Hadisai Arba’in na Imam Husain[AS] |
Written by administrator | |||
Sunday, 15 May 2016 11:36 | |||
Kasantuwar wannan wata da muke ciki na Shaaban wanda a ranar Alhamis ukku ga watan aka haifi Imam Husain[AS] shekara ta hu]u bayan Hijira.Haka nan kuma a darasin Hadisai da aka saba kawowa wa]anda aka ruwaito daga Aimma na Ahlul bayt to an iso ga na Imam Husain wato an gabatar da Hadisai 40 da aka ruwaito daga Imam Ali[AS] da kuma Imam Hassan[AS],saboda haka yanzu insha-Allah za a gabatar da Hadisai 40 da aka ruwaito daga Imam Husain,a darasi na gaba a gabatar da Hadisai 40 da aka ruwaito daga Imam Sajjad haka-haka har a kai ga Insha Allah Hadisai 40 da aka ruwaito daga Imam Mahdi[AF].Imam Husain[AS] kamar sauran Aimma da suka gabace shi da kuma wadanda suka biyo bayansa babu Hadisan sa da yawa a cikin littafan Hadisai na Ahlus sunna, kai baki dayansu ma basu kai guda biyar ba,to tambaya minene ya janyo haka wato na rashin Hadisansa masu yawa,alhali akwai sa’oinsa na ‘ya’yayen sahabbai kamar Abdullahi ]an Umar ko Amru ]an As ko Abdullahi ]an Abbas da dai sauranransa suna da Hadisai masu yawa a cikin wa]annan littafai? Mutum ya binciki tarihi zai bashi amsa,ko kuma a dun}ule yana da Hadisan masu yawa amma ba a son nashi ne,in mutum yana so ya tabbatar da haka to ya binciki littafan Hadisai na ruwayoyin Ahlul bayt zai ga Hadisai masu yawa wa]anda aka ruwaito daga wajensa,saboda haka wa]annan da za a kawo wasu sashe ne na Hadisan da aka ruwaito daga wajensa. 1-An ruwaito daga Imam Husain[AS] ya ce,Manzon Allah[S] y ace, “Duk wanda ya sunnata wata sunna kyakkyawa to yana da ladarta da kuma ladar duk wanda yayi aiki da ita har ya zuwa ranar tashin }iyama.” 2-An ruwaito daga Imam Husain[AS] ya ce, “Babu wani wanda zai kasance cikin aminci a ranar }iyama fa ce wanda ya ji tsoron Allah a Duniya.” 3-An ruwaito daga Imam Husain[AS] ya ce, “Kashedinka daga zaluntar wanda bai da wani wanda zai taimake shi in ba Allah Ta’ala ba.” 4-An ruwaito daga Imam Husain ya ce, “Kashedinka da yin abun da zai kai ka ka bada uzuri,domin muumini ba mai munanawa bane ko mai yin abun da zai bada uzuri.” 5-An ruwaito daga Imam Husain[AS] ya ce,Manzon Allah[S] ya ce, “Ka bar abinda kake kotanto ka koma zuwa ga abinda baka kotanto.” 6-An ruwaito daga Imam Husain[AS] ya ce, “Marowaci shine wanda ya yi rowa da sallama.” 7-An ruwaito daga Imam Husain[AS] ya ce, “Sallama tana da lada saba’in,tis’in da tara na ladar yana ga wanda ya fara sallamar,guda daya ladar kuma ga wanda ya maida sallamar.” 8-An ruwaito daga Imam Husain[AS] ya ce, “Duk wanda ya nemi biyan bukatarsa ta hanyar sa~a ma Allah to wannan yafi kusa ga ku~ucewar biyan bu}atarsa da kuma gaggawan zuwan abinda yake gudu.” 9-An ruwaito daga Imam Husain[AS] ya ce, “Ga wani mutumi da ya yi giba da wani a gabansa,kai ka kame daga yin giba saboda ita mummunar dabi’a ce da take iya kai mutum ga wuta.” 10-An ruwaito daga Imam Husain[AS] ya ce, “Duk wanda ya bauta ma Allah Ta’ala ha}i}anin bauta to Allah zai bashi fiye da abunda yake nema a wajensa.” 11-An ruwaito daga Imam Husain ya ce, “Lizimtar kyakkyawar ]abi’a Ibada ne.” 12-An ruwaito daga Imam Husain[AS] ya ce, “Fadin gaskiya izzane,fa]in }arya ajizanci ne.” 13-An ruwaito daga Imam Husain[AS] ya ce, “Kada ka kallafa ma kanka abunda ba zaka iya ba,kada kuma kayi alkawalin da baka da iko dashi.” 