Sunday, 25 February 2024
Email
Make My Homepage
RSS
Register
Ladubba da kuma ruhin aikin Hajji 1 Print E-mail
Written by administrator   
Wednesday, 14 October 2015 10:02

A darasin da ya gabata an gama babin sallah,wanda a cikinsa an yi bayanai kan fasaloli dabam dabam,to kasantuwar bu}ata da ‘yan uwa maza da mata tsawon lokaci suke ta gabatarwa ta hanyar bugo waya ko text da sauransu cewa darussan da aka gabatar na fannin ilimin Fi}hu,Akla} da Tarihi da kuma Darussa daga Rayuwar Manzon Allah[S] da kuma Aimma na Ahlul bayt[AS] a mai  da su zuwa littafi.Akan asasin haka na yi tunanin cewa zai yi kyau a samu a kammala sashen ibadodi na fi}hun kafin a buga littafin,wato kamar yadda aka ta~a bayani a darasin farko cewa fannin ilimin fi}hu yana da manyan ~angarori guda biyu,~angaren ibadat da kuma ~angaren Mu’amalat,~angaren ibadat yana da manyan babobi kamar haka:

1-Tsarki.

2-Sallah.

3-Azumi.

4-Zakka.

5-Hajji.

kuma ko wane babi yana da fasaloli }ar}ashinsa.To a nan wa]anda ba a yi darasi akansu ba sune zakka da Hajji,sauran an gabatar dai dai gwargwadon iko.Kasantuwar muna fuskantar lokaci na aikin hajji,kuma muna cikin watanninsa  na ga zai yi kyau a fara dashi daga baya sai a kammala da babin Zakka.

          Aikin Hajji yana da ~angarori guda biyu,~angaren ruhinsa wanda shine ba]ininsa.Da kuma ~angaren jikinsa wanda shine zahirinsa.Malaman Irfan ko Tasawwuf sun yi bayanai da kuma rubuce-rubuce dangane da ruhi da kuma asraru na aikin hajji,wato kamar yadda fu}aha ko mujtahidai suka yi bayanai da kuma rubuce-rubuce kan aikin hajji.Idan mutum yayi bincike ma zai gano cewa babu wani babi daga cikin babobin fannin ilimin fi}hu da Mujtahidai masu yawa suka yawaita yin littafi kususan akan sa kamar babin aikin Hajji,wasu Risala ma ta wasu mujtahidai in mutum ya duba zai ga cewa basu kawo babin aikin Hajji ba ko kuma sun kawo amma da bayanai ba masu tsawo ba,maimakon haka sun yi littafi musta}illi ne kan aikin hajin,misali na irin wa]annan littafai sune:

1-Manasikul-Hajj na Imam Khumaini.

2-Ahkam wa adabul Hajj na Ayatullahi Sayyid Gulfaigany.

3-Manasikul Hajj na Ayatullah Sistany.

4-Manasikul Hajj na Ayatullahi Mirza  Jawad attabrizy.

5-Manasikul Hajj na Ayatullahi Bahajaty.

6-Ahkamul-Hajj na Ayatullahi Fadhil Lankarany.

7-Manasikul Hajj na Ayatullahi Safiy da dai sauran wasu Mujtahidai masu yawa a wannan zamani namu da suka rubuta littafai kassatan kan aikin Hajji,wanda mafi yawan wa]annan littafai da suka rubuta sun sa masu suna da Manasikul-Hajj.Saboda haka a wannan darasi insha Allah za a kawo bayanai dai dai gwargwado kuma a ta}aice kan mahangar Malaman Fi}hu da kuma Malaman Irfan kan aikin Hajji.Shi yasa ga wanda zai yi aikin Hajji yana da gayar muhimmanci ya san zahiri da ba]ini ko jiki da ruhi na aikin Hajji,domin yin haka shi zai sa mutum ya samu kamalar aikin hajjinsa da kuma fatar kar~uwarsa wajen Allah Ta’ala.Kuma wannan kiyaye zahiri da ba]ini bai ta}aita ga aikin Hajji ba,a’a a duk ibadodi da mutum yake aikatawa yau da kullum kamar salloli azumi da dai sauransu, to  ana so mutum ya dun ga kula da kuma kiyaye ruhinsu da jikinsu.Ruhi da asraru da kuma ba]inin wa]annan ayyuka na ibadodi galibi Malaman Irfan ko littafan Irfan ne suke bayaninsu,kamar yadda zahiri ko jiki na wa]annan ayyuka na ibadodi galibi Fu}aha ko Mujtahidai ko kuma littafan fi}hu ne suke bayani kansu.Akwai Malaman Irfan ko Tasawwuf da suka rubuta littafi kan Asrar na aikin Hajji,idan ma mutum ya duba littafin  Mahajjatul-Baidha na Ayatullahi Muhsin Kashany ko littafin Ihya’ul Ulumuddin na Gazali zai ga akwai  bayanai kan asraru da ba]ini na aikin Hajji.Bayan wannan shinfi]a bayanai da zasu gudana a wannan darasi sune:

1-Ma’anar aikin Hajji.

2-Shekarar da aka wajabta aikin hajji.

3-Sharu]]an aikin Hajji.

4-Rabe-raben aikin Hajji.

5-Nau’oin aikin Hajji.

6-Bayani kan aikin Hajjin Tamattu’i.

7-Harama da Hajji.

8-Ladubban Zahiri na Hajji.

9-Ladubban ba]ini na Hajji.

10-Ruhin aikin Hajji.

11-Ziyarar Manzon Allah[S] da kuma Aimma na Ahlul bayt[AS] da ke Madina.

