Thursday, 27 January 2022
Email
Make My Homepage
RSS
Register
Karamomin Sayyid Zakzaky (H) Print E-mail
Written by administrator   
Sunday, 19 June 2016 12:07

Kasantuwar wannan wata da muke ciki na Shaaban wanda a ranar Talata 15 ga watan ne shekara ta 1372 Hijiriyya aka haifi Sayyid Zakzaky,a yanzu kenan Sayyid yana da shekaru 65 a duniya,ya kuma faro wannan Da’awa tun yana da shekaru 25 ne wato yanzu ya kwashe shekaru 40 cur yana wannan kiran.To a dai dai wannan lokaci na munasabar haihuwarsa ‘yan uwa sun saba rubuce-rubuce kan janibobi dabam daban na rayuwarsa mai albarka.Insha Allah wannan rubutu zai gudana ne kan Karamominsa.

          Sayyid Zakzaky Allah Ta’ala ya yi masa ni’imomi da kuma baiwowi masu yawa,daga cikin wa]annan ni’imomi akwai karamomi.Karama kamar yadda aka sani Allah Ta’ala kan yi ta ga za~a~~u daga cikin bayinsa salihai wato waliyyansa.Saboda haka karama tana da banbanci da Mu’ujiza,]aya daga cikin banbancin shine ita Mu’ujiza ta kan ke~anta ga Ma’asumai ne misali Annabawa da kuma Aimma ita kuma Karama ta kan ke~anta ga waliyyan Allah Ta’ala ne,kuma su galiban basu cika bayyannata ba amma ita Mu’ujiza ma’abutanta sukan bayyana ta domin su tabbattar da Annabtarsu ko Imamancinsu.Kuma karama da Allah Ta’ala ya ke yi ma bayinsa ta kan kasance ta fuskoki dabam dabam,wato wani bawan Allah ka ga yana da karama kaza da kaza wani kuma kaza da kaza.To Sayyid Zakzaky daga cikin karamomin da Allah Ta’ala ya yi masa akwai amsar addu’a,wato idan ya yi addu’a Allah Ta’ala na amsa.Akwai misalai da dama akan haka musamman ma addu’oinsa ga Azzalumai, wanda ya zauna dashi zai ba da shaida akan haka.

Daga cikin karamomin Sayyid Zakzaky akwai kashafi,shima wannan wanda ya zauna tare da shi zai tabbatar da haka,misali zaka ga duk wani }ulle-}ulle da makirce makirce da ma}iya suka shirya sai ka ga ya tona asirinsu,hatta su abin na basu mamaki suga cewa sun shirya wani shiri,amma kafin su aiwatar sai su ji Sayyid Zakzaky ya tona asirinsu.

Daga cikin karamomin da Allah Ta’ala ya yi ma Sayyid Zakzaky akwai samun albarka ga dukkan al’amuransa,wato duk abun da ya kasance a ciki ko yasa hannu akai to ko abun sai ya yi albarka.

Daga cikin karamomin Sayyid Zakzaky akwai cewa idan yayi hasashen abu,to abun da yayi hasashen sai ka ga daga }arshe ya tabbata,alal misali wannan wa}i’a da muke ciki yanzu tun gabanin ta faru Sayyid Zakzay yayi hasashenta da yadda wa]anda suka afkar da ita zasu yi da na sanin da basu yi ba,misali ga wani hasashensa da yayi a wani jawabi da ya yi tun ma aukuwar wa}i’ar da lokaci mai tsawo, “Idan shawara za mu ba ku,sai mu ce,kada ku yi kuskuren ]aukar matakin }arfi.Amma idan kuka yi kuskure kuka yi,to albishirinku da hasarar duniya da lahira.Albishirinku,za ku tanbatsa al’amarin ta in da ba ku zato.Kuma wallahi tallahi! Sai kun yi da na sani.” Ashe wannan abun da su ka yi bai tambatsa wannan al’amari ba a sassan duniya.Kuma mu duba yadda wa}i’ar ta zama ala}ai}ai ga wa]anda suka ba da umarnin a afkar da ita,wato dai wa]annan maganganu na hasashen Sayyid sun tabbata.

