Sunday, 25 February 2024
Email
Make My Homepage
RSS
Register
Bayani kan sallar Mamaci 1 Print E-mail
Written by administrator   
Sunday, 08 March 2015 19:52

Insha-Allah a wannan darasi bayani zai kasance kan sallar mamaci,kuma shi zai zama kammalawa a babin sallah da aka ]auki lokacin a na gabatarwa.Ga wanda yake bibiyar wannan fili na tambihi a wannan darasi na fi}hu ya san cewa bayanai sun gudana akan wannan babi na salla a wa]annan fasulla:

1-Bayani kan shakka cikin sallah.

2-Sujudar Rafkannuwa.

3-Abubuwan da suke ~ata sallah.

4-Sallar matafiyi.

5-Sallar Khusufi.

6-Sallar Ramuwa.

7-Sallar Jama’a[Jam’i].

8-Sallar Jumma’a.

9-Sallar Idi,da dai sauransu.

Ga mai bu}atar ganin wa]annan darussa da aka gabatar da kuma na sauran fannoni yana iya duba wannan shafin www.tambihi.net. Dawowa  kan wannan fasali na sallar mamaci,kamar yadda sanin ilimi na yadda mutum zai rayu a wannan duniya yake da muhimmanci,to haka nan sanin ilimi na mutuwarsa da abun da zai biyo bayan mutuwar yake da muhimmanci.Mutuwa  kamar yadda kowa ya sani }of a ce wadda kowa sai ya shige ta.Kuma  komi tsawon rayuwar da mutum ya yi a duniya }arshe dai mutuwa za ta zo,saboda haka tattali da guzuri da kuma shiri kafin zuwanta yana da gayar muhimmanci.Akan wannan asasi sanin abinda mutum zai yi ko za a yi masa idan alamomin mutuwa sun fara bayyana gareshi yana da gayar muhimmanci.Wato dai muhimmancin  sanin ladubba na gabanin mutuwa da lokacin mutuwa da kuma bayan mutuwa.Saboda haka bayani kan wannan fasali zai kasance kan wa]annan ababe:

1-Abubuwan da mutum zai yi kafin ya mutu.

2Abubuwan da mutum zai yi,ko za a yi masa idan ya kai gargara.

3-Hukuncin ta~a gawa.

4-Wankan gawa.

5-Sa likkafani ga mamaci.

6-Sallar mamaci.

7-Binne mamaci.

8-Abubuwan da ake yi ma mamaci bayan an binne shi.

9-Yawaita tunanin mutuwa.

          1-ABUBUWAN  DA MUTUM ZAI YI KAFIN YA MUTU:Da farko micece mutuwa? Mutuwa itace rabuwar ruhi da gangar jiki.Wato shi ruhin ]an Adam yana da farko amma bai da }arshe,canjin jiki ne kawai zai dunga samu.A ranar }iyama za a yi masa wani jiki,haka nan idan za a kai shi aljanna ko wuta za a sake masa wani jiki.Ita kuma rayuwar barzahu rayuwa ce ta ruhi ba jiki.Kuma mutuwa itace mataki na ukku na tafiyar ]an Adam daga Allah zuwa ga Allah.Mataki na farko shine kafin zuwan mutum wannan duniya.Mataki na biyu shine daga lokacin da mutum yazo wannan duniya  zuwa mutuwarsa.Mataki na ukku shine daga lokacin da mutum ya mutu zuwa tashin }iyama.Mataki na hu]u shine daga lokacin da aka yi tashin }iyama zuwa ga lokacin da za a yenke ma mutum hukunci na zama a ]ayan gidaje guda biyu wato aljanna ko wuta.Mataki na biyar shine zama a gidan aljanna ko wuta.Idan mutum ya duba zai ga cewa duk wanda yake raye yanzu a duniya,to ya wuto mataki na ]aya yanzu yana mataki na biyu,saura matakai ukku a gabansa.To da mutum zai tambaya a cikin wa]annan matakai guda biyar,wanne ne yafi muhimman ga ]an Adam? Amsa itace wannan mataki na biyu wato rayuwarsa ta duniya,saboda wa]ancan matakai guda ukku dake gabanmu to kowanen su kyawansa ko muninsu ya danganta ga yadda rayuwar mutum a addinance ta kasance a zamansa na duniya.Saboda haka  rayuwar duniya dama ce kuma ni’ima babba  ga mutum domin kyautata wa]ancan matakai guda ukku dake gabansa.To abin ake so mutum ya yi idan }arshe yazo,wato kafin ya mutu daga ciki akwai:

