Thursday, 27 January 2022
Email
Make My Homepage
RSS
Register
Darussa dag yakin Uhud Print E-mail
Written by administrator   
Sunday, 24 July 2016 20:13

Kasantuwar wannan wata da muke ciki wato watan Shawwal wanda a cikinsa ne aka yi ya}in Uhudu,a wata ruwaya yazo akan cewa 5 ga watan ne aka yi wannan ya}i a wata ruwayar kuma 15 ga watan.Idan mutum yayi bincike zai ga cewa a duka ya}o}in da Manzon Allah[S] ya yi to babu wani ya}i da aka samu matsaloli na cikin gida da waje kamar ya}in Uhudu.Haka nan idan mutum ya bibiyi tarihin gwagwarmayar tabbatar da addini zai ga cewa akan samu wata wa}i’a wadda ta kan zama }waya ]aya tilo ko dai kafin tabbatar addinin ko lokacin tabbatarsa ko kuma bayan tabbatarsa wato dai kamar yadda ya auku a wannan ya}i na Uhudu.Haka nan in mutum ya bibiyi tarihin wasu daga cikin bayin Allah Ta’ala da yayi amfani dasu wajen jaddada addini zai ga haka,misali lokacin Shehu Usman ]an Fodiyo cikin ya}o}in da yayi akwai wani ya}i da aka kashe masa jama’a masu yawa.Haka nan a lokacin Imam Khumaini akwai wata rana guda ]aya da aka kashe masa mabiya har dubu goma sha-biyar,wannan ya faru tun gabanin juyin Musulunci ne,da yake ranar Jumma’a wannan abu ya faru shi yasa har yanzu ake yi mata la}abi da, ‘Black Friday’ Muma anan mu duba wannan wa}i’a da ta faru, a ce wa}i’a guda ]aya an kashe ‘Yan uwa sama da dubu,alhali an kwashe shekaru 40 akan wannan tafarki haka bai ta~a faruwa ba,shi yasa wani lokaci in na yi tunani dangane da wannan wa}i’a ni kance Allah Ta’ala yasa ta kasance itace ta farko kuma ta }arshe,wato shigen wa}i’ar da ake samu }waya ]aya tilo a gwagwamaryar tabbatar da addini,sai dai fa a lura ba ana nufin babu wasu wa}i’oi da zasu nan gaba bane,sai dai ana fatan ba zasu yi munin wannan da ta faru ba,misali Manzon Allah yayi ya}o}i bayan ya}in Uhudu amma ba a samu ya}in da yayi muni kamar na Uhudu ba.Haka nan lokacin Imam Khumaini bayan waccan rana ta black Friday da aka kashe mutane har dubu sha-biyar to ba a ta~a samun wata rana makamanciyarta ba ballanta wadda ta fita a tarihin gwagwamayarsa sai sau guda da itama ranar aka kashe mutane dubu takwas shima ya faru ne gabanin juyin Musulinci wato lokacin Shah.Bayan wannan gabatarwa Insha Allah bayani zai gudana kan wannan maudu’i na ya}in Uhudu kan wa]annan ababe:

1-Abubuwan da suka faru gabanin ya}in Uhudu.

2-Abubuwan da suka faru lokacin ya}in Uhudu.

3-Abubuwan da suka faru bayan ya}in Uhudu.

4-Darussa da zamu koya daga ya}in Uhudu.

          1-ABUBUWAN DA SUKA FARU GABANIN YA{IN UHUDU:Da farko dai Uhudu sunan dutse ne kusa da garin Madina kuma alhamdu lillah har yanzu dutsen yana nan,wannan ya}i na Uhudu ya auku ne a shekara ta ukku bayan hijira a watan Shawwal.Dalili ko musabbabin ya}in shine Mushirikan Makka }ar}ashin jagorancin Abu Sufyan a lokacin, suka yi gangami na maya}a suka nufo Madina da nufin kawo hari ga Manzon Allah da kuma al’ummar musulmi,adadin wa]annan gangami na maya}a kamar yadda yazo a tarihi su dubu biyu ne a wata ruwaya su dubu ukku a wata ruwayar kuma dubu biyar ne.Lokacin da wannan abun yake faruwa sai Manzon Allah ya tara sahabbansa ya shaida masu cewa Allah Ta’ala yayi masa wahayi ga abunda ma}iya suke shirin yi,saboda haka wace shawara suke ganin za a yi,wasu suke ce a fita a fuskance su tun gabanin su iso Madina, wa]anda suka ba da wannan shawarar mafi yawansu samari ne,wasu kuma suka ce a tsaya sai sun zo Madina a fuskance su, wa]anda suka ba da wannan shawarar mafi yawansu dattawa ne,daga }arshe Manzon Allah ya ]auki ra’ayin wa]anda suka ce a fita a fuskance su tun gabanin su zo Madina da yake su suka yi rinjaye,saboda haka Manzon Allah ya fita da sahabbai kusan dubu ]aya a wata ruwa an ce su 700 ne,abin mamaki bayan an kama hanya sai wasu daga cikin sahabbai suka ce sun fasa tafiyar su gida zasu koma,adadin wa]anda suka dawo ]in yazo a tarihi cewa ]aya bisa ukkun wa]anda suka fita ne,a littafan tarihi na Ahlus sunna sun nuna cewa wa]anda suka dawo ]in suna cikin munafukai wanda kuma ya jagoranci dawowar tasu shine Ubayyu ]an Salul,wa]anda suka dake tare da Manzon Allah suka cigaba da tafiya har ya zuwa lokacin da suka ha]u da ma}iya a wajen dutsen Uhud suka yi sansani aka kuma fafata a wannan waje.

