Sunday, 25 February 2024
Email
Make My Homepage
RSS
Register
Bayani kan sallar Jumma’a. Print E-mail
Written by administrator   
Saturday, 13 September 2014 19:57

 Insha-Allah a wannan darasi na 12 bayani zai gudana ne kan sallar Jumma’a,kuma wa]annan bayanai zasu kasance ne kan abubuwa kamar haka.1-Hukuncin sallar Jumma’a.2-Wanda Jumma’a take wajaba akansa.3-Sharu]]an sallar Jumma’a.4-Yadda ake sallar Jumma’a.5-Lokacin sallar Jumma’a.6-Khu]ubar sallar Jumma’a.7- Wasu mas’aloli na sallar Jumma’a.Amma kafin shiga cikin wannan darasi zai yi kyau a fara da bayani kan falalar daren Jumma’a da kuma ranar Jumma’a da kuma ayyuka na ibadodi da ake son yi a daren da kuma ranar.

Falalar daren Jumma’a da kuma ranar

Akwai hadisai masu yawa da aka ruwaito daga Manzon Allah[S] da kuma Aimma[AS] dangane da falaloli na daren jumma’a da kuma ranar jumma’a, ga wasu daga cikin hadisan:Manzon Allah[S] yace, “Lalle daren jumma’a da ranar suna da sa’oi 24,ko wace sa’a  Allah ta’ala yana ‘yanta mutane dubu ]ari shidda daga wuta.” Imam Sadi}[AS] yace, “Lalle jumma’a tana da wani ha}}i saboda haka ka da ka tozarta darajar ta,ko kuma ka ta}aita wajen ibada a cikin ta  da kuma kusanci ga Allah ta hanyar ayyuka kyawawa da kuma nisantar zunubi,domin Allah ta’ala yana nunnuka kyawawan aiki a cikin ta,yana kuma yafe zunubai da kuma ]aukaka darajoji.” Haka nan daga Imam Sadi}[AS] yace, “Duk wanda ya rasu tsakanin zawalin ranar Alhamis zuwa zawalin ranar jumma’a to Allah zai tsare shi daga azabar }abari.” An ruwaito daga Imam Ali[AS] yace, “Daga cikin falalolin ranar jumma’a akwai cewa babu wanda zai ro}i Allah ta’ala a cikin ta wata bu}ata face ya kar~a masa.”An samo daga Imam Ba}ir[AS] yace, “Allah Ta’ala yana umartar mala’ika da yayi kira ko wane daren jumma’a tun daga farkon daren har ya zuwa }arshen sa  da cewa:Shin akwai wani bawa muumini da zai ro}e ni ga bu}atun duniyarsa da lahirarsa gabanin ketowar alfijir in amsa masa? Shin akwai wani bawa muumini wanda zai tuba zuwa gare ni daga zunubansa gabanin ketowar alfijir in kar~i tubarsa?Shin akwai wani bawa muumin wanda na }untata masa arzikinsa ya ro}e ni }arin arziki gabanin ketowar alfijir in }ara masa kuma in yelwata masa? Shin akwai wani bawa muumini marar lafiya wanda zai ro}e ni in bashi lafiya gabanin ketowar alfijir in bashi lafiya?Shin akwai wani bawa muumini wanda aka zalunta ya ro}e ni in bi masa ha}}insa kuma in taimake shi akan wanda ya zalunce shi.”An kuma ruwaito hadisi daga Imam Rida[AS] yace,Manzon Allah yace, “Ranar jumma’a it ace shugaban ranaku,Allah ta’ala yana kar~ar addu’oi a ciki,yana yaye ba}in ciki a cikinsa,yana biyan bu}atu masu girma a cikin ta,duk wanda ya tozarta darajar ranar jumma’a ya kuma tauye ha}}inta face sai Allah ma]aukaki ya }ona sa da wuta sai fa in ya tuba.”Da dai sauran hadisai masu yawa wanda suke nuna falaloli na daren jumma’a da kuma ranar.Saboda haka yana da muhimmanci mutum yayi iyaka iyawarsa wajen ganin cewa ya kiyaye daraja da kuma alfarma ta dare da kuma ranar jumma’a wato ta hanyar aikata ayyuka na ibadodi da kuma nisantar zunubai.Kuma in muka duba tarihin bayin Allah magabata da ma wasu a wannan zamanin zamu ga cewa ko wane daren jumma basa barci a cikinsa,wato suna raya shine da ibadodi,akwai ma hadisi da aka samo daga Imam Sadi}[AS] yace, “Idan mutum zai iya raya daren jumma’a da salloli da kuma addu’oi to ya yi,domin Allah ta’ala yana aika mala’iku a cikinta zuwa saman duniya don su nunnunka ayyuka kyawawa su kuma goge zunubai.”Akan asasin haka yana da gayar muhimmanci ga ]an’uwa ko ‘yar’uwa yayi mujahada wajen ganin cewa ya sunnata ma kansa ko wane daren jumma’a ya zamanto ya raya shi da ibadodi.Domin rayuwar duniya fursa ce babba ga mutum ta na ku~ucewa kuma shike nan kuma abinda mutum ya shuka a nan na alhairai da kuma ibadodi shi zai girba a lahira.