12-Aikin Umara.

13-Niyaba a aikin Hajji.

14-Wasu mas’aloli na aikin Hajji.

15-Yadda rayuwar mahajjati ya kamata ta kasance bayan ya dawo gida.

          1-Ma’anar Hajji:Ma’anar Hajj a lugace shine nufi saboda wani abu.Amma a is]ilahin shari’a yana nufin wata ibada ta musamman ke~antacciya,a lokaci ke~antacce,a kuma waje ke~antacce a kuma wata fuska ke~antacciya,misali mutum ba zai iya aikin Hajji ba a wani wata in ba wa]annan watanni na Hajji ba,haka nan ba zai iya yi a wani waje ba,in ba garin makka ba,haka nan ayyuka da ake yi mutum ba zai yi su ba sai yadda shari’a ta shinfi]a.Hajji yana daga cikin ibadodin da ake yinsa da jiki da kuma dukiya,domin wasu ibadodin da jiki kawai ake yin su misali Sallah da Azumi,wasu kuma da dukiya kawai misali Zakka da Khumusi.

          2-Shekarar da aka wajabta aikin Hajji:Aikin Hajji an wajabta shine a Madina shekara ta biyar bayan hijira,mafi yawan Malaman tarihi sun tafi akan haka.Wato dai kamar sauran ibadodi misali Azumi da Zakka suma duka a Madina ne aka wajabta su,an farlanta sune a shekara ta biyu bayan hijira.Sallah ce aka wajabta ta tun a Makka,shi yasa idan mutum ya dubi ayoyin da suka sauka a makka zai ga sun fi Magana kan A}ida da kuma Akla},da }issoshi na Annabawan da suka gabata,ayoyin Madina kuma sun fi Magana kan ibadat da kuma mu’amalata,da kuma al’amuran da suka shafi Jihadi,in mutum na karatun Al}ur’ani ya lura zai ga haka.

          3-Sharu]]an aikin Hajji:Akwai wasu sharu]]a da sai in sun kammala aikin Hajji ke wajaba kan mutum sune:

1-Balaga wato sai mutum ya kai matsayin da taklif na shari’a ya hau kansa hajji yake wajaba masa,saboda haka da a ce yaro wanda bai kai shekarun Taklif  ba wato shekaru tara ga mata,shekaru sha-biyar ga maza to ]ayansu da zai yi aikin Hajji ya inganta, amma  idan taklif ya hau kansa sai ya sake hajjin,wato wanda yayi bai wadatar masa ba daga Hajjin Musulunci.

2-Hankali:Hajji ba ta wajaba ba sai idan mutum na da hankali saboda haka ta fa]i kan mahaukaci.Da a ce mahaukaci a sawwala cewa in zai yiyu yayi duk ayyukan hajji to wannan hajjin bai wadatar masa ba daga Hajjin Musulunci,wato in ya samu lafiya ta Hankali zai sake wani Hajji.

3-‘Yan tuwa:Daga cikin sharu]]an wajabcin Hajji dole ne mutum ya zama ‘yantacce wato ]a ba bawa ba,saboda haka Hajji bata wajaba ga bawa ba.

4-Samun iko:Wato samun iko ta fuskacin dukiyar da mutum zai kashe ya je,da lafiyar jiki da kuma }arfin jiki,da kuma amincin hanya da lafiyarta,da kuma yelwar lokaci da wadatuwarsa wato na yin ayyukan hajjin.Wa]annan sharu]]a da aka kawo suna da mas’aloli masu yawa }ar}ashinsu ga mai bu}ata yana iya duba littafin Tahrirul wasila na Imam Khumaini ko Risala na Mujtahidin da yake Ta}lidi da shi.Amma wata mas’ala anan itace dangane da Hajjin mata,ba a shar]anta samun muharrami a wajen aikin Hajjin mace ba,in dai ta kasance amintacciya ce ga kanta da kuma mutuncinta,kuma anan ba wai sai tana da miji ba,wato ko da ba ta da miji.Idan kuma babu wannan aminci to anan ne ya wajaba akanta ta tafi da muharrami,ko wani wanda take da amintuwa da shi .Wata mas’ala kuma itace,ba a shar]anta iznin miji ga matarsa ba a Hajji na wajibi in har ta samu iko,kuma bai halatta ga shi mijin ya hana ta ba.Amma in da Hajjin mustahabbine to a nan an sha]anta izininsa.

          4-Rabe-raben aikin Hajji:Aikin Hajji ya kasu kashi biyu,akwai Hajjin wajibi akwai kuma Hajjin mustahabbi.Hajjin wajibi shi ake ce ma Hajjin Musulunci,kuma wannan wajibci sau ]aya ne a rayuwar mutum.Mustahabbi ne yin Hajji ga wanda ya ta~a yin Hajjinsa na wajibi,mustahabbi ne mutum ya ri}a maimaita aikin Hajji,kai duk shekara ma idan yana da iko.Makruhine ma barin aikin Hajji har tsawon shekaru biyar a jere in dai yana da iko.Mustahabbine ma mutum ya yi niyyar dawowa aikin Hajji yayin da zai fita daga makkah,amma karhanta mutum yayi niyyar cewa ba zai dawo ba.

          5-Nau’oin aikin Hajji:Aikin Hajji yana da nau’oi guda ukku sune:

1-Tamattu’i.

2-{irani.

3-Ifradi.

Insha Allah a darasi na gaba za a yi bayani akansu.

 
Home Darusan Fiqh Ladubba da kuma ruhin aikin Hajji 1
Copyright © 2024. www.tambihin.net. Designed by KH