Saturday, 02 December 2023
Email
Make My Homepage
RSS
Register
Munasabobin watan Zhul- Hijjah. Print E-mail
Written by administrator   
Monday, 06 October 2014 08:33
 Watan zul-hijjah shine wata na 12 a jerin }idaya na watannin musulunci sha-biyu,kuma yana ]aya daga cikin watanni guda hu]u masu daraja da kuma alfarma a wajen Allah ta’ala,saboda ma daraja da alfarma na wa]annan watanni Allah ta’ala ya hana zaluntar kai acikin su.Kuma shi zaluntar kai bai ta}aita ga aikata zunubi ba,a’a ko da aikata wani aiki na ibada ko ]a’a ya zamanto mutum zai iya aikatawa sai bai aikata ba to duk shima ya shiga cikin zaluntar kai.Haka nan wannan wata na zul-hijja yana daga cikin watanni da ke da ayyuka na ibadodi da kuma munasabobi masu yawa.Kuma kamar yadda aka faro tun daga watan farko wato watan muharram zuwa wannan wata na zul-hijja ko wane wata ana bayanin falalar watan,ayyukan ibadodi da ake aikatawa cikin watan,da kuma wasu wa}i’oi na tarihi da suka auku a cikin watan da kuma munasabobi na wilada da kuma wafati na ma’asumai[AS] da ya  kasance a watan.

FALALAR WATAN ZUL-HIJJA

      Watan zul-hijja wata ne da yake da falaloli masu yawa,kuma kasantuwarsa wata da ake aikin hajji a cikinsa kuma wata wanda Manzon Allah ya bayyana wanda zai kasance khalifa a bayansa ya isa ya nuna falaloli da kuma darajoji dake }unshe a cikinsa.Haka nan idan mutum ya bibiyi    tarihi da kuma rayuwar wasu daga cikin bayin Allah salihai magabata zai ga cewa sun kasance suna yawaita ibadodi a cikin wannan wata na zul-hijja musamman ma goman farkonsa,yama zo a hadisi wanda aka ruwaito daga Manzon Allah[AS] yace, “Babu wasu kwanuka wanda aiki na }warai yafi soyuwa ga Allah ta’ala kamar goman farko na zul-hijja.”Haka nan kuma a wasu hadisai da aka samo daga Aimma na Ahlul bayt[AS] sun nuna cewa wa]annan kwanuka na goman farko na zul-hijja su ake nufi da “Ayyamul-ma’alumat” su kuma “Ayyamul-ma’adudat sune:10,11’12,13 wato na wannan wata na zul-hijja,kuma wa]annan kwanuka na ma’alumat da kuma ma’adudat in mutum ya duba cikin ayoyin da suka zo zai ga cewa suna umarni ne da yawaita zikiri a cikin su.
IBADODIN WATAN ZUL-HIJJA
          Akwai ayyukan ibadodi kamar salloli,addu’oi,azumi,ziyarar Imam Husain[AS] da dai sauransu da ake son aikatawa a cikin wannan wata na zul-hijja.Ga wasu daga cikin ayyukan:1- Sallah,akwai sallah mai raka’a biyu da ake son yin ta  tun daga daren farko zuwa daren goma ga watan.Akwai kuma wasu salloli da ake son yi ranar farko na watan.Haka nan kuma akwai salloli na ranar ghadir da kuma ranar mubahala.Bayan haka kuma akwai wata sallah mai muhimmanci da ake son yi a ranar }arshe na watan zul-hijja.Duka  wa]annan salloli da aka ambata da kuma yadda ake yin su ana iya duba littafin mafatihul jinan babi na biyu fasali na shidda2-Azumi,yana da muhimmanci mutum ya kasance ya azumci kwanaki tara na goman farko na wannan watan, wato tun daga ]aya ga wata zuwa tara ga watan,domin yin haka yana da falaloli masu yawa,amma idan mutum ba zai samu yi ba to a}alla  ya azumci ranar 1,da 8 da kuma 9  na watan.Haka nan kuma ana son azumtar ranar 18 ga wannan watan wato ranar ghadir kenan,da kuma ranar 24 wato ranar mubahala.3-Addu’oi,Akwai addu’a da aka ruwaito daga Imam Sadi}[AS] ana son karanta ta safe da yamma tun daga ranar farko na watan zuwa tara ga wata.Akwai kuma wata addu’a da ake son karanta ta a daren Arfa,bayan haka kuma akwai addu’oi na ranar Arfa.Haka nan kuma akwai addu’oi na ranar ghadir da kuma ranar mubahala,akwai kuma wata addu’a da ake yi a ranar }arshe na wannan wata na zul-hijja wato bayan mutum yayi sallar raka’a biyu da aka ambata.Duka wa]annan addu’oi da aka ambata mutum na iya duba mafatihu ko kuma wasu littafai na addu’oi.4-Ziyarar Imam Husain,ana son karanta ziyarar Imam Husain[AS] a daren arfa da kuma ranar arfa,haka nan kuma a daren idi da kuma ranar idi,mutum na iya duba wa]annan ziyarori a cikin littafin mafatihu babi na ukku fasali na bakwai,da dai sauran ayyuka na ibadodin watan zul-hijja.