          2-ABUBUWAN DA SUKA FARU A LOKACIN YA{IN UHUDU:

A lokacin da aka ja daga Manzon Allah ya shirya sahabbansa sahu-sahu domin fuskantarsu ya mi}a tuta na sahabbansa Muhajirun ga Imam Ali,tutar kuma sahabbansa Ansar ga Sa’ad ]an Ubada,bayan haka kuma wata kusurwa da Manzon Allah yake ganin ma}iya zasu iya biyo tanan yasa wasu maya}a }ar}ashin jagorancin Abdullahi ]an Jubair,sa’annan ya garga]e cewa duk yadda al’amura suka kasance kada su bar wannan waje,ko da ko su suka yi nasara ko kuma aka yi nasara akansu.Bayan haka Manzon Allah yayi khu]uba.Suma ma}iya suka shirya maya}ansu sahu sahu,kafin a soma ya}in sai mai ri}e da tutar ma}iya ya ce akwai mai mubaraza dashi,sai Imam Ali ya fito ya ce nine,sai yake tambayarsa kai wannan yaro minene sunan ka? Ya ce nine Ali ]an Abu ]alib,sai ya ce ni nasan ba wanda zai iya yi mani wannan }arfin halin in ba kai ba,nan nake sai ya kai ma Imam Ali sara imam Ali ya kare shima ya kai masa sara aka nan take ya fa]o daga dokinsa,Imam Ali ya bishi ya rafke shi nan take ya mutu,sai Manzon Allah yayi kabbara sauran musulmi jin haka suka yi kabbara,wani cikin jagororin ma}iyan ya fito Imam Ali ya kashe shi.a ta}aice dai duk jagororinsu haka suka fito ]aya bayan ]aya Imam yana kashe su,jagoransu na }arshe ya fito a fusace yana kunfar baki akan sai shi yaje ya kashe Manzon Allah,Imam Ali ya tunkare shi ya sara shi tun daga kansa sai da ya raba shi biyu daga nan fa aka fara gumuzu na baki ]aya,zuwa wani lokaci musulmi suka samu nasara akansu har suka fara ]ibar ganima,ganin haka wa]ancan maya}an da Manzon Allah ya garga]e su ka da su yarda su bar wajen koya al’amura suka kasance,abin ba}in ciki mafi yawansu sai suka bar wajen da nufin suma suje su kwaso ganima,jagoransu ya ce masu ga fa abunda Manzon Allah ya ce duk da haka dai suka tafiyarsu,sai ya rage a wajen daga shi wannan Abdullahi ]an Jubair da kuma wasu sahabbai da basu wuce mutum goma ba,ganin haka aiko sai ma}iya suka ~ullo ta wajen suka karkashe wa]annan da suka rage,ya kasance yanzu sun samu damar sa musulmi a tsakiya wato gaba da baya ma}iya ne,haka suka dunga bin musulmi suna kashewa,ya zamanto nasarar da musulmi suka samu yanzu ta koma ru}ushi,ana cikin wannan mawuyacin hali sai Shai]an yayi kururuwa cewa an kashe Muhammad!jin haka Musulmi suka ru]e har ta kai suna sarar junansu basu sani,a irin haka ne har wani sahabi ya kashe wani sahabi bai sani ba,wanda aka kashe ]in shine baban Huzaifa wato Huzaifa ]an Yamani to yamanin aka kashe,wasu suka fara gudu abin ba}in ciki suka bar Manzon Allah a tsakiyar ma}iya shi da wasu sahabbai ‘yan ka]an,inna lillahi wa ina ilaihi raji’un haka suka yi ma Manzon Allah rauni a fuskarsa da kansa da kuma wasu sassa a jikinsa,haka Imam Ali ya dunga ba Manzon Allah kariya shi da sahabban da suka rage dama da hagu sai da ta kai ya samu raunuka ajikinsa ]ai-]ai har guda casa’in.Abun ba}in ciki haka dai ya}i ya }are da nasarar ma}iya akan Musulmi wato a zahirance,saboda an jima musulmi da yawa rauni ga kuma wa]anda aka karkashe,domin an kashe sahabbai har guda 70 kuma bayan da suka kashe su kusan dukansa sai da suka yi masu musula wato ~ata kamannin halittarsu kamar su yanke kunnen mutum ko hancinsa da dai makamantansu,bilhasali ma a gawar Sayyid Hamza sai da suka tsaga cikinsa da }irjinsa suka fito da hantarsa suka kaima Hindatu matar Abu Sufyan kuma uwar Mu’awiya tasa hantar a baki da nufin ta tauna ta ha]iye sai Allah Ta’ala ya mayar da hantar kamar dutse wato ya kasa taunuwa mata haka dai ta watsar dashi daga bakinta,bayan haka ta tafi gun gawar Sayyid Hamza ta yenke kunnuwansa da wasu sassa na jikinsa ta yi abun wuya dashi a wajen,ganin haka suma sauran matayen ma}iya suka dunga bin gawawwakin musulmi suna yi masu wannan mummunan aiki suna sawa a wuyansu,wasu kuma suka ]ebe masu kayan jikinsu suka barsu tsirara da dai wasu abubuwa marasa da]in ji da rubutawa da suka aikata.

