Saturday, 02 December 2023
Email
Make My Homepage
RSS
Register
Hadisai 40 na Imam Ja’afarus-Sadiq (AS) Print E-mail
Written by administrator   
Sunday, 25 September 2016 16:54

A darasin da ya gabata an kawo Hadisai 40 na Imam Zainul-Abidin[AS] yanzu kuma mun zo na Imam Sadik[AS].Imam Sadik[AS] in ka cire Imam Ali[AS] to shine Imamin da aka ruwaito Hadisai a wajen sa fiye da sauran Imamai da suka gabace shi da kuma wadanda suka zo bayansa wannan ko bai rasa nasaba na yanayin da ya samu wanda ya ba da damar ya]a Hadisai sosai,kasantuwar lokacin Daular Bani Umayya ta yi rauni tana fafutuka na ta }washi kanta daga Daular Banul-Abbas da suka ]ago.Akwai ma wata shahararriyar magana ta Imam Sadi} da yake ce masu neman ilimin Hadisi,ku zagaya gabas da yamma na duniya ba zaku samu Hadisai kamar wajena ba,shi yasa Malaman Hadisi na Ahlus-sunna da yawa sun ruwaito Hadisai daga wajensa.Akwai ma wani daga cikin mabiyansa mai suna Abana ]an Taglib ya ruwaito Hadisai a wajensa ]ai-]ai har dubu talatin shi ka]ai kawai,Muhammad ]an Muslim shi kuma ya ruwaito Hadisai dubu sha shida a wajensa.Saboda haka Hadisai 40 da za a kawo nan wasu ne daga cikin ]inbin Hadisansa masu yawa da aka ruwaito,amma kafin kawo Hadisan ga wasu sassa na rayuwarsa.

1-    Haihuwarsa:An haife shi ranar jumma’a 17 ga watan Rabiul Awwal shekara ta 83 bayan hijira.

2-    Nasabarsa:Mahaifinsa Imam Muhammad Al-bakir[AS]Mahaifiyarsa Fatimatu ‘yar {asim.

3-    Nash’a ]insa:Imam Sadi}[AS] ya tashi a madina ya rayu a madina ya kuma rasu a cikinta.

4-    La}ubbansa:Yana da la}ubba da yawa amma wanda yafi shahara shine Sadi},kuma ana yi masa kinaya da Abu Abdullah.

5-    Shekarunsa:Ya rayu shekaru 65 a duniya a wani }aulin ma 68.

6-    Muddan Imamancinsa:Shekaru 34.

7-    ‘Ya’yansa:Yana da ‘ya’ya 10.maza 7,mata 3.

8-    Wafatinsa:Ya rasu ranar 25 ga watan shawwal shekara ta 148 bayan Hijira.

9-    {abarinsa:Yana a madina ne a ma}abartar Ba}i’a.

Insha Allah ga jerin Hadisan.

          1-Imam Sadi} ya ce, “Abubuwa ukku suna amfanar mutum bayan mutuwarsa,sadakar da yayi wanda amfaninta na gudana bayan mutuwars,ko ilimin da ya bayar a rayuwarsa ana kuma amfana dashi bayan mutuwarsa ko kuma ]a na salihi da yake yi masa addu’a.”

          2-Imam Sadi} ya ce, “Abubuwa ukku duk wanda ya ri}e su to zai samu biyan bu}ata na bu}atunsa na duniya da lahira.Wanda ya ri}e Allah,ya yarda da abunda Allah ya hukumta,ya kuma kyautata zato ga Allah Ta’ala.”

          3-Imam Sadi} ya ce, “Bawa ba zai samu kamalar imani ba har sai ya kasance yana da ]abi’oi guda ukku:Ilimi a fagen addini.Nizami a rayuwarsa.Dauriya akan musibu.”

          4-Imam Sadi} ya ce, “Munanan ]abi’u guda ukku duk wanda yake dasu tu munafiki ne:In yana Magana yayi }arya.In yayi al}awari ya sa~a.In anbashi amana yaci.”

          5-Imam Sadi} ya ce, “Yana daga cikin kamalar imani mutum yayi so saboda Allah,yayi }i saboda Allah,ya bayar saboda Allah,ya hana saboda Allah.”

