Monday, 20 January 2025
Email
Make My Homepage
RSS
Register
Munasabobin Watan Shawwal Print E-mail
Written by administrator   
Friday, 08 August 2014 20:29

 Watan shawwal shine wata na goma a jerin }idaya na watannin musulunci 12.Yazo a hadisi daga Manzon Allah[S] cewa:Ana ce ma wannan wata shawwal saboda a cikinsa an goge dukkan zunuban mu’uminai.Saboda haka wannan wata wata ne da mutum ke shiga cikinsa yana tsarkakakke daga zunubai,wato kasantuwar mutum ya fito cikin watan Ramadan wanda ana fata a cikinsa Allah[T] ya gafarta ma mutum dukkan zunubansa.Saboda haka watan shawwal wata ne da ake so mutum yayi mujahada wajen ganin cewa tsarkakar da ruhinsa ya samu a watan Ramadan daga zunubai,yayi iyaka iyawarsa wajen ganin cewa bai sake }azantar da ruhinsa ba  ta hanyar aikata zunubai na zahiri da ba]ini,domin zunubi guba ne ga ruhin ]an Adam.Haka nan tarbiyya da mutum ya samu a watan Ramadan na ibadodi da Akla}, mutum yayi }o}ari ya ]ore a kai har ya zuwa wani watan Ramadan insha-Allah.Domin idan ya kasance watan Ramadan ya kama ya fita amma mutum bai samu sauyi a ruhinsa ba,wato zuciyarsa ba ta tasirantu da hasken watan Ramadan ba,to lalle duhun zunubin sa ya mamaye zuciyarsa.Shi yasa yana da muhimmanci bayan watan Ramadan mutum ya zauna yayi ma kansa muhasaba,ya tambayi kansa  cewa akwai banbanci da ya samu a rayuwarsa a addinance a bayan watan Ramadan da kuma kafin watan Ramadan,in akwai banbanci wato mutum yanzu ya samu ci gaba to alhamdu-lillahi haka ake so,in ko yaga ci baya ma yayi to mutum ya zama mai zaluntar kansa,in ko ba wani banbanci wato bai yi gaba ba kuma bai yi baya ba to mutum ya zama mai ta}aitawa.Saboda haka wannan haske da kuma tsarkaka na ruhi da mutum ya samu albarkacin watan Ramadan ka da  mutum ya sake  ya gushe,kuma babbar hanya ta yin haka shine nisantar zunubi.

                                                                AYYUKAN WATAN SHAWWAL

            Ko wane wata kamar yadda Malaman Irfan suka yi bayani yana da ayyuka iri biyu,ayyuka na amma da kuma ayyuka na khassa.Ayyuka na amma sune ayyukan da ake aikatawa ko wane wata misali daren farko na ko wane wata da kuma ranar farko,mai bu}atar ganin wa]annan ayyuka na amma yana iya duba littafin mafatihul jinan babi na biyu fasali na 11.Ayyuka na khassa sune ayyukan da suka ke~anta da ko wane wata,saboda haka ayyuka na khassa na watan shawwal sune:Ayyuka na daren idin }aramar sallah da kuma ranar sallah ]in,ga mai bu}atar ganin wa]annan ayyuka yana iya duba mafatihul jinan babi na biyu fasali na 4.Haka nan daga cikin ayyukan watan shawwal akwai yin azumi shidda,wato wannan azumi shidda kamar yadda yazo a ruwayoyin hadisai na Ahlus-sunna,haka ma yazo a ruwayoyi hadisai da aka samo daga Aimma na Ahlul bayt[AS]misali hadisin da yazo daga Imam Bakir[AS] yace:Duk wanda ya yi azumi shidda bayan idil fi]ir to kamar wanda ya azumci zamani ne dukkansa.Wani tambihi anan shine idan akwai ramakon azumi na wajibi akan mutum to ba zai yi wa]annan azumi shidda na shawwal ba har sai ya yi na wajibin dake kansa tukuna.Amma idan akwai ramakon sallah ta wajibi kan mutum to mutum zai iya yin salloli na nafila ko da ko bai gama rama su ba.A ta}aice dai abun da ake so a fitar a nan shine idan ana bin mutum azumi na wajibi to ba zai yi azumi na nafila ba,akasin da ace sallah ce ta wajibi ake bin mutum to zai iya yin sallar nafila.

