Saturday, 02 December 2023
Email
Make My Homepage
RSS
Register
Hadisai 40 na Imam Zainul-Abidin (AS). Print E-mail
Written by administrator   
Sunday, 21 August 2016 16:45

A darasin Hadisi da ya gabata an gabatar da Hadisai 40 da aka ruwaito daga Imam Husain[AS].A yanzu kuma insha Allah za a gabatar da na Imam Zainul Abidin[AS] a darasi na gaba kuma na Imam Baqir[AS].Imam Zainul Abidin[AS]idan mutum ya dubi abun ta mahangar Ahlus Sunna zai ga cewa yana cikin ]aba}a ]in tabi’ai wato wa]anda basu ga Manzon Allah[S] ba amma sun ga wa]anda suka ganshi kuma suka rayu dashi,kuma in mutum ya bincika zai ga cewa fitattun malamai daga cikin ]aba}a ]in tabi’ai kamar irin su Sa’idu ]an Musayyib,{asim ]an Muhammad,Sa’idu ]an Jubair da dai sauransu to duk a wajensa suka yi karatu.Haka nan kuma malaman Tasawwuf na zamaninsa kamar irin su Hasanul Basary,Malik ]an Dinar,Utbatul Gulam,Rabi’atul Adawiyya da dai sauransu suma sun yi karatu a wajensa,kai wuce nan ma akwai sashen sahabbai da suka ruwaito Hadisai daga gareshi daga cikinsu akwai Abdullahi ]an Umar,ta yiyu wani ya ji mamakin haka to daga cikin khususiyyar da Aimma na Ahlul bayt suke da shi shine cewa dukkan Hadisan Manzon Allah[S] baki ]ayansu sun sansu,wanda baya gasu babu wanda zai iya dukan }irji a wannan al’umma ta Manzon Allah[S] ya fa]i haka,shi yasa a lokacin Aimma idan wani Hadisi ya rikice ma malamai ta fuskoki dabam dabam misali ana shakkar ingancinsa ko akasin haka ko kuma ma ha}i}anin ma’anar Hadisin,ko Hadisin akwai ragi a ciki ko }ari to akan kawo ma Imami ne sai ya yi masu bayani ga yadda Hadisin yake,misali akwai wata rana da Imam Zainul Abidin ya karantar da wasu Hadisai,Abdullahi ]an Umar yana wajen to shine da ya gama sai yake ce masa yadda ka fa]i Hadisan nan haka na ji Manzon Allah ya fa]e su.Saboda haka wa]annan Hadisai 40 da za a kawo wasu ne daga cikin Hadisan da aka ruwaito daga wajensa,duk ko da cewa Imam Zainul Abidin[AS] ya rayune a mawuyacin lokaci wato kasantuwar bayan wa}i’ar Karbala ne mubasharatan,saboda akwai jarabawowi masu yawa da suka bijiro bayan wa}I’ar Karbala kamar rushe-rushen gidaje,a lokacin Yazidu[L] ya aiko da umarni ta hannun gwamnansa na Madina cewa ya rushe gidan Imam Husain[AS] da kuma wasu da suka halarci karbala,saboda haka ko das u Imam Zainul Abidin[AS] suka dawo Madina sun iske duk gidajensu an rusa su,bayan haka kuma ga kuma jarabawa ta izgili da kuma nuna farin ciki kan abunda ya faru dasu,shi yasa in mutum ya dubi wa}i’ar da ta faru a Zariya zai ga cewa tarihi ne ya maimaita kansa domin kusan duk abubuwan da suka auku a wa}i’ar Karbala to sun auku a wannan wa}i’a ta Zariya,haka nan abinda ya biyo bayan wa}i’ar karbala yayi kama da abunda ya biyo bayan wannan wa}i’ar ta Zariya wanda ya karanci tarihi zai tabbatar da haka,saboda alhairai da suka biyo bayan wa}i’ar karbala muna da kyakkyawan zato ga Allah Ta’ala cewa zasu biyo bayan wannan wa}i’a,kai ko yanzu ma in mutum ya lura zai soma ganin natijar abunda aka yi misali yanzu Da’awa ta zama ta duniya wato ta shiga sassa daban daban na duniya yanzu,haka nan sanadiyyar wa}i’ar da yawa sun fahimci wannan Harka a yanzu,haka nan abubuwa masu yawa da aka kwashe shekara da shekaru ana jingina ma wannan Harka yanzu ya bayanna ashe }arya ne da dai sauran wasu fa’idodi wanda wasu sai zuwa gaba insha Allah zasu bayyana.Bayan wannan ‘yar shinfi]a ga jerin Hadisan.