          6-Imam Sadi} ya ce, “Babu wani guzuri da ya kai Ta}awa.Babu ma}iyi mafi cutarwa kamar jahilci.Babu wata cuta mai cutarwa kamar }arya.”

          7-Imam Sadi} ya ce, “Allah Ta’ala yana halakar da shugabanni saboda zalunci.Yan kasuwa kuma saboda yaudara.Malamai kuma saboda Hassada.”

          8-Imam Sadi} ya ce, “Giya itace shugaban kowane zunubi,mabu]in kowane sharri,ba a sa~a ma Allah da wani abu mafi tsanani ba kamar shan giya.”

          9-Imam Sadi} ya ce, “Duk wanda yaji tsoron Allah to Allah Ta’ala zai sa komi yaji tsoronsa.Duk wanda bai ji tsoron Allah ba to zai zamo yana jin tsoron komai.”

          10-Imam Sadi} ya ce, “Allah Ta’ala yana nan inda bawansa mumini yake zatonsa,in alhairi-alhairi,in kuma sharri-sharri.”wato in kayi mashi zaton alhairi to zaka samu alhairi in kuma sharri kayi zato to sharrin zaka samu.

          11-Imam Sadi} ya ce, “Sadar da zumunci da kuma aikata ayyukan alhairi yana sau}a}a ma mutum hisabi ranar }iyama,kuma yana hana mutum daga aikata zunubi,saboda haka ku sadar da zumunci.Haka nan kuma ku kyautata ma ‘yan uwanku koda da maida sallama da kuma kyakkyawan magana.”

          12-Imam Sadi} ya ce, “Duk wanda ya taimaka wajen kashe mumini koda da rabin kalma ne to zai zo ranar }iyama a goshinsa an rubuta ‘Wanda ya yenke tsammani daga rahamar Allah.’

          13-Imam Sadi} ya ce, “Fushi shine mabu]in kowane sharri.Son duniya shine tushen kowane zunubi.”

          14-Imam Sadi} ya ce, “Kuyi ma iyayenku biyayya,’ya’yanku sai suyi maku biyayya.”

          15-Imam Sadi} ya ce, “Duk wanda yake tattali to ina tabbatar masa cewa ba zai ta~a yin talauci ba.”

          16-Imam Sadi} ya ce, “Wanda yafi kowa tsentseni shine wanda ya tsaya gun shubuha-wato bai shiga cikin abinda yake akwai shubuha a cikinsa ba-Wanda yafi kowa zuhudu shine wanda ya guje ma ababen da Allah ya haramta.Wanda yafi kowa mujahada shine mai nisantar zunubai.”

          17-Imam Sadi} ya ce, “Mutum ukku ba zasu shiga aljanna ba:Mai kashe mutane.Mai shan giya da kuma mai yawo da Annamimanci.”

          18-Imam Sadi} ya ce, “Duk wanda ya ce La’ilaha-illallah yana mai ikilasi to zai shiga Aljanna,ikilasin sa shine La’ilaha-illallah ta hana shi aikata ababen da Allah Ta’ala ya haramta.”

          19-Imam Sadi} ya ce, “Duk wanda ya aikata abinda ya sani to Allah Ta’ala zai sanar dashi abinda bai sani ba.”

          20-Imam Sadi} ya ce, “Aikata zunubi yana iya zama sanadiyyar hana bawa arziki daga wajen Allah Ta’ala.”

          21-Imam Sadi} ya ce, “A sama akwai wasu mala’iku guda biyu da aka wakilta su ga bayi,duk wanda ya yi tawadi’u saboda Allah to zasu ]aukaka shi,wanda kuma ya yi girman kai to zasu }as}antar dashi.”

          22-Imam Sadi} ya ce, “Duk wanda ya ta’alla}a zuciyarsa da son duniya to ko zai zauna cikin ba}in cikin da bai }arewa,da burin da ba zai riske shi ba da kuma fatan da ba zai samu ba.”

          23-Imam Sadi} ya ce, “Duk wanda ya kyautata niyyarsa to Allah zai }ara masa arziki.Duk wanda ya kyautata ma iyalinsa to Allah zai }ara masa tsawon rai.”

