Saturday, 02 December 2023
Email
Make My Homepage
RSS
Register
Ranar Arba’in ]in Imam Husain [AS] Print E-mail
Written by administrator   
Monday, 08 December 2014 09:54

Ranar arba’in ]in Imam Husain [AS] rana ce wadda take da muhimmanci,musamman ma  ga mabiya Ahlul bayt [AS],kuma ziyartar Imam Husain a ranar yana daga cikin alamomin mumini,kamar yadda haka yazo a hadisi da aka ruwaito daga Imam Hassan Al-askari [AS],in da yace, “Alamomin mumini [wato ]an shi’a] guda biyar ne.

 1.Yin salla raka’a 51 ko wace rana.

 2.Ziyarar arba’in.

3.Sa  zobe a dama.

4.Sa goshi da kumatu a }asa [ta’afir].

 

 5.Bayyana karatun bismillahi a sallah.”                                                                                  

 

Amma kafin bayani dangane da wannan hadisi da kuma  ranar arba’in ]in,zai yi kyau a ]an yi bayani a ta}aice dangane da matsayin adadin  arba’in  a  addinin musulunci.Adadin  arba’in  yana  da wani asrar gaibiyya a wajen Allah [T] da kuma tarkizi na musamman a wasu ayoyi na Al-}ur’ani mai girma,da kuma wasu hadisai da aka samo daga Manzon Allah [S] da kuma Ahlul bayt [AS],ga misalin wasu daga cikin wa]annan hadisai,an samo daga Imam Sadi} [AS] yace, “Idan mumini ya rasu,mutane 40 daga muminai suka halarci jana’izarsa,[cikin addu’ar da sukayi masa] suka ce ‘ya ubangiji! Bamu san komi dangane dashi ba sai alheri,kai ka  fi mu saninsa, Allah [T] zai ce na zartar da shaidarku,na  gafarta  masa na abin da na sani da abunda ku baku sani ba.”.                                                                                                                                

 

Haka nan kuma daga Imam Sadi} [AS] yace, “Babu wasu jama’a 40 da zasu ha]u  suyi addu’a  a kan wata bu}ata tasu face Allah [T] ya kar~a musu”.har ila yau daga Imam Sadik [AS] yace, “Duk wanda ya gabatar da muminai 40 gabanin addu’arsa,bayan haka ya gabatar da addu’a  ta bu}atarsa,to Allah[T] zai kar~a masa”kuma wannan wani abu ne wanda yake da gayar muhimmanci da falala,na kowannenmu ya sabawa  kansa  da yin haka,wato na addu’oi ga muminai  guda 40,in son sa mune a kowane dare  a }unut na witri,ko kuma bayan ya gama sallar tahajjud ]insa,in ba zai iyayi ko wane dare ba to a}alla duk daren juma’a  mutum ya lizimci hakan,domin yin hakan ya na da fa’idodi masu yawan gaske,kuma sunna ce daga cikin sunnonin ma’asumai [AS],alal misali yazo akan cewa sayyida fatima [AS] in ta gama sallar tahajjud ]inta, takan yi addu’oi  ga muminai na kusa da na nesa,shine har Imam Hasan [AS] yake ce mata “Na kan ji ki kan yi addu’oi  ga mutane,amma ban ji kina addu’a gare ki ba”.shine tace masa, “ma}wabci gabanin gida”.                                                                                                             

 