Daga cikin karamomin Sayyid Zakzaky akwai rashin tsoro,duk wanda ya zauna tare dashi ko ya sanshi zai tabbatar maka da haka kai hatta ma}iyansa sun tabbatar da haka na cewa lalle shi jarumi ne bashi da tsoro,kuma wannan rashin tsoronsa ya yi tasiri da kuma naso ga mabiyansa,kyakkyawan misali mutum ya duba irin dakewa da almajiransa suka yi a lokacin wannan wa}i’a,ta wani malami ya ce in da shine aka kai ma hari irin na Malam Zakzaky to da sai dai a yi dalar takalma ba gawawwaki ba,wato almijiransa za su gudu su barshi ne. A ta}aice dai Sayyid Zakzaky yana da karamomi masu yawa.

          Idan kuma muka juya kan halin da Sayyid yake ciki wato kasantuwarsa a tsare to wannan sunna ce ta Annabawa da Aimma[AS] da kuma duk wa]anda Allah Ta’ala ya yi amfani dasu wajen jaddada Addini,alal misali daga cikin Aimma na Ahlul bayt da aka kama aka tsare akwai Imam Zainul-Abidin[AS] da Imam Muhammad Al-Baqir[AS] da Imam Musa Al-kazim[AS] da Imam Aliy Al-hadi da kuma Hassan Al-askari[AS] dukkan wa]annan Imaman da aka ambata sun yi zaman kurkuku,bilhasali ma Imam Kazim shekararsa goma sha bakwai a cikin kurkuku kai a cikin ma kurkuku ya rasu.

          Saboda haka idan mutum ya bibiyi tarihin wannan Harka Islamiyya zai ga cewa hukumar wannan }asa ta Nigeria tun farkon wannan da’awa da Sayyid Zakzaky ya faro suka soma kama shi,wato dai tun yana ]alibi a jami’ar Ahmadu Bello aka soma kama shi da kuma tsarewa.Kamun farko da aka yi ma Sayyid Zakzaky shine a 1979,wato lokacin yana shekerar }arshe a Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zaria,a lokacin yana ma rubuta jarabawarsa ta kammalawa ne,saboda haka ya soma rubuta wa]ansu faifofi bai kammala ba aka kama shi,da aka kama shi aka tsare shi a Police-Station na ‘yan sanda a Zaria,wani abin mamaki ma a wannan tsarewar da suka yi ma Sayyid Zakzaky shine cewa sun yi kwanaki a}alla kwana ukku basu bashi abinci ba,amma kuma wani iko na Allah Ta’ala a cikin wa]annan kwanaki Sayyid Zakzaky yake cewa bai ji abin da ake cewa yunwa ba,saboda haka bai bu}atu da su bashi abinci ba.Allah Akbar ‘yan’uwa mu duba yadda wannan gwagwarmaya ta faro,shi yasa a lokacin da ‘yan sandan suka fito da Malam daga cikin cell domin su yi masa tambayoyi abun ya basu mamaki,har suna cewa,abun mamaki kamar wanda bai sha yunwa ba,wanda yake nuna ke nan ashe da gangan suka hana Malam abinci.Wannan abu ya faru a zamanin gwamnatin mulkin soja,}ar}ashin shugabancin General Obasanjo.Bayan haka kuma an tsare Sayyid Zakzaky a garin Sokoto a 1981 wanda daga baya aka yenke masa hukunci na zuwa kurkun Inugu na tsawon shekaru hu]u,saboda haka daga 1981 zuwa 1984,Malam yana kurkun Inugu ne,kuma wannan shine karon farko na zartar ma Malam ]auri na zaman kurkuku a tarihin wannan Harka.Wannan abu ya faru ne a zamanin gwamnatin farar hula,}ar}ashin jagorancin Alhaji Shehu Shagari.Sai kuma a }arshen 1984 aka kama shi aka kai shi Lagos aka tsare shi a Kiri-kiri.Wannan ya auku a zamanin gwamnatin mulkin soja,}ar}ashin shugabancin General Muhammadu Buhari,wani tambihi a nan shine a lokacin da yake tsare ne a mulkin Buhari a wancan lokacin aka haifa masa ]ansa na farko wato Sayyid Muhammad a 1985,yau kuma gashi lokacin auren babban ]an nasa da aka yi a wannan wata na Shaaban yana tsare a mulkin farar hula na Muhammadu Buhari wanda in mutum yayi tunani zai ga cewa ita ma wannan wata jarabawa cewa babba.

