Hadisai 40 na Imam Muhammad Al-Baqir (AS). |
![]() |
![]() |
Written by administrator | |||
Sunday, 04 September 2016 17:21 | |||
Kasantuwar wannan wata da muke ciki na Zul-Hijja wanda a cikinsa ne ranar bakwai gareshi wafatin Imam Ba}ir[AS] ya kasance.Kuma ajerin Hadisai 40- 40 da ake kawo na Imamai to an kawo kan na Imam Ba}ir,Amma kasancewar wannan munasaba ta Shahadarsa ga wasu sassa na rayuwarsa. Haihuwarsa: Imam Muhammad al-Ba}ir[AS] An haife shi a Madina,ranar Jumma’a 1 ga watan Rajab shekara ta 57 bayan Hijira.Kuma shine Imam na biyar a jerin }idaya na Imamai 12. 1- Nasabarsa:Sunan Mahaifiyarsa Fa]ima ‘yar Imam Hassan,yazo a kan cewa shine ka]ai ya ha]a irin wannan nasaba,wato cewa Mahaifinsa shine Imam Sajjad ]an Imam Husain[AS] mahaifiyarsa kuma Fadima ‘yar Imam Hassan[AS]. 2- Nash’a ]insa:Imam Ba}ir ya tashi a Madina,gaban mahaifinsa da kuma kakansa,ya rayu tare da kakansa Imam Husain[AS] shekara 4.Saboda haka wa}i’ar karbala tare dashi aka yi wato lokacin yana da shekara 4 a duniya.Ya kuma rayu tare da mahaifinsa shekara 25. 3- La}ubbansa da Kinayarsa:Imam Ba}ir yana da la}ubba masu yawa,amma wa]anda suka fi fice sune Al-Ba}ir da kuma “SHABIH”ana ce masa haka ne saboda yayi kama da Manzon Allah[S] so sai.Ana kuma yi masa kinaya da Abu Ja’afar. 4- Shekarunsa:Imam Ba}ir[AS] ya rayu a duniya shekaru 57. 5- Muddan Imamancinsa:Shekaru 19. 6- ‘ya’yansa:Imam Bakir[AS] yana da ‘ya’ya bakwai,maza biyar,mata biyu. 7- Wafatinsa:Ya rasu ranar litinin 7 ga watan Zul-hijja shekara ta 114 bayan Hijira. 8- {abarinsa:}abarinsa yana Madina ne wato a Ba}i’a. Bayan haka Imam Ba}ir yana daga cikin Imaman da aka ruwaito Hadisai masu yawa daga wajensa,wannan ko sakamakon yana yi da ya samu fiye da sauran Imaman da suka biyo bayansa,haka nan kuma sakamakon an bu]e }ofar karantar da Hadisai wadda aka kulle shekaru kusan saba’in gabanin haka,wanda ya bu]e wannan }ofar ko shine khalifa Umar ]an Abdul-Aziz,haka nan a lokacinsa ne ya maida Fadak ga Ahlul bayt, ya mi}a tane ga Imam Ba}ir,a ta}aice dai a khalifofin Bani umayya baki ]aya shine tarihi bai nuna ya musgunuwa wa Ahlul bayt ba.Saboda haka Hadisai 40 da za a kawo anan wasu ne daga cikin Hadisai masu yawa da aka ruwaito daga Imam Ba}ir[AS] 1-Imam Ba}ir[AS] ya ce, “Komi yana da aibi,aibin ilimi shine manta shi.” 2-Imam Bakir[AS] ya ce, “Mutuwar Malami guda yafi soyuwa ga Ibilis fiye da mutuwar Abidi saba’in.” 3-Imam Bakir[AS] ya ce, “Babu wani abu da zai sa ‘yan uwa su kusanto gareka face ta hanyar kyautata masu.” 4-Imam Bakir[AS] ya ce, “Ba kamalar da ta kai yin ilimi a fagen addini,da kuma dauriya akan musibu da kuma tsakatsaki a rayuwa.” 5-Imam Bakir[AS] ya ce, “Duk abunda Allah Ta’ala ya hukumta ma mumini to alhairi ne a gareshi.” 6-Imam Bakir[AS] ya ce, “Ba a karbar aiki face wanda yake akan asasin ilimi,ilimi kuma anfaninsa idan an yi aiki dashi.” 7-Imam Bakir[AS] ya ce, “Kasala tana cutar da mutum a addininsa da kuma duniyarsa.” 8-Imam Bakir[AS] ya ce, “Mai girman kai kamar yana jayayya da Allah Ta’ala ne.” 9-Imam Bakir[AS] ya ce, “Duk wanda yayi aiki da ilimin da ya sani to Allah Ta’ala zai sanar dashi ilimin da bai sani ba.” 10- Imam Bakir[AS] ya ce, “Sadaka da yin alhairi yana tunkude talauci,yana kuma }ara tsawon rai,yana kuma tunkude mummunar mutuwa.” 11-Imam Ba}ir ya ce, “Abubuwa ukku yana daga cikin manya-manya na kyawawan ]abi’u:Yin afuwa ga wanda ya zalunce ka,sadar da zumuncin wanda ya yenke maka da kuma yin ha}uri ga wanda yayi maka wauta.” 12-Imam Ba}ir ya ce, “Wanda ya kyautata niyyarsa arzikinsa zai }aru,wanda ya kyautata ma iyalinsa zai samu }arin yawancin kwana.” 13-Imam Ba}ir ya ce, “Bawa zai iya aikata wani zunubi haka ya zama sanadiyyar gushewar arzikinsa.” 14-Imam Ba}ir ya ce, “Duk abokantakar da aka yi har ta kai tsawon shekaru 20 to zama zumunta.” 