          ABUBUWAN DA SUKA FARU A TARIHI CIKIN WATAN  
                   A ranar farko na watan zul-hijja aka ]aura auren Sayyida Fa]ima[AS] da kuma Imam Ali[AS].Haka nan kuma a wata ruwaya yazo akan cewa a ranar farko na watan zul-hijja aka haifi Annabi Ibrahim[AS].A ranar  tara ga wata wato ranar  Arfa aka kashe Muslim ]an A}il da kuma Hani ]an Urwa a garin Kufa,wannan kuma ya nuna irin gayar bushewar zuciya da kuma nisa da addini ga wa]annan mutane da suka yi wannan mummunan aiki,ace irin wannan lokaci mai albarka na ranar arfa amma kuma mutum yayi kisan kai. Lokacin da wannan abu ya faru Imam Husain[AS] yana makka ne,amma ya bar makkan ana gobe abin zai faru wato 8 ga watan zul-hijja ya kama hanya zuwa karbala wanda a lokacin Imam Husain yaso yayi aikin hajji ne,amma kasancewar Yazidu[LA] ya aiko da maya}a akan duk in da suka ga Imam Husain a makka su kashe shi ko da ko a jikin ka’aba ne.Saboda Imam Husaini[AS] baya son wani abu ya faru a lokacin aikin hajjin yasa ya canza niyya daga aikin hajji,bayan haka kuma ya bar garin makka ranar Tarwiyya domin tafiya zuwa karbala,mu duba irin wa]annan jarabawowi da Aimma suka fuskanta.Akwai wata addu’a ta Imam Husain wadda aka fi sani da addu’ar sa ta ranar arfa,to Imam Husain[AS] yayi wannan addu’ar ne a aikin hajjin sa na }arshe wato shekara ]aya gabanin wannan aikin hajjin da yaso yayi.Idan mutum ya karanta wannan addu’a ta arfa musamman ma ace lokacin da yake karanta ta zuciyarsa tana a halarce ne kan  abun da yake karantawar,zai ga cewa a cikin addu’ar tamkar Imam Husain a lokacin yana bankwana da al’umma ne,haka nan kuma zai ga ilimummuka da kuma asraru masu yawa dake cikin wannan addu’a ta arfa.In mutum ya duba cikin wasiyyar Imam Khumaini akwai in da yake cewa muna alfahari da wannan addu’ar Imam Husaini ta ranar Arfa.A ranar 18 ga wata al’amarin ghadir ya auku,haka nan kuma ranar 24 ga watan zulhijja al’amarin ranar mubahala ya auku.
MUNASABOBIN WATAN ZUL-HIJJA
          A ranar 7 ga watan zul-hijja ne shekara ta 114 bayan hijira wafatin Imam Muhammad Al-Ba}ir[AS].Nan kuma wasu sassa ne na rayuwarsa:                                                                                      
1-   Haihuwarsa: Imam Muhammad al-Ba}ir[AS] An haife shi a Madina,ranar Jumma’a 1 ga watan Rajab  shekara ta 57 bayan Hijira.Kuma shine Imam na biyar a jerin }idaya na Imamai 12.
