Hujjoji da Nasiha ga masu sukar Maulidin Manzon Allah {S}. |
Written by administrator | |||
Thursday, 01 January 2015 20:42 | |||
Da farko ina taya ‘yan uwa musulmi murnar zagayowar wannan wata mai albarka na Rabi’ul Awwal, wanda a cikinsa aka haifi fiyayyen halitta, kuma wanda yafi kowa matsayi a wajen Allah {T}, wato Manzon Allah {S} wanda saboda so da kuma girmamawa gare shi ne {S} mafiya yawan al’ummar musulmi a wannan }asa da ma sauran }asashen musulmi, suke tarurruka daban-daban da suke da ala}a da haihuwarsa da kuma ayoyin da suka bayyana a lokacin haihuwarsa, rayuwarsa gabanin aiko masa da sa}o, rayuwarsa bayan aiko masa da sa}o da wahalhalun da ya sha wajen isar da sa}on, har ya zuwa hijirarsa daga Makka zuwa Madina da kuma abubuwan da suka gudana bayan komawarsa Madina, wato ya}o}i, kamar su Badar,Uhud, da dai makamantansu, har dai ya zuwa komawarsa ga Allah {T}. A ta}aice wa]annan tarurruka sun }unshi bayani dangane da tarihinsa da kuma rayuwarsa mai albarka. Sai dai duk da haka akwai sashen musulmi da suke suka ga irin wadannan tarurrukan, suna siffanta su da cewa bidi’a ne kuma haramun ne a yi. Saboda haka a nan, Insha Allah zamu kawo hujja daga Alkur’ani mai girma, da hadisai da kuma bayanai na fitattun malamai na Ahlus-Sunnah kan wannan al’amari, wanda daga }arshe mu yi nasiha ga masu irin wannan suka. A cikin Suratul A’araf, aya ta 157, idan mutum ya duba zai ga can wajen }arshen ayar, Allah Ta’ala na cewa wadanda suka yi imani da shi suka girmamashi suka taimake shi, suka kuma bi haske wanda aka saukar tare da shi to wadannan sune masu cin nasara, mahallush- shahid, wato Maganar da ake yi a nan itace wannan kalma ta “Wa’azzaruhu”, da cewa “suka girmamashi” saboda haka kamar yadda aka ambata a baya, ]aya daga cikin manufar yin wadannan tarurruka shine girmamawa ga Manzon Allah {S}, kuma ita wannan girmamawa ba ta ke~anta ga lokacin da yake raye ba, a’a har bayan rayuwarsa. To, abin tambaya anan shine, shin irin wadannan tarurruka da ake gudanarwa wadanda a cikin su a ke bayani dangane da tarihinsa da darajoji da kuma matsayi da Allah Ta’ala yayi mashi a wannan gida na duniya da kuma lahira, ba nau’in girmamawa ne gare shi ba? Da sauran ayoyi da yawa da suka zo cikin Alkur’ani da suke nuni ga girmamawa ga Manzon Allah {S}. Akwai hadisi da aka ruwaito,Manzon Allah {S} yace “Abubuwa guda uku duk wanda yake da su to hakika ya samu za}in imani, ]aya daga cikin su shine Allah da Manzonsa su fi soyuwa gare shi akan kowa”. Har wala yau, akwai wani hadisi wanda yazo cewa Manzon Allah {S} yace “[ayanku ba zai yi imani ba har sai na fi soyuwa gare shi akan ]ansa da iyayensa da mutane baki ]aya” Ashe wadannan tarurruka ba nuna so ne ga Manzon {S} ba? Haka nan kuma idan muka koma ga bayanai na fitattun malaman Ahlus-Sunnah kan wannan taro na Maulidi, zamu ga cewa mafiya yawa ba su yi suka a kan asalin shi taron ba, abinda suka yi suka akai shine, idan an gwamashi da abubuwan da suka sa~a wa shari’a. Ga misalai na bayanan wadansu malamai: Ibnu Taimiyya yana ganin asalin taron Maulidi, duk da cewa magabata ba su yi ba amma bai sa~a wa ka’idar shari’a ba. Mutum ya duba a cikin littafinsa, wanda ake cewa Iktida’us Siradil Mustakim, abinda ya shafi Maulidi ga hakikanin abinda ya fadi a littafin, “Haka nan abinda mutane suka