Friday, 28 January 2022
Email
Make My Homepage
RSS
Register
Ibadodin laylatul Qadr. Print E-mail
Written by administrator   
Sunday, 17 July 2016 15:30

Kasantuwar wannan wata da muke ciki na Ramadan wanda a cikinsa akwai wani dare guda wanda falalarsa da kuma darajarsa ya fi wata dubu,idan mutun ya lissafa zai ga cewa sama da shekaru tamanin kenan,an ruwaito daga Imam Rida[AS] ya ce, “Ana ce ma daren lailatul Qadr saboda a cikin dare ake }addara abin da zai faru a shekara baki ]aya na alhairi ko sharri,mai amfani ko mai cutarwa,da arzikin bayi na shekarar da kuma ajalinsa.” Kuma lailatul Qadr zai wanzu har zuwa ranar tashin }iyama,wato bai ta}aita a lokacin Manzon Allah ba saboda akwai wasu daga cikin Malaman Ahlus sunna da suka tafi akan cewa wai daren lailatul Qadr a zamanin Manzon Allah ne kawai saboda haka a yanzu babu shi,an tambayi Imam Sadi}[AS] akan cewa shin daren lailatul zai cigaba da kasance kowace shekara? Sai ya ce da za a ]auke daren lailatul Qadr to da an ]auke Al}ur’ani.” Wato daga duniya saboda haka daren yana nan kowace shekara a watan Ramadan,to da mutum zai samu muwafa}ar yin ibadodi a daren to za a rubuta masa lada kamar ya kwashe fiye da shekaru tamanin yana ibada ga Allah Ta’ala.To tambaya mutum yana da tabbacin zai kai shekaru tamanin a rayuwarsa? Kuma ko da ya kai yana da tabbacin lafiyar jikinsa da kuma }arfinsa? Domin tsufa kamar yadda Imam Khumaini ya ke cewa yana da nashi jarabawowin misali akwai jarabawa ta samun raunin jiki da kuma ga~o~i wato kana so kayi wani aiki na ibada amma jiki ba }arfi,in mutum yayi muamala da tsofaffi zai ga haka,akwai kakanni na na wajen mahaifiya wato mahaifanta uwa da uba ikon Allah duk suna raye a yanzu,mahaifin yana da shekaru kusan 120 mahaifiyar kuma tana da kusan shekaru 100,kuma wani ikon Allah aurensu abin nan da bahaushe ke ce ma auren saurayi da budurwa wato yanzu sun kwashe sama da shekaru tamanin suna raye tare da juna,to wani lokaci in na tsaya na dubi rayuwarsu ga tsufa kuma jiki yayi rauni ta kowace fuska,in ce ikon Allah mutum yana ro}on Allah yayi masa yawancin kwana amma kuma in har ya samu haka to yana da nashi matsalolin.Saboda haka irin wa]annan lokuta muhimmai yana da gayar muhimmanci mutum ya ribace su idan sun zo,in mutum ya bibiyi rayuwar bayin Allah Ta’ala zamu ga cewa basu wasa da irin wa]annan lokuta masu albarka,misali mu duba yadda Sayyid Zakzaky[H] ya bu}aci da a ]aga lokacin aiki da za a yi na idonsa saboda bai son ya rasa ayyukan ibadodin nisfu shaaban,wannan darasi ne babba garemu.

Insha Allah bayanai zasu gudana kan wannan maudu’i na ibadodin layalil qadr kan wa]annan ababe:

1-Sallar neman dacewa da lailatul Qadr.

2-Tarihin asalin lailatul Qadr.

3-Falalar daren lailatul Qadr.

4-Alamomin daren lailatul Qadr.

5-Muhimmancin raya daren.

6-Ayyana daren lailatul Qadr.

7-Ayyukan daren lailatul Qadr.

          1-SALLAR NEMAN DACEWA DA LAILATUL QADR: Akwai Hadisi da aka ruwaito daga Manzon Allah[S] na yin wata sallah,ya zo akan cewa duk wanda ya yi sallar to zai samu muwafa}ar samun daren lailatul Qadr.Yadda sallar take shine:Raka’a ce guda hu]u kuma za a yi ta bayan sallar Isha’i ne,kowace raka’a bayan karanta Fatiha mutum zai karanta {ulya ayyuhal kafirun sau ukku da kuma {ulhuwallahu shima sau ukku,bayan mutum ya sallame zai ce ‘Astagfurullah’ sau 13 amma sallama guda ake yi a sallar,wato idan mutum ya yi raka’a biyu maimakon ya sallame idan ya yi tashahhud-tahiya-to zai mi}e ne ya ciko raka’a biyu bayan tahiya sai ya sallame.A cikon Hadisin Manzon Allah ya ce na rantse da wanda ya aiko ni da Annabta duk wanda ya yi wannan sallar to sai ya samu dacewar lailatul Qadr.Saboda haka yana da gayar muhimmanci kada mutum ya bar wannan sallar ta ku~uce masa,kuma lokacinta tun daga kamawar watan Ramadan ne har ya zuwa kwanukan layalil Qadr.