Haka nan kuma akwai hadisi da aka samo daga Manzon Allah [S] yace, “Duk wanda ya kiyaye wa al’ummata hadisai 40 da suka shafi al’amarin addininsu,baya  nufin  komai  face  yardar Allah [T] da kuma gidan lahira,to Allah zai  tashe shi ranar }iyama a matsayin  fa}ihi kuma Malami” wannan hadisin yasa  da yawa daga cikin malaman madrasah ]in Ahlul bayt [AS] da kuma ta Ahlus  sunna,  suka rubuta littafai na hadisai  40 domin samun falalar wannan hadisi,misali  anan  shine  littafin hadisi 40 na Imam khumaini da kuma littafin hadisi 40 na Imam Nawawi,in mutum ya duba littafin hadisi 40 na Imam khumaini, zai ga cewa a wajen gabatarwa na littafin yana cewa ya tattara wannan hadisai ne da fatan ya samu shiga cikin hadisin Manzon Allah [S] da yazo  akan cewa “wanda ya kiyaye wa al’ummata hadisai 40 da suke amfana  dasu,to Allah zai ta da shi ranar al }iyama  a matsayin fa}ihi kuma Malami”.da dai hadisai da dama da suka  zo  akan Tarkizi kan 40,wanda ba za a iya kawo su ba saboda  gudun  tsawaitawa.Dawowa ga wannan hadisi da  aka samo  daga Imam Askari [AS] na alamomin mumini guda biyar,alama ta farko,kamar yadda yazo a hadisin,shine  yin Raka’a 51 ko wace rana,wannan raka’a 51 ya ha]a da sallolin wajibi da nafilfilinsu da kuma sallar tahajjud  tare da shafa’i da witri,a warware  ga lissafin adadin raka’oin na sallolin wajibi,wato daga sallar Asuba zuwa sallar Isha’i, in mutum ya ha]a zai ga 17 ne,sai nafilfilinsu,sune  raka’a  2  gabanin  Asuba,raka’a 8  gabanin sallar zuhur,raka’a 8 gabanin sallar Asar,raka’a 4 bayan sallar maghrib,raka’a 2 a zaune bayan isha’i [watira].amma biyun nan yana matsayin  raka’a ]aya ne,sallar tahajjud raka’a 8,shafa’i 2 witri 1,in mutum ya ha]a  zai ga lissafin ya tashi 34,wato na raka’oi na nafilfilin,in mutum ya hada da wa]ancan raka’oi na wajibi 17, zai ga ya tashi akan 51,To,wa]annan raka’oi 51 sune  ake  so kowane mumini,wato mabiyin Ahlul bayt [AS] ya tsayu da yinsu kowace rana  ba tare  da yin fashi ba.ko da zata kai a ce mutum bai samu yin su nafilfilin ba, saboda wani uzuri,to yazo akan cewa ana son mutum ya rama su.misali a ce  bai  samu yin nafilfilin  zuhur da asar ba,ya na iya ramka su acikin yini ]in,ko kuma da daddare.in kuma bai samu yin nafilfilin dare ba, wato kamar maghrib ko isha’i,ko kuma  sallar tahajjud ]insa,to ya na iya ramka su a daren,ko kuma washe gari cikin yini.wato ya tsayu akan yin haka kowa ce rana ba tare da fashi ba.A in da kawai wa]annan nafilfilin suka fa]i shine a halin tafiya,a nan nafilfilin  zuhr  da  asar sun fa]i,amma sauran nafilfilin na sallar maghrib da isha’I da asuba,da kuma tahajjud,shafa’i da witri,su basu fa]i ba.Wato dai a halin tafiya nafilflin sallolin rana ne suka fa]i,amma nafilflin dare basu fa]i ba. kuma wa]annan raka’oi  51 mutum ya kwatanta su da raka’a dubu ]aya da Imam Aliy [AS],Imam Husain [AS],Imam zainul Abidin [AS] da kuma Imam Ridah [AS] suke yi ko wace rana ,idan mutum ya lissafa zai  ga ]aya bisa 20 ke nan.Saboda haka idan mutum ya samu isti}ama da sabati kan yin wa]annan raka’oi 51 ko wace rana to ya samu alama ]aya daga cikin alamomin mumini.                                                                                                                                         

 

