Tuesday, 23 July 2024
Email
Make My Homepage
RSS
Register
Ladubba da kuma ruhin aikin Hajji 2 Print E-mail
Written by administrator   
Wednesday, 14 October 2015 09:54

5-Nau’oin aikin Hajji:Aikin Hajji nau’i iri ukku ne sune:

1-Hajjin Tamattu’i.

2-Hajjin Ifradi.

3-Hajjin {irani.

Hajjin Tamattu’i shine wanda mutum zai yi ayyukan Umara da farko bayan haka kuma yayi ayyukan Hajji.Hajjin Ifradi kuma shine wanda mutum da farko zai yi ayyukan Hajji daga baya kuma yayi ayyukan Umara.Hajjin {irani kuma shine wanda mutum zai gwama tsakanin Hajji da Umara.Akwai sa~ani tsakanin mazhaba ta Ahlus sunna da kuma ta Ahlul bayt kan yin wa]annan nau’uka  na aikin Hajji.A mazhabobi na Ahlus sunna misali Malikiyya,Shafi’iyya,Hanafiyya da kuma Hanbaliyya sun tafi akan cewa mutum na da za~i yayi wanda yake so daga cikin wa]annan nau’ukan aikin Hajji guda ukku,sai dai sun sa~a a tsakaninsu na cewa to a cikinsu wane yafi.Malikiyya sun ce Ifradi shi yafi,Hanafiyya suka ce {irani shi yafi falala,Shafi’iyya suka ce Ifradi da Tamattu’i suka fi falala,Hanbaliyya suka ce Tamattu’i shi yafi falala.Amma a mazhaba ta Ahlul bayt Tamattu’i shi yafi falala.Kuma a mazhaba ta Ahlul bayt Hajjin Tamattu’i wajibi ne ga wanda yake ba cikin garin makka ba,wato wanda yake da nisa daga makka.Hajjin Ifradi da kuma {irani wajibai ne ga wanda yake cikin garin Makka ko kuma wanda bashi da nisa daga Makka.Nisan anan shine mil 48 wato ta kowane ~angare daga Makka.Saboda haka a Imamiyya duk wanda yake a wajen garin Makka da tsawon mil 48 to Hajjin Tamattu’i ne ya wajaba akansa,wato ba zai yin na Ifradi ko {irani ba sai in da wata lalura misali }urewar lokaci.

          6-Bayani kan Hajjin Tamattu’i:Kasantuwar Hajjin Tamattu’i a mazhaba ta Ahlul bayt shine hajjin da mafi yawan mahajjata kan aikata a lokacin aikin hajji yasa anan za a kawo bayaninsa a ta}aice.Da farko mutum zai yi niyya da kuma ]aura Harami a cikin watanni na aikin Hajji wato Shawwal,Zul-}ida da kuma Zul-Hajj daga ]aya daga cikin mi}atoti da cewa zai yi Umrar Tamattu’i da kuma aikin Hajji.Bayan haka sai ya shiga garin Makka,ya yi ]awafi a ]akin Kaaba sau bakwai,bayan haka sai ya yi sallah raka’a biyu a Ma}am Ibrahim,bayan haka kuma sai ya yi sa’ayi tsakanin Safa da Marwa shima sau bakwai,sai kuma Ya yi ]awafin mata amma a bisa ihtiya]i istihbabiy shi ma sau bakwai,bayan haka ya yi sallah raka’a biyu ta shi ]awafin,ko da yake dai fatawa mafi }arfi shi ne ba wajibi ba ne yin ]awafin mata ]in da kuma sallar tasa.Bayan haka kuma sai ya yi saisaye,sai ya kasance duk abin da ya haramta a gare shi lokacin da yake da Harami yanzu ya halatta a gare shi.Wannan ita ce surar Umrar tamattu’insa wadda ita ce ]aya daga cikin juz’oi biyu na aikin Hajjinsa.Sai kuma ya sake yin Harami don aikin Hajji daga Makkan wato a lokacin da yake da tabbacin cewa zai riski tsayuwar arfa.Abin da ya fi falala shine afkar da shi ]aura Haramin a ranar Tarwiyya [wato takwas ga watan Zulhijja] bayan mutum ya yi sallar Azahar.Saannan sai ya fita ya tafi Arfa ya tsaya a can,tun daga zawalin rana na yinin Arfa har ya zuwa fa]uwarta.Daga nan kuma sai taso daga Arfa ya wuce zuwa Muz]alifa ya kwana a can,zai kuma zauna a wajen bayan ketowar alfijir na ranar goma ga watan Zulhijja har ya zuwa hudowar rana.Saannan ya wuce zuwa Mina domin yin ayyukan ranar yin suka,sai ya yi jifa wato jamratul-A}aba,ya yi suka,ko kuma ya yanka Hadayarsa,ya kuma yi aski in ya kasance Hajjin farko ce ya yi a bisa ihtiya]i na wajibi.Shi kuwa waninsa wato wanda ba Alhajin farko ba,to shi yana da za~i tsakanin yin aski da kuma yin saisaye.Amma mata su saisayene ya ayyana akansu.Bayan mutum ya yi saisayen sai ya kasance komai ya halatta masa in banda mata da kuma sa turare.Bayan haka kuma sai ya tafi makka in yaso tafiya a ranar.In yaje sai ya yi ]awafin aikin Hajji,ya yi kuma sallah raka’a biyu ta ]awafin,sai kuma ya yi sa ayi-sa’ayin ]awafin,idan mutum ya yi wannan to turare ya halatta masa.Bayan haka kuma sai ya yi ]awafin mata da kuma sallarsa raka’a biyu,bayan ya yi haka to mata sun halatta masa.Bayan haka sai ya dawo Mina ]in don yi jifar jimar,sai ya kwana a nan dararen Tash-ri} wato dare na sha-]aya da na sha-biyu,da na sha-ukkunma,sai dai kwanansa na sha-ukkun a wasu halulluka ne.A cikin yinin dararen ne zai yi jifan guda ukku.Idan kuma baya son dawowa makka a wannan rana,wato maimakon haka sai ya yi zamansa a Mina har sai ya yi jifarsa baki ]aya.Amma abin da ya fi falala ya kuma fi zamowa ihtiya]i shine ya wuce zuwa Makka ]in a ranar Suka,kai bai kamata ba ma mutum ya yi jinkiri zuwa washe-garin Ranar ballantana kuma ya yi jinkiri har ya zuwa ranakun Tash-ri},sai fa idan akwai wani uzuri.