2-   Nasabarsa:Sunan Mahaifiyarsa Fa]ima ‘yar Imam Hassan,yazo a kan cewa shine ka]ai ya ha]a irin wannan nasaba,wato cewa Mahaifinsa shine Imam Sajjad ]an Imam Husain[AS] mahaifiyarsa kuma Fadima ‘yar Imam Hassan[AS].
3-   Nash’a ]insa:Imam Ba}ir ya tashi a Madina,gaban mahaifinsa da kuma kakansa,ya rayu tare da kakansa Imam Husain[AS] shekara 4.Saboda haka wa}i’ar karbala tare dashi akayi wato lokacin yana da shekara 4 a duniya.Ya kuma rayu tare da mahaifinsa shekara 25.
4-   La}ubbansa da Kinayarsa:Imam Ba}ir yana da la}ubba masu yawa,amma wa]anda suka fi fice sune Al-Ba}ir da kuma “SHABIH”ana ce masa haka ne saboda yayi kama da Manzon Allah[S] so sai.Ana kuma yi masa kinaya da Abu Ja’afar.
5-   Shekarunsa:Imam Ba}ir[AS] ya rayu a duniya shekaru 57.
6-   Muddan Imamancinsa:Shekaru 19.
7-   ‘ya’yansa:Imam Bakir[AS] yana da ‘ya’ya bakwai,maza biyar,mata biyu.
8-   Wafatinsa:Ya rasu ranar litinin 7 ga watan Zul-hijja shekara ta 114 bayan Hijira.
9-   {abarinsa:}abarinsa yana Madina ne wato a Ba}i’a.
         
A ranar 15 ga watan zul-hijja ne a shekara ta 212 bayan hijira aka haifi Imam Ali Al-Hadi[AS]. Nan kuma wasu sassa ne na raruwarsa:
1-   Wiladarsa:Imam Ali al-Hadi[AS]shine Imam na goma a jerin }idaya na Imamai 12.An haife shi a wani gari kusa da Madina a  na ce masa Sarya,a ran 15 ga watan Zul-hijja.shekara ta 212 bayan Hijira.
2-   Nasabarsa:Sunan mahaifiyarsa Sumanatu,amma an fi saninta da Sayyida,kuma ana yi mata kinaya da Ummul-Fadhal.kuma yazo a tarihinta cewa ta kasance mai yawan ibada,musamman ma ta ~angaren azumi.kuma ta kasance mai ta}awa da kuma zuhudu wato gudun duniya.Sunan mahaifinsa Imam Jawad[AS]
3-   Nash’a ]insa:Imam Ali al-Hadi[AS]ya tashi a madina,ya rayu a cikinta shekaru 22,ya kuma rayu tare da mahaifinsa shekara 8.{arshen rayuwarsa ta kasance a Ira} ne,domin ya zauna a cikinta shekaru 20.
4-   La}ubbansa da kinayarsa:Imam Ali al-Hadi[AS] ya kasance yana da la}ubba masu yawa,amma wa]annan biyun su suka fi fice.wato Al-Hadi da kuma Anna}iy.Haka nan anai masa kinaya da Abul-Hassanus-salis.
5-   Shekarunsa:Ya rayu a duniya shekaru 42.
6-   Muddan Imamancinsa:shekaru 33,a wata ruwaya 34.
7-   ‘ya’yansa:Yana da ‘ya’ya 5,maza 4.mace 1.
8-   Wafatinsa:Ya rasu ranar litinin 3 ga watan Rajab shekara ta 254 bayan hijira,ya rasu ne sakamakon guba da khalifan Abbasawa mai suna Mu’utazz yasa masa.
9-   {abarinsa:}abarinsa yana samarra,a }asar Ira} kusa dashi akwai }abarin ]ansa Imam Hassan al-askari[AS]. 
 
Home Munasabobi Munasabobin watan Zhul- Hijjah.
Copyright © 2023. www.tambihin.net. Designed by KH