          24-Imam Sadi} ya ce, “Duk wanda Allah Ta’ala ya yi masa ni’imar-dukiya- to ya yelwata ma iyalinsa,in ko bai yi haka to ni’imar tana iya gushewa.”

          25-Imam Sadi} ya ce, “Bawa mumini ba zai gushe ba yana tarbiyyatar da iyalinsa kyakkyawar tarbiyya da kuma ilimantar dasu to wannan zai iya zama sanadiyyar shigar su aljanna baki ]aya gidan.Haka nan idan mummunar tarbiyya yake gina su akai to wannan zai iya zama sanadiyyar shigar su wuta baki ]aya gidan.”

          26-Imam Sadi} ya ce, “Kuyi musafaha,domin yin musafaha da juna yana gusar da }iyayya da gaba.”

          27-Imam Sadi} ya ce, “Ibilis bai da wata runduna mai tsanani kamar fushi da kuma mata.”-wato yana amfani dasu wajen halakar da ]an Adam-

          28-Imam Sadi} ya ce, “Duniya kurkukun mumini ne,dauriya shine maganin zamansa,Aljanna itace makomarsa.Duniya Aljannar kafiri ce,{abari shine kurkukunsa,Wuta kuma itace makomarsa.”

          29-Imam Sadi} ya ce, “Dariyar mumini itace murmushi.Yana daga cikin sunna sa zobe.”

          30-Imam Sadi} ya ce, “Abubuwa ukku Allah Ta’ala bai yi ma wani rangwame akansu ba:Kyautata ma iyaye salihai ne ko fajirai.Cika al}awari ga salihi da kuma fajiri.Ri}e amana ga salihi ko fajiri.”

          31-Imam Sadi} ya ce, “Duk wanda ya tsaya a in da za a iya tuhumarsa,to kada ya zargi wanda ya munana masa zato.”

          32-Imam Sadi} ya ce, “Baza ka kasance Mumini ba har sai ka kasance mai tsoron Allah da kuma kwa]ayinsa.Ba zaka kasance mai tsoro da kwa]ayi ba har sai ka kasance mai aiki ga abinda kake jin tsoro ko kwa]ayi.”-wato in kana jin tsoron wuta ko azabar Allah to mutum ya nisanci aikin da zai shigar dashi wuta ko azaba,haka nan idan mutum na kwa]ayin aljanna to yayi aikin da zai kai shi aljannar-

          33-Imam Sadi} ya ce, “Kashedinku yima juna Hassada,domin shi kafirci asalinsa daga Hassada ne.”

        34-Imam Sadi} ya ce, “Abubuwa ukku suna gadar da so:Ri}o da addini.Tawadi’u.Kyauta.”

          35-Imam Sadi} ya ce, “Abubuwa ukku suna sabbaba gaba da }iyayya:Munafinci.Zalunci da kuma girman kai.”

          36-Imam Sadi} ya ce, “Mutane ukku baka iya saninsu sai a waje ukku:Ba a sanin mai ha}uri sai lokacin fushi,ko jarumi sai lokacin ya}i,ko aboki sai lokacin bu}ata.”

          37-Imam Sadi} ya ce, “Ku yawaita addu’a domin Allah yana son bayinsa masu yawan addu’a.”

          38-Imam Sadi} ya ce, “Ku yawaita zikirin Allah daidai gwargwadon ikon ku dare da rana saboda Allah yayi umarni da yawan zikirinsa.”

          39-Imam Sadi} ya ce, “Kashedinku son ranku ya kai ku zuwa ga ababen da Allah Ta’ala ya haramta.”

          40-Imam Sadi} ya ce, Manzon Allah ya ce, “ Addu’ar musulmin da aka zalunta kar~a~~iya ce.”Insha-Allah a darasi na gaba za a kawo Hadisai 40 da aka ruwaito daga Imam Musa Alkazim[AS].

 
Home Darusan Hadisai Hadisai 40 na Imam Ja’afarus-Sadiq (AS)
Copyright © 2023. www.tambihin.net. Designed by KH