Friday, 28 January 2022
Email
Make My Homepage
RSS
Register
Addu’a a mahanga ta Ahlul bayt[AS]. Print E-mail
Written by administrator   
Saturday, 07 May 2016 10:23

Kasantuwar wa]annan watanni da muka shiga masu albarka na ibadodi da kuma wannan hali da yanayi da muke ciki na jarabawa wanda a tsawon tarihin wannan Harka Islamiyya ba a ta~a fuskantar irinsu ba.Wato shekaru 39 da aka kwashe a wannan tafarki na gwagwamarya,wanda shekara mai zuwa wato 2017 za a cika shekaru 40 kenan cur da faro wannan Daawa wato tun daga 1977,to tsawon wa]annan shekaru am fuskanci jarabawowi dabam dabam a kuma lokuta dabam dabam amma wannan itace mafi tsauri da aka fuskanta.Saboda haka a wannan yanayi da muke ciki bamu da wani makami da ya wuce addu’a da kuma dogaranmu ga Allah Ta’ala.Kuma lalle muna ganin tasirin wa]annan Addu’oi da kuma dogaro ga Allah Ta’ala.

          Idan mutum yayi bincike Addu’a a mahanga ta Ahlul bayt wato a bisa karantarwa ta Ahlul bayt zai ga cewa Addu’oin da aka samo daga Aimma na Ahlul bayt babu wani da aka samo irinsu a wannan al’umma ta Manzon Allah[S] wannan a bayyane yake duk wanda yayi bincike zai ga haka misali mutum ya kwatanta littafan Addu’oi da ake dasu a Shia da kuma Sunna,wato zai ga cewa littafan Addu’oi a Shia sun fi yawa kan na sunna,in mutum yayi tunani zai ga cewa }ila wannan bai rasa nasaba da irin halin da Aimma da kuma shi’arsu suka kasance na jarabawowi dabam dabam tsakaninsu da hukumomi da kuma jama’a na zamunnansu.Saboda haka duk wanda yake riyawar cewa yana bin Aimma na Ahlul bayt amma yaga babu wata jarabawa da yake fuskanta to ya binciki kansa ko dai ba tafarkinsu yake biba.Saboda dukkan Aimma da mabiyansu sun sha wahala an kuma cutar dasu ta fuskoki dabam dabam,kai baki ]ayansu daga wanda aka kashe sai wanda aka sa ma guba,kuma mutum ya tambayi kansa idan Imam Mahdi[AF] ya bayyana Gwagwarmaya zai yi domin tabbatar da Addini ko zama zai yi ya ba da karatu shike nan? Mu kuma duba tarihin Imam Khumaini yayi gwagwamarya domin tabbatar da Addini ya kuma ba da karatu.

          Idan mutum ya bibiyi littafan Addu’oi zai ga cewa addu’oi sun kasu kashi hu]u sune:

1-Na yaumiyya wato wa]anda ake karantawa kowace rana,misali na safe da yamma ko na bayan salloli da dai sauransu.

2-Na Usbu’iyya wato wa]anda ake karantawa kowace rana cikin mako,misali na ranar Jumma’a,Asabar,Lahadi……

3-Shahariyya wato wa]anda ake karantawa kowane wata misali daren farko ko ranar farko na wata, da kuma kowace rana a cikin wata kamar ranar 1,2,3,har ya zuwa 30 ga wata.

4-Sanawiyya wato wa]anda ake karantawa kowace shekara misali Addu’ar Ummi Dawud ko yaumul-mab’as ko Addu’ar sha’abaniyya ko Addu’oin watan Ramadan wato wanda in mutum yayi su sai kuma wani watan Ramadan.To ana so mutum ya dunga bibiyar wannan nizami na Addu’oi a rayuwarsa.Akwai malamai da suka rubuta littafai na Addu’oi kan kowanne daga cikin kashi hu]u na Addu’in da aka ambata,misali littafin Falahis-Sa’il addu’oin dake ciki baki ]aya na Yaumiyya ne.Akwai kuma littafin Jamalul-Usbu’i shi kuma Addu’oin dake ciki duka na mako ne.Akwai kuma littafin Duru’ul waqiya shi kuma Addu’oin dake ciki baki ]aya na Wata ne.Akwai kuma littafin Iqbal shi kuma Addu’oin dake ciki duka na Shekara ne.Saboda haka idan zai yiyu yana da kyau mutum ya mallaki wa]annan littafan domin lizimtar wa]annan Addu’oi akan wannan tsari da aka ambata guda hu]u.