          1-Imam Zainul Abidin[AS] ya ce, “Allah Ta’ala ya ~oye yardarsa cikin ]a’arsa saboda haka kada ka wala}anta komi na ]a’arsa,ta yiyu yardarsa tana ciki amma baka sani ba.”

          2-Imam Zainul Abidin ya ce, “Allah Ta’ala ya ~oye fushinsa cikin sa~a masa saboda haka kada ka wala}anta komi na sa~onsa,ta yiyu fushinsa yana cikin sa~on amma baka sani ba.”

          3-Imam Zainul Abidin ya ce, “Allah Ta’ala ya ~oye amsar addu’arsa cikin addu’arsa saboda haka kada ka wala}anta komi na addu’arsa,ta yiyu akwai amsar addu’ar ciki amma baka sani ba.”

          4-Imam Zainul Abidin ya ce, “Allah Ta’ala ya ~oye waliyyinsa cikin bayinsa saboda haka kada ka wala}anta wani bawa daga cikin bayin Allah,ta yiyu waliyyinsa ne amma baka sani ba.”

          5-Imam Zainul Abidin ya ce, “Kaji kunyar Allah Ta’ala saboda kusancinsa gareka." 

          6-Imam Zainul Abidin ya ce, “Duk wanda ya wadatu da abinda Allah Ta’ala ya bashi to zai kasance mafi wadatar mutane.”

          7-Imam Zainul Abidin ya ce, “Ku guji yin }arya ga kowane al’amari }arami ko babba saboda duk wanda zai iya yin }arya ga }aramin abu to zai iya samun }arfin hali da zai iya yin }arya ga babban abu.”

          8-Imam Zainul Abidin[AS] ya ce, “Ya isa taimakon Allah gareka ka ga ma}iyin ka yana sa~a ma Allah saboda kai.”

          9-Imam Zainul Abidin[AS] ya ce, “Aiki bai }aranta in dai yana tare da ta}awa,ta yaya zai }aranta alhali kar~a~~e ne.”

          10-Imam Zainul Abidin ya ce, “Kamalar addinin musulmi shine ya bar magana ga abunda ba ruwansa.”

          11-Imam Zainul Abidin ya ce, “Babu wani abu da yafi nauyi a maaunin mutum a ranar }iyama da ya kai kyawawan ]abi’u.”

          12-Imam Zainul Abidin ya ce, “Yadda da abubuwan }i ga mutum na abun da Allah Ta’ala ya hukumta shine }ololuwar ya}ini.”

          13-Imam Zainul Abidin ya ce, “Mafi soyuwarku a wajen Allah shine wanda ya fiku kyawawan ayyuka.”

          14-Imam Zainul Abidin ya ce, “Wanda yafi tsira a cikinku daga azabar Allah shine wanda ya fiku tsoron Allah Ta’ala.”

          15-Imam Zainul Abidin ya ce, “Mafi matsayinku a wajen Allah Ta’ala shine wanda ya fiku Ta}awa.”

          16-Imam Zainul Abidin ya ce, “Wanda yafi kusanci ga Allah Ta’ala a cikinku shine wanda ya fiku kyawawan ]abi’u.”

          17-Imam Zainul Abidin ya ce, “Wanda Allah Ta’ala yafi yarda dashi a cikinku shine wanda yafi kyautata ma iyalinsa.”

          18-Imam Zainul Abidin ya ce, “Kashedinka da abuta da ma}aryaci saboda shi kamar }awalwalniyane yana kusanto maka da nesa,yana kuma nisanta maka kusa.”

          19-Imam Zainul Abidin ya ce, “Kashedinka da yin aboki da marowaci saboda shi zai hana ka dukiyarsa lokacin da kake bu}ata.”

          20-Imam Zainul Abidin ya ce, “Kashedinka da abokantaka da wawa saboda shi zai iya nufin ya amfane ka amma kuma sai ya cutar da kai.”