Sai kuma alama ta biyu kamar yadda yazo a hadisin,wato ziyarar Arba’in ]in Imam Husain [AS] a 20 ga watan safar,wato kwanaki 40 bayan shahadarsa [AS],yin haka ya na daga cikin alamomin mumini wato mabiyin Ahlul Bayt [AS].Kuma ita wannan ziyarar, imma ta kasance daga kusa ne ko daga nesa,wato in mutum ya na da iko da kuma damar zuwa karbala domin ziyarar to haka aka fi so,in kuma bai da hali da kuma ikon zuwa to sai ya yi wannan ziyarar daga garin da yake.A kan wannan asasin ne zamu ga mabiya Ahlulbaiti [AS] daga sassa na  duniya  daban -daban da suke da ikon  zuwa  karbala,da kuma wa]anda suke cikin garuruwa dabam dabam na }asar ira}i,suke tururuwa zuwa karbala domin wannan ziyarar ta Arba’in,wanda mutum zai iya dukan }irji a wannan zamanin namu, yace babu wani taro da yake tara mutane a doron }asa kamar wannan ziyarar ta Arba’in a karbala.                                                           Ta yi wu mutum yayi tunanin taron aikin hajji fa ? To,duk shekara taron aikin hajji  bai  kai wa miliyan biyar,galibi miliyan biyu ne zuwa uku.To,amma mu duba taron jama’a na ziyarar arba’in ]in Imam Husain [AS] a karbala na shekarun bayan  nan da suka wuce, akan samu jama’a sama da miliyan 15,kuma ko wace   shekara  adadin  }aruwa  ya ke yi,wannan  aya  ce babba  ga masu tunani.In mutum bai san na shekarun baya ba to ya bibiyi na wannan shekarar ya gani.Kuma wani abin lura shine ma fi yawa dake  cikin }asar Ira}i  sukan  tako ne  da }afa daga garuruwansu,har ya zuwa karbala domin wannan ziyarar.Za ka gansu maza da mata yara da manya da ma dattijai.kuma a irin wa]annan hanyoyi na  zuwa  karbala  zaka  ga akwai bayin Allah [T] daban daban da suke gabatar da hidima ta fuskoki daban daban ga wa]annan matafiyan zuwa karbala,kuma dukkan wa]annan hidimomin kyauta suke gabatar dasu.Akwai masu bada abinci a hanyoyin,akwai masu bada masaukai,misali mutum ya yo tafiyan mai nisai  daga garinsu,ya na son ya huta kafin ya cigaba da tafiya,to, ga masauki fisabilillah.Akwai likitoci,ga masu gyaran takalmi,ga masu hanyoyi na sadarwa,wato tarho  shima  duk  kyauta  ga wa]annan matafiya zuwa karbala,to na wannan shekarar ma a Ira}in akwai wasu bayin Allah da suka tsaya akan hanyoyin da wa]annan maziyarta ke bi suna ba da gudummawa ta ku]i ga wanda yake bu}ata, da dai abubuwa da yawa daba a ambata ba na hidimomi, da wasu ke gabatarwa  fisabilillah.                                                              

 

Ita ziyarar Imam Husain [AS] ta kasu kashi biyu,akwai ziyara mu] la}a,wato itace ziyara wadda bata ke ~anta da wani zamani  ayyananne  ba.Akwai  kuma  ziyara mak susa,wato ta ke ~anta da wani zamani ayyananne .To,ziyarar Arba’in ta na daga cikin ziyara mak susa.A wata ma’ana ziyara mak susa, ana  ce mata ziyara  sanawiyya,wato ta shekara-shekara.Domin idan kayi ta sai kuma wata shekara,misali wannan ziyara ta Arba’in.Ziyarar Imam Husain [AS] mak susa,kuma sanawiyya guda 10 ne sune:             