15-Imam Ba}ir ya ce, “Malamin da ake amfanuwa da iliminsa yafi Abidi dubu saba’in.” 16-Imam Ba}ir ya ce, “Mutum ba zai kasance Malami ba har sai ya kasance bai hasada ga wanda yake sama dashi,bai kuma wala}anta wanda yake }asa dashi.” 17-Imam Ba}ir ya ce, “Munanan ]abi’u guda ukku mai yinsu ba zai bar duniya ba har sai yaga sakamakonsu sune:Zalunci,yenke zumunci da kuma rantsuwa akan }arya.” 18-Imam Ba}ir ya ce, “Wanda yake cikin shi’armu shine mai tsoron Allah,mai ]a’a ga Allah Ta’ala,mai tawadi’u,mai ri}on amana,mai yawan ambaton Allah da azumi da sallah da kuma karatun Al}ur’ani.” 19-Imam Ba}ir ya ce, “Kashedinka da kasala da kuma }osawa domin mabu]in sharrine,saboda duk mai kasala to ba zai iya tsayuwa da aikin alhairi ba,duk mai }osawa to ba zai iya dauriya ba.” 20-Imam Ba}ir ya ce, “Tawadi’u shine yarda da komabaya a wajen zama,yin sallama ga wanda ka ha]u dashi,da kuma rashin yin jayayya ko da ko kai keda gaskiya.” 21-Imam Ba}ir ya ce, “Mu’umini ]an uwan muminine bai munana masa zato,bai zaginsa,bai kuma hana shi abu.” 22-Imam Ba}ir ya ce, “Murmushi da kuma sakin fuska yana janyo soyayya da kuma kusanci zuwa ga Allah,gintse fuska yana janyo }iyayya da kuma nisantar Allah Ta’ala.” 23-Imam Ba}ir ya ce, “Allah Ta’ala yana bada duniya ga wanda yake so da kuma wanda baya so,amma baya ba da addini sai ga wanda yake so.” 24-Imam Ba}ir ya ce, “Na horeku da yin mujahada da fa]in gaskiya da kuma ri}on amana.” 25-Imam Ba}ir ya ce “Sadar da zumunci yana tunku]e musibu,yana kuma sau}a}e hisabi ranar }iyama.” 26-Imam Ba}ir ya ce, “Da a ce mai ro}o yasan illar dake cikin ro}o da bai tambayi kowa ba.Da a ce wanda aka ro}a ya san illar dake cikin }in bayarwa idan an ro}e shi to da bai hana kowa komi ba.” 27-Imam Ba}ir ya ce, “Allah Ta’ala yana son ya]a sallama,yana son kuma mai kunya,mai ha}uri da kuma kamun kai” 28-Imam Ba}ir ya ce, “Ku fa]a ma mutane mafi kyawan abinda kuke so a fa]a maku.” 29-Imam Ba}ir ya ce, “Mutum ba zai iya ku~uta daga zunubi ba har sai in ya tsare harshensa.” 30-Imam Ba}ir ya ce, “Yana daga cikin giba ka fa]i wani abu ga ]an uwanka da Allah Ta’ala ya rufa masa asiri akai.” 31-Imam Ba}ir ya ce, “Baya daga cikin ]abi’oin mumini hassada da kuma fadanci.” 32-Imam Ba}ir y ace, “Allah Ta’ala yana cewa,ya kai ]an Adam ka nisanci ababen dana haramta maka sai ka kasance mafi tsentsenin mutane.” 33-Imam Ba}ir y ace, “Kunya da imani a ha]e suke,in ]ayansu ya tafi,]ayan sai ya bishi.” 34-Imam Ba}ir ya ce, “Malami idan an tambaye shi wani abu alhali bai sani ba to ya ce, “Allahu A’alam”. 34-Imam Ba}ir ya ce, “Ka yi shawara cikin al’amuranka ga wanda yake tsoron Allah Ta’ala.” 35-Imam Ba}ir ya ce, “Ka duba abinda ka keso ya kasance tare da kai idan kaje gaban ubangijinka to ka lizimce shi,ka kuma duba abinda ka ke gudun ya kasance tare da kai idan kaje gaban ubangijinka to ka nisance shi.” 36-Imam Ba}ir ya ce, “Masu }arfinku su taimaka ma raunananku,mawadatanku su tausaya ma matalautanku.” 37-Imam Ba}ir ya ce, “Idan Allah Ta’ala yayi maka ni’ima ka ce Alhamdu lillah.Idan wani abu ya ba}anta maka rai ka ce “La haula wala }uwwata illa billah.” 38-Imam Ba}ir ya ce, “Ku nemi ilimi,saboda neman ilimi abu ne mai kyau kuma ibada ne.” 39-Imam Ba}ir ya ce, “Kashedinka da yin husuma domin tana ~ata zuciya kuma tana haifar da munafunci.” 40-Imam Ba}ir[AS] ya ce, “Zalunci ya kasu kashi ukku:1-Akwai zaluncin da Allah baya gafartawa.2-Akwai zaluncin da Allah yake gafartawa.3-Akwai zaluncin da baya barinsa.Zaluncin da baya gafartawa shine shirka dashi.Zaluncin da yake gafartawa shine wanda mutum yayi tsakaninsa da Allah- misali ya sa~a ma Allah Ta’ala-Zaluncin da baya bari shine wanda ke tsakanin mutane.”Insha-Allah a darasi na gaba za a kawo Hadisai 40 da aka ruwaito daga Imam Sadi}[AS].
|