          3-ABUBUWAN DA SUKA FARU BAYAN YA{IN UHUDU:Bayan da aka gama ya}i abu na farko da Manzon Allah ya sa ayi shine tattara wa]anda aka karkashe domin yi masu jana’iza irin ta shahidan da aka kashe a fagen fama,bayan Manzon Allah yai masu sallah saannan yasa aka binne su a wajen,bayan an gama jana’izar wa]annan shahidai sai Manzon Allah ya ce wa]annan sune zan yi ma shaida ranar }iyama,jin haka sai Abubakar ya ce mufa ya Manzon Allah? Sai Manzon Allah ya ce ku ban san abunda zaku yi a bayana ba,ga mai bu}atar ganin wannan magana ya duba cikin littafin Muwa]]a Malik a kitabul jihad babin shahidai.Bayan haka Manzon Allah ya ce a kawo masa dokinsa ya hau,aka kamo hanya zuwa Madina tare da sauran sahabbai mafi yawan su akwai raunuka a jikinsu,haka aka shigo Madine mataye suka fito,gari ya ru]e da kuka saboda yanayin da suka ga Manzon Allah da sauran sahabbai na raunuka a jikkunansu,bayan haka kuma sai zaman makoki da aka yi a gidaje dabam-dabam,ana cikin wannan hali na juyayi sai labari yazo akan cewa ma}iya su Abu Sufyan kasantuwar ru]uwa da suka yi na cewa su suna ganin wai sun samu nasara akan musulmi,maimakon su wuce Makka sai suka yi shawar bari su je Madina su karkashe sauran Musulmi,Mala’ika Jibril ya kawo ma Manzon wannan labari,sai Manzon Allah yasa a yi yakuwa na cewa duk wanda yasan dashi aka tafi ya}in Uhudu to ya fito koda ko akwai rauni a jikinsa,haka Manzon Allah da sauran Musulmi suka fita suka kama hanya domin fuskantar wa]annan ma}iya har suka isa wani waje da ake ce masa Hamra’ul- Asad mil takwas ne tsakaninsa da Madina,ana haka sai su Abu Sufyan suka samu labarin cewa Manzon Allah da sahabbansa sun fito domin tinkararsu nan take suka yanke cewa lalle batun zuwa Madina a fasa,a kama hanya kawai a dawo Makka,shi yasa koda suka dawo Makka basu dawo da izza ba,sun dawo suna cikin zullumi basu san mi zai biyo baya ba.Haka nan daga cikin abubuwan da suka faru bayan ya}in Uhud akwai ayoyi da suka sauka na hukunce-hukuncen gado wanda gabanin haka babu su,wannan }ila bai rasa nasaba da adadin musulmi da aka kashe a wannan ya}i na Uhud saboda a ya}in Badar an samu shahidai 14 ne.

          4-DARUSSA DA ZAMU KOYA DAGA YA{IN UHUDU:Akwai darussa masu yawa da zamu koya daga ya}in Uhud,amma ga wasu daga ciki:

1-Muhimmancin zama cikin shiri:Duk wanda yake tafarkin gwagwarmayar tabbatar da addini to yana da muhimmancin ya zauna da tunanin cewa ko da wane lokaci komi zai iya faruwa daga ma}iya,idan muka dubi wannan ya}i na Uhudu kusan yazo ba zato ba tsammani ga musulmi a lokacin.

