Wednesday, 24 April 2024
Email
Make My Homepage
RSS
Register
Munasabobin watan Zhul Qadah. Print E-mail
Written by administrator   
Sunday, 31 August 2014 09:04
Watan Zhul-Qadah shine wata na 11 a jerin }idaya na watannin musulunci 12.Kuma wannan wata yana ]aya daga cikin watanni hu]u masu al farma da daraja da kuma matsayi a wajen Allah Ta’ala wa]anda aka hana zaluntar kai a cikinsu,wato kamar yadda yazo a cikin Al-}ur’ani mai girma a suratu-Taubah aya ta 36.
Ranar farko na watan ne aka haifi Sayyida  Ma’asuma [AS],wato wadda  kabarin ta ke birnin -}um,ita ce kuma babbar ‘yar Imam kazim [AS].}an-wa ke nan take ga Imam Ridha[AS]saboda haka,Anan  tabarrukan  za’a kawo tarihinta a ta}aice.                                                                                                         
        1.WILADARTA: Watau haihuwarta,an haife ta a madina,1 ga watan zul }adah,Hijira ta 173.                      
        2.NASABARTA: Mahaifinta shine Imam kazim [AS],sunan mahaifiyarta [ahira,wato mahaifiyarsu  ]aya da Imam Ridah [AS],kuma ita wannan mahaifiya tasu,[ahira bai war Allah ce mai yawan ibada, kamar yadda yazo a tarihinta.Ya mazo a tarihinta cewa,lokacin da ta haifi  Imam Ridah [AS] ta bu}aci a nemo mata mai raino,aka tambaye ta dalili,sai tace ibadodin da ta saba yi sun ragu,saboda haka tana bu}atar taimakawa wajen reno domin ta cike gi~in ibadodinta.Kakanta shine Imam Sadi} [AS].Yazo akan cewa tun gabanin a haife  ta yayi albishir da haihuwarta da kuma fa]in falalar ta da kuma  ziyarar  ta.Daga cikin falalar ta da Imam Sadik [AS] ya fa]i,akwai  cewa tana da matsayi a wajen Allah [T].Shi yasa wanda duk Allah [T] yayi wa muwafa}a da ziyarar haramin kabarinta dake birnin }um,a kofar shiga haramin  zai ga an rubuta “Ya Fa]ima ki ce ce ni a wajen Allah,domin ki na da matsayi a wajensa”.Allah Ta’ala ya saka mu cikin wa]anda zata ceta.                                                                       
3.LA{UBBANTA: Tana da la}ubba masu yawa,amma biyun  nan su suka  fi  fice,sune Karimatu- Ahlulbayt  da  kuma Ma’asuma.Wannan la}abi na Ma’asuma yazo akan cewa Imam Ridah [AS] yayi mata la}abi da shi,wanda wannan yana alam ta, gayar kamalar ta da kuma matsayin ta.       