kirkira, imma saboda kwaikwayon nasara ga haihuwar Annabi Isa {AS}, ko kuma saboda son su da kuma girmamawa ga Manzon Allah {S} to Allah zai yi masu sakamako na lada akan wannan so da kuma wannan ijtihadi amma ba’a kan bidi’a ba”. Idan kuma mutum ya koma ga abinda Suyudi yace dangane da taron Maulidi, a duba a cikin littafinsa mai suna Al-hawi Lil Fatawi, ga hakikanin abinda ya ce a cikin wannan littafi nasa “A wurina asalin yin maulidi wanda shine taron mutane da karantar da abinda ya saukaka daga cikin Alkur’ani da ruwayoyi na hadisai wanda suka zo dangane da haihuwar Manzon Allah {S} da kuma ayoyi da suka bayyana a lokacin haihuwarsa, sannan bayan haka aci abinci a watse ba’a kara komai akai ba, to wannan bidi’a ce kyakkyawa wadda za’ayi wa wanda yayi haka sakamako mai kyau. Saboda abin da haka ya kunsa na girmamawa ga Manzon Allah {S} da kuma nuna farin ciki da kuma albishir ga wannan haihuwa tasa mai daraja”. Wannan ke nan a takaice, haka nan yazo daga Shafi’i wanda shine shugaban mazhabar Shafi’iyya cewa “Abubuwan da aka kirkira na al’amura sun kasu kashi biyu, na daya abinda aka kirkira wanda ya sa~awa Kur’ani ko Sunnah ko Ijma’i, to wannan bidi’a ce ~atatta. Na biyu, abinda aka kirkira na alheri wanda bai saba wa wadannan abubuwa da aka ambata ba, to wannan abinda aka kirkira ba abin suka ba ne”. Saboda haka, hujjar da masu wannan suka na taron Maulidi suke kawowa na cewa wannan taro Manzon Allah {S} bai yi ba, sahabbai ba su yi ba, a kwatanta da maganar wadannan fitattun malamai musamman maganar Shafi’i. in kuma mai irin wannan fahimta yace shi duk bai yarda da hujjojin da aka kawo ba, to akwai hadisi wanda Muslim ya ruwaito, wanda kuma sanannen hadisi ne cewa Manzon Allah {S} yace “Duk wanda ya sunnata sunnah kyakkyawa a cikin musulunci to yana da ladarta da kuma ladar wanda ya aikata ta a bayansa” Ashe a taru a tunatar da kuma ilmantar da juna dangane da tarihin Manzon Allah {S} da kuma rayuwarsa mai albarka da wahalar daya sha wajen isar da wannan sako da yazo da shi, ba sunnah kyakkyawa bace.Saboda haka ba hujja ba ce ka ce wai Annabi bai yi ba,ko sahabbai ba su yi ba,domin duk wanda ya ce maka Manzon Allah[S] bai yi maulidi ba to ya kawo maka in da Manzon Allah[S] ya ce ka da a yi.Ko ya ce sahabi bai yi ba,to ya kawo maka in da sahabin ya ce ka da a yi.Masu irin wannan fahimta ta sukar yin Maulidi,alal misali musabakar Alkur’ani da suke yi,alhamdu-lillah abu ne mai kyau a wajenmu,to amma da za a tambaye su,su kawo wani hadisi da Manzon Allah[S] yace a yi musabakar har idan mutum ya yi nasara a kawo wani abu a ba shi? Kuma idan muka koma ga fanni na Usulul fikhi, zamu ga cewa, ka’ida ga asalin abubuwa itace halasci, sai dai idan nassi yazo da yake nuni ga haramcinsa, ala ayyi halin dai wannan ke nan dai a takaice. Saboda haka yin taron Maulidi mafi yawan Malaman Ahlus-sunna magabata sun tabbatar da shi sun kuma kwadaitar da jama’a ga yi.Haka nan ko da a wannan zamani namu in mutum ya bincika zai ga mafi yawan Malaman Ahlus-sunna basu sukar yin maulidi.Saboda haka masu sukar maulidi in mutum ya duba zai ga cewa ‘yan kadan ne cikin Ahlus Sunna,masu ra’ayin kafirta musulmi.Shi yasa idan mutum ya yi bincike mai zurfi zai gano cewa,asasin fahimta ko mashaya ta Madrasar Ahlus-Sunna ta kasu kashi biyu:Akwai wa]anda