Kusantowar bayyanar Imam Mahdi {AF}. |
Written by administrator | |||
Thursday, 03 July 2014 19:36 | |||
Wannan maudu’i mai taken Kusantowar bayyanar Imam Mahdi[AF] maudu’i ne mai gayar muhimmanci musamman idan muka yi la’akkari da halin da duniya take ciki.Haka nan kuma idan muka dubi hadisai da suka zo daga Manzon Allah[S]da kuma Aimma na Ahlul bayt[AS]da suke bayanin alamomin bayyanar Imam Mahdi[AS]zamu ga cewa dukkan wa]annan alamomi sun bayyana,yanzu alamomin da suka rage sune wa]anda za su kasance gab da ya bayyana wato misali alamomin da zasu kasance a shekarar da zai bayyana,da kuma alamomin da za su kasance idan ya bayyana.Domin alamomin bayyanar Imam Mahdi[AS] sun kasu kashi ukku:1-Alamomin da za su kasance kafin ya bayyana.2-Alamomin da za su kasance gab da ya bayyana.3-Alamomin da za su kasance idan ya bayyana.Bayanan wa]annan alamomi duka sun zo a cikin hadisai.To alamomin farkon duk sun bayyanna misalinsu shine:1-Yawaitar zalunci da kuma danniya a duniya.2- Yawaitar kashe-kashe da kuma mutuwa da musibobi a duniya.3-Yawaitar fasadi da kuma sa~o a duniya.4-Yawaitar sa~ani da rarraba tsakanin musulmi.5-Ci gaban ilimin kimiyya.6-Ta~ar~arewar tattalin arziki na duniya,shima wannan yana daga cikin alamomin bayyanarsa.7-Yawaitar bayyanar ayoyi a halittun Allah dabam-dabam.8-Ya]uwar fahimta ta Ahlul-bayt[AS].Shima wannan yana daga cikin alamomin bayyanarsa,mutum ya dubi yadda fahimta ta Ahlul bayt take ta yaduwa a sassan duniya,in ma mutum bai san na wani waje ba to ya dubi na wannan nahiya da yake ciki.9-Yun}uri na neman sauyi a sassa na duniya shima wannan yana daga cikin alamomin bayyanarsa,da dai sauran alamomi na kafin bayyanarsa.Saboda haka yanzu alamomin da suka rage sune na biyu da na ukku.Alamomin da za su auku gab da bayyanarsa sune:1-Bayyanar Sufyani:An samo daga Imam Ba}ir[AS]yace, “Fitar Sufyani da Mahdi shekara guda ne.”Wasu ruwayoyi na hadisai sun nuna tsakanin Sufyani da bayyanar Mahdi[AS] watanni ne.Shi Sufyni kamar yadda yazo a ruwayoyi na hadisai mutum ne,wanda nasabarsa ta na tu}ewa ne ga Abu Sufyan shi yasa ake ce masa Sufyani.Asalin sunansa shine Harb, sunan babansa Anbasa shi kuma ]an Murra ]an Kalb ]anSalma ]an Yazid ]an Usman ]an Kalid ]an Yazid ]an Mu’awiya ]an Abu Sufyan,wannan itace nasabars kamar yadda yazo a wani hadisi da aka samo daga Imam Ali[AS].Akwai ma hadisan da suka zo da bayanin siffarsa ta jiki.Kuma zai bayyana a Sham ne,kuma zai yi ~arna a bayan }asa ta fuskoki dabam-dabam musamman ma karkashe mutane,sai dai watanni ne zai yi yana wannan ~arna,wata ruwaya tace wata tara,wata ruwayar kuma wata shidda ne zai yi.Kuma idan Suyani ya bayyana zai kasance duk wasu masu }iyayya da Ahlul bayt da kuma shi’arsu zasu kasance a bayansa,wato dai umayyanci zai dawo sabo,daga }arshe Imam Mahdi[AS]zai kashe shi anan Sham tare da magoya bayansa.2- Bayyanar Dajjal:Shima zai kasance ne gab da bayyanar Imam Mahdi[AS]kuma bayanansa yazo a hadisai masu yawa,misali sunansa,in da zai bayyana,mabiyansa yazo cewa mafi yawan mabiyansa yahudawa ne da kuma ‘ya’yan zina.irin ~arnar da zai yi,in da za a kashe shi, yazo cewa a {udus ne za a kashe shi,wanda zai kashe shi yazo akan cewa Annabi Isa[AS] ne zai kashe shi,a wata ruwayar kuma Imam Mahdi[AS] ne.kai hatta ma da lokacin da za a kashe shi, yazo cewa