Thursday, 27 January 2022
Email
Make My Homepage
RSS
Register
Kwanaki Arba’in na Waki'a Print E-mail
Written by administrator   
Saturday, 23 January 2016 19:59

Innalillah-wa-inna-ilaihi-rajiun.Wa-saya’alamullazina-zalamu-ayya-mun}alabin-yan}alibun.La-tahsabuhu sharrallakum-bal-huwa-kharallakum,likullim-ri’inm-minhum-maktasaba minal-isim,wallazi-tawalla-kibrahu-minhum-lahu-azabun-Azim.Yanzu kwanaki 40 kenan da aukuwar wannan babbar wa}i’a wadda ta fara aukuwa a ranar ]aya ga watan Rabi’ul-Awwal.Saboda idan mutum ya bibiyi tarihin wannan Harka-Islamiyya zai ga cewa duk da an yi wa}i’oi dabam-dabam a lokuta dabam-dabam a kuma wajaje dabam-dabam amma ba a ta~a samun wa}i’a wadda aka kar-kashe ‘Yan uwa kuma aka cutar dasu ta fuskoki dabam-dabam kamar ita wannan wa}i’a,kuma wa}i’ar tazo ma ‘yan uwa ba zato ba tsammani,amma ga wasu bayin Allah daga cikin ‘yan uwa basu ji mamakin aukuwar ta ba saboda Sayyid[H] ya jima yana shaida ma ‘yan uwa a}alla tun 2010 cewa akwai shiri da ake yi na afka ma ‘yan uwa da nufin kisan kiyashi.Idan mutum ya tsaya yayi tunanin dalilin da aka shaida ma duniya na cewa saboda wai an tare hanya ne,to abinda ya biyo baya na kashe-kashe da kuma rushe-rushe ya isa ya nuna ma mutum cewa lalle wannan wani abune tsararre domin a cimma wata manufa.To tambaya a nan itace an cimma wannan manufa? Tarihi zai ba da amsa.Kuma idan mutum ya bibiyi tarihin wannan Harka Islamiyya da Sayyid Zakzaky yake jagoranta  wanda ta faro tun daga 1977 zai ga cewa ba yanzu aka fara aukar da irin wa]annan wa}i’oi ba,illa dai kawai ba a ta~a samun wa}i’ar da tayi muni kamar wannan ba.Haka nan kuma duk wa}i’on da suka auku a tarihin wannan Harka an ga alherinsu daga baya,misali sanadiyyar wa}i’ar Kafancan wanda ta auku a 1987 wannan Harka ta shiga manyan birane na }asar nan,alhali gabanin haka tana cikin makarantu ne.Haka nan sanadiyyar wa}i’ar Abaca wannan Harka Islamiyya ta shiga }auyuka na biranan }asar nan.To wannan wa}i’ar da aka afkar a yanzu idan mutum ya lura kuma yayi tunani zai ga cewa ta yi sanadiyyar shiga }asashe dabam-dabam  na duniya,domin hatta ‘yan uwa na Harka Islamiyya abin ya basu mamaki yadda suka ga wasu daga cikin }asashen yamma suna muzaharori kan a saki Sayyid Zakzaky kuma suna ]auke da hotunansa,wannan in baka ce yin Allah Ta’ala bane to mizaka ce,misali }asashe irinsu England,America,Canada,Australia,sweden,Thailand,India  da dai sauransu,ga kuma }asashe na Musulmi irinsu Iran,Ira},Lebonan,Pakistan,maleshiya,indonisiya  da dai sauransu kamar dai yadda muka gani a tashar press TV.Saboda haka insha-Allah wannan abu da aka yi mana zai zama alhairi duniya da lahira.Su kuma wa]anda suka afkar da wannan wa}i’a sun yi abun da suka yi,sai su jira sakamako daga wajen Allah Ta’ala ko a wannan gida na duniya ko ranar Al-}iyama.Saboda muna da ya}ini wannan zalunci da kuma keta mutunci da ~arnata dukiyoyi da aka yi Allah Ta’ala ba zai bar abun haka ba sai yayi sakamako,yazo a Hadisi Manzon Allah[S] ya ce ka ji tsoron Addu’ar wanda aka zalunta