          Siffar aikin Hajjin Ifradi kamar ta Hajjin Tamattu’i ne sai a waje guda ne kawai suka sa~a,in da suka sa~a kuwa ko shine cewa,Hadaya wajiba ce a aikin Hajjin Tamattu’i,amma mustahabbi ce a aikin Hajjin Ifradi.

          Haka nan siffar Umrar Ifradi kamar ta Umrar Tamattu’i ce sai a wasu wajaje ne suka sa~a,wajajen ko sune:

1-Ita Umrar Tamattu’i saisaye ne yake ayyana kan mutum aski baya halatta,a cikin Umra Mufrada ko mutum na da za~i tsakaninsu wato ko saisayen ko askin.

2-A aikin Umrar Tamattu’i babu ]awafin mata,ko da yake dai ihtiya]i ne na mustahabbi ayi shi.Amma a cikin Umra Mufrada wajibi ne yin ]awafin matan.

3-Mi}atin wajen ]aura Harami Umrar Tamattu’i shine ]aya daga cikin mi}atoti ayyanannu.Shi kuwa mi}atin Umra Mufrada kusa da Harami ne,ko da yake dai ya halatta a ]aura Haramin a wa]ancan mi}atoti.

          MI{ATOTI:Wato sune wuraren da aka ayyana domin ]aura Harami,kuma su biyar ne na umrar aikin Hajji:

          Na farko:Zul-Hulaifa,shine mi}atin mutanen Madina,da kuma duk mai bi ta hanyarsu.

          Na biyu:Al’a}i},shine mi}atin mutanen Najadu da Ira}i da kuma duk mai bi ta wajen.

          Na ukku:Juhfa,shine mi}atin mutanen Sham da Misra da Magrib da kuma wanda yake bi ta wajajen.Juhfa shine mi}atin mutanen wannan nahiya tamu.

          Na hu]u:Yalamlam,shine mi}atin mutanen Yaman,da kuma duk mai bi ta hanyar.

          Na biyar:{arnul-Manazil,shine mi}atin mutanen [a’ifa da kuma wanda zai bi ta wajen.

          Akwai sa~ani tsakanin madrasa ]in Ahlus sunna da kuma madarasa ta Ahlul bayt kan yin Ihrami gabanin mi}ati,Mazahib na Ahlus sunna sun halatta yin ihrami gabanin mi}ati,amma a mazhaba ta Ahlul bayt bai halatta sai dai a bisa wasu yanayoyi.Sai dai mazahib na Ahlus sunna da kuma na Ahlul bayt sun yi ittifa}i akan cewa bai halatta mutum ya wuce mi}ati bai yi ihrami ba,in  ko har ya wuce to wajibi ne ya dawo ga mi}atin,in da suka sa~a shine cewa to idan bai dawo bafa,Ahlus sunna suka tafi akan cewa ya aikata zunubi amma Hajjinsa ya inganta kuma hadaya ta hau kansa.Amma a mazhaba ta Ahlul bayt yazo akan cewa idan da gangan ne yayi haka kuma babu wani mi}ati a gaba da zai yi ihramin to hajjinsa ta ~aci,amma idan akan asasin mantuwa ne ko jahilci,kuma zai iya yiyuwa ya dawo mi}atin to sai ya dawo,in ko ba zai yiyu to sai yayi a wani mi}ati da yake gaba,ko kuma a wajen Harami ko cikin Harami.

          Insha-Allah a darasi na gaba za a ]ora akai.

 
Home Darusan Fiqh Ladubba da kuma ruhin aikin Hajji 2
Copyright © 2024. www.tambihin.net. Designed by KH