   4.FALALAR ZIYARAR KABARINTA: An samo daga Imam Ridah [AS] cewa duk wanda ya ziyarce ta,Aljanna ta tabbata a gare shi.Haka nan makamancin wannan Hadisin,an samo daga Imam Jawad [AS] cewa duk wanda ya ziyarce ta,Aljanna ta tabbata gare shi.                                                                                                            
5.KARAMOMINTA: Ma’asuma [AS] ta kasance  ta na da karamomi masu yawa,tun tana raye da bayan wafatinta,kai har wannan zamanin namu kullum karamominta da]a bayyana suke.Za kaga masu ziyararta, zasu yi tawassuli da ita kan bu}atocin su,kuma ka ga Allah ya biya musu bu}ata.marasa lafiya zaka  ga an kawo su,ayi tawassuli da ita,ka ga Allah ya basu lafiya.shi yasa wani daga cikin malaman tarihi yake cewa babu wani daga cikin ‘ya’yan ma’asumai [AS] da yake da karamomi masu yawa kamar ta.Haka nan yau a doran }asa babu wata bai war Allah da take samun masu yawan ziyara kamar yadda take samu.Domin idan mutum yaje Haramin ta zai ga dare da rana maziyar ta ne,daga cikin karamominta daya bayyana  a  wannan  zamanin  namu  a shekarun baya,shine  akwai  gyaran  ainihin shi kabarin ta da akayi ,aka za~i manyan malamai daga ciki akwai Ayyatullah Najafi Almar’ashi,shine yake cewa babu wani abun daya canza na likkafanin ta da kuma jikinta,yace kamar kace yau aka sata.                                                                  

6.JARABAWOYIN TA: Ma’asuma [AS] ta fuskanci jarabawoyi masu yawa a rayuwarta,musamman a }arshen rayuwarta,misali  bankwana  da kuma zafin rabuwa da ]an uwanta Imam Ridah [AS] lokacin da zai bar madina zuwa khurasan,tafiya wadda ba zai dawo ba,kamar yadda ya shaida masu.Duk da sun yi  bankwana,amma  ta hau soron dakin na gidansu, tayi ta kallon Imam Ridah [AS] har ta dai na ganinsa,kuma wannan shine }arshen ganinta da Imam Ridha,a gidan duniya domin bayan haka basu sake ha]uwa ba.Ala}a da kuma sha}uwa na Imam Ridah [AS] da Sayyida Ma’asuma,kamar  ala}a  da kuma sha}uwa na Imam Husain [AS] da  kuma Sayyida Zainab [AS]ne. Bayan haka  ga kuma jarabawar mahaifinta, wato Imam kazim [AS] da ta gani na zamansa a kurkuku da kuma shahadarsa  a ciki, da dai sauran jarabawowi masu yawa da ta  fuskanta,wanda ba za’a iya kawo su ba saboda gudun tsawaitawa.                      

7.ILIMINTA:Sayyida  Ma’asuma [AS]  ta kasance mai yawan ilimi,akwai wani abin da ya ta~a faruwa,wanda ya nuna matsayinta a ilimi wannan abin ko shi ne akwai wani lokacin da wasu daga cikin mabiyan Imam kazim [AS] suka zo daga garinsu zuwa madina,domin su ga Imam kazim [AS] su gai she shi,su  kuma gabatar da wasu tambayoyi, da suka zo madina suka isa gidan Imam kazim [AS]sai suka samu bai nan yayi tafiya,sai suka rubuta tambayoyi  suka ba Sayyida Ma’asuma [AS] cewa in ya dawo ta bashi,kashe  gari sai suka dawo suka samu bai dawo ba,alhali su kuma suna son su koma garinsu a ranar,sai  Sayyida Ma’asuma [AS] ta rubuta masu amsoshin  tambayoyin, suka  amsa  suna farin ciki.Kan hanyarsu ta komawa sai suka ha]u da Imam kazim [AS] yana dawowa sai suka shaida masa ma}asudin zuwan su da kuma abinda ya faru sai Imam Kazim [AS] yace su kawo amsar takardar ya gani,bayan ya gani ya fa]i wannan kalmar sau uku, “ta fanshi babanta”.                                                                                           

8.IBADARTA: Ta kasance mai yawan ibada.Hatta in da take yin ibadar ta,salloli da makamantansu yana nan har yanzu a birnin }um ana ma kai ziyara wajen.                                                                      
9.WAFATINTA: Ta rasu tana da shekaru 30 a duniya,sababin rasuwar ta shine; ta bar madina ita da wasu ‘yan uwanta da nufin su tafi khurasan wajen Imam Ridah [AS], akan hanya a wani waje mai suna SAWA rashin lafiya ya kama ta,ta bu}aci a tafi zuwa }um,da suka isa kwanan ta 17 Allah yayi mata rasuwa.
