Monday, 20 January 2025
Email
Make My Homepage
RSS
Register
Bayani kan Sallar Idi. Print E-mail
Written by administrator   
Saturday, 27 September 2014 08:22
 Insha- Allah a wannan darasin fi}hu na 13 bayani zai kasance kan sallar Idi,kuma bayanan za su gudana kan wa]annan ababe:1-Falalar dare da kuma ranar Idi.2-Ayyukan ibadodi na dare da kuma ranar Idi.3-Hukuncin sallar Idi.4- Lokacin sallar Idi.5-Yadda ake sallar Idi.6-Khu]ubar sallar Idi.7-Wasu mas’aloli na sallar Idi.

          1-Falalar dare da kuma ranar Idi:Daren idi da kuma ranar idi na sallah babba da kuma sallah }arama lokuta ne masu albarka da kuma darajoji kamar yadda yazo a hadisai da aka ruwaito daga Manzon Allah[S] da kuma Aimma[AS].Saboda ma falalolin da ke cikin daren sallah ana son ma raya shine da ibadodi wato ya kasance daren baki ]aya mutum ya zamanto bai yi barci ba,idan mutum ya bibiyi tarihin Aimma na Ahlul bayt zai ga cewa sun kasance haka suke yi.Alal misali yazo akan cewa Imam Ali Zainul-Abidin[AS] ya kasance yana raya daren idi da yin salloli har ya zuwa asuba.An samo daga Imam Sadi}[AS] yace:Amiril-muuminin Ali[AS] ya kasance yana girmama darare hu]u sune daren farko na Rajab,daren nisfu shaaban,daren }aramar sallah da kuma daren babbar sallah,kuma ya kasance yana raya su da ibadodi.”Akwai hadisi da aka ruwaito daga Manzon Allah[S] yace: “Duk wanda ya raya daren idi to zuciyarsa ba za ta mutu ba ranar da zukata ke mutuwa.”Haka nan kuma a wani hadisi Manzon Allah[S] yace, “Allah ma]aukaki yana da za~a~~u a cikin  duk abin da ya halitta,amma za~a~~unsa a cikin darare sune dararen jumma’a,daren nisfu shaaban,daren lailatul-}adr,da kuma daren idin }aramar sallah da kuma babbar sallah.Za~a~~unsa kuma daga cikin ranaku sune ranakun jumma’a da kuma ranakun idi.”A ta}aice dai dararen idi da kuma ranakunsu lokuta masu muhimmanci da ya kamata mutum yayi amfani da su wajen neman kusanci ga Allah  ta hanyar aikata ibadodin dake cikin su.

