Littafin Hadisai 100 na Sayyida Fa]imatu-Zahra[AS]. |
![]() |
![]() |
Written by administrator | |||
Saturday, 07 May 2016 09:52 | |||
Da farko ina ta ya ‘yan uwa maza da mata murnar zagayowar wannan wata mai albarka na haihuwar shugabar mataye kuma Ummul-Aimma Sayyida Fa]imatu-zahra[AS] wadda darajojinta da kuma Hadisanta suka ~oyu ga mafi yawan Musulmi na wannan al’umma ta Manzon Allah[S],wanda da mutum zai gwada yanzu yaje ya samu wani malami daga cikin malaman Ahlus-sunna ya ce yana son ya kawo masa Hadisai guda goma wa]anda aka ruwaito daga ‘yar Manzon Allah Fa]ima,to mutum zai sha mamaki domin mafi yawansu ba zasu iya kawowa ba.Kuma wannan ba wai Malaman Ahlus-sunna na yanzu ba ko a magabatansu haka abin yake,alal misali a cikin wani littafi na Suyu]i mai suna, “Assugurul-basima-fi-hayati-sayyidatuna-Fa]ima” yake ce wa a cikin littafin,baki ]ayan Hadisai da aka ruwaito daga wajen Fa]ima ba su kai Hadisai goma ba.Kuma duk wanda yayi karatu ya san cewa Suyu]i yana ]aya daga cikin manya-manya kuma fitattun Malamai na Ahlus-suna,wanda da wuya ka samu wani fanni na ilimin Addinin Musulunci wanda Suyu]i bai rubuta littafi akai ba wato dai mutafannini-ne,kuma duk wanda ya karanta littafansa zai ga cewa yana yawan kawo ruwayoyi da suka shafi Ahlul bayt,shi yasa wasu daga cikin Malaman zamani na yanzu basu yarda da maganarsa,domin haka ya ta~a ha]a ni da wani daga cikin irinsu muna tattaunawa kan wasu sa~ani da aka samu tsakanin sunna da shi’a na wasu mas’aloli to sai na kawo masa hujjoji a wasu littafai na Suyu]i,abin mamaki kawai sai ya kada baki ya ce man ai su littafan Suyu]i basu yarda dasu ba, na ce masa saboda me? Sai ya ce man saboda littafansa suna goyon bayan ‘yan shi’a ne,wannan magana ta ban mamaki sosai,to shine na ce masa amma ko da zaka yi bincike da ka gano cewa a cikin fitattun Malamai na Ahlus-sunna da suka bada gudun-mawa a fagen ilimin addinin Musulunci,to in ana lissafin ]aya,biyu,ukku to Suyu]i da wuya ka kai ga goma baka sashi ba,kuma ko a wannan nahiya tamu babu wani malami cikin na Ahlus sunna da littafansa suka yi tasiri kamar na Suyu]i,duk wanda yayi karatun zaure zai fahimci abunda nike nufi,alal misali littafin Tafsirinsa na Jalalaini shi ake karantawa,haka nan littafinsa na Ulumul-Hadis shi ake karantarwa a zauruka na karatu,wanda sai karatun mutum yayi zurfi sosai yake sa wa]annan littafan.To idan babban Malami kamar Suyu]i zai ce baki ]ayan Hadisan Fa]ima basu kai goma ba to ina ga wani bashi ba.To tambaya shin Sayyida Fa]ima ba tada Hadisai da taji daga Manzon Allah ne? Amsa tana dasu an ~oye nata ne,saboda yawancin Hadisanta suna bayani ne kan wilayar Ahlul bayt.Wanda ko da mutum ba a fagen ilimi yake ba, to ya auna da hankalinsa a ce ‘yar Manzon Allah wadda aka haifa a gidan wahayi ta girma a gidan wahayi ta kuma rayu tare da Manzon Allah a}alla shekaru 18 a wata ruwaya shekaru 24 a ce a rayuwarta baki ]aya hadisai da taji daga Manzon Allah basu kai goma ba,amma a ]aya gefen mutum ya kwatanta da Aisha matar Manzon Allah wadda ta rayu dashi tsanani shekaru goma ta ruwaito Hadisai masu yawa,domin ta tare gidan Manzon Allah bayan komawarsa Madina,kuma Manzon Allah ya rayu a Madina shekaru goma ne. Amma alhamdu-lillahi in mutum yayi