Sunday, 25 February 2024
Email
Make My Homepage
RSS
Register
Bayani kan sallar mamaci [2}. Print E-mail
Written by administrator   
Sunday, 08 March 2015 19:45

A darasin da ya gabata bayani ya gudana  kan:

1-Abubuwan da mutum zai yi kafin ya mutu.

2-Abubuwan da mutum zai yi ko za a yi masa idan ya kai gargara.

3-Hukuncin ta~a gawa.Insha-Allah a wannan darasi bayani zai kasance kan:

1-Wankan gawa.

2-Sa likkafani ga Mamaci.

          1-WANKAN  GAWA:Hukuncin wankan gawa ta musulmi wajibi ne.Haka nan wajibi ne wanke gawar ‘ya’yayen musulmi ko da ko ta ]an zina ne,ko kuma  misali a haihu ba rai,kai ko da ma ~ari ne in dai ya kai wata hu]u to wajibi ne a yi masa wanka da likkafani sai a binne shi kamar yadda aka sani,amma da ~arin }asa da wata hu]u ne to anan ba wajibi ba ne a yi masa wanka,za a lullu~e shi a }yalle sai a binne.Amma gawar kafiri ko wanda aka yi ma hukunci da kafirci a cikin musulmi kamar Nawasib ko Kawarij to bai halatta a yi masu wanka ba.Wankan gawa farali ne kifa’i,wato idan wani ko wasu suka yi to nauyin ya fa]i akan saura.Haka nan shara]i ne wajen wankan gawa a samu abin da ake ce ma “Mumasala” tsakanin mai wankin gawar da kuma mamacin, wato namiji ya wanke namiji,mace ta wanke mace,akasi bai halatta ba.In da kawai akasi ya halatta sai idan gawar ta yaro ne ko yarinya wanda ba su wuce shekaru ukku ba,to a nan namiji zai iya wanke yarinya ko mace ta wanke yaro ba matsala.Haka nan mata da miji ko wannensu in ya rasu zai iya wanke ]ayan shima ba matsala.Haka nan ba matsala mutum ya wanke muharramarsa ko muharraminta amma fa da shara]in in ba bu mumasil.To idan ba a samu mumasil ba,misali namiji ne ya rasu ba kowa a wajen kuma sai mata,ko kuma irin abubuwan da suke faruwa a }asar nan yanzu a dirar ma gari ko }auye a kashe mazaje,a bar mata da gawawwakin to a nan wankan gawa ya fa]i.Amma a cikin gawawwakin idan akwai wadda akwai mijinta ko muharraminta to wajibi ne ta yi masa wanka.

          Yadda ake wankan gawa:Da farko wajibi ne a gusar da najasa daga jikin mamaci idan akwai.Bayan haka kuma wajibi ne a yi masa wanka sau ukku.Na farko za a yi masa wanka da ruwan da aka caku]a da magarya.Wanka na biyu kuma da ruwan da aka caku]a da kafur.Na ukku kuma da ruwa tsantsa wato wanda ba a ha]a shi da ko mai ba.To da a ce a lokacin da za a yi wankan an yi neman ]ayan wa]annan abubuwa biyu ba a samu ba,misali an nemi magarya ko kafur ba a samu ba,ko dukkansu biyun ba a samu ba,to anan maimaikon kowanne za a yi wankan ne da ruwa tsantsa,misali kamar a ce a wanka na farko da ake sa magarya to an nema babu to sai a yi masa wankan farkon da ruwa tsantsa,wanka na biyun da kafur in akwai,in shima babu sai a sake yi masa wanka da ruwa tsantsa.na ukkun dama shi da ruwa tsantsa ake yi.Wani tambihi anan shine wajibi ne wankan ya kasance akan tartibin da aka yi bayani,wato na farko ruwan a ha]a da magarya,na biyu ruwan a ha]a da kafur,na ukku ruwa tsantsa,to da a ce a wankar farko sai aka soma da ruwan da aka ha]a da kafur na biyu aka yi da na magarya,to anan sai an sake wankan,wato a soma da na magarya saannan na kafur.Yadda kuma ake ko wane wankan nan guda ukku shine irin yadda ake wankan janaba,wato a soma wanke kai da wuya.Saannan gefen jikin dama.Sai kuma gefen jikin hagu.Wata mas’ala kuma itace da a ce ba ruwan da za a yi ma mamacin wanka,ko kuma wankan ba zai yi yu ba  ga mamacin,to a nan maimakon wankan za a yi masa taimama ukku ne.Haka nan kuma da a ce akwai ruwan amma fa wanka guda kawai zai yi masa,to a nan sai a yi masa wanka gudan da shi bayan haka kuma sai a yi masa taimama guda biyu.Wata mas’ala kuma itace da mamaci zai rasu amma akwai wankan janaba akansa ko kuma wankan haila ko nifasi akanta,to anan idan an yi wankan gawar ya wadatar.Haka nan kuma lokacin da ake yi ma mamaci wanka sai wani abu na jikinsa ya fita misali gashinsa ko akaifa ko fata to lokacin da ake sa masa likkafani za a sa a ciki wato a binne su dashi.

