai ga cewa da yawa Malaman Sunna sun jahilci al’amura da dama na Shi’a akan haka suke munanan maganganu wa]anda suke haifar da sa~ani tsakan-kanin mutane.”

          26-Imam Jawad ya ce, “Duk wanda ya sakan-kamaka da yi maka godiya to ha}i}a ya baka fiye da abun da ya amsa a wajenka.”

          27-Imam Jawad ya ce, “Mafificiyar ibada shine Iklasi-Wato ya kasance duk ayyukan mutum ya gina sune a kan asasi iklasi,in ko ba haka ba zai kasance basu da wani daraja a wajen Allah Ta’ala.”

          28-Imam Jawad ya ce, “Allah Ta’ala bai yi wata ni’ima ga wani bawa ba daga cikin bayinsa,kuma bawan yasan cewa ni’imar daga wajen Allah ne,to face Allah ya rubuta shi mai godiya ga ni’imar tun kafin ma ya gode masa da harshensa-misali ya ce Alhamdu-lilla wato kan ni’imar da ya yi masa.”

          29-Imam Jawad ya ce, “Bawa bai aikata wani laifi na zunubi ba kuma lokacin da yake aikata zunubin ya san cewa Allah Ta’ala fa yana ganinsa in yaso zai azabta shi in kuma yaso ya gafarta masa,to in mutum yayi tunanin haka Allah zai gafarta masa tun kafin ya nemi gafarar zunubin a wajen Allah.”

          30-Imam Jawad ya ce, “Mai bin sha’awoyin ransa to ba zai gushe ko da wane lokaci cikin kurakurai ba.”

          31-Imam Jawad ya ce, “Duk wanda ya bi son ransa to tamkar ya biya ma ma}iyinsa bu}atarsa ne.” Abin nufi anan shine duk lokacin da mutum ya bar abinda yake shine dai-dai ya bi son ransa to yayi abunda Shai]an yake so.

          32-Imam Jawad ya ce, “Wanda ya aikata zalunci,da wanda ya taimaka wajen aikata zaluncin da kuma wanda ya yarda da zaluncin to dukkansu sun yi tarayya cikin zunubi.”

          33-Imam Jawad ya ce, “Ka sani cewa koda wane lokaci ba zaka ~uya ba daga ganin Allah Ta’ala saboda haka kayi tunanin ya zaka kasance.” Wato cikin aikin ]a’a ko zunubi.

          34-Imam Jawad ya ce, “Ku tausaya ma raunana daga cikinku,ku nemi tausayawar Allah Ta’ala ta hanyar tausaya masu.”

          35-Imam Jawad ya ce, “Kada ka kasance masoyin Allah a bayyane amma kuma ma}iyinsa a ~oye.” Wato kada ka kasance a bayyane kana ]a a ga Allah amma kuma a ~oye kana sa~a masa.

          36-Imam Jawad ya ce, “Ka daure a kan abinda ka ke }i matu}ar dai abin gaskiya ne.”

          37-Imam Jawad ya ce, “Ka daure akan barin abinda ka ke so matu}ar dai abin na bin son rai ne.”

          38-Imam Jawad ya ce, “Kashedinka daga yin abota da mutumin banza,kuma ka sa~a ma son ranka.”

          39-Imam Jawad ya ce, “Jinkirta Tuba ru]i ne daga Shai]an.Dogara ga Allah ba tare da yin aiki ba halaka ne.” Misali mutum bai yi aikin shiga Aljanna ba ya ce ya dogara ga Allah.

          40-Imam Jawad[AS] ya ce, “Duk wanda ya aikata wani aiki ba akan asasin ilimi ba to abinda yake ~atawa yafi abinda yake gyarawa.

          Insha Allah a darasi na gaba za a kawo Hadisai 40 da aka ruwaito daga Imam Ali Al-hadi[AS].

 
Home Darusan Hadisai Hadisai 40 na Imam Muhammad Jawad (AS)
Copyright © 2024. www.tambihin.net. Designed by KH