                                1.Ziyarar Ashura,wato 10 ga muharram.                                                                                                                                 2.Ziyarar Arba’in,wato 20 ga watan safar.                                                                                                                              3.Ziyarar ranar farko, ta watan Rajab.                                                                                                                                        4.Ziyarar 15 ga watan Rajab.                                                                                                                                                                5.Ziyarar 3 ga watan sha’aban,wato ranar haihuwar Imam Husain [AS].                                                                       6.Ziyarar daren 15 ga watan sha’aban.                                                                                                                                    7.Ziyarar daren lailatul }adr 19,21,23 na watan ramadan.                                                                                                8.Ziyarar daren idi }arama da kuma daren idi babba.                                                                                                        9.Ziyarar rana kun idi }arama da babba.                                                                                                                 10.Ziyarar ranar Arfa,wato 9 ga zul hijja.To dukkan wa]annan kwanaki da aka ambata, mustabbine mutum ya ziyarci Imam Husaini [AS]a cikin su daga kusa ko nesa.To idan mutum ya duba zai ga cewa a dukkan wa]annan ziyarori na Imam Husain guda goma da aka ruwaito a hadisai to babu wadda take tara mutane masu yawa kamar Ziyarar Arba’in,wato wannan ya nuna wannan ziyara ta Arba’in ta na da wani khususiyya da kuma asrar na musamman a cikinta,a ta}aice dai ziyarar Arbain ]in Imam Husain[AS] shinfi]a ce ga bayyanar Imam Mahdi[AF].                                                                                           Alama ta ukku ta mumini kamar yadda yazo a wannan hadisi da aka samo daga Imam Hassan Al-askari itace:Sa zobe a hannun dama,duk da cewa ta yiyu mutum yaci karo da wasu hadisai da suke nuna cewa za a iya sawa a hannun hagu.To akwai malamai na imamiyya da suka yi bayanin cewa irin wa]annan hadisai sun ]oru ne kan asasin ta}iyya,saboda an yi zamanin da musamman ma zamanin Bani Umayya da sa zobe a hannun dama an mai da shi fitina babba,domin da an ga zoben mutum a hannun dama sai a ce to wannan ]an shi’a ne,kuma wani abun mamaki har yanzu akwai gwuggu~in haka,a tsakankanin wasu musulmi musamman ma }asashen larabawa.Domin sa zobe a hannun hagu kawai Muawiya ne ya sunna ta shi kuma ya gina jama’a a kai,wato saboda ya sa~a ma Imam Ali[AS] da kuma mabiyansa.Akwai ma wani da ya tambayi Imam Kazim[AS] cewa mi yasa Imam Ali yake sa zobe a hannun dama? Sai ya ba shi amsa da cewa:Yana sa zobe a hannun dama ne saboda shine shugaban ma’abuta dama bayan Manzon Allah,kuma Allah ya yabi ma’abuta dama,ya kuma soki ma’abuta hagu.Kuma Manzon Allah ya kasance yana sa zobe ne a hannun damansa,kuma alama  ce ta shi’armu da ake gane su da shi.”A ta}aice dai sa zobe a hannun dama itace sunna ta Manzon Allah[S],sa shi kuma a hannun hagu sunna  ce ta Mu’awiya.Wani abun mamaki in mutum ya duba tarihi zai ga cewa akwai wasu daga cikin Malaman Ahlus sunna da suka ba da fatawar cewa,Na’am sun cewa sa zobe a hannun dama shine sunna ta Manzon Allah,to amma tun da ya zama alama ta ‘yan shi’a,to a sa~a masu a mai da shi hannun hagu.