          Ayyukan ibadodi na daren jumma’a da kuma ranar jumma’a.

 

Akwai ayyuka na ibadodi masu yawa da ake son aikatawa a daren jumma’a da kuma ranar,kuma wa]annan ayyuka sun zo ne a ruwayoyi na hadisai da aka samo daga Manzon Allah[S]da kuma Aimma[AS].Idan mutum ya duba a cikin littafin mafatihul jinan babi na farko fasali na hu]u zai ga ya kawo ayyuka na daren da kuma ranar.Alal misali a daren jumma’a in mutum ya duba zai ga ya kawo ayyukan ibadodi guda goma.A kuma ranar jumma’a in mutum ya duba zai ga ya kawo ayyuka na ibadodi har 31.To yana da kyau a ce mutum ya bi su ]aya bayan ]aya,bayan haka kuma sai yayi mujahada wajen ganin cewa ya aikata su har ta kai sun zamar masa jiki wato ya saba da aikatawa,kuma wannan mai yiyuwa ne domin wa]annan ayyuka na ibadodi na daren jumma’a da kuma ranar da suka zo cikin mafatihul jinan ka]an ne in mutum ya kwatanta su da wa]anda suka zo a wasu littafai,misali mutum ya duba cikin littafin Misbahul-Mutahajjid na Shaikh [usiy ko kuma littafin Jamalus-Usbu’i na Sayyid ibn [awus,dukkan su ya duba a fasalin dake bayani kan ayyukan daren jumma’a da kuma ranar zai ga cewa ayyukan da suka zo a mafatihu na daren da kuma ranar kusan mutum zai iya cewa kamar ]aya bisa ukku ne.Yanzu anan za a kawo wasu sashe na ayyukan daren da kuma ranar ne.A dun}ule sune kamar haka:1-Salloli.2-Karatun wasu surori daga cikin Al}ur’ani.3-Azkar.4-Addu’oi.5-Ziyarori na Ma’asumai.6-Sadaka.7-Wasu ladubba.Nan bayani ne na kowannensu amma a ta}aice:1-Salloli:A daren jumma’a akwai salloli masu yawa ga ukku daga ciki.Raka 2 ko wace bayan fatiha,}ulhullahu 70.bayan sallama sai istigfari sau 70 wato Astagfirullah….Akwai kuma sallah mai raka’a 4 ko wace bayan fatiha }ulhullahu 50.Akwai kuma sallah mai raka’a 2,ko wace raka’a bayan fatiha mutum ya karanta izazul 13.Sai kuma ranar jumma’a shima yana da salloli da yawa ga 2 daga ciki.Akwai sallah mai raka’a 8 ko wace bayan fatiha ya karanta }ulhullahu sau 1.Haka nan kuma akwai sallah mai raka’a 20 an ruwaito ta ne daga Imam Ridha[AS] yadda ake yin sallar da kuma addu’ar da ake karantawa bayan ko wace raka’a 2 na sallar yana iya duba sahifatus-sajjadiyya wato jami’a  can wajen }arshen sahifan zai duba.2- Karatun wasu surori na Al}ur’ani:Akwai surorin da ake son karantawa a daren jumma’a ga  su:Suratul-}amar,suratu-[ur,suratul-Ah}af,suratu-Dukan,suratu-Fussilat,suratu Sad,suratu Yasin,suratu Sajadah da dai sauran wasu surori.Haka nan kuma a ranar jumma’a shima akwai surorin da ake son karantawa kamar suratu-Ali-imran,suratl-Hud,suratul-khahafi da dai sauransu.3-Azkar:Ana son yawaita salati ga Manzon Allah da kuma alayensa a daren jumma’a da kuma ranar jumma’a,da kuma yawaita wannan zikiri na subhanallahi,walhamdu-lillahi-walailaha illallah-wallahu Akbar wato a}alla mutum yayi sau 100 ko 1000.Haka nan kuma ana son mutum ya yawaita fa]ar Astagfurullah-wa atubu ilaihi,a}alla shima sau 100,da dai sauran wasu azkar.4-Addu’oi:Akwai addu’oi masu yawa da suka zo a daren jumma’a wato baya ga Du’au Khumail,ga mai bu}atar ganin wa]annan addu’oi yana iya duba mafatihu ko misbahul mutahajjid.5-Ziyara na Ma’a sumai:Wannan mutum na iya duba ta cikin mafatihu babi na 3 fasali na 3, kan babin shine Ziratul-Hujaju]-[ahirin.Haka nan kuma ana son karanta ziyarar Ashura ko wane daren jumma’a in mutum bai samu yi ba sai yayi a ranar jumma’a .6-Sadaka:Ana son mutum yayi sadaka ko kyauta a duk jumma’a wato kamar yadda aka samo haka daga Imam Ba}ir[AS].Domin yazo hadisi cewa ana nunnuka ladar sadaka a daren jumma’a da kuma ranar har sau dubu.7-Wasu Ladubba:Wato kamar su wankan jumm’a,sa tufafi mai kyau,yenke a kaifa,sa turare,da]a kyautata ma iyali da dai sauran ladubba na daren jumma’a da kuma ranar jumma’a kamar yadda suka zo a hadisai.Sai kuma bayani kan ababen da aka ambata sama dangane da sallar jumma’a.