Haka nan a cikin wannan wata na Zhul-Qadah aka haifi Imam na 8 wato Imam Ali Arrida,domin yazo a tarihi cewa an haife shi ranar Alhamis 11 ga watan zul }ada a shekara ta 148 bayan hijira.Ya rasu 23 ga watan zul }ada shekara ta 203 bayan hijira.Amma a wata ruwaya,yazo a kan cewa rasuwarsa ta kasance a watan safar ne.Shaikh Abbas Al-}ummiy  ya tafi akan 23 ga watan zul }ada, kamar yadda ya kawo a littafinsa na mafatihul Jinan.Har ya ci gaba da cewa sunna ne ziyarar Imam Ridha[AS]a ranar daga kusa ko kuma nesa.In mutum ya duba littafin mafatihul jinan zai ga ya kawo  ziyarori dabam-dabam na Imam Ridha[as].In mutum zai iya biya su duka a ranar yana da kyau,ko kuma ya karanta abinda ya sau}a}a masa na ziyarar.Haka nan in aka duba za a ga cewa tsakanin haihuwar Imam Ridha[AS] da rasuwar Imam Sadi}[as]Kusan kwanaki 15 ne.Domin wafatin Imam Sadi}[as] a watan shawwal ne 25 gare shi,shekara ta 148,shi kuma wiladarsa 11 ga watan zul }ada shekara ta 148.Ya mazo a kan cewa Imam Sadi}[as] yayi fata da shau}in ha]uwa da Imam Ridha[as]domin  ya gan shi,har ambatonsa yayi da kalmar MALAM,tun gabanin a haife shi.Imam Ridha[AS]kamar yadda aka ambata shine Imam na takwas a jerin Imamai 12,an haife shine a Madina,sunan mahaifiyarsa, [ahira,sunan mahaifinsa kamar yadda aka sani Imam Kazim[AS]kuma yana da la}ubba da yawa,amma  wanda  yafi  shahara  shine  wannan  la}abi nasa  na Arri-dha.An tambayi Imam Jawad[AS]cewa mi  yasa ake cewa babanka  Arri-dha,ya  ba da  amsa da cewa;Saboda ma}iyan sa sun yarda da shi,kamar yadda masoyan sa suka yarda  dashi.yace haka bai kasance  ga Imamai da suka gaba ce shi ba.Shekarunsa  a  duniya 55,muddan shekarun Imamancinsa 20,wato ya na da shekaru 35 a duniya Imamanci ya dawo gare shi.kabarinsa yana a khurasan ne,wato a }asar Iran.Kuma  yaro ]aya yake da shi shine,Imam  Jawad[as]idan mutum ya bincika zai ga cewa Imam Ridha[as]shine mafi }arancin’ya’ya, idan an kwatanta da Imaman da suka gabace shi da kuma wa]anda suka biyo bayansa,in ka ]ebe Imam Hasan Al-askari[as]da yake yazo akan cewa shima ]a ]aya yake dashi,shine Imam Mahdi[AF].Haka nan kuma a }arshen wannan wata na Zhul-Qada ne wafatin Imam Jawad.Nan wasu sassa ne na rayuwarsa:
Wiladarsa:An haifi Imam Jawad[AS] a madina,ranar 10 ga watanRajab shekara ta 195 bayan hijira.Kuma shine Imam na 9 a jerin }idaya na Imamai 12.
Nasabarsa:Sunan mahaifiyarsa Sabika.sunan mahaifinsa Imam Ali- Arrida[AS]
Nash’a ]insa:Ya tashi a madina,ya rayu tare da mahaifinsa shekara 18.Amma }arshen rayuwarsa ta kasance a Ira} ne.
La}ubbansa da kuma kinayarsa:Yana da la}ubba masu yawa,amma wa]anda suka fi fice sune Al-Jawwad da kuma Atta}iy.Kuma anai masa kinaya da Abu Ja’afarus-sani.kuma yazo akan cewa Imam Ridha[AS] saboda Ta’aziminsa bai ambatonsa da sunansa sai dai da wannan kinaya ta Abu Ja’afar.