          2-TARIHIN ASALIN LAILATUL QADR:Idan mutum ya yi bincike dangane da asalin lailatul Qadr zai ga cewa wata baiwa ce da kuma kyauta da Allah Ta’ala ya yi ma Bani Adam da ita,saboda haka akwai ta a alummomin da suka gabaci wannan alumma ta Manzon Allah,sai dai banbanci shine a wancan lokacin ta kan kasance a duk shekara ]ari sau ]aya ake yinta,wato sa~anin wannan alumma ta Manzon Allah wadda take kasancewa a kowace shekara.A wata ruwaya kuma yazo akan cewa wani Mala’ika ya shaida ma Manzon Allah cewa,wani mutum daga cikin Bani Isra’ila ya ]auki makami wata dubu yana jihadi dashi a tafarkin Allah,sai Manzon Allah ya ji mamaki ya kuma yi fatan haka ya kasance cikin alummarsa,shine ya yi addu’a ya ce, “Ya Ubangiji ka sanya al’ummata tana da gajerun shekaru da kuma }arancin aiki,to shine Allah Ta’ala ya bashi lailatul Qadr.”Wato daga cikin abubuwan da suka banbanta wannan alumma da kuma alummun da suka gabace ta akwai yawan shekaru,a wancan lokacin mutum sai ka ga ya rayu a duniya shekaru dubu ko dubu biyu da dai sauransu,saboda a lokacin ]an shekaru 300 ko 500 yana ganin shi yaro ne,kyakkyawan misali mu duba Annabi Nuhu ya zo a ruwaya cewa ya rayu shekaru 2,500 ne a duniya,ya yi shekaru 850 a duniya kafin aiko masa da sa}o,ya kwashe shekaru 950 yana Da’awa,ya kwashe shekaru 700 bayan an halakar da mutanensa,amma ‘yan wannan alumma ta Manzon Allah ]ai ]ai suke wuce shekaru ]ari a duniya,wanda Allah Ta’ala ya yi ma tsawon rai a wannan alumma ta Manzon Allah shine Imam Mahdi[AF] a yanzu yana da shekaru 1,182 ne a duniya.A kan wannan asasi lailatul Qadr Allah Ta’ala ya bada kyautarsa ga wannan alumma ta Manzon Allah kowace shekara saboda samun cike gi~i na shekaru in an kwatanta da alummun da suka gabata,misali a ce ka rayu shekaru 50 ko 60 ko 70 a duniya kuma ka samu muwafar lailatul Qadr guda 30 a rayuwarka,to mutum ya lissafa wata dubu sau 30 zai ga shekaru ne masu yawa.Saboda haka yana da muhimmanci idan watan Ramadan ya kama to mutum ya yawaita addu’oi na neman dacewar lailatul Qadr domin samun wannan falala mai yawa.         

          3-FALALAR DAREN LAILATUL QADR:Babu wani dare daga cikin dararen shekara da ya kai daren lailatul Qadr falala da kuma daraja,mu duba a yadda ya zo a nassin Al}ur’ani mai girma cewa yafi alhairi daga wata dubu.Daren lailatul Qadr dare ne da Allah Ta’ala yake hukumta dukkan abun da zasu auku a cikin shekara kyakkyawa ne ko mummuna, wato a matsayi na ]ai-]aiku da kuma jama’a baki ]aya saboda haka duk abun da zai samu mutum a shekara to a daren ne ake }addara shi mai kyau ko marar kyau.Haka nan kuma a daren lailatul Qadr ne ake tantance duk wa]anda zasu mutu a shekarar.Haka nan a daren lailatul Qadr ake ba Mala’iku sababbin takardu da zasu rubuta aikin kowane mutum na shekara baki ]aya.Manzon Allah[S] ya ce, “Allah Ta’ala a cikin ranaku ya za~i ranar Jumma’a,a cikin watanni ya za~i watan Ramadan,a cikin darare to ya za~i daren lailatul Qadr.”Imam Sadi}[AS] ya ce, “Ruhi da kuma zuciyar watan Ramadan shine lailatul Qadr.”