Sai kuma a 1987 aka sake kama shi aka tsare a kurkukun Port Harcout,ya fito daga kurkukun a 1989.Wannan kamun ya faru ne a zamanin gwamnatin mulkin soja }ar}ashin shugabancin Generar Ibrahim Babangida.Sai kuma a 1992 aka sake kama Malam a filin jirgin sama na Kano,lokacin zai yi tafiya ne zuwa Ingland kan wani program na addinin musulunci da aka gayyace shi.Bayan an kama shi aka kai shi Lagos,saannan kuma aka wuce dashi Kiri-kiri,amma tsarewar ba ta yi tsawo ba,kimanin mako guda ne.Wannan ya auku a zamanin mulkin soja,}ar}ashin shugabancin Babangida.Sai kuma a shekarar 1996 aka sake kama Sayyid Zakzaky aka sake kai shi kurkukun Port Harcout,ya fito daga kurkukun a shekarar 1998.Wannan ya auku ne a zamanin gwamnatin mulkin soja,}ar}ashin shugabancin General Sani Abaca.A takaice dai daga shekarar 1981 zuwa 1998 Sayyid Zakzaky ya kwashe sama da shekaru goma a kurkuku dabam dabam na }asar nan.Haka nan ya zauna a gidajen kurkuku dabam daban na arewaci da kuma kudancin }asar nan har guda tara.

        To tun daga 1998 har ya zuwa shekarar 2015,ba a sake kama Sayyid Zakzaky ba ko aka tsare shi sai a ranar Litinin 14 ga watan Disemba 2015 wato an samu tazara ta shekaru kusan 18.Saboda haka in mutum ya lura zai ga cewa tun da Malam ya faro wannan Harka,ba a ta~a samun lokaci mai tsawo wanda ba a kama shi ba aka tsare sai wannan lokaci.Amma fa a lura cewa ba yana nufin cewa Gwamnatocin da suka biyo bayan na Abaca sun ha}ura daga makirce-makirce da }ulle-}ulle ga wannan Harka ba ne.A’a sun lura ne cewa duk kame-kame da suka yi ma Sayyid Zakzaky a baya,ya da]a ha~aka abin da yake kira akai ne.A kan asasin haka suka ga cewa wannan kamun da ]auri bai da wani amfani ga manufarsu,saboda haka sai suka canza salo da kuma makirci,wannan sabon salon shine yun}urin kashe Sayyid Zakzaky,shi yasa in muka duba a cikin wa]annan shekaru da aka samu tazara na rashin kama Malam,babban abun da suka sa ma gaba shine kashe Malam ta halin ko }a}a.Zamu ga sun yi }ulle-}ulle da makirce-makirce iri-iri domin su cimma wannan manufa tasu,amma Allah Ta’ala bisa ikonsa duk ya wargaza shirin nasu.Kyakkyawan misali mu duba irin shirin da aka yi na kashe Malam zamanin mulkin Alhaji Umaru Musa ‘yar’aduwa.Mu kuma duba shiri dabam dabam da aka yi zamanin mulkin Good lock Jonathan domin kashe Malam,amma duk Allah Ta’ala ya kare Malam ya kuma wargaza shirinsu.