suka assasu akan koyarwar Bani umayya,masu irin wannan fahimta za ka ga su suke sukar Maulidi.Haka kuma duk wani abun da ya shafi Ahlul bayt suna nisantar sa ko kuma ba su girmama shi.Haka nan za ka same su suna da tsananin }iyayya da gaba ga mabiya Ahlul bayt wato ‘Yan shi’a.Kuma suna kafirta sauran musulmi.Haka nan duk wani abu na neman tabarruki daga bayin Allah suna fa]a da shi cewa wai yin haka shirka ne.A ta}aice dai masu irin wannan fahimta in mutum ya bibiyi tarihi da kuma wannan zamani da muke ciki zai ga cewa sun zama babbar matsala ga alummar musulmi,haka nan kuma suna ba da mummunan sura ga musulunci da musulmi.Ko a wannan }asa da muke ciki duk wanda ya kai shekaru 40 zuwa sama zai tabbatar maka cewa ya taso bai ji ana sukar maulidi ba,saboda haka wannan guba daga baya ta shigo mana.Kashi na biyu sune wa]anda suka assasu akan koyarwar sahabbai,ta yi yu mutum ya yi tambaya yace to su wa]ancan kashin farko basu bin koyarwar sahabbai ke nan? Abin da ake nufi shine tasirin umayyanci a fahimtar su tafi yawa,shi yasa zaka ga hatta ga ‘yan’uwansu Ahlus sunna akwai sa~ani ta fuskoki dabam dabam musamman ma ga abubuwan da suka shafi Ahlul bayt ko kuma darajoji na Manzon Allah da makamantansu. Amma in muka juya ga mabiya Ahlul bayt za mu ga akasin haka,wato babu wani ]an shi’a da zaka ji yana sukar maulidi.Wanda wannan maulidi bai ta}aita ga na Manzon Allah[S] ba,dukkan maulidodi na Imaman Ahlul bayt da kuma na Sayyida Fadima[AS] ba bu wanda bas u yi.Haka nan kuma dukkanin munasabobi na ranakun wafatin su ko shahadarsu ba bu wanda ba su yi.Shi yasa mabiya Ahlul bayt kusan ko da wane lokaci suna damfare ne da wata munasaba ta addini,saboda ko wane wata na musulunci za ka samu wata munasaba a cikinsa ko ta haihuwar wani Ma’asumi ko kuma wafatinsa.Kuma irin wadannan ranaku na wadannan munasabobi galiban akwai ayyuka na ibadodi da ake yi a cikinsu.Saboda haka kiyaye irin wadannan munasababo suna da fa’idodi masu yawa,wato baya ga ladar da mutum zai samu da kuma ilimantarwa,domin a tarurruka na wadannan munasabobi akan tunasar da juna da kuma ilimantar da juna. Daga }arshe nasiha ga masu wa]annan soke-soke, yana da kyau su yi tunani dangane da halin da Musulunci da Musulmi suke ciki a wannan kasa dama sauran kasashen Musulmi na yadda ma}iya addinin musulunci da ‘yan barandansu suka hada kansu suka dunkule suna fada da Musulunci da Musulmi, mu dubi abinda yake faruwa a Palasdin, Afganistan, Irak, , da dai sauransu. Ashe wannan ba darasi ba ne cewa mu ma musulmi na wannan kasa mu hada kai mu dunkule waje daya, amma maimakon haka sai mu rinka wa’azi ko bayanai na suka, da ma kafirta juna, wanda irin wannan ba abin da zai janyo mana face rauni da kuma rarraba a tsakaninmu. Daga karshe makiyanmu su za su amfana daga wannan rauni da kuma rarraba. kuma idan muka dubi magabatanmu zamu ga cewa duk da banbance –banbancen dake tsakaninsu na mazhabobi da ma akidu, haka suka rayu da juna suka yi wa musulunci aiki, har suka koma ga Allah {T} a haka. Kuma mu duba mu yi tunani ga ayoyi da hadisai da suka yi nuni ga muhimmancin hadin kai da kuma wadanda suke nuni da kuma kashedi ga rarraba. Allah Ta’ala ya da]a ha]a zukatanmu da kuma kawukanmu, ya kuma nisanta duk abinda zai zama rarraba da sa~ani a tsakaninmu,ya kuma taimakemu akan ma}iyanmu.
|