          4-ALAMOMIN DAREN LAILATUL QADR:Daren lailatul Qadr yana da wasu alamomi da suke nuna cewa shine ko bashi bane,wa]annan alamomi sun zo ne a ruwayoyi na Hadisi da aka ruwaito daga Manzon Allah da kuma Aimma na Ahlul bayt[AS],ga wasu daga cikin Hadisan:Manzon Allah ya ce, “Daren lailatul Qadr dare ne wanda ba sanyi a cikinsa haka nan kuma ba zafi wato tsaka-tsaki,haka nan kuma washe-garinsa rana zata fito fes.”Haka nan an tambayi wani daga cikin Aimma na Ahlul bayt dangane da lailatul Qadr sai ya ce, “Alamarta shine iska zata yi da]i a daren,in lokacin sanyi ne to sanyin zai sau}a}a,in kuma lokacin zafi ne to zafin zai sau}a}a.Haka nan yazo akan cewa a daren za a ji }arancin haushin karnuka da kuma hayaniya na jama’a.

          5-MUHIMMANCIN RAYA DAREN LAILATUL QADR:Yana da gaya-gayar muhimmanci ya kasance daren lailatul Qadr baki ]ayansa wato tun daga farkonsa har }arshe mutum ya kasance bai yi barci ba,ya kasance ya raya daren da ibadodi dabam dabam,kai koda a ce bai yi ibadodi ba mujarradin daren bai runtsa ba saboda albarkacin daren to yin haka yana da falala masu yawa,ko da ma a ce babu Hadisai da suka zo akan haka to kasantuwarsa dare ne da ake }addara al’amura na shekara ga bawa,to bai kamata a ce mutum ya kwashe daren yana shararar barci ba,to ballantana kuma akwai Hadisai masu yawa da aka ruwaito wa]anda suke nuni ga falalar raya shi,ga wasu daga ciki:An ruwaito daga Imam Ba}ir[AS] ya ce, “Duk wanda ya raya daren lailatul Qadr to Allah Ta’ala zai gafarta masa zunubansa baki daya.” Imam Kazim[AS] ya ce, “Duk wanda yayi wanka daren lailatul Qadr saannan ya raya daren har ya zuwa ketowar alfijir to zai tsarkaka daga zunubansa baki daya.”

            6-AYYANA DAREN LAILATUL QADR:Akwai zantuka dabam dabam na wane dare ne na lailatul Qadr tsakanin Malaman Ahlul bayt da kuma na Ahlus-sunna.A mahanga ta Ahlul bayt daren lailatul Qadr ya kan kasance ne a ]ayan darare ukku sune:Daren 19,21 da kuma 23 amma an fi }arfafawa a daren 23 ne.An tambayi Imam Sadi} dangane da daren lailatul Qadr sai ya ce a nemeta a daren 19, 21,23, aka tambaye shi wane mutum zai fi }arfafawa a cikinsu ya ce daren 23.A mahanga ta Ahlus-sunna daren lailatul Qadr ya kan kasance ne a ]ayan wa]annan darare sune:Daren 21,23,25,27 da kuma 29 amma a wajensu sun fi }arfafawa akan daren 27 ne.Wannan sa~anin na sunna da shi’a kan wannan al’amarin ya kasance kan asasin ruwayoyi na Hadisai da suka zo na wa]annan makarantu guda biyu,idan mutum ya ha]a ruwayoyin yayi amfani dasu duka babu laifi,ko ba komai akwai ruwaya da tazo na nuna muhimmancin }ara }aimi wajen ibada a goman }arshe na watan Ramadan,shi yasa ma al’amarin Iitikafi a goman }arshe ya zo.

          7-AYYUKAN DAREN LAILATUL QADR:Ayyukan ibadodi da ake aikatawa a dararen lailatul Qadr sun kasu kashi biyu,kashi na farko sune ayyukan da ake aikatawa a kowane dare cikin darare ukku da aka ambata wato 19,21,23.Kashi na biyu sune wa]anda suka ke~anta a kowane dare misali daren 19 na da nasa,haka na 21 da kuma 23.Ga mai bu}atar ganin wa]annan ayyuka na ibadodi sanka-sanka yana iya duba littafin, ‘Minhajul jinan fi a’amali shahari Ramadan’ wannan littafi yana da gayar muhimmanci mutum ya mallake shi,saboda idan mutum ya yi bincike zai ga kusan babu wani littafi da ya tattaro ibadodin watan Ramadan baki ]aya kamarsa,kuma alhamdu lillahi ana samun littafin,mawallafin littafin shine Ayatullahi Sayyid Abbas Alkashaniy,Kashan wani gari ne kusa da birnin Qum.Ga wanda bai da littafin yana iya duba sauran littafan Addu’oi kamar Mafatihul Jinan zai ga ayyukan dai dai gwargwado.Amma ga wasu daga cikin ibadodin da ake son yi a wannan dare mai albarka.Ibadodin da ake yi a cikin kowane dare cikin ukkun sune:

1-Wanka:Wato mutum zai yi shine shigen yadda yake wankan Janaba.