1-Tuba wato ya tuba ga Allah Ta’ala daga dukkan zunuban da ya aikata a rayuwarsa wa]anda ya sani da wa]anda bai sani,na zahiri da ba]ini,manya da }anana

.Kuma tuba kamar yadda malaman Akla} suka yi bayani  ta kasu kashi ukku: Akwai tuba ta awwam,itace tuba daga zunubi.Akwai tuba ta kusus wato za~a~~un bayin Allah,itace tuba daga gafala.Akwai tuba ta kususul-kusus wato za~a~~un za~a~~un bayin Allah,itace tuba daga ta}aitawa ga bautar Allah.Shi yasa yana da muhimmanci a rayuwar mutum ya dunga ro}on Allah ya azurta shi da tuba gabanin mutuwa.

2-Mutum ya zauna ya yi tunani idan akwai wani ha}}i na mutane akansa ko kuma na Allah Ta’ala to ya yi }o}ari ya ga ya sauke wannan ha}}in kafin ajali ya sauka.

3-Neman gafara da afuwa tun daga iyalinsa,mahaifansa in suna raye,’yan’uwansa na jini,da sauran ‘yan’uwa da abokan arziki,saboda ba mamaki a cikin su akwai wanda ya yi masa wani abu ya sani ko bai sani ba.

4-Godiya ga  Allah Ta’ala na halittarsa da ya yi,kuma ya raya shi da kuma ni’imomi masu yawa da yayi masa a rayuwarsa.

5-Addu’a wato mutum ya ro}i Allah Ta’ala tare kuma da yin tawassuli da Manzon Allah[S] da kuma Ahlul bayt[AS] cewa wannan karshe nasa da yazo a wannan rayuwa ta duniya,Allah Ta’ala ya tausaya masa,ya kasance tare dashi,ya kiyaye shi daga azaba, ya saka shi cikin rahamarsa.

6-Wasiyya:Wato ya yi wasiyya ga iyalinsa ko ya’yansa  ko wani nasa na jini ko na addini.

7-Tazkiyyar naf’s ]insa wato mutum ya yi mujahada wajen ganin cewa ya tsarkake kansa,zuciyarsa ke nan da ga~o~insa, ya kasance dai kamar yadda yazo duniya yana tsarkake to ya bar duniya yana tsarkake,saboda kamar yadda Imam Khumaini ya yi bayani akan cewa rashin tazkiyya na naf’s yana haifar da tsanani da zafin fitar rai a lokacin mutuwa.

8-Ya tattali likkafaninsa:Mustahabbi ne mutum ya sai likkafani ya a je.Imam Sadi}[AS] yace, “Duk wanda ya tattali likkafaninsa ya aje a ]akinsa, to ba za a rubuta shi cikin gafalallu ba,saannan kuma za a rubuta masa lada duk lokacin da ya dubi likkafanin.”Akwai bayin Allah masu yawa ma’abuta himma da likkafanin su yake a je,kai wasu ma har }aburburansu suka gina da hannayensu tun gabanin rasuwarsu.

9-Idan }arshe ya zo ana so ya yenke tunaninsa baki ]aya daga duniya,ya mai da tunaninsa baki ]aya zuwa ga lahira.

            2-ABUBUWAN DA MUTUM ZAI YI KO ZA A YI MASA IDAN YA KAI GARGARA:Wato ya kai matakin da zai fuskanci tafiyar da ba dawowa,tafiya zuwa lahira,tafiyar da ta }unshi abubuwa na ban tsoro da tsanani da kuma tsawo.To a wannan lokaci ana so mutum ya }arfafa tunanin fata da }auna ga Allah Ta’ala da kuma kyautata zato gareshi.Wato dai a wannan marhala ana son fatansa ga Allah ya rinjayi tsoronsa.