          2-SA LIKKAFANI GA MAMACI:Shima hukuncinsa wajibi ne.Abubuwan da suke wajibi a likkafani guda ukku ne sune:

1-Gyafto wanda zai rufe tsakanin cibiya zuwa cinyoyinsa.

2-Riga wadda za ta kai zuwa ga rabin }waurin sa.

3-Mayafi wanda zai lullu~e duk jikin mamacin.Sauran abubuwan da ba wa]annan da aka ambata ba misali kamar sa rawani ga namiji ko ma}na’a ga mace da dai sauransu to suna matsayin mustahabbi ne.Haka nan mustahabbine  yadin likkafani ya kasance sabo,kuma ya kasance fari,ya kasance  wanda aka yi da auduga.Haka nan kuma mustahabbi ne likkafanin ya kasance wanda aka rubuta Jaushanul-Kabir a jiki.Daga cikin abubuwan da ya wajaba a yi ma mamaci bayan an yi masa wanka gabanin a sa masa likkafani ko lokacin da ake sa masa akwai TAHNI[,yadda ake yinsa shine za a shafa masa kafur a wajaje bakwai na sujudarsa sune:

1-Goshi.

2-Tafukan hannunsa biyu.

3-Kan gwiwowin }afafuwansa biyu.

4-Kan babban yatsun }afafuwansa biyu.Amma sawa a kan hanshinsa mustahabbine,wato wa]ancan ne suke wajibi. Haka nan kuma mustahabbi ne ga mutum tun yana raye lafiyar shi lau,ya tanadi kayan jana’izarsa ya aje,kamar likkafani,abubuwan wanka irin su magarya da kafur,da dai sauran abun da za a bu}ata lokacin jana’izarsa.Idan mutum ya bibiyi tarihin wasu bayin Allah zai ga haka suka yi tun suna raye,kai akwai ma bayin Allah da suka gina }abarin su da hannunsu tun suna raye,akwai wani da ya gina }abarinsa bayan haka ya sauke Al}ur’ani a cikinsa.Akwai kuma wani da ya gina }abarin nasa to ko wace rana ya kanje ya kwanta cikin kabarin na wani lokaci yana ro}on Allah ya mai da shi duniya zai yi aiki mai kyau,can sai ya tashi yai ma kansa waazi cewa an sake ba shi daman  ya da]a ayyuka,saboda haka kada ya yi wasa da wannan fursa da ya samu,a ta}aice yi ma mutuwa tanadi tun gabanin ta zo yana da fa’idodi masu yawa,wato baya ga samun lada na yin haka,ga kuma hutarwa ga ‘yan’uwa da abokan arziki bayan mutum ya mutu,saboda duk abin da za a je a nemo misali likkafani ne ko magarya ko kafur da dai sauransu to ya yi tanadin abunsa tun yana raye sai dai kawai a ]auko.Haka nan mustahabbi ne a caku]a kafur wanda za a yi tahni] da shi da Turba –Husainiyya,sai dai in an ha]a da ita ]in to ba za a shafi manyan yatsun }afarsa ba da ita,wato saboda girmamata kamar dai yadda Imam Khumaini ya yi bayani a cikin littafin Tahriril-wasila.Wata mas’ala itace kasantuwar yin wannan tahni] ]in wajibi ne,to idan ba a samu abun da za a yi dashi ba ya ke nan?,shi ke nan sai a yi masa jana’iza ba tare da tahni] ]in ba.Ko kuma akwai kafur ]in amma bai da yawa misali wanka ne kawai za a iya yi da shi,to nan za a yi wankan da shine sai a bar Tahni] ]in.Bayan haka kuma daga cikin sunnoni masu }arfi akwai sanya reshen itatuwa biyu ]anyayyu a jikin mamaci,wannan mamaci namiji ne ko mace,yaro ne ko babba.Itacen da aka fiso a yi dashi a mataki na farko shine itacen dabino,sai kuma itacen magarya,sai kuma itacen rumman,in ba a same su ba ana iyasa ko wane itace amma da shara]in ya kasance ]anye ne.Tsawon itacen ba a so ya wuce tsawon zira’i,}asa da zira’in duk ba matsala.Yadda ake sa shi shine:[aya za a sa shi gefensa na dama daga wuya zuwa in da ya kai,wato za a sa shi manne da jikinsa mubasharatan.Na biyu za a sa shi a gefensa na hagu shima daga wuya zuwa in da itacen ya tsaya,sai dai a wannan zai kasance ne saman rigarsa  }ar}ashin lifafarsa,wato dai za a sashi tsakanin rigarsa da lifafa,na farko kuma ya ta~a jikinsa.Sa wa]annan ]anyayyun reshen itatuwa da aka ambata yana da falaloli masu yawa kamar yadda yazo a ruwayoyi na hadisai,daga ciki akwai cewa ya kan zama sanadiyyar nisantar mutum daga azabobin }abari.Haka nan kuma akwai falala mai yawan gaske da kuma lada ga wanda ya raka janaza ko ya sallace ta.Haka nan kuma akwai ladubba masu yawa na ]aukar janaza,ga wasu daga ciki akwai:

1-Lokacin da mutum zai ]auki janaza ana son ya biya wannan addu’a “Bismillahi wa billahi wasalllahu ala Muhammad wa ali Muhammad,Allahumma  gfir lilmu’uminina wal-muuminat.

2-In dai ma}abartar ba ta da nisa to a ]auki gawar kan kafa]u ya fi a sata akan abun hawa,domin akwai falala da aka ruwaito a hadisi na ]aukar gawa akan kafa]u.Sai dai ko da ma}abartar ba ta da nisa in ansa gawar ga abun hawa ba komai,sai dai rasa waccan ladar da aka yi.

3-Wa]anda ke rakiyar gawa ana son ko wane mutum ya kasance cikin kushu’i,saannan ya kasance cikin tafakkur wato tunani na ya sawwala a ransa cewa kamar shine ya rasu an ]auko shi za a je a binne,amma ya nemi Allah Ta’ala ya dawo dashi duniya,kuma ya amsa masa.

4-Daga cikin ladubban janaza akwai cewa an fi son a yi tafiya bayan janaza ko gefenta,wato ya kasance gawar na gaba ana binta a baya ko gefenta, ba wai ta kasance a baya ba.

5-Daga cikin ladubban akwai cewa ya kasance wanda aka yi ma mutuwa in zai yiyu ya zamanto wajen jana’izar ba takalmi.Makruhine  a lokacin rakiyar janaza yin surutai ko dariya ballantana lagawu.Haka nan makruhi ne yin sauri da gawa wato a lokacin tafiya a }asa ko akan abun hawa,ana so a tafi tsaka-tsaki.Da dai sauran ladubba wa]anda suke mustahabbi ne ko makruhi aikata su ga jana’iza,ba za a iya kawo su duka ba saboda gudun tsawaitawa,ga mai bu}atar ganinsu yana iya komawa ga Risala-Amaliyya na mujtahidin da yake Ta}lidi da shi.Wani tambihi anan shine yana da gayar muhimmanci yin duk wasu ayyuka ko ladubba ga mamaci wa]anda suke matsayin wajibi da mustahabbi,da kuma nisantar duk wasu abubuwa da suke matsayin makruhi ballantana kuma haramun.Saboda  wannan mataki ko marhala shine katma ga rayuwar mamaci ta duniya,wato dai ya kasance kitamuhu-misk.Insha-Allah a darasi na gaba za a kammala wannan babin.

 

 
Home Darusan Fiqh Bayani kan sallar mamaci [2}.
Copyright © 2024. www.tambihin.net. Designed by KH