          1-Hukuncin sallar Jumma’a:Sallar jumma’a wajiba ce a lokacin da Imami Ma’asumi yake a halarce wato a bayyane.Amma a zamanin gaiba wato na fakuwar Imami kamar wannan zamanin da muke ciki tana matsayin wajibi ne wanda ake ce ma wajibi-takariyyi,wato wajibi na za~i ko dai mutum yayi sallar juma’ar ko kuma yayi sallar azahar.Amma abin da yafi zama ihtiya]i wato taka tsantsan shine mutum ya ha]a tsakanin su wato bayan yayi sallar jumma’a sai yayi sallar Azahar sai dai tambihi anan shine yin haka ba wajibi ba ne.In kuma cikin biyun zai za~i guda ne to yin jumma’ar ita tafi falala,sallar azahar kuma ita tafi zama ihtiya]i.Saboda haka anan mutum na da hanyoyi ukku ko dai yayi sallar jumma’a,ko yayi sallar azahar,ko kuma ya ha]a tsakaninsu wato yayi jumma’a bayan haka kuma yayi sallar azahar,kuma duk wanda yayi cikin ]ayan ukkun nan yayi.

          2-Wanda Sallar jumma’a take wajaba kansa:Sallar jumma’a ta na wajaba kan 1-Baligi wato ba ta wajaba kan yaro ba.2-Namiji wato ba ta wajaba kan mace ba.3-Mazauni wato bata wajaba kan matafiyi ba.4-[a wato ba ta wajaba kan bawa ba.5-Mai hankali wato ba ta wajaba kan mahaukaci ba.6-Mai gani wato ba ta wajaba kan makaho ba,ko kuma mai wata lalura ta rashin lafiya.7-Haka nan ba ta wajaba akan tsoho tukuf-tukuf  ba.8-Kada ya kasance tsakanin in da yake da masallacin jumma’a ya wuce farsaki biyu wato in ya wuce farsaki biyu to ya na daga cikin wa]anda jumma’a ba ta wajaba kan su ba,Farsaki ]aya shine kilomita biyar da rabi saboda haka farsaki biyu shine kilomita 11.Kamar yadda mazauna cikin birane da }auyuka za su iya tsaida sallar jumma’a haka nan mazauna daji kamar ruga ta Fulani ko kuma mazauna tantuna misali ‘yan gudun hijira duk suma za su iya tsaida sallar jumma’a idan an cika sharu]]anta.To tambaya a nan da a ce wanda juma’ar ba ta wajaba kansa ba misali matafiyi ko mace sai yaje yayi juma’ar to ta wadatar? Amsa ta wadatar wato da matafiyi zai bi sallar jumma’a shike nan ba sai yayi azahar ba  haka nan macen, wato dai wa]annan da bata wajaba akan su ba, in da za su yi sallar juma’ar to ta wadarta masu daga yin sallar azahar.