          Idan ma mutum bai san wa]ancan ba to ya duba abunda ya faru a wannan wa}i’a da muke ciki yadda aka yi amfani da }arfin da ya wuce }ima kuma ya sa~a ma hankali kan a kashe Sayyid da mabiyansa aga kuma bayan Harka Islamiyya,to tambaya an cimma wa]anna manufofi? Wanda wannan ka]ai ya isa ya nuna ma duk wani mai hankali da basira cewa lalle wannan Malami ga dukkan alamu Allah yana tare dashi da kuma al’amarinsa,mu duba yadda aka kwana aka wuni ana ta lugudan wuta saboda akai zuwa gareshi,aka kashe ‘yan uwa masu yawa da kuma raunata adadi masu yawa aka kuma kama da dama daga cikinsu,daga }arshe aka cinna ma gidan wuta amma bisa tsarewa da kuma kariya ta Allah Ta’ala ba abunda ya samu Malam da iyalinsa a lokacin,haka Malam ya kwana a cikin gidan bisa kariya ta Allah Ta’ala har ya zuwa wayewar garin safiyar litinin,saannan suka ce sun samu bayanai na asiri akan cewa Malam na cikin gidan,wanda wannan in mutum yayi tunani zai ga cewa wannan karama ce babba ga Malam,haka nan da suka iso wajen Malam suka bu]e wuta ga iyalinsa nan take suka kashe ‘ya’yansa guda ukku,suka harbi matarsa,saanan shima suka har-har-be shi a duk in da suke ganin makisa ne,amma saboda Allah Ta’ala ya nuna shine mai iko ne akan kome kuma komi da izininsa yake aukuwa ya kautar da in da aka nufa zuwa ga wasu wajaje a jikinsa.Mutum yayi tunani a ce Malamin nan tun 1978 aka soma yun}urin akashe shi har ya zuwa yanzu bai kasu ba anya wannan ba wata ajiya bace ta Allah Ta’ala ba, sai ranar da yaso zai ]auki abinsa.Idan mutum ya bibiyi tarihin wa]anda Allah Ta’ala yake amfani dasu wajen jaddada addininsa zai ga cewa yana basu kariya ta musamman wadda ba a saba ganin irinta ba a al’ada,alal misali mutum ya karanci tarihin Shehu Usman ]an Fodiyo da kuma na Imam Khumaini yaga yadda masu tafi da iko na zamunnasu suka yi ta yun}urin kashe su amma Allah Ta’ala ya kare su.Haka nan mu duba yadda Sayyid Zakzaky ya faro wannan da’awa tun yana shi ka]ai ya samu wa]anda suka amsa masa har suka kai gomomi,suka kai ]aruruwa,suka kai dubbani,yau gashi sun kai miliyoyi,wanda in mutum yayi tunani zai ga cewa wa]anda aka faro wannan da’awa dasu yanzu suna matsayin kakanni ne,wato sun haifi ‘ya’yansu a cikin wannan da’awa,’ya’yan da suka haifa suma sun haifa,amma saboda tsuke tunani da kuma rashin hangen nasa jama’ar da suka kai wannan mustawa a ce za a kauda su baki ]aya.In mutum yayi tunani zai ga cewa mafi yawan wa]anda aka karkashe a cikin wannan wa}i’a ‘ya’yan ‘yan uwa ne wato su a cikin gwagwamaryar aka haife su,wanda shi kan shi wannan kyakkyawan fata ne da kuma albishir cewa wannan gwagwamarya da aka faro ta tabbatar da addini to ko bayan ba iyayen za ta cigaba har ya zuwa lokacin da Allah Ta’ala zai hukunta nasara.Kuma wannan nufin shafe ma’abuta Harkar da aka so ayi to bawai ]aya bisa ]ari ba,to ko ]aya bisa dubu na ma’abuta Harkar ba a kashe ba.Saboda haka wannan al’amari in dai mutum bai ce yin Allah bane to ba abunda zai ce.Shi yasa wani lokaci in mutum yayi tunani zuzzurfa zai ga cewa su masu afkar da irin wa]annan wa}i’oi sune abun tausayi a duniya da lahira,saboda suna fa]a da Allah Ta’ala ne amma basu sani ba,fa]a da Allah shine fa]a da Addinninsa,fa]a da Addini shine fa]a da ma’abuta addini,shi yasa sai dai mutum ya yi iyaka duk zaluncin da zai yi,ya gama zamaninsa ya wuce kafin wani shima yazo yayi nasa, amma kuma abun da ya yi fa]an yana nan kuma yana cigaba,mu dai duba gwamnatoci dabam dabam da aka ambata wa]anda suka kama Malam suka tsare yau duk abun ya zama tarihi,to haka shima wannan da aka yi yanzu zai zama tarihi,saboda haka lalle wannan abun tausayi ne a ce a duniya ka yi fa]a da abunda ba za ka samu nasara ba