bayan sallar Asuba ne za a kashe shi,wato dai akwai ruwayoyi na hadisai masu yawa akan haka.3-Daga cikin abin zai auku gab da bayyanar Imam Mahdi[AS]akwai kashe wani bawan Allah kuma jikan Manzon Allah[S] wanda ake masa la}abi da Nafsuz-Zakiyya,yama zo a hadisi cewa tsakanin kashe shi da kuma bayyanar Imam Mahdi[AS] kwana 15 ne.4-Daga cikin abin da zai auku a shekarar da Imam Mahdi zai bayyana shine a watan Ramadan na shekarar da zai bayyana za a yi wani irin khusufi na rana da wata wanda ba a saba ganin haka ba,a hadisin ma ya nuna cewa tun da aka halicci duniya haka bai ta~a faruwa ba.wato za a yi khusufin rana a tsakiyar watan,khusufin wata kuma a }arshen watan,saboda abin da ya saba aukuwa shine khusufin rana yana kasancewa ne a }arshen wata,na wata kuma a tsakiyarsa.Da dai sauran wasu alamomi da zasu kasance gab da bayyanarsa.Sai kuma alamomin da za su kasance idan ya bayyana:Da farko dai ranar da zai bayyana za ta kasance ne Jumma’a ko Asabar,watan kuma zai kasance watan Muharram goma gare shi wato ranar Ashura,shekarar kuma za ta kasance ne ko da 1 ko 3 ko 5 ko 7 ko 9.in da kuma zai bayyana a makka ne,akwai ruwaya akasin haka,zai bayyana ne tare da tutar Manzon Allah[S] kuma yana bayyana mataimakansa na musamman su 313 za su zo su yi masa bai’a.Sai dai wani tambihi muhimmi anan shine ainihin lokacin da Imam Mahdi[AS] zai bayyana babu wanda ya sani sai Allah Ta’ala,akwai ma ruwayoyi na hadisai da suka yi kashedi na ayyana lokacin bayyanarsa.Haka nan kuma a ranar da ya bayyana za a ji sauti daga sama wanda ke fa]in cewa yaku jama’a Mahdi ya bayyana,ku bishi ku shiriya kada ku sa~a masa ku ~ace,gaskiya ta na wajen Ahlu baitin Muhammad.Wannan sautin yazo akan cewa babu wani mutum da yake doron }asa wanda ba zai ji shiba,kai hadisin ya nuna mutum ko barci yake sai yaji,haka nan kuma ko wane yare mutum ke Magana dashi zai ji.Haka nan daga cikin abubuwan da zasu kasance idan Imam Mahdi[AS] ya bayyana akwai saukar Annabi Isa[AS]. Duk wa]annan abubuwan da aka kawo suna nan a hadisai da aka samo daga Manzon Allah[S] da Aimma[AS].Bayan Imam Mahdi[AF] ya bayyana za a fafata ya}i sosai a duniya,domin ba da bayyanarsa ne komi zai koma dai-dai,a’a sai an fafata ya}i an kauda zalunci da kuma azzalumai da kuma masu ~arna a bayan }asa a lokacin, kamar Sufyani da Dajjal da dai sauransu,bayan kauda su adalci zai shinfi]u a duniya baki ]aya,haka nan ni’imomi da albarkoki zasu mamaye duniya,kowa zai zama mawadaci ya ma zo akan cewa mutum zai fitar da zakka a lokacin ya kasance ba wanda za a ba,saboda kowa ya wadata.Kuma za a samu aminci a bayan }asa ba wai ga mutane kawai ba,a’a hatta a tsakankanin dabbobi sai an samu amincin,alal misali yazo cewa saboda gayar aminci zaki da akuya za su iya kiwo a waje guda ba da ya yi ma ta wani abu ba.Haka nan addini zai dawo kamar yadda yake a lokacin Manzon Allah[S].Kuma iko da mulki na Imam Mahdi[AS] a lokacin zai kasance a duniya ne dukkanta wato ba wani sashe na ta ba.Sai dai a lura nan ba a nufin kowa zai zama musulmi bane ko mabiyin Ahlul bayt,abun da ake nufi shine kowa dole ya zauna }ar}ashin musulunci da kuma fahimta ta Ahlul bayt.Domin wasiyyar nan da Manzon Allah[S] yayi a Ghadir kum, wanda wasu suka shiga tsakani na tabbatuwar ta a aikace to itace za ta tabbata a lokacin Imam Mahdi[AS],saboda