                Alama ta hu]u itace:Ta’afir wato sa goshi da kumatu na dama da hagu a lokacin sujudu shukur.Kamar yadda aka sani idan mutum ya yi ko wace sallah daga cikin wa]annan salloli wajibai to mustahabbi ne bayan ya yi abin da ake ce ma Ta’a}ibat na Amma da kuma kassa,ya yi sujudi shukur.Yadda ake yi shine zai sa goshinsa da hancinsa akan abin da ake sujuda a kai ya yi addu’a,bayan haka sai yasa kumatunsa na dama ya yi addu’a,bayan haka sai ya sa kumatunsa na hagu ya yi addu’a,sa’annan kuma sai ya mai da goshinsa ya yi addu’a.Addu’oin da ake yi a lokacin wa]annan ababe,addu’oi ne da aka ruwaito daga Ma’asumin,mutum na iya duba littafin Misbahul- Mutahajjid ko Mafatihul jinan zai ga wa]annan addu’oi,idan kuma mutum bai san wa]annan addu’oi ba ko kuma bai hardace su ba,to a lokacin da yake wa]annan ababe da aka ambata ana son a}alla ya ce “Shukran Lillah” sau ukku wato a sujudar da kuma lokacin da yasa kumatunsa na dama da hagu.Kuma wannan Sujuda ta shukur ba ta ta}aita ga salloli na wajibai ba,a’a hatta salloli na nafilfili ana yi masu musamman ma sallar Tahajjud.A ta}aice dai wannan Ta’afir na sujuda ta godiya ana so mutum ya lizimci yin su ga dukkan al’amuranra na yau da kullum, wato ya kasance duk lokacin da Allah Ta’ala ya yi maka wata ni’ima,ko ya tunku]e maka wata musiba sai mutum ya yi wannan sujuda ta shukur.Domin yin ta ya na da fa’idodi masu yawa ga duniyar mutum da addininsa da kuma lahirarsa,alal misali daga cikin fa’idodin yin ta akwai }aruwar ni’imar da Allah ya baka,da kuma da]a tsare mutum daga dukkan musibu.Haka nan daga cikin fa’idodinta idan mutum ya yi ta bayan  sallarsa to idan  ruhin sallar ta shi na da na}asu,to wannan sujuda tana cike gurbin na}asun.Kuma in muka duba tarihin rayuwar Aimma na Ahlul bayt zamu ga misalan masu yawa na sujudu shukur daga rayuwarsu misali yazo cewa,Imam Zainul Abidin ya kasance duk ni’imar da Allah ya yi masa ko ya tunku]e masa wata musiba to sai ya yi wannan sujuda ta shukur.Haka nan yazo a tarihin Imam Kazim[AS] cewa ya kwashe shekaru masu yawa ko wace rana ya kan yi wannan sujuda ta shukur tun daga hudowar Rana har ya zuwa Zawal.Akwai kuma hadisi da aka samo daga Imam Sadi}[AS] yace,Babu wani mumini da zai yi sujuda ga Allah,sujuda ta godiya kan ni’imar da ya yi masa, to za a rubuta masa lada,a goge zunubinsa a kuma ]aukaka darajojinsa.