          3-Sharu]]an sallar jumma’a:Sallar jumma’a ta na da sharu]]a wanda sai in akwai sune za a iya tsaida ita ga su:1-Adadi dole ne adadin wa]anda zasu yi sallar jumma’a a mazhabar ja’afariyya  a}alla su kai mutum biyar  wasu mujtahidan sun ce a}alla mutum bakwai amma idan }asa da haka ne to jumma’a ba zata yi yu ba,kuma wannan adadi na mutum biyar ko bakwai  dole ne dukkansu su kasance mazaje,da a ce maza hu]u ne da mace ]aya to nan jumma’a ba zata yiyu ba.A mazhabar malikiyya kuma adadin a}alla sai ya kai 12 ne.A mazhabar shafi’iyya su kuma adadin sai ya kai mutum 40.A mazhabar Hanafiyya kuma a}alla mutum 3.A mazhabar Hanbaliyya kuma a}alla adadin sai ya kai mutum 50 ne.2-Daga cikin shara]i na jumma’a akwai khu]uba wato jumma’a ba ta }ulluwa in ba da ita ba,bayani kanta zai zo nan ga ba.3-Daga cikin sharu]]a na jumma’a akwai cewa dole ne ya kasance tsakanin wannan masallaci ko muhalli na jumma’a zuwa ga wani masallaci na jumma’a sai an samu a}alla mil ukku tsakani.Amma idan an samu mil ukku tsakani to dukkan jumma’ar ta inganta,idan ko tsakaninsu }asa da mil ukku ne to ]aya sallar jumma’ar ba ta in ganta ba wato shi masallaci na biyun,amma fa wannan a mazahabar ja’afariyya ke nan amma a mazahib na Ahlus-sunna ba su da wannan hukuncin,shi ya sa kana iya samun gari guda da massallatan jumma’a masu yawa.Akasin ko }asashe na shi’a in mutum yaje can zai ga cewa kusan ko wane gari massacin jumma’a ]aya ne saboda haka sai ka ga miliiyoyin jama’a ne ke ha]uwa waje ]aya.Akwai wata mas’ala wanda ita ma aka samu sa~ani akai na cewa ina ake sallar jumma’a? To a mazhabar Ja’afariyy,Hanafiyya,Shafi’iyya da kuma Hanbaliyya sun tafi akan cewa babu wani ayyanannan waje na yin ta wato za a iya yin ta a masallaci ko ba a masallaci ba,to amma a mazhabar malikiyya sun tafi akan dole sai a masallaci za a yi sallar jumma’a,in ko aka yi ta ba a cikin masallaci ba to ba ta inganta ba.

          5-Yadda ake sallar Jumma’a:Sallar jumma’a kamar yadda aka sani raka’a biyu ce wato kamar sallar Asuba.Mustahabbi ne bayyana karatu a cikin ta saboda haka da liman zai yi karatun ta a ~oye kamar sallar azahar sallar ta yi sai dai an rasa ladar mustahabbi.Kuma mustahabbi ne karanta suratul jumma’a wato bayan fatiha a raka’a ta farko,a raka’a ta biyu kuma suratul munafi}un,kuma ko da ace sallar azahar mutum yayi ba sallar jumma’a ba to su ake so mutum ya karanta.Haka nan kuma sallar jumma’a ta na da }unuti biyu ne,na farko shine a raka’a ta farko bayan mutum ya kammala sura kafin ya tafi ruku’u zai yi }unuti,na biyu a raka’a ta biyu bayan kammala sura sai a yi ruku’u, to idan an ]ago daga ruku’un  kafin a wuce sujuda sai ayi }unuti, ana ga ma }unutin sujuda za a wuce kai tsaye,idan ko aka sake ruku’i to sallah ta ~aci.A wannan waje ne kawai ake }unuti bayan ruku’u a mazhabar ja’afariyya kamar yadda yazo daga Imam Sadi}[AS] yace duk }unuti ana yi ne gabanin ruku’u sai na sallar jumma’a a raka’a ta biyu shi bayan ruku’u ake yi.

