Muhimmancin Hadin kai {Wahda}. |
Written by administrator | |||
Thursday, 01 January 2015 20:57 | |||
Kasantuwar wannan wata da muke ciki na Rabiul-Awwal,a kan yi taron makon ha]in kai a wannan nahiya ta mu da kuma sauran }asashe musamman ma na mabiya Ahlul bayt.Wanda a irin wa]annan tarurruka a gan gayyaci Malamai na wa]annan makarantu guda biyu wato sunna da shi’a tare da ba su maudu’oi dabam dabam da za su gabatar da jawabai a kai.Saboda haka wannan maudu’i na ha]in kai,maudu’i ne mai muhimmancin gaske musamman ma saboda halin da Musulunci da musulmi suke ciki a wannan zamani na mu a kuma duniya baki ]aya.Domin in mutum ya bibiyi tarihin wannan al’umma ta Manzon Allah[S] zai ga babu wani lokaci da take da tsananin bu}ata na ha]in kai kamar wannan lokaci.Saboda idan mutum ya duba tarihin wannan al’umma ta musulmi zai ga cewa an yi wani lokacin da da]i da ba da]i musulmi na da izza kuma musulunci na da izza.Amma mu duba wannan lokaci da muke ciki yadda a ke cin zarafin musulmi a ke kuma izgili da addinin Musulunci wato ana ~arna da zubar da jinanan mutane da sunan wai addinin Musulunci.A irin wannan mawuyacin lokaci da musulmi ke da bu}atuwa babba ta ha]in kai a tsakaninsu,amma abin ta}aici da ba}in ciki rarraba tsakanin musulmi ta na da]uwa. Duk da cewa idan mutum ya yi bincike zai ga akwai hadisai da suka zo da bayanin cewa daga cikin alamomin da za su auku gabanin bayyanar Imam Mahdi[AS] akwai tsanantar rarraba tsakanin musulmi da kuma salla]uwar kafircin duniya akan musulmi,amma wannan ba zai hana yin sa’ayi ta fuskoki dabam dabam domin ganin cewa musulmi sun samu ha]in kai ba.Akan wannan manufa ne Imam Khumaini[KS] ya assasa makon ha]in kai a 1982,wanda bayan haka wasu }asashe na musulmi suma suke yi,kyakkyawan misali a wannan }asa da muke ciki.Wanda a yanzu haka an kwashe shekaru ko wace shekara a wannan wata akan gudanar da mako na ha]in kai cikin wannan Harka }ar}ashin jagorancin Sayyid Zakaky[H].Bayan wannan ‘yar shinfi]a bayani kan wannan maudu’i na Ha]in kai zai kasance kan wa]annan ababe 1-Ma’anar Ha]in kai. 2-Muhimmancin Ha]in kai. 3-Addinin musulunci ya assasu kan ha]in kai. 4-Illolin rashin Ha]in kai. 5-Fa’idodin Ha]in kai. 6-Abubuwan da suke janyo rashin Ha]in Kai. 7-Abubuwan da suke janyo ha]in kai. 8-Gudunmawar Sayyid Zakzaky[H] domin Ha]a kan musulmin wannan }asa. 1-Ma’anar Ha]in kai:Da yawa wasu daga cikin musulmi in ana maganar ha]in kai su kan ]auka kowa ya bar fahimtar sa ya zo ga wata fahimta.Saboda haka yana da kyau a fahimci cewa ha]in kai tsakanin musulmi ba yana nufin ]an Malikiyya ya zama ]an Ja’afariyya ba ne,ko kuma mai bin mazhabar Shafi’iyya ya koma mazhabar Hanafiyya,ko mutum na kan A}ida ta sunna ya koma ta Shi’a.A’a ko ya ri}e A}idar sa da Mazhabarsa,amma a kusanci juna ta yadda za a samu fahimtar juna,domin ci gaban Musulunci da kuma dun}ulewa domin fuskantar ma}iya Musulunci da musulmai.Akwai Ta’arifin da Ayatullah Shahid Mu]ahhary ya yi na ma’anar ha]in kai,yake cewa, “Ha]in kai ba shine narkewar mazhabobi dabam-dabam zuwa ga mazhaba guda ba,ko kuma ayi ri}o da abubuwan da aka ha]u a kuma yi watsi da abubuwan da aka sa~a,wannan a hankalce da kuma a aikace ba zai yi yu ba,abin da yake nufi shine musulmi su dun}ule sahu guda saboda fuskantar ma}iyansu. 2-Muhimmancin ha]in kai:Ko da a ce babu ayoyi ko hadisai da suka zo da bayani dangane da muhimmancin ha]in kai to hankali da ]abi’a sun isa su tabbatar da muhimmancinsa to ballantana kuma ga ayoyi na Al}ur’ani da Hadisai na Manzon Allah[S] masu yawa da suke nuna muhimman ha]in kai tsakanin musulmi da kuma yin kashedi dangane da rarraba.Saboda haka ha]in kai yana daga cikin mas’alolin da addinin musulunci ya }arfafa.Shi yasa zamu ga ma}iya Musulunci da musulmi babbar hanyar da suke bi domin raunana musulmi da kuma mallakarsu,shine haifar da rarraba da sa~ani a tsakaninsu. 