saboda ba ta da shamaki tsakaninta da Allah Ta’ala.” Ma’ana addu’ar kar~a~~iya ce,Mutum ya bibiyi tarihin wannan Harka zai ga cewa duk wa]anda suka zalunci ‘yan uwa kuma suka cutar dasu ko suka gallaza masu yaya }arshensu  yake kasancewa.Kuma in zamu yi ma kanmu adalci da fa]in gaskiya a duk }ungiyoyi da ake dasu na Addini a }asar nan babu wasu da suka fi kowa son zaman lafiya da kuma rungumar kowa da kowa ko da ko a wace fahimta kake kamar Malam Zakzaky da kuma Jama’arsa,saboda mabiyin zakzaky ne za ka same shi zai iya bin sallah bayan ]an [ari}a ko ]an Izala ko ]an {ala-}ato kamar yadda ake ce masu.Kai bama Musulmi hatta kiristoci na }asar nan su suka fi kowa zaman lafiya dasu,saboda har gayyatar su suke wajen tarukansu,kuma a lokuta na rikici suna basu kariya daga wasu musulmi  kada su  ta~a su.Wuce-nan ma hatta jami’an tsaro dabam-dabam da ake amfani dasu wajen afka ma ‘yan uwa,to mutum ya binciki tarihin wannan Harka Islamiyya ko ‘yan uwa suna binsu suna kashewa kamar yadda wa]ansu suke yi,in mutum bai san baya ba to ya dubi wannan abun da ya faru yanzu duk da ]imbim ‘yan uwa masu yawa da aka kashe maza da mata yara da manya, amma ba jami’in tsaro guda ]aya da aka kashe domin da akwai da an fa]a ma duniya,kuma Alhamdu-lillahi duk rushe-rushen da aka yi da kuma binciken da aka yi babu makami }wara ]aya da aka gani,domin da an gani da an nuna ma duniya.To yanzu wannan bai isa ya zama hujja na cewa lalle ‘yan uwa mutane ne ma’abuta zaman lafiya ba! Kuma labarurrukan da aka ji daga ‘yan uwan da wannan wa}i’a ta rutsa dasu shine cewa wasu daga cikin jamian tsaron sun tausaya ma ‘yan uwa kuma abubuwan da aka ce masu sun ga ba haka bane,misali an ce masu suna da makamai basu ga makaman ba,an ce masu arna ne basu sallah amma yanzu sunga suna sallah kuma suna karatun Al}ur’ani.To saboda Allah ko da ace Arna ne basa sallah to miye ala}ar jami’in tsaron }asar nan da A}idar mutum,a yanzu a cikin dokokin }asar nan akwai wata doka wadda ta ce ba a yarda mutum yayi a}idar shi’a ba,amma abin mamaki an ji wasu jami’an tsaro bayan da suka yi abubuwan da suka yi a gidan Malam suna cewa yau sun kashe Shi’a babu sauran shi’a.Shi yasa idan mutum yayi tunani zai ga cewa abun da aka ce na cewa asasin wannan abu shine wai ‘yan uwa sun taka dokar }asa na tare hanya to tambaya anan su jami’an tsaron tun daga faruwar wannan abu zuwa yanzu dokoki nawa suka taka na }asa,misali wace doka ce tace hukuncin wanda ya tare hanya shine akashe shi? Ko a tsare shi a hana kowa ya ganshi da dai sauransu? Ya kamata muyi ma kanmu adalci.kuma miyasa ba a ta}aita abun in da ya faru ba,wato in ma kisan shine hukunci ga duk wanda ya tare hanya a wajensu,to mi yasa aka je gidan Malam aka yi kashe-kashe da kuma rusa gidan? Wanda yasa mutanen gari da yawa da sun yarda da abunda aka ce amma ganin abubuwan da suka biyo baya sai suka canza tunani cewa lalle wannan al’amari akwai lauje cikin na]i.Kuma in muka duba zamu ga cewa daga cikin ayyuka na jami’an tsaro shine su kiyaye rayuka da dukiyoyi da