          5-Lokacin sallar Jumma’a:Lokacin sallar jumma’a shine daga lokacin da rana ta yi zawali,idan aka yi ta gabanin zawal to ba ta inganta ba,amma yin khu]uba ita za a iya fara ta ko da zawal bai yi ba.sai dai ihtiya]i a fara ta lokacin da zawal yayi.Kuma idan lokacin sallar jumma’a ya fita to sallar azahar ita ta wajaba domin ba a ramakon sallar jumma’a wato in lokacinta ya fita sai dai ayi sallar azahar.Haka nan wani abun da ke  da ala}a da lokacin sallar jumma’a shine batun kiran sallah,a mazhabar ja’a fariyya kiran sallah  guda ]aya ake yi kuma sai lokaci ya shiga ake yi wato sa~anin yadda yake a mazhabobi na Ahlus-sunna akwai abin da suke ce ma kiran sallah na farko da kuma na biyu,kuma wani abun mamaki hatta a littafansu sun tabbatar da cewa lalle ba wannan kiran a lokacin Manzon Allah  Bani-umayya ne suka }ir}ire shi.

          6-Khu]ubar sallar Jumma’a:Yin khu]ba a sallar jumma’a wajibi ne,idan aka yi sallar jumma’a ba a yi ta ba to sallar jumma’a ba ta yi ba,kuma a na yin wannan khu]ubar ne gabanin sallar jumma’a.Yadda ake yin khu]ubobin shine da yake guda biyu ne,Khu]uba ta farko liman zai fara da godiya ga Allah ta’ala da kuma yabonsa,bayan haka kuma yayi salati ga Manzon Allah[AS] da kuma Ahlul bayt[AS] bayan haka kuma sai yayi wasiyya da tsoron Allah ma]aukaki,saannan sai ya karanta sura gajera kamar suratu Asar ko suratul Iklas.A khu]uba ta biyu kuma ya yi salati ga Manzon Allah da kuma Ahlul bayt da kuma ambaton sunayensu ]aya bayan ]aya,bayan haka kuma yayi istigfari ga mu’uminai maza da mata.Haka nan kuma a cikin khu]uba ana son ayi bayani dangane da halin da musulmi da musulunci suke ciki a lokacin a addininsu da kuma duniyarsu.Kuma wajibi ne lokacin da liman yake khu]uba ya kasance a tsaye ba a zaune ba.Haka nan kuma wajibi ne liman ya raba tsakanin khu]ubar farko da ta biyu da zama ]an ka]an.Haka nan kuma wajibi ne ya kasance wanda zai yi khu]uba ya kuma zamo shi zai yi limanci,baya kasance mai khu]uba dabam kuma liman dabam ba.Wata tambaya itace shin ita khu]ubar dole sai da larabci za a yi ko za a iya yi da wani harshe misali hausa? Amsa za a iya yin ta da ko wane harshe ba sai larabci ba amma a wajen godiya ga Allah da kuma salati ga Manzon Allah da kuma alayensa shi da larabci zai yi, sauran bayanai ya na iya komawa ga harshen da mutanen ke ji  misali harshen hausa.Amma a mazhabar malikiyya dole ne khu]uba ta kasance da larabci.Haka nan kuma lokacin da ake yin khu]uba mutum zai yi shiru ne ya kuma saurara.To tambaya anan mi ye hukuncin yin Magana lokacin khu]uba? A mazhabar jaafariyya makruhi ne amma a mafi yawan mazhabobi na Ahlus sunna haramun ne.

          7-Wasu mas’aloli na sallar jumma’a:Yin ciniki wato saye da sayarwa da kuma sauran mu’amaloli a ranar jumma’a bayan kiran sallah a wannan zamani da muke ciki na gaiba bai haramta ba kamar yadda Imamu khumaini ya yi bayani a cikin littafinsa na Tahrirul-wasila.Idan mutum ya samu liman a ruku’un raka’a ta biyu to ya samu jumma’a, amma da zai same shi bayan ]agowarsa daga ruku’u a raka’a ta biyu to anan sallar Azahar zai yi.Haka nan kuma shakka a adadin raka’oin sallar jumma’a yana ~ata sallah,wato ana shakka raka’a ]aya aka yi ko biyu.

Wannan kenan baki daya dangane da bayani akan Sallar Jumma’a.

 
Home Darusan Fiqh Bayani kan sallar Jumma’a.
Copyright © 2024. www.tambihin.net. Designed by KH