            Kuma idan mutum yayi addu’a to ]ayan ukku,ko dai Allah Ta’ala ya biya ma mutum bu}atarsa a lokacin,ko ya jinkirta biyan bu}atar zuwa wani lokaci da zai fi zama alhairi ga bawan,ko kuma Allah ya tunku]e ma bawan wata musiba da ta fuskantoshi amma shi bai sani ba,saboda haka duk lokacin da bawa yayi addu’a sai bai ga biyan bu}ata ba,to ]ayan wa]annan abubuwa ukku ne da aka ambata.Wani lokaci kuma bawa zai iya yin addu’a ya zamanto Allah Ta’ala bai biya masa bu}ata ba a wannan gida na duniya,sai a ranar lahira ya bashi wani sakamako akai,har ta kai bawa yace ina ma dai dukkan addu’oinsa ba a kar~a masa ba a gidan duniya,an bashi irin wannan sakamako a yau.Amma akwai lokacin da bawa zai iya yin addu’a ya zamanto Allah Ta’ala bai amsa masa ba,wato sakamakon wani zunubi ko zunubai daga wajen bawan.Addu’a tana da ladubba da kuma ruhi kamar yadda malaman Irfan ko Akla} suka yi bayani,kuma kiyaye wa]annan ladubba sune zasu taimaka wajen amsar addu’ar bawa.Saboda haka bayani dai dai gwargwadon iko insha Allah zai gudana kan wa]annan ababe:

1-Falalar Addu’a.

2-Ladubban zahiri da ba]ini na addu’a.

3-Addu’a na tunku]e bala’oi.

4-Lokutan amsar addu’a.

5-Addu’a ga wasu ba da sun sani ba.

6-Abubuwan da suke hana amsar addu’a.

7-Illolin rashin yin addu’a.

8-Addu’ar wanda aka zalunta.

          1-Falalar Addu’a:Akwai hadisai masu yawa da suka zo da bayani kan falalar Addu’a,ga wasu daga ciki:1-Imam Ali[AS] yace, “Mafi soyuwar aiki zuwa ga Allah a bayan kasa shine Addu’a.A wani hadisi yace,Addu’a garkuwa ce ga mumini.” Idan mutum ya bibiyi tarihin Imam Ali zai ga cewa ya kasance mai yawan addu’a.2-Manzon Allah[S] yace, “Shin in nuna maku wani makami wanda zai tseratar daku daga makiyanku,ya kuma bubbugar maku da arziki? Suka ce na’am,sai Manzon Allah yace kuyi addu’a dare da rana,domin makamin mumini shine Addu’a.”3- Imam Sadik[AS] yace, “Na horeka da yin Addu’a domin ita waraka ce ga dukkan matsaloli.”4-Imam Zainul-Abidin[AS] yace, “Addu’a tana tunkude bala’i wanda ya sauka da wanda bai sauka ba.”5-Imam Kazim[AS] yace, “Lalle Addu’a tana tunkude abin da aka kaddara da kuma abinda ba a kaddara ba.”

            2-Ladubban zahiri na Addu’a:Akwai ladubban zahiri masu yawa,nan wasu daga ciki ne:1-Mustahabbi ne idan mutum zai yi addu’a ko neman wata biyan bu}ata wajen Allah Ta’ala ya kasance yana da alwala.2-Lokacin da mutum zai yi addu’ar ana so idan zai yiyu ya fuskanci al}ibla.3-Haka nan mustahabbi ne lokacin addu’ar ya ]aukaka hannayensa biyu,Manzon Allah[S] ya ce, Allah Ta’ala yana jin kunyar bawan da zai ]aga hannunsa zuwa gareshi lokacin addu’a ya zamanto bai biya masa bu}ata ba.4-Mustahabbi ne bayan mutum ya kammala addu’ar to kafin ya sauke hannunsa ya shafi fuskarsa dasu.5-Haka nan ana so mutum ya bu]e addu’arsa da godiya da kuma yabo ga Allah Ta’ala da kuma salati ga Manzon Allah da alayensa da dai sauran ladubba na zahiri.

