Saturday, 02 December 2023
Email
Make My Homepage
RSS
Register
Hadisai 40 na Imam Musa Al-Kazim[AS] Print E-mail
Written by administrator   
Sunday, 06 November 2016 10:56

A darasin da ya gabata an kawo Hadisai 40 da aka ruwaito daga Imam Sadik[AS] a wannan darasi kuma insha Allah za a kawo na Imam Musa Al-kazim[AS] amma kafin kawo Hadisan ga wasu sassa na rayuwarsa.

1-    Wiladarsa:An haifi Imam Kazim[AS] a wani gari da ake ce masa Abwa,yana tsakanin Makka da Madina ne.ranar lahadi 7 ga watan safar,shekara ta 128 bayan Hijira.Kuma shine Imam na bakwai a jerin }idaya na Imamai 12.

2-    Nasabarsa:sunan mahaifiyarsa Hamida,yazo a tarihinta cewa a fagen ilimi ta kai mustawa-aliya,har ta kai Imam Sadi}[AS] yakan umarci mataye dasu koma wajenta dangane da hukunce-hukuncen addini.Akwai ma lokacin da yake cewa Hamida tsarkakkiya ce daga dukkan aibobi.sunan mahaifinsa Imam Sadik[AS].

3-    La}ubbansa da kuma kinayarsa:Ya kasance yana da la}ubba masu yawa,amma wa]anda suka fi fice sune Al-kazim da kuma Babul-Hawa’ij.Ana yi masa kinaya daAbu Ibrahim da kuma Abul-Hassan.

4-    Nash’a ]insa:ya tashi a madina,ya kuma rayu tare da mahaifinsa shekaru 20.}arshen rayuwarsa ya kasance a Ira} ne.

5-    Shekarunsa:Y a rayu shekaru 55 a duniya.

6-    Muddan Imamancinsa:shekaru 35.

7-    ‘Ya’yansa:yana da ‘ya’ya 36,maza 17,mata 19.Imam kazim[AS] shine mafi yawan ‘ya’ya idan an kwatanta da Imaman da suka gabace shi da kuma wanda suka zo bayansa.kamar yadda Imam Ridha[AS] da kuma Imam Askari[AS] sune mafi}arancin ‘ya’ya,domin ko wannensu yana da ]a ]aya ne.wato Imam Jawad[AS] da kuma Imam Mahdi[AF]

8-    Wafatinsa:Imam Kazim[AS]ya yasu ranar Jumma’a 25 ga watan Rajab,shekara ta 183 bayan Hijira,kuma ya rasu a kurkune,sakamakon guba da aka saka masa.

9-    {abarinsa:}abarinsa yana kazimiyya ne a }asar Ira}.

Ga Hadisai 40 da aka ruwaito daga wajensa.

            1-Imam Kazim[AS] ya ce, “Na hore ku da yawaita addu’oi domin addu’a tana tunkude bala’oi.”

            2-Imam Kazim[AS] ya ce, “Kyakkyawan makwabtaka ba ita ce kawai kamewa daga cutar da makwabci ba,a’a ita ce dauriya daga cutarwar makwabci.”

            3-Imam Kazim[AS] ya ce, “Duk wanda jiya da yau ]inshi duk ]aya suke to ha}i}a ya samu na}asu.” Wato idan ya kasance a fagen addini jiya da yau duk ]aya ga mutum ba wani bambamci to wannan na}asu ne,abin da ake so ga mutum kowace rana ya }ara samun kamala a fagen addini misali kamalarsa ta yau tafi ta jiya ta wannan watan tafi ta wancan watan,ta wannan shekarar tafi ta shekarar da ta gabata haka-haka har ya zuwa saukar ajalinsa,amma a ce ada mutum yafi kamala a fagen addini kan yanzu to wannan hasara ce babba,saboda a }arshen Hadisin Imam Kazim yana cewa “Duk wanda ya kasance cibaya yake a fagen addini to wannan mutuwa tafi masa alhairi kan cigaba da rayuwa.”

          4-Imam Kazim ya ce, “Sallar nafiloli kusanci ne zuwa ga Allah Ta’ala ga kowane Mumini.”

          5-Imam Kazim ya ce, “Komi yana da zakka,zakkar jiki itace azumin nafiloli.”

          6-Imam Kazim ya ce, “Mafificiyar ibada bayan sanin Allah Ta’ala shine jiran bayyanar Imam Mahdi[AF].”Jiran bayyanar Imam Mahdi kamar yadda Malamai suka yi bayani shine yin sa’ayi wajen bada gudunmawa a fagen addini ta fuskoki dabam dabam da kuma siffata da shi addini domin haka ya kasance kamar shinfida ga bayyanarsa,wato ba wai mutum ya zauna bai yin komi ba domin cigaban addini.

            7-Imam Kazim ya ce, “Duk wanda ya fara addu’a ba tare da ya soma yabon Allah ba da kuma yima Manzon Allah[S] salati ba to kamar wanda yayi harbi ne da gwafa ba dutse.”

            8-Imam Kazim ya ce, “Duk wanda ya kasance mai tattali to ba zai yi talauci ba.”

            9-Imam Kazim ya ce, “Yawaita damuwa da kuma ba}in-ciki yana haifar da saurin tsufa.”

        10-Imam Kazim ya ce, “Duk wanda yasa mahaifansa suka yi fushi to ha}i}a ya sa~a masu.”

          11-Imam Kazim ya ce, “Mutum bai samun ladar musibar da Allah Ta’ala ya jaraba shi da ita face sai idan ya daure kan musibar.”