haka a lokacin mutum ko ya}i ko ya so dole ya zauna a }ar}ashin fahimta ta Ahlul bayt.Akwai ma wani bayani da wani Arifi daga cikin arifai na Ahlus sunna ya yi akan cewa,idan Imam Mahdi ya bayyana zai gusar da duk sa~ani da kuma ra’ayoyi a bayan }asa wato na mazhabobi.Zai dawo da addini tsantsa,kuma wasu sashen musulmi na zamaninsa za su yi }iyayya da shi a ~oye,kasantuwar yadda suka ga yana tafiya sa~anin yadda limaman mazhabobinsu suka tafi akai,saboda I’iti}adin da suke da shi na cewa Allah Ta’ala ba zai samar da wani da ya fi limaman mazhabobinsu ilimi ba.Sai dai zasu yi ma Mahdi biyayya dole saboda tsoron ikonsa da kuma kwa]ayin abin da ke gare shi na dukiya.Ya ci gaba da bayani cewa zai dawo da Musulunci kamar yadda yake a lokacin Manzon Allah.Idan mutum na son yaga wannan bayani ya duba cikin littafin Kashful gumma,ya duba a mu}addimar littafin,kuma shi wannan Arifi mai suna Shaikh Sha’araniy ya rayu ne a }arni na goma.Tsawon zamanin da Imam Mahdi[AS] zai yi yana mulki akwai ruwayoyi dabam-dabam akai,wata ruwayar tace zai yi shekara 7 ne,wata ruwayar shekara 20,a wata 30.a wata 40 kai akwai ma wata ruwayar da tace zai yi shekaru 309 ne.Akwai ma ruwayar da tazo akan cewa zai yi mulki har ya zuwa yadda Allah yaso.Bayan wannan mulki na duniya baki ]aya da Imam Mahdi[AS] zai yi daga }arshe zai yi shahada ne wato za a kashe shine,domin imamai baki ]ayansu Shahidai ne kamar yadda yazo a hadisi daga Imam Hassan[AS] .kuma rayuwa zata kasance ba da]i a bayansa kamar yadda haka yazo a hadisi. Daga }arshe babban abun da ya hau kanmu a wannan zamani na gaiba,kuma zamani na gab da bayyanar Imam Mahdi[AS]shine ko wannenmu yayi ma kansa muhasaba wato hisabi ya zauna ya tambayi kansa yaya dangartakarsa take da Imam Mahdi[AF] dangantaka ce kyakkywa kuma mai }arfi? ko ko akasin haka!Saannan kuma yayi tunani akan cewa ya yake wajen Imam Mahdi[AS] ya kuma Imam Mahdi[AS] yake a wajensa?Haka nan kuma ya ya ala}arsa take da Imam Mahdi[AS] a zahirance da kuma a ba]inance? Irin wannan muhasaba yana da kyau mutum ya dunga yi ma kansa lokaci bayan lokaci,domin yin haka zai taimaka ma mutum wajen kyautata dangartakarsa da Imam Mahdi[AF].Bayan haka kuma kamar yadda muke da I’iti}adin cewa ayyukan da muke aikatawa ana kai su ga Imam Mahdi[AS]kasantuwar shine Imamin wannan zamani.To mutum ya dunga tunanin ayyukan da yake aikatawa ayyuka ne wa]anda idan an kai masa zai yi farin ciki da su,ko kuma ayyukane da zai yi ba}in ciki da su.Domin yadda mutum yake wajen Imam Mahdi[AS] ya danganta ne ga irin ayyukansa da ake kai masa.Ayatullahi Bahjati yana cewa mutum yafi damuwa da kyautata dangartakarsa da Imam Mahdi[AS] fiye da tunanin bayyanarsa,yace domin bayyanarsa a hannun Allah Ta’ala yake,amma kyautata dangantaka da shi a hannun mutum yake.Haka nan kuma a wani waje Ayatullahi Bahjati yana cewa ka da ya kasance muna addu’ar cewa Allah ya gaggauta bayyanar Mahdi amma kuma muna jirkintar da zuwansa da ayyukanmu,akwai zantuka masu yawa da Ayatullahi Bahjati yayi dangane da Imam Mahdi[AS] ga mai bu}atar ganin irin wa]annan zantuka yana iya duba littafi na tarihinsa mai suna Uswatul-Arifin.Wannan ke nan baki ]aya a ta}aice sai kuma shekara mai zuwa a watan Shaaban insha-Allah za a yi bayani ga wani maudu’i da yake da ala}a da Imam Mahdi[AF].
|