bincike a ~angaren littafan Hadisai na Ahlu-bayti zai ga Hadisai na Sayyida Fa]ima masu yawa wa]anda ta ruwaito daga Manzon Allah,wanda akan asasin haka bisa muwafa}a da Allah Ta’ala yayi mani na tsitsinto wa]annan Hadisai da Sayyida Fa]ima ta ruwaito kamar guda ]ari na tattara su waje guda a matsayin littafi,sunan da nasa ma littafin shine, “Mi’atu Ahadisu-Fa]imatu-zahra[AS]” wato Hadisai ]ari na sayyida Fa]imatuz-zahra.Insha-Allah wannan wata da muke ciki na Jimada-Sani littafin zai fito tare da wasu littafai guda biyu,]aya ya shafi hukunce-hukunce da kuma ladubban karatun Al}ur’ani mai girma da kuma Haddarsa,]aya kuma ya shafi Fi}ihu na mata akan asasin fatawowi na Imam Khumaini,a ta}aice dai ga sunayen littafan: 1-Fi}ihun-Nisa’i. 2-Ahkamu tilawatil-{ur’anil-karim-wa-Hifzihi. 3-Mi’atu Ahadisu Fa]imatu- Zahra.Amma yanzu insha-Allah a wannan darasi za a kawo Hadisai 40 daga cikin littafin tabarrukan. 1- An ruwaito daga Fatima[AS]tace:Manzon Allah[S] ya ce mani, “Ya Fatima duk wanda yayi salati gare ki,Allah zai gafarta masa,kuma zai riskar dashi dani duk in da nike a Aljanna.” 2- An ruwaito daga Fatima ‘yar Manzon Allah tace:Manzon Allah[S] ya ce ma Ali[AS] .“Lalle kai ya Ali da shi’arka kuna cikin Aljanna.” 3- An ruwaito daga Fatima ‘yar Manzon Allah tace: Lallai Manzon Allah[S] ya ce, “Duk wanda na kasance waliyyin sa to Ali waliyyin sa ne.Duk wanda na kasance Imaminsa to Ali Imamin sa ne.” 4- An ruwaito daga Fatima ‘yar Manzon Allah tace:Manzon Allah[S] ya ce, “Duk wanda ya mutu akan son Ahlul-bayti to ya mutu shahidi.” 5- An samo daga Ali ibn Husain[AS] ya ce, Fatima ‘yar Manzon Allah[S] wani makaho ya nemi iznin shiga wajen ta sai tai mai hijabi,sai Manzon Allah yace mata:mi ya sa ki ka yi masa hijabi al-hali baya ganin ki?sai tace ya Manzon Allah in bai ganina,ai ni ina ganin sa,sai Manzon Allah[S] yace:Lalle na shaida ke tsoka ne daga gare ni. 6- An ruwaito daga Fatima ‘yar Manzon Allah tace:Naji Manzon Allah[S] yana cewa, “Lalle a ranar jumma’a akwai wata sa’a babu wani mutum musulmi da zai yi muwafa}a da ita yana ro}on Allah ta’ala a cikin ta alhairi face ya bashi.Sai Fatima tace ya Manzon Allah wace sa’a ce wannan? Sai ya ce idan rana tana gab da fa]uwa.” 7- An ruwaito daga Fatima[AS] tace:Manzon Allah[S] ya ce mani, “Na aura maki wanda yafi kowa ilimi,wanda kuma shine farkon wanda ya musulunta,wanda kuma yafi kowa ha}uri.” 8- An ruwaito daga Fatima[AS] tace:Manzon Allah[S] ya ce, “Duk wanda yasa zoben A}i} to ba zai gushe ba yana ganin alhairi.” 9- An ruwaito daga Fatima[AS] tace:Manzon Allah[S] ya kasance idan zai shiga masallaci ya kan ce, “Allahumma igfirli zunubiy waf tahali abwaba rahmatika.Haka nan idan zai fita ya kan ce, “Allahumma igfirli zunubiy waf-tahali abwaba fadlika.” 10- An ruwaito daga Fatima[AS] tace:Manzon Allah[S] ya ce mani, “Ya masoyiyar babanta dukkan abu mai sa maye haramun ne,kuma dukkan abu mai sa maye giya ne.” 11- An ruwaito daga Fatimatuz-Zahra[AS]tace:Naji babana Manzon Allah[S] yana cewa a lokacin rashin lafiya wadda a cikin ta ya rasu, “Yaku mutane ta yiyu in rasu ba da jimawa ba,to ku saurara lalle ni na bar maku littafin Allah ta’ala da kuma Ahlu baytina.Saannan sai ya kama hannun Ali yace wannan Ali yana tare da Al}ur’ani,Al}ur’ani yana tare da Ali ba zasu rabu ba har sai sun same ni a tabki.” 