Friday, 04 October 2024
Email
Make My Homepage
RSS
Register
Hadisai 40 na Imam Ali Arrida (AS) Print E-mail
Written by Administrator   
Sunday, 22 January 2017 20:25

Imam Ali Arrida[AS] shine imami na takwas a jerin }idaya na imamai 12.Idan mutum ya bibiyi tarihin Imam Rida zai ga cewa ya fuskanci wata irin jarabawa wanda ta sa~a ma Imaman da suka gabace shi da kuma wa]anda suka biyo bayansa,

            Wannan jarabawa itace ta “ Waliyyul-Ahd” watau na]a shi a matsayin khalifa mai jiran gado wanda khalifan Abbasawa Ma’amun yayi,wanda in mutum ya dubi abin a zahiran ce,zai ]auka ko abu mai kyau Ma’amun yayi,alhali abin ba haka nan yake ba,a ba]ininsa makirci ne da kuma yaudara.Asasin wannan abu ya taso ne daga shi wannan khalifa na Abbasawa Ma’amun,lokacin daya hau khalifanci yaga matsaloli sun yi masa yawa,ga matsalar ]an uwansa mai suna Amin,wanda yana ya}ar sa domin ya tunku]e shi shi ya hau.Ga kuma ta wa]anda suka yi masa tawaye daga sassa daban daban a lokacin,musamman ma daga ~angaren mabiya Ahlulbait [AS],Saboda abin da baban shi Ma’amun watau Harunar-Rashid, yayi na kashe Imam Kazim [AS] a kurkuku,ta hanyar sa masa guba.To,wa]annan matsaloli daya ga sun yi masa yawa,kuma matsalar da yafi jin tsoro daga cikin wa]annan matsaloli,ita ce ta ~angaren mabiya Ahlulbait [AS],sai yayi tunani shi a }ashin kansa ba tare da yayi shawara da kowa ba,na bari ya ]auko Imam Ridah [AS] daga madina ya kawo shi khurasan,lokacin itace cibiyar tafi da ikonsa.Domin ya bashi mu}ami na khalifa mai jiran gado. Manufarsa ~oyayya itace domin ya kwantar da wancan tawaye da mabiya Ahlulbait [AS] suke yi a sassa daban daban, wanda daga }arshe idan abubuwa suka lafa,komai ya koma dai dai na ikonsa sai ya kashe Imam Ridah [AS] ta hanyar sa masa guba.Wannan ‘plan’ ]in shi a }ashin kansa ya kitsa.Imam Ridah [AS] ne ya tona asirin haka.lokacin daya ha]u dashi yace masa,nasan manufarka.Sai Ma’amun yace masa mece ce manufata? Imam Ridah [AS] ya fa]a masa,nan take ya daburce ya fusata,saboda ya san wannan abin bai fa]a wa kowa ba,amma gashi Imam Ridah [AS] ya fa]i,don hatta ‘yan uwansa na jini,lokacin da ya ba Imam Ridah [AS] wannan matsayi,sun maganganu me yasa zai yi haka? Don bai bayyana wa kowa manufarsa ba.

            A ta}aice dai Imam Rida bai samu yana yi na tsangwama da kuma gallazawaba daga masu tafi da iko a zamaninsa ba a bayyane sai dai a ~oye,akan asasin haka a lokacinsa ya samu damar ya]a ilimin Ahlul bayt musamman ma abun da ya shafi Hadisai,saboda haka Hadisan da za a kawo wasu ne daga cikin ]inbin Hadisai da aka ruwaito daga wajensa.Amma kafin kawo Hadisan ga wasu sassa na rayuwarsa mai albarka:

          1-Haihuwarsa:An haifi Imam Rida[AS] ranar 23 ga watan Zul-qida shekara ta 148 bayan hijira.

          2-Nasabarsa:Sunan mahaifiyar Imam Rida[AS] [ahira,Sunan Mahaifinsa Imam Musa Alkazim[AS].

            3-Tasowarsa:Imam Rida[AS] an haife shi a Madina ne kuma ya taso a Madina ,ya kasance a Madinar har ya zuwa kusan karshen rayuwarsa da khalifa na Abbasawa a lokacin ya maida shi Khurasan da zama.

            4-Lakubbansa: Imam Rida[AS] yana da lakubba masu yawa amma wanda yafi shahara shine Arrida,an tambayi Imam Jawad[AS] cewa mi yasa ake ce ma mahaifinsa Arrida sai ya ce ana ce masa haka ne saboda makiyansa sun yarda dashi kamar yadda masoyansa suka yarda dashi.