14-An ruwaito daga Imam Husain[AS] ya ce, “Yin kyauta mabu]in arziki ne,yin rowa kuma mabudin talauci ne.” 15-An ruwaito daga Imam Husain[AS] ya ce, “Mutuwa cikin izza yafi rayuwar cikin }as}anci.” 16-An ruwaito daga Imam Husain[AS] ya ce, “Kuka saboda tsoron Allah yana tseratarwa daga azabar Wuta.” 17-An ruwaito daga Imam Husain[AS] ya ce, “Mafi gajiyawar mutane shine wanda ya gajiya daga Addu’a.” 18-An ruwaito daga Imam Husain[AS] ya ce, “Duk wanda yaso Ahlul bayt saboda Allah da Manzonsa to zai kasance tare dasu ranar kiyama.” 19-An ruwaito daga Imam Husain[AS] ya ce, “Idan kaji wani mutum yana ta~a mutuncin mutane to ka yi }o}ari kada ya sanka.” 20-An ruwaito daga Imam Husain[AS] ya ce, “Abin mamaki ga wanda yake da ya}ini ga Hisabi amma kuma yana aikata zunubi.” 21-An ruwaito daga Imam Husain[AS] ya ce, “Bai kamata ga mumini ba yaga wani yana sa~a ma Allah Ta’ala bai yi inkarinsa ba.” 22-An ruwaito daga Imam Husain[AS] ya ce, “Duk wanda ya nemi yardar Allah da fushin mutane to Allah zai magance masa matsalolin mutane.” 23-An ruwaito daga Imam Husain[AS] ya ce, “Duk wanda ya nemi yardar mutane da fushin Allah to Allah zai barshi da mutanen.” 24-An ruwaito daga Imam Husain[AS] ya ce, “Mafi sharrin halin masu mulki sune gallazawa ga raunana,nuna tsoro ga makiya,da kuma rowa.” 25-An ruwaito daga Imam Husain[AS] ya ce, “Shi’armu sune wa]anda zukatansu suka tsarkaka daga dukkan hassada ko }yeta da kuma algusshu.” 26-An ruwaito daga Imam Husain[AS] ya ce, “Rayuwa tare da azzalumai halaka ne.” 27-An ruwaito daga Imam Husain[AS] ya ce, “Mutuwa a tafarkin Allah Ta’ala Sa’adane.” 28-An ruwaito daga Imam Husain[AS] ya ce, “Mutane bayin duniya ne,galibi addininsu a fatar baki ne suna juyawa dashi inda bukatunsu suka juya,idan jarrabawa tazo to masu Addini sukan }aranta.” 29-An ruwaito daga Imam Husain[AS] ya ce, “Yin sallama gabanin Magana,kada kuyi izini ga wani har sai yayi sallama.” 30-An ruwaito daga Imam Husain[AS] ya ce, “Wasu mutane sun bauta ma Allah saboda kwadayin lada to wannan itace ibadar ‘yan kasuwa,wasu kuma sun bauta ma Allah saboda tsoron u}uba to wannan itace ibadar bayi,wasu kuma sun bauta ma Allah saboda godiya gareshi to wannan itace ibadar ‘ya’ya kuma itace mafificiyar ibada.” 31-An ruwaito daga Imam Husain[AS] ya ce, “Mai hankali baya bada labari ga wanda yake tsoron zai karyata shi.” 32-An ruwaito daga Imam Husain[AS] cewa ya kasance kowace rana yana yin sallah raka’a dubu ta nafila,haka nan kowace rana a watan Ramadan yana sauke Alkur’ani mai girma.” 33-An ruwaito daga Imam Husain[AS] cewa, ya yi aikin Hajji a rayuwarsa har sau 25,kuma ya kasance ya kan tako ne a kafa tun daga Madina har zuwa Makka ba tare da ya hau dabba ba.” 34-An ruwaito daga Imam Husain[AS] cewa ya kasance mai yawan sadaka da kuma kyauta,ya kasance ya kan dauki kayayyakin abinci cikin kowane dare yana raba ma miskinai a cikin Madina.” 35-An ruwaito daga Imam Husain[AS] ya ce, “Allah Ta’ala shaida ne na kasance ina son Sallah,karatun Alkur’ani da yawan Addu’a da kuma Istigfari.” 36-An ruwaito daga Imam Husain[AS] ya ce, “Farin cikinka ya kasance a cikin biyayya ga Allah Ta’ala ne.” 37-An ruwaito daga Imam Husain[AS] ya ce, “Arzikin bayi yana a sama ta 4 ne,Allah Ta’ala yana saukar dashi dai dai gwargwado.” 38-An ruwaito daga Imam Husain[AS] ya ce, “Shin baku ganin yadda ba a aiki da gaskiya,ba a kuma nisantar karya saboda haka kowane Mumini yaso saduwarsa da Allah Ta’ala.”Imam Husain ya ce haka ne a ranar Ashura. 39-An ruwaito daga Imam Husain[AS] ya ce, “Istidrajin Allah ga bawa shine ya yi masa ni’imomi amma kuma bai samu muwafakar godiya ga Allah Ta’ala.” 40-An ruwaito daga Imam Husain[AS] wani ya tambaye shi ma’anar wannan Aya, “Wa amma bini’imati Rabbika Fahaddis.” Ya ce shine ka ba da labari ga ni’imomin da Allah Ta’ala ya yi maka na Addini.”
|