          2-Ayyukan ibadodi na daren idi da kuma ranar:Akwai ayyuka na ibadodi dabam-dabam da ake son aikatawa a cikinsu,haka nan kuma akwai ladubba masu yawa da ake son mutum ya aikata  ga mai bu}atar ganin wa]annan ayyuka da kuma ladubba yana iya duba littafin I}bal na sayyid ibn [awus ko Zadul-maad na Allama majlisi ko kuma littafin mafatihul jinan.Kuma wa]annan ayyuka na daren idi da kuma ranar idi yana da muhimmanci mutum ya bisu ]aya bayan ]aya ya yi mujahada wajen ganin cewa ya aikata su,domin irin wa]annan lokuta masu albarka da falala dama ce da kuma fursa babba ga mutum wato dai lokuta ne na baje kolin kasuwar lahira.
          3- Hukuncin sallar Idi:Sallar Idi yin ta wajibi ne a lokacin da Imami maasumi yake a halarce kuma yake tafi da iko.Amma a zamanin gaiba wato wannan zamani da muke ciki ta na matsayin mustahabbi ne.A kuma sauran mazahib na Ahlus-sunna misali malikiyya tana matsayin sunna mai }arfi,a Mazhabar Hanbaliyya kuma tana matsayin faralu kifaya ne.
          4-Lokacin sallar Idi:Lokacin sallar idi daga hudowar rana ne zuwa zawal,kuma ba a ramakon ta idan lokacin ta ya fita,wato da ace mutum bai samu yinta ba a tsakankanin wannan lokaci har zawal yayi to ba zai ramata ba.kuma wannan lokaci na ta wato daga fitowar rana zuwa zawal duka mazhabobi na sunna da shi’a sun tafi akan haka,misali babu wata mazhaba wadda tace za a iya yinta bayan zawal ko kuma kafin ketowar rana.
          5-Yadda ake sallar Idi:Yadda ake sallar Idi a mazhabar Ja’afariyya ya ]an banbanta da mazhabobi na Ahlus-sunna musamman wajen yin kabbarori da kuma yin }unuti.A mazhabar Ja’afariyya ga yadda ake yinta:Raka’a ce guda biyu,ko wace raka’a mutum zai biya fatiha da sura,surar da aka fiso mutum ya karanta a raka’a ta farko itace suratul-A’ala wato sabbi,a raka’a ta biyu kuma an fi son mutun ya karanta suratul-gashiya wato Hal-ataka hadisul-gashiya ko kuma suratu shams wato wasshamsi.Bayan mutum  ya gama karatun fatiha da sura a raka’a ta farko zai yi kabbarori guda biyar da kuma }unuti biyar.A raka’a ta biyu kuma bayan fatiha da sura zai yi kabbarori hu]u da kuma }unuti hu]u,a dukkan wa]annan kabbarori  na raka’ar farko da ta biyu to bayan ko wace kabbara zai yi }unuti ne.Wannan }unuti mutum zai iya biya ko wace addu’a ko zikiri amma an fi son biya addu’ar, “Allahumma ahlal-kibra’i wal-azama………..”ana iya duba littafin mafatihul jinan babi na biyu fasali na hu]u za a ga cikon addu’ar,ko da ace mutum bai har-dace ba zai iya karantawa da littafi ko a takarda ba matsala.A mazhabar Ja’afariyya da kuma Shafi’iyya kamar yadda za a iya yin sallar idi a jama’a wato jam’i haka kuma za a iya yin ta a ]ai-]aiku wato mutum zai iya yin sallar idi shi ka]ai,amma a mazhabar malikiyya,hanbaliyya da kuma hanayya wajibi ne ayi ta a jam’i.Haka nan kuma mustahabbi ne bayyana karatu a cikin ta,wato ko da mutum shi ka]ai yayi sallar idin to ana so mutum ya bayyana karatu.Haka nan kuma mustahabbi ne a dukkan wa]annan kabbarori mutum ya ]aga hannayensa lokacin yinsu.
          6-Khu]ubar sallar Idi:Khu]ubar sallar idi tana da banbanci da khu]ubar sallar jumma’a wajen hukunci da kuma wajen yi,alal misali a sallar jumma’a wajibi ne ayi ta in ma ba a yi ba to jumma’a ba ta yi ba,kuma ita khu]ubar jumma’a ana yinta gabanin sallah ne,to amma ita khu]ubar sallar idi ana yinta bayan an yi sallah ne,kuma yinta a sallar idi mustahabbi ne wato ko da za a yi sallar idin cikin jam’i amma sai ba a yi khu]ubar ba to sallar ta yi.A khu]ubobi na idi idan a babbar sallah ne to ana son liman cikin khu]ubar tashi yayi bayani dangane da layya,idan kuma a }aramar sallah ne ana son cikin khu]ubar tasa yayi bayani kan zakatul-fitr.
          7-Wasu mas’aloli na sallar Idi:1-A sallar idi ba a azan wato kiran sallah ko i}ama gabanin ta,wato in an zo yinta za a yi niyya ne da kabbarar harama mubasharatan,sai dai mustahabbi ne idan a jam’i za a yi ta ace Assalat……..sau ukku.2-Da mutum zai yi shakka a adadin kabbarori ko }unuti da yayi to in yana tsaye ne bai yi ruku’u ba  sai yayi gini akan ka]an,misali a ce yana shakka akan kabbara biyu yayi ko ukku,ko kuma }unutin da yayi na biyu ne ko na ukku to anan sai yayi gini akan biyu yayi.3-Liman bai ]auke ma mamu kome a sallar idi sai karatun fatiha da sura,amma abin da ya shafi zikirori na ruku’u ko sujuda ko kuma yin kabbarori da kuma }unuti duk mutum shi zai yi da kansa,amma fa nan a lura sai bayan liman yayi kabbarar mutum zai yi kabbarar.4-Idan mutum yazo sallar  idi  ko da  ya iso liman har yayi ruku’u,to shi ke nan zai bishi a ruku’un kuma ya samu raka’ar,amma da ace liman yana tsaye ne ya same shi alhali limamin yayi wasu kabbarori da }unuti gabanin zuwansa to anan bayan yayi kabarar harama zai yi wa]ancan kabbarori da }unuti da suka ku~uce masa wato ko da ace liman ya wuce ruku’u shi sai ya ]an tsaya ya kammala kabbarorin da }unutin saannan ya same shi,sai dai a lura a irin wannan yana yi ana son mutum ya ta}aita }unutin misali yace subhanallah wato bayan yayi kabbara to ya wadatar.5-Da a ce mutum zai manta sai ya yi i}ama gabanin sallar idi,to sallar idin ta yi wato haka bai ~ata sallar ba.6-Da ace mutum zai manta yin wa]annan kabbarorin ko }unuti yana cikin ruku’u ko bayan ya ]ago daga ruku’u sai ya tuna,to anan zai ci gaba da sallah ne a hakan kuma sallar tayi wato ba matsala.7-A wannan zamani na gaiba da muke ciki ga wanda zai yi layya, ba sai ya jira liman ya yanka ba kafin ya yanka wato akasin yadda mazhabobi na Ahlus-sunna suka tafi akan cewa sai liman yayi yanka tukuna,duk da cewa suma sun sa~a akan wane limami ake nufi na sallah ko kuma Abbasiy?Wannan ke nan a ta}aice dangane da bayani kan sallar Idi.
 
Copyright © 2025. www.tambihin.net. Designed by KH