          3-Ladubban ba]ini na Addu’a:Shima suna da yawa amma ga wasu daga ciki:1-Halartar da zuciya lokacin addu’a,wato ana so lokacin da mutum yake addu’a ya kasance tunaninsa ba yana wani waje bane.Yazo a hadisi cewa Allah baya amsar addu’ar mutumin da yana addu’ar amma zuciyarsa ko tunaninsa yana wani waje,wato ba ga addu’ar ba.2-Idan mutum yayi addu’a ana son mutum ya samu ya}ini a cikin zuciyarsa cewa Allah Ta’ala ya amsa ko zai amsa masa.Manzon Allah[s] yace,ku ro}i Allah tare da ya}inin zai amsa maku.3-Ana so lokacin da mutum yake addu’a ya dun ga shu’urin gayar }as}antar da kai ga Allah Ta’ala da kuma bu}atuwa zuwa gareshi da kuma khushu’i.

          4-Lokutan amsar addu’a:Akwai wasu lokuta na musamman da idan mutum yayi addu’a ana fata da sa rai cewa Allah Ta’ala zai amsa,misali daren Jumma’a da kuma ranar Jumma’a,ko kuma lokacin zawal da kuma }arshen dare,ko kuma lokacin da mutum yake azumi ko bu]e baki,ko bayan salloli na wajibi,ko lokacin saukar ruwan sama,ko lokacin da mutum ya sauke karatun Al}ur’ani mai girma da dai sauransu.A ta}aice dai akwai wasu lokuta da bayaninsu yazo a ruwayoyi na hadisi cewa idan mutum yayi addu’a a lokacin to Allah zai amsa masa.Saboda haka yana da gayar muhimmanci irin wa]annan lokuta masu albarka mutum ya ribatu dasu,

          5-Addu’a ga wasu ba da sun sani ba:Yin addu’a ga wasu misali ga ‘yan uwansa muminai ba da sun sani ba yana da falala mai yawa,kuma hanya ce ga mutum ta samun amsar addu’arsa a wajen Allah Ta’ala kamar yadda yazo a hadisi.An ruwaito daga Imam Sadi}[AS] ya ce, “Addu’ar mutum ga ]an uwansa alhali bai sani ba,to tana ~u~~ugar da arziki kuma tana tunku]e abubuwan }i.”A wani hadisi Manzon Allah[S] ya ce, “Babu wani mumini da zai yi addu’a ga muminai maza da mata face Allah Ta’ala ya bashi abinda ya ro}a masu.”An ruwaito daga Imam Ba}ir[AS] ya ce, “Addu’ar da aka fi gaggawar kar~a itace wadda kayi ma wani ]an uwanka bai sani ba.”Yazo a tarihin Sayyida Fa]ima[AS] cewa,Imam Hassan[AS] ya ga tana ibada tun daga farkon dare har ya zuwa }arshensa,da ta gama salloli sai yaji tana addu’oi ga muminai maza da mata,sai ya tambaye ta ban ji kina yi ma kanki addu’a ba,sai tace masa,ya kai ]ana ma}wabci saannan gida.

          6-Abubuwan da suke hana amsar addu’a:Akwai abubuwa masu yawa da in mutum ya aikata su to suna hana amsar addu’a misali cin haram ko shubuha,yazo a hadisi wanda aka ruwaito daga Imam Sadi}[AS] ya ce,”Duk wanda yake so a amsa masa addu’arsa to ya tsarkake hanyar neman abincinsa.”A wani hadisil-}udisi Allah Ta’ala ya ce, Babu addu’ar da take da shamaki a wajena face addu’ar maciyin haram.Manzon Allah[S] yana cewa, “Ibada tare da cin haram tamkar gini ne kan yashi.”Akwai wani da yazo wajen Manzon Allah ya ce yana son Allah ya ri}a amsar addu’arsa,sai Manzon Allah ya ce masa,kada haramun ya shiga cikinka.Daga cikin abubuwan da suke hana amsar addu’a akwai aikata zunubi,yama zo a hadisi cewa wani lokaci mutum zai yi addu’a,Allah Ta’ala ya amsa masa,amma sakamakon aikata zunubi da yayi,sai ya zama masa shamaki daga samun biyan bu}ata.Yazo a cikin addu’ar Du’au Khumail “Ya Ubangiji ka gafarta min zunuban da suke tsare addu’a” wato daga kar~uwa,a wani waje kuma aka ce “Ya Ubangiji ina ro}on ka da izzarka kada mummunan aiki na ya shamakance addu’a ta”A ta}aice dai zunubi guba ce babba mai kisan ruhin ]an Adam.

