Sunday, 25 February 2024
Email
Make My Homepage
RSS
Register
Bayani kan sallar mamaci [3] Print E-mail
Written by Administrator   
Sunday, 08 March 2015 19:36

A darasin da ya gabata a cikin wannan babi,bayani ya kasance ne kan wankan gawa da kuma sa likkafani.To a wannan darasi wanda da shi insha-Allah za a kammala wannan babin bayani zai gudana ne kan:

1-Sallar mamaci.

2-Binne mamaci.

3-Abubuwan da za a yi ma mamaci bayan jana’izar sa.

          1-Sallar mamaci:Hukuncin yin sallah ga mamaci Musulmi wajibi ne.Kuma lokacin da ake yin sallah ga mamaci shine bayan an yi masa wanka an sa masa likkafani,idan aka yi masa sallar gabanin wankan da likkafani to bata yi ba.Haka nan sallar ba ta fa]uwa domin misali a ce ba ruwan da za a yi ma mamacin wanka ko kuma ba likkafanin da za a sa mashi ko kuma ba in da za a binne shi,wani misali da Imam Khumaini ya bayar a wannan mas’ala itace  a samu gawar musulmi a dokar daji ya kasance kuma ba zai yi yu ayi masa wanka ba,ko sa masa likkafani ko kuma binne shi ba,to shi ke nan sai ai masa sallar kawai.Haka nan ba shara]i ba ne wanda zai yi ma mamaci salla ya zama wajibi sai namiji,mace ko mataye za su iya gabatar da sallar kuma ta yi.Haka nan mustahabbi ne yin sallar mamaci cikin jam’i,wato a ha]u a yi ta jamaatan ya fi falala.saboda haka da mutum guda zai yi ma mamaci salla shi ka]ai to sallar ta yi.Wata mas’ala itace idan aka haifi yaro ko yarinya ba rai, to ba sai an yi masa sallah ba.Haka nan idan yaro ko yarinya suka kai shekara shidda to wajibi ne yi masu salla idan sun rasu,amma idan }asa da shekara shidda ne to mustahabbine yi masu sallar.

YADDA AKE SALLAR MAMACI

                    Da farko bayan mutum ya yi niyya na ita sallar mamacin,zai  yi kabbarori guda biyar,bayan ko wace kabbara akwai addu’a da mutum zai yi,addu’oin akwai masu tsawo akwai kuma gajeru.Ma fi }arancin addu’ar da mutum zai yi itace,Bayan mutum ya yi kabbara ta farko sai yace:Ashadu anla’ilaha illah-wa ashadu anna Muhammadan Rasululluh.Bayan mutum ya yi kabbara ta biyu sai yace:Allahumma salli ala Muhammad wa ali Muhammad.Bayan kabbara ta ukku sai yace:Allahumma gfir lilmuuminina-wal-muuminat.Bayan kabbara ta hu]u sai yace:Allahumag fir lihazal mayyit.Amma a nan idan mamacin yaro ne }arami to ana son yace:Allahumma ij-alhu-li-abwaihi-wa-lana-salafan wa-ajran.Bayan haka sai mutum ya yi kabbara ta biyar,shi ke nan  ya gama sallar mamacin.Ga mai bu}atar ganin wasu addu’oi da suka fi wannan tsawo,yana iya duba littafin Tahriril-wasila.Bai halatta mutum ya yi }asa da kabbarori biyar ba sai idan akan asasin ta}iyya ne,Idan muka duba zamu ga cewa ita sallar mamaci ba kiran salla cikinta ko i}ama ko karatu na Al}ur’ani,ko ruku’u ko sujuda ko tashahhud wato tahiya ko kuma sallama.Amma a mahanga ta ‘yan’uwanmu Ahlus sunna zamu ga cewa akwai sallama,haka nan kuma kabbarorin da suke yi guda hu]u ne ba biyar ba.A sallar mamaci ba shara]i ba ne sai mutum na da alwala,saboda haka za a iya yin ta ko da ba alwala,kai ko da ma mutum janaba yake da shi ko haila duk za a iya yi.Wata mas’ala itace idan mutum ya riski an soma sallar jana’iza,misali an yi kabbara ta biyu ko ta ukku to zai iya bi,amma ko da ana kabbara ta biyun ko ukun to zai kasance shi na shi a matsayin kabbara ta farko ne,idan liman ya kai kabbara ta biyar to sai shi ya }arasa nashi kabbarorin tare da addu’oin da ake yi tsakani,idan yin addu’oin ba zai yi yu masa ba,to sai ya yi kabbarorin a jere wato ba tare da yin addu’oin ba.Wata mas’ala kuma itace idan ana sallar jana’iza sai shakka ta kama mutum,misali yana shakka kan kabbara ta 2 ake ko ta 3 to a nan sai mutum ya yi gini a kan ka]an,wato ya ]auka kan ta 2 yake.Bayan haka kuma akwai wasu ladubba da ake son mutum ya kiyaye su a lokacin sallar janaza,ga wasu daga ciki:

1-Ya kasance mutum na da alwala lokacin sallar.

2-Idan an zo za a yi sallar to mutum ya cire takalmi.

3-Kabbarorin da ake yi guda biyar to ana so ko wace kabbara mutum ya ]aga hannuwansa biyu lokacin yin ta.

4-Idan sallar mamacin ta namiji ne to ana son liman ya tsaya a tsakiyar gawar mamacin,idan kuma mace ne to ya tsaya wajen }irjin ta,da dai sauran ladubba mutum na iya dubawa cikin risala amaliyya ta mujtahidin da yake bi.

          2-BINNE MAMACI:Shima hukuncin sa wajibi ne.Daga cikin mas’alolin da suke da ala}a da binne mamaci akwai wa]anda suke wajibine yin su,akwai kuma wa]anda suke mustahabbi ne yin su.Akwai kuma wa]anda suke yin su makaruhi ne,akwai wa]anda suke yin su haramun ne.Bayanan su sanka-sanka yana cikin littafan fi}hu.Wani tambihi anan shine wasu bayin Allah Ta’ala su kan bar wasiyya da cewa idan sun rasu asa kaza da kaza a cikin }abarin su,misali Ayatullahi Sayyid Mar’ashiy Annajafiy kafin ya rasu ya bar wasiyyar cewa idan ya rasu a saka a cikin }abarinsa }asa ko tur~aya da ya ]ebo ta daga }aburburan Imaimai da ya ziyarta.Haka nan ba}a}en tufafin da yake zaman makoki dasu suma asa mashi su cikin }abarinsa.Haka nan hankicin da yake share hawaye da shi wajen zaman makoki shima asa masa shi cikin }abarinsa.Haka nan tasbaha wato carbi da yake azkar dashi shima asa masa ciki.Haka nan wata darduma da ya kwashe shekara saba’in yana sallar tahajjud akan ta ita ma asa masa cikin }abarin sa.In muka duba zamu ga Sayyid Zakzaky[H] ya koyar damu wannan darasi a lokacin jana’izar ‘ya’yansa,yazo da turba Husainiyya da kuma duwatsu da aka ciro daga Haramin Imam Husain[AS] da na Abul Fadl Abbas[AS] ko wannen su ya sa masa cikin kabarinsa.Yin haka yana da fa’idodi masu yawa,wato baya ga kasancewarsu guzuri ga mamaci,to sukan kasance haske da ni’ima cikin kabarin mutum,a ta}aice dai za su da]a nawwara }abari.

          3-ABUBUWAN DA ZA A YI MA MAMACI BAYAN BINNE SHI:Akwai wasu ayyuka ko ladubba da ake son yi ma mamaci bayan kammala jana’izarsa,sai dai wa]annan ayyuka ko ladubba dukkansu mustahabbi ne yin su wato ba wajibi ba,amma saboda wannan shine ranar farko ko daren farko ga mamaci a rayuwarsa ta }abari yana da muhimmanci ya zamanto an yi su,domin yanzu ya zo maharlar da kowa zai ta fi ya bar shi,ya zamanto daga shi sai aikinsa,wato dai kamar yadda yazo a hadisi cewa idan mutum ya mutu abu ukku suna raka shi zuwa }abarin sa,iyalinsa dukiyarsa da kuma aikinsa.Iyalinsa da dukiyarsa za su dawo,aikinsa zai zauna tare dashi.Saboda haka yana da gayar muhimmanci ‘yan’uwa na jini ko na addini ga mamaci su aikata wa]annan ladubba ga mamaci bayan binne shi,domin zasu taimaka masa wajen samun sau}i ga zaman }abari ko kuma samun ni’ima da haske a makwancinsa.Ga wasu daga cikin wa]annan ladubba:

1-Tal}in,wato za a la}}ana ma mamaci Usul na a}idarsa misali abinda ya shafi tauhidi,nubuwwa da imama da dai sauransu.Akwai littafai na addu’oi da kuma Risala amaliyya ta wasu fu}aha da suka kawo sigar yadda ake wannan tal}in ]in misali mutum yana iya duba littafin Misbahul-mutahajjid a farko-farkonsa.Daga cikin fa’idodin wannan tal}in ]in shine yana tunku]e ma mamaci tambayoyin }abari.

2-Sa tafin hannunsa na dama akan }abarin,bayan haka ya karanta Inna anzalnahu }afa bakwai.Yazo a hadisi cewa duk wanda ya karanta Ina anzalnahu sau bakwai a }abarin mumini,to Allah Ta’ala zai aika da wani mala’ika ya dun ga ibadar Allah a jikin }abarin.

3-Yima mamacin addu’oi dabam dabam maasurai da wa]anda ba maasurai ba,wato wa]anda suka zo a ruwaya daga maasumai,in mutum ya duba cikin littafin Tahriril wasila na Imam Khumaini akwai addu’a maasura da ya kawo.

4-Yayyafa ruwa akan }abarinsa,yadda ake yi shine mutum zai fuskanci al}ibla sai ya soma yayyafa ruwan ta wajen kan mamacin har ya zuwa wajen }afafuwansa,saannan sai ya yayyafa a duka  sassan }abarin.

5-Salatul Wahasha,mustahabbine idan an binne mamaci to a darensa na farko da binnewar ayi masa wannan sallah ta wahsha.Yadda ake yinta raka’a biyu ne,raka’a ta farko bayan fatiha sai mutum ya karanta ayatul-kursiyyu sau ]aya.A raka’a ta biyu bayan fatiha sai ya karanta Ina anzalnahu sau goma.Bayan ya yi sallama sai yace, Allahumma salli ala muhammadin wa ali Muhammad,wab’as sawabaha ila }abri……..wato sai ya ambaci sunan mamacin.A wata ruwaya a raka’a ta farko bayan fatiha zai karanta {ulhuwallahu sau biyu,a raka’a ta biyu bayan fatiha zai karanta Alhakumu takasur sau goma,duk wanda mutum ya yi ba matsala.Ita wannan sallar wahasha ]in da daddare ake yin ta,sai dai mutum na da za~i ya yi ta ko da wane lokaci a cikin daren,wato ko a farkon daren ko tsakiyarsa ko kuma }arshensa,sai dai an fi son ayi ta a farkon daren wato bayan sallar isha’i.Wata mas’ala da wasu mujtahidai suka fitar itace,idan ya kasance mamaci ya rasu amma ba a yi jana’izar shi a ranar ba,sai kashe-gari ko kwanaki to ya sallar wahasha zata kasance? Amsar da suka bayar shine mutum ya yi ]ayan biyu,ko dai ya bar sallar har ya zuwa ranar da aka binne mamacin,ko kuma ya yi sau biyu wato ya yi a ranar da mamacin ya rasu da daddare da kuma ranar da aka binne shi da daddare,wannan shi ya fi zama ihtiya]i.Kuma yana da kyau mutum ya saba ma kansa yin wannan sallah ta wahasha ga ‘yan’uwansa na jini da kuma addini idan sun rasu,akwai ma wani ]an’uwa da na sani ko wane dare sai yayi wannan sallar ta wahasha da niyyar duk wani mumini ko mumina da suka rasu a ranar a duniya baki ]aya.

 


 
Home Darusan Fiqh Bayani kan sallar mamaci [3]
Copyright © 2024. www.tambihin.net. Designed by KH