ABUBUWAN DA SUKA FARU A TARIHI A WATAN SHAWWAL

Wannan wata na shawwal akwai abubuwa da yawa a tarihi da suka auku a cikinsa ga wasu daga ciki:1-A biyar ga watan shawwal shekara ta 60 bayan hijira Muslim ]an A}il ya isa Kufa,kuma wannan ya nuna wa}i’ar karbala ba kamar yadda mafi yawa aka ]auka ba cewa wa}i’a ce wadda ta faro aka kuma gama ta cikin kwanaki ka]an,a’a wa}i’a ce wadda a }alla an kwashe wata shidda wato daga farowar ta zuwa }arshen ta.Domin wannan wa}i’a ta faro ne tun watan Rajab shekara ta 60 bayan hijira har ya zuwa 10 ga watan Muharram shekara ta 61 bayan hijira,mu duba tun 5 ga watan shawwal Imam Husain ya aika Muslim ]an A}il zuwa Kufa,wanda in mun lissafa zamu ga wata ukku gabanin shahadar Imam Husain[AS].2-Daga cikin abubuwa na tarihi da suka auku a watan shawwal akwai cewa a ranar 8 ga watan shawwal shekara ta 1344 bayan hijira wahabiyawa suka rusa ginin }abarin Imam Hassan[AS] Imam Sajjad[AS] Imam Bakir[AS] da kuma Imam Sadik[AS]wato a ma}abarta ta Ba}i’a dake Madina.Ga wanda ya san tarihi da kuma A}idu na wahabiyawa wannan ba zai bashi mamaki ba,in ma mutum bai san tarihinsu ba ko a}idunsu to ya dubi masu fahimta irin nasu a wannan nahiya da yake zaune zai ga in sun samu dama suna aiki irin nasu,misali sai ka ga gine-gine na }aburbura na wasu sai a wayi gari an rushe gine-ginen.A kan wannan asasi in muka duba zamu ga a yau wajaje masu yawa na tarihi a makka da madina an rasa su,misali gidan da aka haifi Manzon Allah a makka,tsawon tarihi wannan gida mai albarka yana nan har massallaci aka yi a wajen,musulmi na ziyartar gidan da kuma massallacin su yi sallah ciki domin neman tabarruki, amma abun ba}in ciki a shekarar 1926 mahukunta sa’udiyya suka sa aka rusa gidan da masallacin.Haka nan ma }abarin mahaifin Manzon Allah shima aka rusa aka yi titin mota a wajen,wannan a madina ke nan domin mahaifin Manzon Allah ya rasu a madina ne.Dalilin zuwan sa madina shine lokacin da mahaifiyar Manzon Allah wato Aminatu  bintu Wahab tana da cikin sa wata bakwai,sai kakan Manzon Allah Abdul-Mu]allab ya tafi madina tare da mahaifin Manzon Allah wato Abdullahi,saboda su sawo kayan walima idan ta haihu.To bayan isar su madina ba da jimawa ba sai Abdullahi ya kamu da rashin lafiya,bayan jinya da yayi ta kwana 15 sai ya rasu aka binne shi a madina,kuma }abarin sa  tun wancan lokacin har ya zuwa shekaru 50 da suka wuce yana nan,domin akwai wani malami dana ji yana bayani a wannan munasaba ta rusa ginin }aburburan Aimma[AS] da ke Baki’a yake cewa shekaru 40 zuwa 50 da suka wuce in ya tafi aikin hajji ya kasance yak an ziyarci kabarin mahaifin Manzon Allah[S]to amma abin mamaki wani zuwa da yayi sai ya ga an rusa kabarin titin mota ya biyo ta wajen.Ire-ire wa]annan