2-Muhimmancin bin jagoranci:Idan mutum ya yi tunani zai ga cewa asasin abinda ya hana cin nasara a wannan ya}i na Uhudu shine rashin bin jagoranci,wato kasantuwar wa]anda Manzon Allah ya aje su a wurin da ma}iya zasu iya biyowa ta wajen,ya ce duk yadda al’amura suka kasance kada su bar wajen,amma abun ba}in ciki sai suka sa~a ma maganar Manzon Allah suka bar wajen,ganin haka ma}iya suka ~ullo ta wajen.

3-Illar son duniya:In mutum ya yi tunani zai ga cewa wa]annan da suka sa~a ma wannan umarni na Manzon Allah to babban abun ya haifar masu da haka shine son duniya,domin ganimar da suke ribibin su je su kwasa tarkace ne na duniya.

4-Muhimmancin dogara ga Allah Ta’ala,yana da gayar muhimmanci duk wanda yake tafarkin gwagwamarya ya zamanto koda wane lokaci dogaransa ga Allah ne ba ga yawa ba ko }arfi kowata dibara da dai sauransu,mu dubi abunda ya faru a ya}in Hunainu yadda wasu daga cikin musulmi suka dogara ga yawansu haka yayi sanadiyyar rashin cin nasara a farkon ya}in.

5-Muhimmancin zama cikin tunanin cewa mutum zai iya fuskantar kowace irin jarabawa wato ba sai yadda yake tsammani ba,kuma wannan jarabawa zata iya kasancewa ko da bayan rayuwarsa ,misali a kashe shi a wala}anta gawarsa kamar yadda ma}iya suka yi ma wa]annan shahidai na Uhudu domin ba wanda basu yi ma gawarsa Musla ba fa ce ta sahabi guda shine Hanzala,ko shima abinda yasa shine mahaifinsa da yake yana cikin ma}iya shine ya tsaya ya ce ba wanda zai ta~a gawar ]ansa.Mu duba yadda suka yi da gawar Sayyid Hamza,wanda yazo akan cewa lokacin da Manzon Allah ya ga yadda suka yi kaca-kaca da gawarsa sai da ya ce tun da yake bai ta~a tsayawa a wani waje da yayi ba}in ciki kamar wannan muhalli ba.ko mu anan mu duba yadda aka yi da gawawwakin ‘yan uwanmu a wannan wa}i’a,aka }ona wasu bayan haka kuma aka je aka ha}a rami aka binne ba tare da bin matakai na jana’iza ba kamar wanka,yi masu likkafani,yi masu sallah da dai sauransu.

6-Muhimmancin koyon zama da matsaloli na cikin gwagwarmaya da kuma wajen gwagwamarya,in da za a kawo bayanai sanka-sanka na irin matsalolin da aka fuskanta a wannan ya}i na Uhudu na cikin gida da waje da an ji mamaki,musamman ma na irin maganganun da wasu musulmi suka yi bayan an dawo ya}in Uhudu ]in.Saboda haka matsaloli a tafarkin gwagwarmayar tabbatar da addini abun ne wanda za a ta fuskantarsa har bayan tabbatar addini.

7-Muhimmancin ba jagora kariya:Mu duba lokacin da ma}iya suka zagaye Manzon Allah da nufin sai sun kashe shi a wannan ya}i na Uhudu,a lokaci guda aka samu wasu daga cikin sahabbai suka dake wajen ba Manzon Allah kariya cikin su ko har da sahabbai mata suma haka suka dake suka dunga fafatawa da ma}iyan domin ba Manzon Allah kariya,musamman ma wata sahabiya mai suna Nusaiba ta fafata da ma}iya masu yawa a lokacin ba da wannan kariya ga Manzon Allah har ta kashe wasu.saboda duk ya}o}in da Manzon Allah yayi to babu ya}in da ma}iya su kai ta run}urin su kashe shi sai wannan ya}i na Uhudu.domin ya zo akan cewa an kai ma Manzon Allah sara da takobi har kusan sau saba’in a wannan ya}i,kai yama zo akan cewa saboda raunukan da Manzon Allah ya samu a ranar to sallah ma a zaune ya yi,kuma ya zo akan cewa a ranar Sayyida Fa]ima[AS] itace ta wanke ma Manzon Allah[S] jinni na raunukan da aka yi masa da kuma yin wasu hikima domin tsaida jinin.

Saboda haka cutarwa da gallazawa a tafarkin Allah abubuwa ne da suke nuna lalle ana kan hanyar Annabawa saboda sunnar Allah bata canzawa, wato in dai mutum yabi tafarkin Annabawa to lazim zai fuskanci abubuwan da suka fuskanta na cutarwa daga masu tafi da iko da kuma mutanen gari.

 
Home Maudu'oi daban-daban Darussa dag yakin Uhud
Copyright © 2022. www.tambihin.net. Designed by KH