            Alamar mumini na biyar shine bayyanar da Bismillah wato a sallah:Shima wannan yana daga cikin mas’alolin da mabiya Ahlul bayt suka ke~anta da shi.Domin idan mutum ya bibiyi mazhabobi na Ahlus sunna zai ga cewa sun sa~a a tsakaninsu kan wannan mas’ala ta Basmala,alal misali sun sa~a akan cewa Bismillahir-Rahmanir-Rahim shin aya ce cikin fatiha ko kuma aya  ce ta ko wace sura? Saannan kuma sun sa~a akan cewa a bayyane ake karanta ta ko a ~oye? Saannan kuma sun sa~a akan cewa karanta ta wajibi ne ko mustahabbi? Da dai sauran sa~ani da suka yi kan wannan mas’ala.Akwai ma Malamai daga cikinsu da suka rubuta littafi kan wannan al’amari na Basmala,saboda akwai zamanin da aka yi kace-nace tsakanin Malamai kan wannan al’amari.Amma idan mutum ya bibiyi mas’alar a mazhabar Ja’afariyya zai ga cewa baki ]ayan Malamanta sun tafi akan cewa Bismillahir-Rahmanir-Rahim juz’i ne na ko wace sura,saboda haka wajibi ne a cikin sallah duk surar da mutum zai karanta sai ya ha]a da ita,domin ita sashen surar ne,in da kawai ba a karanta ta a farkon sura sai a suratu Tauba.Wani Tambihi a nan muhimmi shine cewa duk lokacin da mutum yake sallah to lazim ne kafin ya yi Basmala  ya ayyana a zuciyarsa Surar da zai karanta,wato ba sai ya yi Basmala ba saannan ya yi tunanin Surar da zai karanta.To kan kuma mas’alar bayyana ta ake a karatun sallah ko ~oyewa? To a Ja’afariyya sallolin da ake bayyana karatu a ciki misali sallar Asuba ko Magriba to mutum zai bayyana ne,haka nan kuma a raka’oi biyu na farko na sallar da ake ~oye karatu wato sallar Zuhur da Asar shima bayyanawa zai yi,bilhasali ma ita wannan alamar mumini na biyar wato bayanna Bismillahi khususan kan raka’oi biyu na farkon sallar Azuhur da Asar ake nufi.Amma a raka’oin biyu na }arshe,kamar yadda aka sani mutum na da za~i ko ya yi tasbihi wato Subhanallah-Walhamdu Lillah-Wala’ilaha illallah-Wallahu Akbar sau ukku ko kuma ya karanta Surar Fatiha,to anan in mutum ya za~i ya karanta fatiha to zai ~oya karatun Basmalar ne wato ba bayyanawa zai yi ba,haka nan ma a raka’oin biyu na }arshen Isha’i da raka’ar }arshe ta Magriba.Wata mas’ala  kuma ita ce wannan bayyana karatun Basmala a raka’oin farko na sallar azahar ko la’asar matsayin wajibi yake ko mustahabbi? Matsayin mustahabbi yake,saboda haka da mutum zai yi sallarsa sai bai bayyana Basmalar ba to sallarsa ta yi sai dai ya rasa ladar wannan mustahabbi.

            Daga }arshe wannan wata addu’a ce da Imam Sadi}[AS] ya kasance yana yi ga masu ziyarar Imam Husain[AS]Saboda haka yana da muhimmanci ga mutum idan zai iya ko wace rana ya dun ga karanta wannan addu’ar ga Zuwwar na Imam Husain[AS] Ga addu’ar, “Ya Allah ka gafarta mani,ka gafarta ma ‘yanuwana,ka gafarta ma masu ziyarar Imam Husain wa]anda suka ciyar da dukiyar su,suka kuma fito da gangar jikinsu saboda biyayya garemu.da kuma kwa]ayin ladarka,haka nan kuma domin sa farin ciki ga Manzon ka,ba dun komi ba face saboda neman yardar ka.Ya Allah ka tsare su dare da rana.Ka kiyaye iyalinsu da ‘ya’yansu da suka baro.Ka tsare su daga dukkan sharrori na mutane da aljannu.Ya Allah ka basu fiye da abun da suke fata da buri a wajenka a wannan ba}unci na su.Ya Allah ma}iyanmu suna aibanta wannan fita tasu,amma haka bai hana su fita ba.Ya Allah ka tausaya ma wa]annan fuskoki da rana ta yi butu-butu dasu.Ya Allah ka tausayawa ma wa]annan idanuwa da suka zubar da hawaye saboda abun da aka yi mana.Ya Allah ka tausayawa ma wa]annan zukata da suke jin zafi da zogi saboda mu.Ya Allah ka tausayawa ma wannan sauti dake kururuwa saboda mu.Ya Allah ka tsare kuma ka kiyaye wa]annan rayuka har mu ha]u da su ranar }iyama.” Ga mai bu}atar ganin wannan addu’a cikin larabci yana iya duba littafi mai suna “Mir’atul-Kamal” Juz’i na ukku.

 

 
Home Shia/Sunnah Ranar Arba’in ]in Imam Husain [AS]
Copyright © 2023. www.tambihin.net. Designed by KH