          21-Imam Zainul Abidin ya ce, “Kashedinka da yin abuta da mai yenke zumunci saboda shi la’ananne ne a cikin littafin Allah.”

            22-Imam Zainul Abidin ya ce, “Mumini idan yayi addu’a to ]ayan ukku:Ko dai ya samu biyan bu}ata nan take,ko kuma a jinkirta masa biyan bu}atar zuwa wani lokaci,ko kuma Allah Ta’ala ya tunku]e masa wani bala’i da zai same shi.”

          23-Imam Zainul Abidin ya ce, “Munafiki yana umarni da alhairi amma shi baya aikatawa,haka nan kuma yana hani da mummuna amma shi yana aikatawa.”

          24-Imam Zainul Abidin ya ce, “Misalin dauriya da imani kamar kai ne da jiki,babu imani ga wanda bai da dauriya.”

          25-Imam Zainul Abidin ya ce, Allah Ta’ala ya ce, “Ya kai ]an Adam ka yarda da abun dana baka zaka kasance daga cikin mafi zuhudun mutane.”

          26-Imam Zainul Abidin ya ce, Allah Ta’ala ya ce, “Ya kai ]an Adam ka aikata abunda na farlanta maka zaka kasance daga cikin mafi ibadar mutane.”

          27-Imam Zainul Abidin ya ce,Allah Ta’ala ya ce, “Ya kai ]an Adam ka nisanci abubuwan dana haramta maka zaka kasance daga cikin mafi tsantsenni na mutane.”

            28-Imam Zainul Abidin ya ce, “Duk wanda ya guje ma duniya to musibunta zasu sau}a}a masa.”

          29-Imam Zainul Abidin ya ce, “Allah Ta’ala bai son wanda yake marowaci kuma mai ro}o.”

          30-Imam Zainul Abidin ya ce, “Yana daga cikin ]abi’un mumini infa}i dai dai gwargwadon iko da yelwatawa dai dai gwargwadon iko da kuma fara sallama.

          31-Imam Zainul Abidin ya ce, “Abubuwa ukku masu tseratarwa ne ga mumini:Kame harshensa daga mutane,shagaltar da kansa daga abinda zai amfane shi a duniyarsa da lahirarsa da kuma kuka ga zunuban da ya aikata.”

          32-Imam Zainul Abidin ya ce, “Kallon mumini ga fuskar ]an uwansa mumini saboda so da }auna ibada ne.”

          33-Imam Zainul Abidin ya ce, “Duk wanda yaji tsoron wuta to dole ne ya kame daga sa~a ma Allah Ta’ala.”

          34-Imam Zainul Abidin ya ce, “Ya kai ]an Adam ba zaka gushe ba kana kan alhairi matu}ar kana yi ma kanka hisabi.”

          35-Imam Zainul Abidin ya ce, “Ya kai ]an Adam ka sani zaka mutu,za a tada kai,za kuma ga tsaya gaban Allah Ta’ala,saboda haka ka tanaji jawabi.”

          36-Imam Zainul Abidin ya ce, “Kuji tsoron Allah yaku bayin Allah kuma ku yi aiki domin abinda aka halicce ku akai.”

          37-Imam Zainul Abidin ya ce, “Ku kasance ‘ya’yan lahira kada ku kasance ‘ya’yan duniya,ku kasance masu guje ma duniya masu kwa]ayin lahira.”

          38-Imam Zainul Abidin ya ce, “Idan an zalunceka to kai kada kayi zalunci,idan an yaudareka to kai kada kayi yaudara,idan an }aryataka to kada kayi fushi.”

          39-Imam zainul Abidin ya ce, “Kashedinka daga gafala saboda yana busar da zuciya”

          40- Imam Zainul Abidin y ace, “Magana mai kyau tana }ara arziki da kuma sanadiyyar shiga Aljanna.” Da dai sauran hadisai masu yawa da aka ruwaito daga Imam Zainul Abidin[AS] kamar Addu’ar jaushanil kabir daga wajensa aka ruwaito ta da kuma Addu’ar Abu Hamzata Assumaly.

 
Home Darusan Hadisai Hadisai 40 na Imam Zainul-Abidin (AS).
Copyright © 2023. www.tambihin.net. Designed by KH