12- An samo daga Zahra’a[AS] tace:Manzon Allah[S] ya shiga gare ni na shinfi]a shinfi]a ta domin yin barci,sai yace ya Fatima kada ki yi barci face kin aikata abubuwa hu]u,1-Kin sauke Al}ur’ani.2- Kin sa Annabawa su zama masu cetonki.3- Kin yardar da muuminai.4-Kin yi hajji da umra,sai tace ya Manzon Allah kayi umarni da abu 4 wanda ba zan iya yin su duka ba a yanzu!sai Manzon Allah yayi murmushi,sai ya ce mata idan kika karanta }ulhuwallahu sau ukku kamar kin sauke Al}ur’ani,idan kin yi man salati da kuma Annabawan da suka gabace ni zamu kasance masu cetonki ranar }iyama.Idan kika yi istigfaru ga muuminai duka zasu yarda dake.Idan kika ce subhanallahi,walhamdu lillahi,wala-ilaha-illah,wallahu Akbar to kamar kin yi hajji da umra ne.” 13- An ruwaito daga Fatima ‘yar Manzon Allah cewa ta shiga wajen Manzon Allah sai ya shinfi]a mayafi sai ya ce mata ta zauna akai,saannan Hassan ya shigo sai ya ce masa:ka zauna tare da ita,saannan Husaini ya shigo sai ya ce masa ka zauna tare dasu,saannan Ali ya shigo sai ya ce masa ka zauna tare dasu,bayan haka sai Manzon Allah ya ce:Ya ubangiji su daga gareni ne, ni kuma daga gare sune,ya ubangiji ka yarda dasu kamar yadda ni na yarda dasu.” 14- An ruwaito daga Fatima[AS]tace:Manzon Allah[S] ya ce mani, “ kashedinki da rowa domin aibi ne wanda bai kasance wa ga mai mutunci,kuma rowa itaciya ce cikin wuta.Kuma na hore ki da kyauta domin kyauta itaciya ce daga cikin itacen aljanna.” 15- An ruwaito daga Fatima[AS] tace:Manzon Allah[S]ya ce, “Za~a~~unku sune wa]anda suka fi ku kyawawan ]abi’u,kuma suka fi kyautatawa matayen su.” 16- An ruwaito daga Fatima ‘yar Manzon Allah tace:Kun manta cewar Manzon Allah ranar ghadir kum ya ce, “Duk wanda na kasance shugabansa ne to Ali shugabansa ne.Da kuma cewar Manzon Allah, kai gare ni kamar matsayin Haruna da Musa ne.” 17- An ruwaito daga Fatima[AS] tace:Manzon Allah[S] ya ce, “Idan bawa yayi rashin lafiya Allah ta’ala ya kan yi wahayi zuwa ga mala’ikunsa ku ]auke al}alami ga bawana matu}ar yana cikin rashin lafiya,domin ni na tsare shi har in kar~e shi ko in }yale shi.”A wata ruwaya na hadisin Allah zai yi wahayi ga Mala’ikunsa ku rubuta ma bawa na ladar abun da ya kasance yana aikatawa lokacin da yake da lafiya. 18- An ruwaito daga Fatima[AS] taga Manzon Allah yana kuka tace:Ya baba na in zamo fansa gare ka miya sa kake kuka? Sai ya ambata mata wasu ayoyi da Jibril ya saukar,Wa inna jahannama lamau’idum ajma’in…….jin haka sai Fatima ta fa]i tana cewa azaba saannan azaba ya tabbata ga duk wanda ya shiga wuta.” 19- An ruwaito daga Fatima[AS] tace lokacin da aka yi nufin }wace fadak daga gare ta:Yaku mutane shin baku ji Manzon Allah[S] ya ce, “Lalle ‘ya ta Fatima itace shugaban matayen aljanna? Su kace lalle mun ji daga Manzon Allah,sai tace to yanzu shugaban matayen Aljanna zata yi }arya ta kar~i abin da ba nata ba?” 20- An ruwaito daga Fatima[AS] tace: Babana ya ce, “Duk wanda yayi man sallama da kuma ke,kwana ukku to yana da Aljanna,sai aka tambaye ta shin wannan ana nufin lokacin da Manzon Allah da ke kuke raye ko har bayan rasuwar ku? Tace muna raye da kuma bayan rasuwar mu.” 21-An ruwaito daga Fa]ima tace Manzon Allah ya ce ma Ali, “Ya Ali lallai kai da shi’arka zaku shiga Aljanna.” 