abubuwa na shafe da kuma kauda ababe na tarihi da mahukumta sa’udiyya suka yi kuma suke kan yi suna da yawa,wato a }o}arinsu na kau da duk wani abu dake tunasar da mutane tarihin addinin musulunci ko kuma hana mutane neman tabarrukinsu.3-Daga cikin abubuwa da suka auku a watan shawwal na tarihi akwai cewa a 15 ga watan shawwal shekara ta ukku bayan hijira aka yi ya}in Uhud,kuma a wannan rana ce sayyiduna Hamza yayi shahada,akan asasin haka anai masa la}abi da shugaban shahidai wato na zamaninsa wato kamar yadda Sayyida Maryam take shugaban mataye na zamaninta.4-Daga cikin abun da suka auku a tarihi a watan shawwal akwai cewa a 17 ga watan shawwal shekara ta 5 bayan hijira aka yi ya}in khanda} ana kuma ce masa ya}in Ahzab.5- Haka nan a ranar 25 ga watan shawwal shekara ta 148 bayan hijira Imam Sadi}[AS] ya rasu a madina.Nan wasu sassa ne na rayuwar Imam Sadik[AS] 1-Haihuwarsa:An haife shi a madina ranar jumma’a 17 ga watan Rabiul-Awwal shekara ta 83 bayan hijira.2- Nasabarsa: Sunan mahaifiyarsa Fatimatu ‘yar {asim,sunan mahaifinsa Imam Muhammad Al-ba}ir[AS] 3-Nash’a ]insa:Imam  Sadi} ya tashi a madina ya rayu a madina ya kuma rasu a madina wato baki ]aya rayuwarsa a madina ne ta kasance.4- La}ubbansa:Yana da la}ubba masu yawa amma wanda yafi shahara shine Sadi},kuma ana yi masa kinaya da Abu Abdullahi.5-Shekarunsa:Imam Sadi} ya rasu yana da shekaru 65 a duniya a wata ruwaya 68,a cikin imamai baki ]aya in ka cire Imam Mahdi[AF] to Imam Sadik[AS] ne yafi su yawan shekaru a duniya.,mai bi mashi a yawan shekaru shine Imam Ali[AS] ya bar duniya yana da shekaru 63 ne.6-Muddan Imamancinsa:Shekaru 34 ne.7-‘Ya’yansa:Imam Sadik[AS] yana da ‘ya’ya 10,maza 7,mata ukku.8-Wafatinsa:Ya rasu 25 ga watan shawwal shekara ta 148 bayan hijira.9-Kabarinsa:Yana a madina ne.5-Haka nan daga cikin abubuwan da suka auku a tarihi a watan shawwal akwai rasuwar Imam Khumaini,domin a lissafi na watannin musulunci Imam Khumaini ya rasu ne a 28 ga watan shawwal shekara ta 1409 bayan hijira,a lissafin miladiyya kuma ya rasu ne 3 ga watan June 1989.Nan kuma wasu sassa ne na rayuwar Imam Khumaini.1-Haihuwarsa:An haife shi a garin da ake ce ma khumain a ranar 20 ga watan Jimada-sani shekara ta 1320 bayan hijira.2- Nasabarsa:Sunansa Sayyid Ruhullah,sunan mahaifinsa Sayyid Ayatullah Mustapha,sunan mahaifiyarsa sayyida Hajar,wato shi sayyid ne ta wajen uwa da uba.3-Shekarunsa: Ya rayu a duniya shekaru 93 ne.4-Shekarun da yayi bayan juyin musulunci:Ya rayu kusan shekaru 10 ne.5-‘Ya’yansa:Yana da ‘ya’ya biyar maza biyu mata ukku.6-Kabarinsa:Yana a birnin Tehran ne wato babban birnin Iran.Wannan kenan a ta}aice dangane da munasabobin watan shawwal.

 

 
Copyright © 2025. www.tambihin.net. Designed by KH