          12-Imam Kazim ya ce, “Duk wanda ya kasance mai wadatar zuciya kuma mai tattali to ni’imar da Allah yayi masa zata wanzu.”

          13-Imam Kazim ya ce, “Duk wanda ya kasance bai da tattali kuma mai almubazzaranci to ni’imar da Allah Ta’ala yayi masa zata gushe.”

          14-Imam Kazim ya ce, “Ri}on amana da kuma fa]in gaskiya suna janyo arziki.”

          15-Imam Kazim ya ce, “Yin {arya da kuma Yaudara suna janyo talauci da kuma munafunci.”

          16-Imam Kazim ya ce, “Musiba ga wanda ya Daure guda ]aya ce,ga wanda kuma bai daure ba guda biyu ce.”Wato musibar da kuma ra]a]in rashin dauriyar a cikin zuciyarsa.

          17-Imam Kazim ya ce, “Taimakonka ga rarrauna yana daga cikin mafificiyar sadaka.”

          18-Imam Kazim ya ce, “Idan ka zaga domin yin bawali ko ga’i]i to kada ka fuskanci Al}ibla ko ka bata baya.”

          19-Imam Kazim ya ce, “Kaji tsoron Allah,ka kuma fa]i gaskiya ko da zata janyo maka matsala saboda yin haka shine tsiranka.”

          20-Imam Kazim ya ce, “Kaji tsoron Allah,ka kuma nisanci yin }arya ko da zaka samu wani amfani ga yinta saboda yin haka shine halakarka.”

          21-Imam Kazim ya ce, “Allah Ta’ala yana da hujjoji biyu akan mutane,hujja ta zahiri da kuma hujja ta ba]ini.Hujja ta zahiri sune Manzanni da kuma Aimma.Hujja ta ba]ini shine Hankali.”

          22-Imam Kazim ya ce, “Duk wanda ya kame fushinsa daga mutane to Allah zai kame fushi daga gareshi ranar }iyama.”

          23-Imam Kazim ya ce, “Duk wanda ya kame kansa daga ta~a mutuncin mutane to Allah zai yafe masa laifuffukansa ranar }iyama.”

          24-Imam Kazim ya ce, “Mafificin abinda Bawa zai kusanci Allah dashi baya ga sanin Allah shine Sallah,biyayya ga iyaye da kuma barin Hassada,Ujubu da alfahari.”

          25-Imam Kazim ya ce, “Mutum ba zai kasance Mumini ba har sai ya kasance mai tsoron Allah mai kuma kwa]ayin abinda ke wajen Allah Ta’ala.”

          26-Imam Kazim ya ce, “Fushi shine mabu]in dukkan sharri.”

          27-Imam Kazim ya ce, “Wanda yafi kamalar imani cikin Muminai shine wanda ya fisu kyawawan ]abi’u.”

          28-Imam Kazim ya ce, “Ka daure kan yima Allah Ta’ala ]a’a,ka kuma daure kan nisantar sa~a ma Allah Ta’ala.”

          29-Imam Kazim ya ce, “Kashedinka da girman kai saboda ba zai shiga Aljanna ba wanda akwai }wayar zarra na girman kai a cikin zuciyarsa.”

          30-Imam Kazim ya ce, “Baya daga cikinmu wanda bai yi ma kansa hisabi kowace rana,idan ya aikata ayyuka na }warai sai ya }ara,idan kuma ya aikata mummunan aiki sai ya nemi Allah gafara ya kuma tuba gareshi.”

          31-Imam Kazim ya ce, “Yana daga cikin ]abi’oin mumini }arancin Magana da kuma yawan aiki,]abi’ar munafiki kuma shine yawan Magana da kuma }arancin aiki.”

          32-Imam Kazim ya ce, “Kashedinka daga kwa]ayi domin kwa]ayi mabu]i ne ga }as}anci.”

          33-Imam Kazim ya ce, “Kayi hankali da kuma takatsantsan daga duniya da kuma ma’abuta duniya,domin son duniya yana haifar da gushewar tsoron lahira a cikin zuciya.”

          34-Imam Kazim ya ce, “Kashedinka da kasala da kuma }osawa domin suna tauye ma mutum rabonsa na duniya da kuma lahira.”

        35-Imam Kazim ya ce, “Fifikon Malami akan mai ibada kamar fifikon rana ne akan taurari.”

          36-Imam Kazim ya ce, “Ku nemi ilimin addini saboda shi ilimi mabu]in basira ne kuma dalili zuwa ga ma]aukakan darajoji.”

          37-Imam Kazim ya ce, “Kashedinka Allah Ta’ala ya ganka a wani zunubi da ya hana ka.”

          38-Imam Kazim ya ce, “Kashedinka Allah Ta’ala ya kasance bai ganka ba ga wani aikin ]a a da ya umarce ka dashi ba.”

          39-Imam Kazim ya ce, “Kada ka fitar da kanka wajen tunanin ta}aitawarka ga ibada da kuma ]a a ga Allah Ta’ala.”

          40-Imam Kazim[AS] ya ce, “Kayi }o}ari ko da wane lokaci kana cikin aikata ababe ]ayan hu]u:Ko dai kana ibadar Allah Ta’ala,ko kana sa’ayi na neman abincinka,ko kana tare da ‘yan uwa na addini ko kuma kana ba jikinka ha}}insa.”

Insha Allah a darasi na gaba za a kawo Hadisai 40 da aka ruwaito daga Imam Ridha[AS].

 
Home Darusan Hadisai Hadisai 40 na Imam Musa Al-Kazim[AS]
Copyright © 2023. www.tambihin.net. Designed by KH