          7-Illolin rashin yin addu’oi:Akwai illoli masu yawa ga mutum idan ya zamanto bai damu da yin addu’oi ba sai idan wata musiba ko matsala ta same shi,wato ana so mutum ya kasance mai yawan addu’a ko da wane lokaci misali yana halin yelwa na arziki bai sai ya shiga }unci na rayuwar ba,yana halin lafiya bai sai ya shiga halin rashin lafiya ba,yana halin aminci bai sai ya shiga hali na rashin aminci ba da dai sauransu.Daga cikin fa’idodin yin haka shine duk lokacin da wata matsala ta same shi to zata ta}aita,ko ya kasance Allah Ta’ala ya tunku]e musibar ko matsalar baki ]aya,sa~anin ko in bai yin addu’a sai matsala ta bijiro,sai kaga in ta bijiro sai ta tsananta ko ta jima bata koranye ba. An ruwaito daga Imam Sadik[AS] ya ce, “Duk wanda yake so Allah Ta’ala ya kar~a masa addu’a lokacin tsanani to ya yawaita addu’a lokacin yelwa.” An wani Hadisi da aka ruwaito daga Imam Ba}ir[AS] ya ce, “Babu wanda Allah yafi }i kamar mai girman kai ga bauta masa kuma baya ro}onsa.”

         

          8-Addu’ar wanda aka zalunta:Daga cikin Addu’oin da Allah Ta’ala yake gaggawar kar~a shine Addu’ar wanda aka zalunta,yazo a wani Hadisi Manzon Allah[S] yana cewa, “Kuji tsoron Addu’ar wanda aka zalunta ko da ko kafiri ne domin ba tada shamaki tsakaninta da Allah.” To ina ga zaluntar Musulmi kuma Muumini.A wani Hadisi Manzon Allah[s] ya ce, “Addu’ar wanda aka zalunta kar~a~~iya ce.” Imam Ba}ir yana cewa kashedinka da zaluntar wanda bai da wanda zai taimake shi ba in ba Allah ba.”Imam Ali yana cewa, “Kada kayi zalunci kamar yadda baka so a zalunce ka, ka kasance wanda aka zalunta kada ka kasance Azzalumi.” Saboda zalunci musiba ne kuma duhu ga mutum ranar }iyama.Haka nan kada mutum ya kasance mataimaka ga azzalumai ko kuma mai yarda da zaluncinsu.Manzon Allah[S] ya ce, “Azzalumai da masu taimaka masu duka ‘yan wuta ne.”Imam Ali[S] ya ce, “Mai zalunci da masu taimaka masa,da wa]anda suka yarda da zalunci dukkan su sun yi tarayya cikin zunubi.” Saboda haka akwai hatsari babba ga mutum ranar }iyama a yi zalunci }uru-}uru amma mutum ya goyi baya ko yaji da]in abun da aka yi, saboda yin haka zai iya sabbaba mutum in da aka kai azalumai shima akai shi can.Manzon Allah[S] ya ce, “A ranar }iyama mai kira zai yi kira ina azzalumai ina kuma mataimakansu da duk wanda ya a gaza masu da wani abu komi }an}antarsa a tara su tare dasu.” Saboda haka masu irin wa]annan tunani su yi hattara domin lahira itace abin ji.  

         

 
Home Maudu'oi daban-daban Addu’a a mahanga ta Ahlul bayt[AS].
Copyright © 2022. www.tambihin.net. Designed by KH