2-Sallah:Raka’oi ne guda biyu,kowace raka’a bayan fatiha mutum zai karanta {ulhuwallah so bakwai.Akwai kuma Sallah raka’a 100 bayan fatiha ana so mutum ya karanta {ulhullahu sau goma ko bakwai ko biyar ko ukku,ko a}alla sau ]aya,in mutum ba zai iya wa]annan raka’oi 100 a tsaye ba to zai iya yinsu a zauna ne,ko kuma ya yi wasu a tsaye wasu kuma a zaune.Haka nan kuma akwai addu’oi da ake yi bayan kowace raka’a biyu na wannan sallah mai raka’a 100,da yake littafin Mafatihu da kuma Diya’us-salihin ba a kawo addu’in ba mutum iya duba su a littafin I}bal ko Misbahul mutahajjid ko kuma littafin Addu’oin nafilolin watan Ramadan na Sayyid Zakzaky[H]. Wa]annan salloli na raka’oi 100 suna cikin sallah na raka’a 1000 da ake so kowane mumini ya yi a watan Ramadan ne,kuma wa]annan raka’oi 1000 sune sallar Asham a mahanga ta Ahlul bayt,ga yadda suke sanka sanka:Tun daga daren farko na watan Ramadan mutum zai fara sallar,bayan ya yi sallar magariba da nafilolinta sai ya tashi ya yi raka’oi 8,bayan kuma ya yi sallar Isha’i da nafilolinta sai ya yi raka’oi 12,kullum haka mutum zai ta yi har ya zuwa daren 20 ga watan Ramadan.To a daren 21 zuwa daren 30 ga watan Ramadan 8 ta bayan magariba tana nan babu canji,amma na bayan Isha’i akwai canji,maimakon 12 da ya saba yi to yanzu zai dunga yin 22 ne bayanta,haka nan kuma a dararen 19,21,23 bayan wa]annan zai kuma yi raka’oi 100.To in ka ha]a su baki ]aya zaka ga sun tashi raka’oi 1000,misali tun daga daren farko har zuwa daren ishirin raka’oi 20, to 20 so 20 ya kama 400.daren 21 zuwa na 30 kullum raka’oi 30, to 30 so 10 ya kama 300,idan an ha]a sun kama 700,to ga kuma wa]annan raka’oi 100 na kowane dare na lailatul Qadr 300, kenan in an ha]a zai bada 1000 kenan.Wani tambihi anan shine so da yawa akan rasa raka’oin daren farko saboda galibi akan ji labarin ganin wata bayan sallar Isha’in ne,saboda haka hanya guda na magance wannan matsala itace,mutum na sallar magariba na daren da za a yi duban wata mutum ya faro wa]annan salloli,sai ya kasance in an ga watan kai dama Alhamdu lillahi ka fara ayyukan watan Ramadan ]inka in kuma ba a gani ba to kana da ladar nafilolin da ka yi.

3-Karanta Addu’ar Jaushan.

4-Karanta ziyarar Imam Husain[AS].

5-Karanta Addu’ar Tawassuli da Al}ur’ani wato wanda ake yi bayan an ]ora Al}ur’ani akai da dai sauransu.Sai kuma ayyukan da ake aikatawa cikin kowane dare na wa]annan darare guda ukku ana iya duba su cikin littafan da aka ambata misali a daren 23 ana son karanta Suratul Ankabut da kuma Suratu Rum.

          Daga }arshe a wa]annan darare na layalil Qadr mu }ara }aimi na yin Addu’oi kan wa]anda suka afkar da wannan wa}i’a da kuma shahidanmu da kuma ‘yan uwan da aka raunata da kuma ‘yan uwan da suke tsare wa]anda suka bayyana garemu da kuma wa]anda basu bayyana ba da kuma kawukanmu.Muna ro}on Allah Ta’ala ya kar~i ibadodi da kuma Addu’in da muka yi a wannan wata na Ramadan ya kuma saka mu cikin ajin bayinsa wa]anda zasu fita cikin wannan wata na Ramadan da Satifiket na Ta}awa.

         

 
Home Maudu'oi daban-daban Ibadodin laylatul Qadr.
Copyright © 2022. www.tambihin.net. Designed by KH