mutumci na ‘yan }asa.To tambaya su ‘yan uwa ba ‘yan }asar nan bane da aka zubar da jinanansu,aka ~ata dukiyoyinsu aka keta mutuncinsu? In ma ana ganin laifi suka yi dokar }asa abinda  ta ce shine jami’in tsaro ya kama mai laifi ya bincika in ya tabbatar da laifinsa ya kaishi kotu.Saboda haka mu zama masu adalci ga dukkan al’amuranmu,mu tuna cewa ba zamu dawwama a wannan gida na duniya ba,ko ba jima ko ba]e mutum zai mutu zai koma wajen Allah Ta’ala da ya hallicce shi,kuma zai yi masa HISABI ga dukkan abubuwan da ya aikata a wannan gida na duniya masu kyau da marasa kyau,saboda haka idan mutum yana ganin yana da }arfin iko ko yana da makami a hannunsa,yana kuma amfani da ikon ko makamin ga wanda yake so ko yake }iyayya dashi to ya tuna ha]uwarsa da mala’iku a cikin }abari bayan ya mutu,wato daga shi sai su ba ikon ba kuma makamin.Yazo a Hadisi Manzon Allah[S] ya ce, “Wanda zai fi kowa shan azaba a ranar lahira shine wanda ya azabtar da mutane a gidan duniya.”

          Ga sauran jama’ar gari musamman wa]anda suke murnar abubuwa da suka faru to yazo a Hadisi cewa duk wa]anda suka so ko suka goyi bayan ayyukan da wasu suka aikata masu kyau ko marasa kyau to Allah Ta’ala zai yi tarayya dasu a cikin lada ko zunubi na aikin ranar }iyama.To tambaya yanzu mutum zai so ayi tarayya dashi cikin zunubai na wa]annan ayyuka da aka yi,wani abun mamaki ma shine wasu Malamai suna ganin abin da ya samu ‘yan uwa wai sakamakon sakin hanya ne.To mutum ya tambayi tarihi, Annabawan Allah baki ]aya basu fuskanci cutarwa da kuma zalunci daga masu tafi da iko na zamaninsu ba wasu Annabawan ma an karkashe su! Misali mutum ya duba tarihin shugaban Annabawa baki ]aya wato Annabi Muhammad[S] ba a yi masa jina-jina ba a garin [a’ifa,ba a yi masa raunuka a Uhudu ba wanda sai da ta kai a ranar Manzon Allah sallah a zaune yayi ta wato saboda raunukar da ak jimasa.Saboda haka wannan abun da ya faru bai }ara mana komai face imani da kuma ya}ini cewa lalle muna kan tafarkin Annanbawa,kuma Insha-Allah mataki ne zai wuce wato dai kamar yadda aka yi wa}i’oi a baya, sun zo sun wuce sun kuma zama tarihi,ita ma wannan wa}i’ar da muke ciki a yanzu zata zama tarihi kuma za a girbi alhairanta insha-Allah.Sayyid Zakzaky[H] yana cewa a cikin wani jawabi da yayi tun ma kafin aukuwar wannan wa}i’ar, “Idan shawara za mu ba ku,sai mu ce,kada ku yi kuskuren ]aukar matakin }arfi.Amma idan kuka yi kuskuren kuka yi,to albishirinku da hasarar duniya da lahira.Albishirinku,za ku tambatsa al’amarin ta in da ba ku zato,kuma wallahi tallahi! Sai kun yi da na sani.” Mutum yayi tunani ya gani ba a je ko ina ba a cikin wa]annan kwanaki 40 basu tambatsa wannan da’awar ba a sassan duniya dabam dabam ba? Sun kuma tambatsa ta cikin jami’an tsaron }asar nan,saboda yanzu wasu jami’an tsaron sanadiyyar wannan abun da aka yi sun fahimci cewa abubuwan da ake fa]i dangane da ‘yan uwa ashe ba haka bane,sun ma yi nadamar abun da suka yi,wato kamar dai yadda ‘yan uwa da aka sako suka ba da labari.Kuma mu duba yadda wannan