1-Idan mutum ya kai ga wannan mataki na ganin alamomin mutuwa ko matakin fitar rai to WAJIBI ne a fuskantar da shi zuwa ga al}ibla,wato za a kwantar dashi ta rigin-gine,  }afafuwansa su kasance suna duban al}ibla ta yadda da za a zaunar dashi zai kasance yana duban al}ibla ne.Kuma yin wannan wajibi ne ga ko wane irin mamaci wato namiji ne ko mace,yaro ko babba.Idan haka bai yi yu ba,to sai a kwantar dashi ta sashen damansa yana mai fuskantar al}ibla ko kuma ta hanyar da ya sau}a}a ta fuskantar al}ibla.

2-Bayan haka kuma mustahabbi ne a la}}ana masa Kalmar shahada,da kuma furuci da Imaman Ahlul bayt  sha biyu.

3-Haka nan kuma mustahabbi ne  karanta masa suratu Yasin da kuma suratus-saffat.Haka nan kuma da karanta masa addu’ar faraj,yazo a ruwaya cewa karanta wa]annan surori da kuma wannan addu’a suna sau}e}e fitar rai.

4-Bayan haka idan mutum ya cika to mustahabbi ne a rufe masa idanuwa,a kulle bakin sa,a mi}ar da hannuwansa da kuma }afafuwansa,saannan kuma a lullu~e shi da tufafi wato kafin wanka ke nan.

5-Makruhi ne idan mutum ya kai gargara a barshi shi ka]ai.Haka nan makruhi ne idan ya kai wannan hali na fitar rai mai haila ko janaba ya kasance yana kusa dashi.

          3-HUKUNCIN TA~A GAWA:Idan mutum ya rasu,to duk wanda ya ta~a shi bayan jikinsa ya yi sanyi,ko kuma ya ta~a shi lokacin da ake yi masa wanka kafin a kammala,to WAJIBI ne mutum ya yi wanka,saboda haka ko da yana da alwala lokacin da ya ta~a shi,to alwalarsa ta warware.Amma da a ce lokacin da ya ta~a shi jikin nasa bai yi san yi ba ga baki ]aya ba,ko kuma ya ta~a shi lokacin da aka kammala masa wanka,to a wa]annan fuskoki guda biyu ba zai yi wanka ba.Haka nan ba zai yi wanka ba in ya ta~a shi da Hand glob wato irin safar hannu ta leda.Shi wannan hukunci na yin wanka ga wanda ya ta~a mamaci a wa]ancan fuskoki da aka ambata ya ke~anta ne  ga mazhabar Ja’afariyya,amma a fi}hun mazhabobi na Ahlus sunna kamar malikiyya,hanafiyya da sauransu ba su da wannan hukunci.Wani tambihi a nan shine wannan mamaci da ta~a gawarsa ke wajabta wanka ba wai sai ta musulmi kawai ba,a’a ko da ta kafiri ne.Haka nan kuma ba ta babba kawai ba,a’a hatta ma ta yaro,kai ko da ma ~ari ne in dai ya kai wata hu]u shima sai mutum ya yi wanka,kamar yadda Imam Khumaini ya yi bayani a littafin Tahriril wasila.Amma shahidin da aka kashe shi a fagen fama,ko kuma wanda aka kashe akan asasin haddi ko }isasi,to duka wa]annan idan mutum ya ta~a gawarsu ba zai yi wanka ba.Wata mas’ala kuma  ita ce maimaita shafar mamaci ko mamata bai maimaitar da wanka,wato da mutum zai ta~a mamata goma a lokaci guda to wanka ]aya zai yi.Haka nan da zai shafi mamaci,sai daga baya yana shakka shin gabanin jikin ya yi san yi ne ko bayan sa,to hukunci a nan shine wanka bai wajaba akan sa ba.Wata mas’ala kuma itace idan wani yanki na jikin mutum ya fita,misali a yi hatsari sai hannu ko }afa suka fita daga jiki,to idan mutum ya ta~a hannun ko }afar shima sai ya yi wanka.To tambaya ya ake wannan wanka na mamaci? Amsa shine  yadda ake wankar janaba.Insha Allah a darasi na gaba za a ]ora akai.

 
Home Darusan Fiqh Bayani kan sallar Mamaci 1
Copyright © 2024. www.tambihin.net. Designed by KH