            5-Shekarunsa:Imam Rida[AS] ya rayu a duniya ne shekaru hamsin da biyar.

            6-Tsawon shekarun imamancinsa:Imam Rida[AS] ya yi Imamanci na tsawon shekaru Ashirin.

            7-‘Ya’yansa:Imam Rida[AS] yana da ]a ]aya ne shine Imam Jawad amma akwai wata ruwaya sa~anin haka misali akwai ruwayar da ta zo akan cewa yana da ]iya mai suna Fa]ima har ma ta ruwaito Hadisai daga wajensa.

          8-Rasuwarsa:Imam Rida[AS] ya yi shahada ranar 23 ga watan Zul-qida a wata ruwaya karshen watan Safar shekara ta 203 bayan hijira.

            9-Kabarinsa:Imam Rida[AS] kabarinsa yana a birnin Mash-had ne wato a kasar Iran.Wannan kenan dai a takaice na wasu sassa daga rayuwarsa sai kuma Hadisai guda 40 da aka ruwaito daga wajensa.

          1-Imam Rida[AS] ya ce, “Duk wanda Allah Ta’ala yayi ma ni’ima to wajibine ya yelwata ma iyalinsa.”

          2-Imam Rida[AS] ya ce, “Lokacin da bawa ya fi kusanci ga Allah Ta’ala shine lokacin da yake cikin sujuda.”

            3-Imam Rida[AS] ya ce, “Mai kyauta yana kusa da Allah,yana kusa da Aljanna,yana kusa da mutane,yana kuma nesa daga wuta.”

            4-Imam Rida[AS] ya ce, “Marowaci yana nesa da Aljanna,yana nesa da mutane,yana kuma kusa da Wuta.”

            5-Imam Rida[AS] ya ce, “Kyauta wata itaciya ce cikin Aljanna rassanta na cikin Duniya,to duk wanda yayi riko da wani reshe daga cikin rassanta to zai shiga Aljanna.”

            6-Imam Rida[AS] ya ce, “Duk wanda ya yi ma kansa hisabi to zai rabauta,wanda kuma ya gafala da yi ma kansa hisabi to zai yi hasara.”

            7-Imam Rida[AS] ya ce, “Mafificiyar dukiya itace wadda mutum ya kiyaye mutuncinsa da ita.”

            8-Imam Rida[AS] ya ce, “Mumini ko da ya fusata to fusatarsa ba zata sa ya yi abinda ya sa~a ma shari’a ba.”

          9-Imam Rida ya ce, “Bawa ba zai samu ha}i}anin kamalar imani ba har sai ya siffata da abu ukku:Ilimi a fagen addini.Tsaka-tsaki a fagen rayuwa.Dauriya akan jarabawowi na musibu.”

          10-Imam Rida ya ce, :Imani yana da ginshi}ai guda hu]u sune:Dogara ga Allah,yadda da hukuncin Allah,sallamawa ga al’amarin Allah da kuma fawwala al’amura zuwa ga Allah.”

          11-Imam Rida ya ce, “Duk wanda bai gode ma Mutane kan wani abin alhairi da aka yi masa ba to ko ba zai gode ma Allah ba.”

          12-Imam Rida ya ce, “Musulmi shine wanda sauran Musulmi suka ku~uta daga harshensa da kuma hannunsa.” Wato baya cutar da ‘yan uwansa Musulmi da harshensa misali yi masu giba ko Annamimanci da dai sauransu.”

          13-Imam Rida ya ce, “Ka kyautata zato ga Allah Ta’ala saboda duk wanda ya kyautata zato ga Allah to Allah yana nan a yadda yake zatonsa.”

          14-Imam Rida ya ce, “Taimaka ma raunanna yana daga cikin mafificiyar sadaka.”

          15-Imam Rida ya ce, “Yana daga cikin Sunnar Manzon Allah yin walima lokacin Aure.”

          16-Imam Rida ya ce, “Ibada ba itace yawan sallah da azumi ba,amma ibada itace yawan tafakkuri-tunani- ga al’amarin Allah Ta’ala.”

          17-Imam Rida ya ce, “Marowaci bai da hutu,mai hassada kuma bai da jinda]i,ma}aryaci kuma bai da mutunci.”