wa}i’ar ta zama ala}a}ai ga wa]anda suka ba da umarnin afkar da ita,wato dai maganar Malam ta tabbata na cewa sai kun yi dana sanin da baku yi ba.Ga kuma zuwa lahira ko bajima ko bada]e.Yazo akan cewa Imam Husain a ranar Ashura bayan da yayi duk wa’azin da zai yi domin hana  sojojin yazidu yin abun da suke so su yin a kashe shi,sai aka ga Imam Husain yana kuka aka tambaye shi dalili y ace, yana tausayin sune saboda wannan abun da zasu yi zai sanadiyyar zuwansu wuta.A cikin Al}ur’ani  Allah Ta’ala  a suratu Nisa’I aya ta 93, “Duk wanda ya kashe Mu’umini da gangan to sakamakonsa wutar Jahannama,kuma zai tabbata a ciki,kuma Allah yayi fushi dashi,kuma ya tsine masa,kuma yayi masa tattalin azaba mai girma.” Saboda haka duk rayukan da aka kashe in an ~oye ma mutane to fa bai ~oyu wajen Allah Ta’ala,kuma dukkanmu da mu da aka yi ma da wa]anda suka yi mana nan da shekaru 100 ban yi tsammanin za a samu ]aya daga cikinmu ba,duk mun mutu mun koma ga mahalliccinmu,saboda haka wallahi lahira itace abin ji.kuma babu abu mai ha]ari a ranar }iyama a lokacin hisabi kamar zalunci ga wani mutum a ransa ne,ko mutuncinsa ko a dukiyarsa,kuma mutum yayi tunani idan nan gidan duniya an sa shine yayi,to ranar }iyama wa]anda suka sashi ba zasu iya kare shi ba,suma zai kasance suna ta kansu ne.Kuma mutum yaji tsoron fa]a da Allah Ta’ala.Fa]a da Allah Ta’ala shine fa]a da Addininsa,fa]a da Addininsa shine fa]a da wa]anda suka ri}e addinin.Haka nan wannan wa}i’ar ta zama sanadiyyar fahimtar wasu daga cikin mutanen gari cewa lalle wa]annan mutane su suke kan tafarkin Annabawa.Akwai wani abun da ya ta~a faruwa bayan fitowar Malam daga kurkuku na wa}i’ar Abaca,wasu ‘yan Izala suka zo suka same shi,bayan sun gaisa sai suka ce dalilin zuwansu shine,su sun karanta Al}ur’ani  kuma sun binciki tarihi sun ga cewa babu wani Annabi daga cikin Annabawan da Allah Ta’ala ya aiko fa ce sai da ya sha wahala daga shugabbannin zamaninsa,amma sai suka ga Malamansu ko wa ce gwamnati tazo suna ]asawa da ita ne,a lokaci guda kuma sai sauka ga wasu gungun musulmi duk gwamnatin da ta zo sai su ga ta  diyar masu  ko sun tasa su gaba da cutarwa da }iyayya da kuma musgunawa,saboda haka suka yi tunani lalle wa]annan mutane nasu yafi kama dana Annabawa,saboda haka sai suka yenka shawarar cewa zasu zamo cikin ‘yan wa]annan Harka Islamiyya.Wannan abu ya faru ne a 1999.Kuma idan mutum ya lura da ]abi’ar mutane in dai na kan gaskiya ko da a duniyance ne ba wai a fagen addini ba za ka ga ba a sonsa,misali idan mutum maaikaci ne ko ]an kasuwa in dai mai son komi a yi shi cikin gaskiya ne to zaka gaba a sonsa,to ballantana kuma a fagen addini.Shi yasa mutum ya tambayi kansa wa]annan mutane da ake yi ma gayar }iyayya haka,alhali tsakaninsu da jama’a ba duka ba zaki duk da ko irin }azafi }aryaryaki da ake yi masu.Saboda haka zai fi ma mutum sau}i ranar Al}iyama ya kasance mutum bai cikin Harkar amma bai cutar da maabutanta ba,ko kuma an cutar dasu kuma ya goyi baya,saboda haka mutum yayi hattara lahira itace abin ji.