3-Addinin Musulunci ya assasu kan ha]in kai:Idan mutum ya dubi addinin Musulunci ta ko wace fuska mutum zai ga cewa ya ginu akan ha]in kai,domin bai san banbancin }abila ko harshe ba,ko launin fata,ko ‘yan }asanci ko kuma ~angaranci da dai sauransu.Haka nan in mutum ya duba ibadodi da aka wajabta mana misali Sallah,Azumi,Hajji duk suna nuna manufa ta ha]in kai,wato salloli na jam’i da ake yi na ko wace rana,da sallar jumma’a a ko wane mako,haka nan sallar Idi sau biyu a ko wace shekara.Ga kuma taron musulmi na aikin hajji ko wace shekara da dai sauransu.Haka nan kuma idan mutum ya duba a janibobi dabam dabam na addini, musulmi baki ]aya sun yi tarayya akai,shi yasa in mutum ya lura da kyau zai ga cewa abubuwan da muka ha]u akai sun fi yawa kan abubuwan da suka rarraba mu. 4-Illolin rashin ha]in kai:Idan mutum ya yi nazari zai ga cewa illolin da rashin ha]in kai na musulmi ya janyo suna da yawa kuma ta fuskoki dabam dabam,alal misali ya janyo rauni tsakaninsu.Ya janyo salla]uwar ma}iya akan su.Ya janyo gaba da }iyayya tsakanin su.Ya janyo cin zarafi da izgili da addinin su.Ya janyo }as}anci da wala}anci garesu.Ya janyo rashin mutunta juna da kuma munana ma juna zato.Ya janyo jifar juna da miyagun maganganu da }aryaryaki.Ya janyo kafirta juna da yi ma juna sharri da makirce-makirce.A ta}aice dai illolin da rashin ha]in kan musulmi ya haifar ba ka]an bane wato la tuaddu wala tuhsa. 5-Fa’idodin ha]in kai:Da al’ummar musulmi za su ha]a kai to fa’idodin da haka zai haifar masu yawa ne.Misali za su kasance su da addininsu masu izza.Za su kasance abun tsoro ga ma}iyansu.Za su kasance masu ‘yanci wajen gudanar da al’amuransu na addini.Za su kasance masu so da kuma }aunar juna.Za su kasance masu girmama juna da kuma fahimtar juna.Za su zamo masu yi wa juna uzuri da kuma kyautata zato.Zai janyo taimaka ma juna.Zai janyo kyakkyawan zamantakewa da juna.Zai janyo ci gaban Musulunci,da dai sauran fa’idodi masu yawa. 6-Abubuwan da suke janyo rashin ha]in kai:Wa]annan abubuwa suna da yawa amma ga wasu daga ciki.1-Jahilci:So da yawa za ka ga wasu sakamakon sun jahilci fahimtar wasu ko abin da suke akai,sai ka ga haka ya haifar da adawa da }iyayya.Alhali da za su yi karatu ko bincike da sun samu waraka dangane abubuwan da ba su fahimta ba,domin ba mamaki su ga hujjojin abin da wa]ancan suke akai a littafansu.2-Ta’assubanci:Wani lokaci kuma rashin ha]in kai ya kan kasance ne sakamakon ta’assubanci,wato mutum ya ga cewa fahimta ta A}ida ko mazhabar da yake akai itace kawai dai dai,na sauran musulmi kuma ba dai dai bane.Ko kuma ta’assubanci akan asasin abun da mutum ya gada, wato mutum yaga cewa fahimtar da ya gada ta addini itace kawai dai dai,wata fahimta sabuwa da ya ga ta shigo ita ba dai dai ba ne.3-Son duniya:Wani lokaci kuma daga cikin abubuwan da suke janyo rashin ha]in kai,akwai son tarkacen duniya misali matsayi ko dukiya da dai makamantansu,saboda haka sai ka ga wani malami da yazo a ha]a kai, saboda wa]annan tarkacen duniya da yake so ko yake samu,sai gwammace yana ware shi da almajiransa. 7-Abubuwan da suke janyo ha]in kai:Suma suna da yawa daga ciki akwai:1-Duba littafan juna,wato ya kasance ana karanta littafan da ma’abuta fahimtar suka rubuta,ba littaffan da ma}iyinsu suka rubuta ba,domin wani abin mamaki sai ga wanda yake daawar shi malami ne ya ]auki abinda ma}iyan wa]ansu suka rubuta akansu na }aryaryarki da }age-}age ya zauna akai kuma yana ya]awa.2-Sa maslahar addinin Musulunci a gaba wato ba maslahar kawukanmu ba.Ya kasance tunaninmu da kuma fa]i tashinmu ya za mo wajen cigabar da addinin ne.3-Mutum ya fahimci cewa addinin musulunci yana da fa]in gaske,saboda haka ya kasance yana da yelwatacciyar zuciya na kar~ar abun da yake ganin ba}o ne a gare shi,wato akan asasin hujjojin da ya gani ko yaji.4-Daga cikin hanyoyin da ke janyo ha]in kai,ya kasance mutum na da bu]a]]iyar zuciya na iya yin kyakkyawan muamala da wanda fahimtar su ba ]aya ba.Domin wani za ka ga ba wai muamala ba, ko sallama ka yi masa ba zai amsa ba,da dai sauran hanyoyi. 