          18-Imam Rida ya ce, “Allah Ta’ala yayi umrni da Sallah da kuma ba da Zakka to wanda yayi sallah amma bai ba da zakka ba to ba za a kar~i sallar shi ba.”

        19-Imam Rida ya ce, “Mumini shine wanda idan ya aikata mummuna to ya kan yi istigfari.”

          20-Imam Rida ya ce, “Duk wanda ya kwatanta Allah Ta’ala da halittarsa to yayi shirka,duk kuma wanda ya jingina masa abunda aka hana a jingina masa to ya kafirta.”

        21-Imam Rida ya ce, “Yana daga cikin alamomin Fa}ihi ha}uri,ilimi da kuma yawan shiru.”

          22-Imam Rida ya ce, “Allah Ta’ala baya son yawan ro}o da kuma tozarta dukiya.”

          23-Imam Rida ya ce, “Kowane Mumini Musulmi ne amma ba kowane Musulmi yake Mumini ba.”

          24-Imam Rida ya ce, “Yana daga cikin ]abi’oin Annabawa yin tsafta da kuma sa turare.”

          25-Imam Rida ya ce, “Ka sadar da zumunci ko da ko da kur~in ruwan sha ne,mafificin abinda zaka sadar da zumunci dashi shine kamewa daga cutarwa.”

          26-Imam Rida ya ce, “Duk wanda yayi biyayya ga Allah Ta’ala to za a yi masa biyayya.”                                                                                   

          27-Imam Rida ya ce, “Duk wanda ya ji tsoron Allah Ta’ala to za a ji tsoron sa.

          28-Imam Rida ya ce, “Sallah a farkon lokaci yafi falala,kuma ka da ka yi sallah a bayan fajiri.”

          29-Imam Rida ya ce, “Mai sata ba zai yi sata ba lokacin da yake satar yana da imani.Mai shan giya ba zai sha giya ba lokacin da yake shan giyar yana da imani.Mai kisa ba zai yi kisa ba ba tare da ha}}i ba lokacin da yake kisan yana da imani.”

          30-Imam Rida ya ce, “Imani shine }udurtawa da zuciya,furuci da harshe da kuma aiki da ga~o~i.”

          31-Imam Rida ya ce, “Manzon Allah[S] ya ce, “Duk wanda ya ganni a cikin barcinsa-mafarki-to ha}i}a ya ganni domin Shai]an bai iya siffata cikin siffata.”

          32-Imam Rida ya ce, “Babu wani Mumini da zai ziyarce ni fa ce Allah ma]aukaki ya haramta jikinsa daga wuta.”

          33-Imam Rida ya ce, “Za a kashe ni ta hanyar sa mani guba,kuma kabari na zai kasance wajen kai komo na shi’ata, to duk wanda ya ziyarce ni to zan ziyarce ranar kiyama.”

          34-Imam Rida ya ce, “Duk wanda ya ziyarci kabarina to Allah Ta’ala zai rubuta masa ladar shahidi dubu ]ari kuma za a ta da shi a cikinmu.”

          35-Imam Rida ya ce, “Wallahi babu wani daga cikinmu-Aimma- face an kashe shi domin ya kasance shahidi.”

          36-Imam Rida ya ce, “Duk wanda ya yarda da ka]an na arziki da Allah ya bashi to Allah zai yarda da aikinsa ka]an da ya gabatar.”

          37-Imam Rida ya ce, “Wani zamani zai zo ma mutane zaman lafiya in ka kasa shi kashi goma a lokacin to kashi tara yana ga nisantar mutane,kashi guda kuma ga yin shiru.”

          38-Imam Rida[AS] ya ce,Imam Ali[AS] ya ce, “Bai halatta ga wani Musulmi ba ya tsorata ]an uwansa Musulmi.”

          39-Imam Rida[AS] ya ce Manzon Allah[S] ya ce, “Duk wanda ya kame fushinsa to Allah Ta’ala zai kame daga yi masa azaba.”

          40-Imam Rida[AS] ya ce,Manzon Allah[S] ya ce, “Duk wanda ya kyautata halayensa to Allah Ta’ala zai kai shi ga matsayin mai yawan Sallah da kuma Azumi.”

          Insha Allah a darasi na gaba za a kawo Hadisai 40 da aka ruwaito daga Imam Jawad[AS].

 
Home Darusan Hadisai Hadisai 40 na Imam Ali Arrida (AS)
Copyright © 2024. www.tambihin.net. Designed by KH