Shekarunsa:Ya rayu a duniya shekaru 25.Wato shine mafi}arancin shekaru idan an kwatanta da Imaman da suka gabace shi da kuma wa]anda suka biyo bayansa.Kamar yadda Imam Sadi}[AS] shine mafi yawan shekaru,a cikin Aimma[AS] domin ya rasu yana da shekaru 65,a wata ruwaya 68.
Muddan Imamancinsa:Shekaru 17 ne.
‘Ya’yansa:Yana da ‘ya’ya 4.maza biyu,mata biyu.
Wafatinsa:Imam Jawad[AS] ya rasu ranar Asabar }arshen watan Zul-}ida,shekara ta 220 bayan Hijira.kuma ya rasu sakamakon guba da khalifan Abbasawa mai suna Mu’utasim yasa asa masa.wato kamar yadda aka sa guba ga Imaman da suka gabace shi da kuma wa]anda suka biyo bayansa,in ka ]ebe Imam Ali[AS] da kuma Imam Husain[AS] su da takobi ne aka aka kashe su.kamar dai yadda yazo daga Imam Sadik[AS] yace, “Babu wani daga cikinmu face wanda aka kashe da takobi ko aka sa mai guba.”
Kabarinsa:}abarinsa yana a kazimiyyane wato a Ira}, kusa dana kakansa Imam Kazim[AS].
Ayyukan Ibadodi na watan Zhul-Qadah
 
Yazo a hadisi cewa watan Zhul-Qadah wata ne da ake amsar addu’oi musamman ma lokacin da ake cikin tsanani.Saboda haka yana da muhimmanci mutum ya yawaita addu’oi a cikin wannan watan.Haka nan akwai wata sallah raka’a 4 da ake son yinta a ranar lahadin farko na wannan wata,amma idan mutum bai samu yinta ba to zai iya yinta a ranar lahadi ta biyu ko ta ukku ko ta hu]u.Kuma wannan sallah tana da falaloli masu yawan gaske saboda haka kada mutum ya kasance bai yi ta ba.Ga mai bu}atar ganin falaloli na sallar da kuma yadda ake yinta yana iya duba littafin mafatihul jinan Babi na biyu fasali na biyar.Haka nan ana son raya daren 15 na wannan wata da Ibadodi,wato akwai falala mai yawa ga yin haka.Saboda haka idan mutum zai iya ana son daren baki ]ayansa mutum ya kwana yana ibada ne.Yazo akan cewa ladar wanda yayi ibada a daren kamar wanda ya shekara 100 yana azumi kuma bai sa~a ma Allah ta’ala ba a cikin su ba.Haka nan kuma yazo a hadisi cewa, “Duk wanda ya ro}i Allah wata bu}ata a daren to Allah zai ba shi abun da ya ro}a.” Haka nan daren 25 da kuma ranar 25 ga wannan wata na Zhul-Qadah lokuta ne masu tarin al-barka domin yazo akan cewa rana ce da aka shinfi]a }asa a wannan duniya.Ga mai bu}atar ganin ayyuka na ibadodi da ake son yi a ranar yana iya duba mafatihul jinan babi na biyu fasali na biyar.Ko da mutum bai samu yin wasu ayyuka na ranar ba to kada ya yarda azumin ranar ya ku~uce masa,saboda yazo akan cewa duk wanda ya raya daren da ibada kuma ya azumci ranar to za a rubuta masa lada kamar wanda ya shekara 100 yana ibada.Bayan haka kuma yazo daga Imam Ridha[AS] cewa a daren 25 ga wannan wata na Zhul-Qadah aka haifi Annabi Ibraheem[AS] da kuma Annabi Isa[AS].Wannan ke nan a ta}aice dangane da munasabobin watan Zhul-Qadah.  
 
Home Munasabobi Munasabobin watan Zhul Qadah.
Copyright © 2024. www.tambihin.net. Designed by KH