8-Gudun mawar Sayyid Zakzaky domin ha]a kan musulmin wannan }asa:Idan mutum ya bibiyi tarihin wannan Harka zai ga yadda Sayyid[H] ya yi sa’ayi,yake kuma yi wajen ha]a kan al’ummar musulmi da kuma ganinsu a matsayin musulmi.misali gudanar da makon ha]in kai,ziyarar malamai a lokutan jauloli da dai suransu na ababe da ke kawo ha]in kai da kuma kusantar juna.Wanda idan mutum ya dubi dukkan jama’a na }ungiyoyi dabam-dabam da ake da su a wannan }asa zai ga babu wasu da suke sa’ayi wajen samun ha]in kan musulmi kamar Sayyid[H] da mabiyansa,kuma idan mutum ya bibiyi tarihin wannan da’awa zai ga haka abun ya faro,wato tun farko Malam bai tsuke kansa ba akan cewa ga wasu sashe na musulmi da bai mu’amala da su ko kuma a ce yana ganin su a matsayin wa]anda ba musulmi ba,shi yasa in mutum ya duba zai ga cewa Sayyid[H] tun farkon Harkar nan ya gina mu na yin sallah a ko wane masallaci wato ba tare da banbancewa ba na cewa ai wannan masallacin na ‘yan kaza ne ko ‘yan kaza.Haka nan mu duba yadda Sayyid[H] ya gina almajiransa wajen ziyartar sauran malamai da kuma zuwa jajanta masu idan wata musiba ta same su.Haka nan mu duba yadda Sayyid[H]yake taimaka ma ma}wabtansa ba tare da banbancewa ba na fahimtar da ka ke akai, da kuma masu neman taimako da kuma yadda almajiransa suke taimaka ma gajiyayyu da kuma mabu}ata musamman ma a lokutan maulidodi.Wanda ire-iren wa]annan abubuwa da aka ambata wanda Sayyid[H] yake yi da kuma almajiransa to hanyoyi ne na samun ha]in kan alummar musulmi,kuma a wannan fage lalle mutum ko ya}i ko ya so Sayyid[H] ya samu babbar nasara akai.Wanda mutum zai ga cewa sassan mutane dabam-dabam suna godiya da kuma yaba ma Sayyid[H] akai,kuma wannan ba ya ta}aita ga musulmi ba, a’a hatta wasu wa]anda ba musulmi ba zaka ji suna yaba ma Sayyid[H] akan haka, kai wasu ma wa]anda ba musulmi ba har ziyara suke kai masa domin yin godiya na irin taimakawa da kuma kariya da almajiransa suka basu a lokutan rikice-rikice. Daga }arshe nasiha ga masu sa ayi wajen haifar da rarraba da sa~ani tsakanin musulmi, yana da kyau su yi tunani dangane da halin da Musulunci da Musulmi suke ciki a wannan kasa dama sauran kasashen Musulmi na yadda ma}iya addinin musulunci da ‘yan barandansu suka hada kansu suka dunkule suna fada da Musulunci da Musulmi, mu dubi abubuwan da suke faruwa a wannan kasa da muke ciki da Palasdin, Afganistan, Irak,Pakistan , da dai sauransu. Ashe wannan ba darasi ba ne, cewa mu ma musulmi na wannan kasa mu hada kai mu dunkule waje daya, amma maimakon haka sai mu rinka wa’azi ko bayanai na suka, da ma kafirta juna, wanda irin wannan ba abin da zai janyo mana face rauni da kuma rarraba a tsakaninmu. Daga karshe makiyanmu su za su amfana daga wannan rauni da kuma rarraba. kuma idan muka dubi magabatanmu zamu ga cewa duk da banbance –banbancen dake tsakaninsu na mazhabobi da ma akida, haka suka rayu da juna suka yi wa musulunci aiki, har suka koma ga Allah {T} a haka. Saboda haka yana da muhimmanci mu yi tunani da kuma nazari na hali da kuma yanayin da alummar musulmi a duniya baki ]aya suke ciki,saboda haka akwai gayar bukatar ta fahimtar juna da kusantar juna domin samun wannan hadin kai. Allah Ta’ala ya da]a ha]a zukatanmu da kuma kawukanmu, ya kuma nisanta duk abinda zai zama rarraba da sa~ani a tsakaninmu,ya kuma taimakemu akan ma}iyanmu.
|