wajen kauda shi,bilhasali ma matakan da ka ]auka na cutarwa da kuma gallazawa shine yake taimaka ma cigaban abun da kake so ka kawar,misali ita wannan wa}i’ar da aka afkar mu duba yadda al’amarinta ya watsu a sassan duniya dabam dabam, wanda da ba a yi ba, to da haka bai faru ba,wannan a duniya kenan a lahira kuma azabar Allah tana jira,mu duba abun da Allah Ta’ala ya ce a cikin Al}ur’ani mai girma a suratu Nisa’i aya ta 93 ga duk wanda ya kashe muumini, “Duk wanda ya kashe muumini da gangan to sakamakonsa,1-Jahannama.2- kuma zai tabbata a cikinta.3-Kuma Allah ya yi fushi dashi.4-Kuma ya tsine masa.5-Kuma ya yi masa tattalin azaba mai girma.A wajen Allah Ta’ala wannan shine sakamakon dake jiran duk wanda ya kashe muumini da gangan.Shiyasa wannan abun da aka yi na kar-kashe bayin Allah maza da mata yara da manya ake ta kuma rufa-rufa akai,to tambaya anan itace idan an ~oye ma mutane za a iya ~oye ma Allah ne? Mutun ya auna da hankalinsa ba wai mutane ba ko da dabbobine a ce ka kama su ka kashe guda ]ai ]ai har 347 saannan kaje ka ha}a rami ka binne su,duk mai hankali zai ga cewa lalle baka kyauta ba to ballantana a ce mutane.Saboda haka wannan abun da aka yi tarihi ba zai manta dashi ba.Kuma wa]anda suka afkar dashi su shirya fuskantar Hisabi gaban Allah Ta’ala ranar }iyama,saboda haka da]in abun ko bajima ko bada]e mutum sai ya koma ga Allah Ta’ala,kuma duk abinda ya aikata zai yi masa hisabi akai saboda haka lahira ita ce abun ji,kuma a wajen hisabi babu abinda ya fi tsanani da hatsari kamar na jinin da aka zubar ba tare da ha}}i ba.Saboda haka idan mutum ba zai yi wannan Harka Islamiyya ba,to ya fi mashi alhairi ya zama ]an kallo da ya zamanto kai ba ka yi kuma kana fa]a da masu yi,domin addini ake yi kuma lahira ake nema ba duniya ba.Saboda ranar }iyama akwai hisabi iri biyu da za a yi ma mutane,akwai hisabi na ]ai-]aiku,akwai kuma hisabi na al’umma,hisabi na al’umma shine Allah Ta’ala zai tambaye mu ya aiko mana da Manzo? Ya zo mana da sa}o? mun yi aiki da sa}on? Amsa ya aiko mana da Manzo shine Annabi Muhammad[S] ya zo mana da sa}on Al}ur’ani,to yanzu ana aikata wannan Al}ur’ani a matsayinmu na al’umma? To wannan shine kiran da Sayyid Zakzaky[H] ya kwashe shekaru arba’in kenan yana yi na cewa jama’a su zo su aikata wannan karantawar ta Al}ur’ani a matsayinsu na ]ai ]aiku da kuma al’umma,kuma akan haka ne shi da wa]anda suka amsa masa tsawon wannan shekaru suke fuskantar }iyayya da gaba da cutarwa iri-iri.Kuma kira irin wannan in ya bayyana mutane sukan kasu gida ukku sune:1-Wasu su amsa kiran.2-Wasu su yi fa]a da kiran.3-Wasu kuma su zama ‘yan kallo,to gara mutum in har ba zai amsa kiran ba ya zama ]an kallo da ya zama mai fa]a dashi,domin mutum ya bibiyi tarihin wannan Harka ya ga wa]anda suka yi fa]a da ita misali masu mulki ne,ko masu ku]i,ko malamai da dai sauransu ya ya Allah Ta’ala ya ke hukumta }arshensu,wato galibi basu kwashewa da duniya lafiya kuma hakan ya kan kasance sanadiyyar lalacewar al’amuransu na duniya. Kuma kowanne cikin ukkun nan ranar }iyama zai samu sakamako mummuna ko kyakkyawa na gudunmawar da ya bayar.Saboda haka lahira ita ce abin ji ba duniya ba.

          Daga }arshe wannan wata na Ramadan da Allah ya kawo mu dama ce da kuma fursa babba garemu na neman kusanci ga Allah Ta’ala da kuma kai kukanmu gareshi na zaluncin da aka yi mana da kuma tsarkake kawukanmu.Wato dai kowannenmu ya nunnuka ibadodinsa da kuma Addu’oinsa kan yadda ya saba a shekarun baya a irin wannan wata mai albarka.Muna ro}on Allah Ta’ala ya kar~a mana ibadodinmu da kuma addu’oinmu.

 
Home Maudu'oi daban-daban Karamomin Sayyid Zakzaky (H)
Copyright © 2022. www.tambihin.net. Designed by KH