22-An ruwaito daga Fa]ima tace naji Manzon Allah yana cewa, “Ali shine Imami kuma Khalifa a bayana,sai jikokina Hassan da Husain da kuma Imamai tara na zuriyyar Husaini.Idan kuka bisu to zaku shiryu,in kuka sa~a masu to sa~ani zai kasance cikinku har ya zuwa ranar }iyama.” 23-An ruwaito daga Fa]ima tace lokacin da na haifi Husaini Manzon Allah yazo wajena bayan da ya ]auke shi,sai ya mi}o man shi ya ce amshe shi ya Fa]ima lalle shi Imami ne ]an Imami kuma baban Imamai tara.” 24-An ruwaito daga Fa]ima ta ce, “Shi’armu sune za~a~~un ‘yan Aljanna.” 25-An ruwaito daga Fa]ima ta ce Manzon Allah ya ce, “Idan Allah yana son bawa to zai jarrabe shi da bala’oi.” 26-Manzon Allah ya ce, “Ya Fa]ima ki daure ma ]ashin zaman duniya saboda ki rabauta da ni’imar har abada.” 27-An ruwaito daga Fa]ima tace:Manzon Allah ya ce, “Duk wanda yayi imani da Allah da ranar lahira to ya fa]i alhairi ko yayi shiru.” 28-An ruwaito daga Fa]ima tace:Manzon Allah ya ce, “Duk wanda yayi imani da Allah da ranar lahira to kada ya cutar da ma}wabcinsa.” 29-An ruwaito daga Fa]ima ta ce:Manzon Allah ya ce, “Lalle kunya tana daga cikin imani.” 30- An ruwaito daga Fa]ima tace:Manzon Allah ya ce, “Allah Ta’ala yana son mutum mai ha}uri kuma mai kamun kai.” 31-An ruwaito daga Fa]ima tace, “Wanda ya fiku kusa da Allah shine wanda ya fiku kyauta.” 32-An ruwaito daga Fa]ima tace:Naji babana yana cewa, “Lalle Malaman shi’armu za a tada su ranar }iyama cikin kwalliya da ado na karamomi gwargodon ilimin kowannensu da kuma }o}arinsu wajen ilimantar da bayin Allah.” 33-An ruwaiti daga Fa]ima tace, “Yin murmushi ga ]an uwanka mumini yana iya kai ka Aljanna. 34-An ruwaito daga Fa]ima tace:Manzon Allah ya ce, “Duk wanda aka kai ayyukansa wajen Allah tare da iklasi,to Allah Ta’ala zai biya masa muhimman bu}atunsa.” 35-An ruwaito daga Fa]ima tace, “Abubuwa ukku da nafi so a duniya sune:Karatun Al}ur’ani.Duban fuskar Manzon Allah.Infa}i fisabillilah. 36-An ruwaito daga Fa]ima tace:Manzon Allah ya ce Mala’ika Jibrilu ya ce man, “Mai arzikin lahira shine wanda yaso Ali.” 37-An ruwaito daga Fa]ima tace:Manzon Allah ya shaida man cewa, “Ni ce farkon wanda zai riske shi a bayansa.” 38-An ruwaito daga Fa]ima tace:Naji Manzon Allah yana cewa, “Lokacin da akayi Isra’i dani zuwa sama na shiga Aljanna,sai naga a }ofarta an rubuta,babu abun bautawa sai Allah,Muhammad Manzon Allah ne,Ali shugaban mutane.” 39-Wani mutum ya ce ma matarsa cewa ta tafi wajen Sayyida Fa]ima ta tambayeta shin ni ina daga cikin shi’arku ko a’a? Sai taje ta tambaya,sai Sayyida Fa]ima tace mata,ki ce masa, “In kana aiki da umarninmu,kana kuma hanuwa da haninmu to kana cikin shi’armu,in ko ba haka to A’a. 40-An ruwaito daga Sayyida Fa]ima cewa tayi addu’a a rashin lafiya da tayi gabanin rasuwarta tana cewa, “Ya Ubangiji na ina ro}onka albarkacin bayin ka da ka za~a,da kuma kukan ‘ya’yana saboda rabuwa dani ka gafarta ma masu zunubi cikin shi’ata da kuma shi’ar zuriyyata.” Insha-Allah ga mai bu}atar ganin sauran Hadisan da kuma littafan da aka tsamo su yana iya neman littafin,sai dai littafin da larabci ne aka rubuta shi saboda haka zai kasance mai fa’ida a cibiyoyi na karantarwa.
|