          Ga ‘yan uwa wannan lokaci da muke ciki lokaci ne da zamu da]a komawa ga Allah Ta’ala ta hanyar kusanci zuwa gareshi da ayyuka na ibadodi dabam-dabam,da kuma dogaro gareshi saboda bamu da wani }arfi ko dibara in bada ga wajen Allah Ta’ala ba.Kuma mu yawaita Addu’oi dabam dabam musamman wa]anda aka ruwaito daga Aimma na Ahlul bayt.Haka nan kuma mu kasance masu ha}uri da dauriya musamman tsakaninmu da mutanen gari saboda zamu ji izgili da sharri kala-kala,hakan  bai da wani magani in ba dauriya da ha}uri ba,kuma duk yadda al’amura suka kasance ka da mu yarda a tunzuramu ko a harzu}amu mu yi abinda bai da ce ba, ko kuma ya sa~a da tarbiyyar da Malam yayi mana wato na yin komai akan asasin hankali da ilimi da kuma nizami.Zan kammala wannan rubutu da wasiyyar da Sayyid Zakzaky ya yi ma ‘yan uwa a 2010 wato lokacin da aka so a afkar da wa}i’a  irin wadda aka afkar yanzu a zamanin mulkin Umaru Musa Yar’aduwa,sai Allah Ta’ala ya kiyaye bata afku ba.Ga abun da Malam ya ce a lokacin, “Sa’annan kuma ga ‘yan uwa sai in ce,ko abin a kashe ni ne,kar ku ce zaku rama kan kowa!! Illa iyaka dama mutuwa,ko basu kashe ni ba zan mutu.Saboda haka in tafiya tazo falillahil hamd.Ita da’awa ba za ta mutu ba.Don an kashe ni, ba ya na nufin da’awa ta mutu bane! Insha Allah sai dai ta yi }arfi.Domin da’awa Alhamdu lillahi ta riga ta shiga zukatan mutane,kuma lalle bindiga ba zai bindage ta ba.Ko da ko kun yi abinda kuka kira  massacre wato kisan kiyashi.Saboda haka in wani abu ya faru, naku addu’a insha-Allah.” Allahu-Akbar wannan jawabi Malam yayi shine a watan Ramadan shekara ta 1430 bayan hijira wato yau kimanin shekaru bakwai kenan.Mu yi nazarin wa]annan maganganu masu rai na Malam,kamar ka ce a yanzu ya yi su.

          Daga }arshe muna ro}on Allah Ta’ala duk wa]anda suke da hannu cikin wannan abu na ~oye dana bayyane na cikin gida da waje Allah Ta’ala ya saka mana akansu da abun da yaso ya kuma yi inti}ami,wa]anda kuma aka karkashe maza da mata yara da manya Allah Ta’ala ya saka su cikin ajin bayinsa shahidai,wa]anda kuma aka raunata Allah Ta’ala ya basu lafiya,wa]anda kuma suke tsare wa]anda aka sani da wa]anda ba a sani ba Allah Ta’ala ya basu faraj,wa]anda kuma suke waje Allah Ta’ala ya da]a basu isti}ama da kuma sabati.Sauran al’umma Musulmi da wa]anda ba musulmi ba wannan abu ya da]a bu]e zukatansu ga fahimtar tafarki na gaskiya.

 
Home Maudu'oi daban-daban Kwanaki Arba’in na Waki'a
Copyright © 2022. www.tambihin.net. Designed by KH