Munasabobin watan Sha’aban. |
Written by administrator | |||
Thursday, 05 June 2014 03:31 | |||
Watan Shaaban shine wata na takwas a jerin lissafi na watannin musulunci 12.Haka nan kuma yana da munasabobi dabam dabam.Watan Shaaban yana da khususiyya na cewa dukkan munasabobin da ke ciki na wiladar[Haihuwar] Ma’asumin ne ba na wafatinsu ba.Wato babu wani daga cikin Imaman Ahlul-baiti wanda ruwaya ta zo da rasuwar sa cikin watan.Ruwayoyin da suka zo sune na wiladar Imam Husain[AS]Imam Sajjad[AS]Imam Mahdi[AF].Wato dai wannan wata na Shaaban akasin watan Muharram ne wanda shi ma yake da khususiyyar cewa babu wani daga cikin Ma’asumin da wiladarsa ta zo a cikin watan.Ruwayoyin da suka zo sune na shahadar Imam Husain[AS]da kuma Imam Sajjad[AS]. Watan Shaaban wata ne na Manzon Allah[S]kamar yadda yazo a ruwayoyi na hadisai,saboda haka wata ne da ke da falaloli masu yawa.Ga wasu daga cikin falalolin wannan wata.An samo daga Imam Ali[AS] cewa Manzon Allah[S]yace:Shaaban wata na ne,duk wanda ya azumci wata na,zan kasance mai cetonsa ranar }iyama.” Haka nan a wani hadisi Manzon Allah[S] yace, “Shaaban wata na ne,duk wanda ya azumci rana guda daga cikin wata na,to Aljanna ta tabbata gare shi.”An samo daga Imam Sadik[AS]yace,Manzon Allah[S] ya kasance idan watan Shaaban ya kama,ya kan sa a yi sanarwa cikin Madina,da cewa:Shaaban wata na ne,Allah ya yi rahama ga wanda ya taimake ni cikinsa.[Taimakon sa a nan shine ta hanyar yin ibadodi dabam-dabam a cikin watan]Yazo a hadisi cewa tun da Imam Ali[AS] yaji wannan sanarwa bai ta~a fashin azumin watan Shaaban ba,yace kuma in har yana duniya to duk watan shaaban idan ya zagayo sai ya azumce shi dukkansa.Kuma an tambayi Manzon Allah[S] wane azumi ne yafi falala,sai Manzon Allah yace azumin shaaban.Haka nan a wani hadisi Manzon Allah[S] yace, “Watan Shaaban wata ne mai daraja,kuma wata na ne,mala’iku na girmama shi kuma sun san ha}}insa,kuma wata ne da ake }ara arzikin ba yi a cikinsa saboda watan Ramadan,a ke kuma }awata aljanna,da dai hadisai masu yawa dangane da falalolin wannan watan.Kuma idan mutum ya duba cikin wasu daga cikin littafan hadisai na Ahlus-sunna zai ga cewa sun tabbatar da cewa Manzon Allah ya kasance yana azumtar watan Shaaban baki ]ayansa. Sai kuma abun da ya shafi munasabobi na wannan watan.A ranar Alhamis 3 ga watan Shaaban shekara ta hu]u bayan hijira aka haifi Imam Husain[AS]Bayan da aka haifi Imam Husain[AS]aka je aka shaida ma Manzon Allah[S] ya zo wannan gida mai albarka yana murna da farin ciki.Yace ma Asma’u ‘yar Umais ta mi}o masa shi.Manzan Allah ya kar~e shi ya rungume shi ya yi masa kiran sallah a kunnensa na dama,saannan yayi masa i}ama a kunnen sa na hagu,sai ya aza shi a cinyarsa mai albarka ya yi kuka.Sai ita Asma’u ‘yar Umais ta ce: “Babana da Mamana su kasance fansa gareka ya Manzon Allah,wannan kukan fa?”Sai Manzon Allah yace mata:Ina kuka ne saboda abin da zai same shi a bayana,wa]ansu jama’a azzalumai za su kashe shi a bayana,ba za su samu cetona ba.”Bayan haka sai Manzon Allah[S] yace ma Imam Ali[AS] ka sa masa suna.Sai yace ban kasance zan rigaka ba wajen sa masa suna.Sai Manzon Allah[S] yace ka sa masa suna Husain.Haka nan a rana ta bakwai da haihuwa,Manzon Allah[S] da yaje wannan gida mai albarka,ya ]auki Imam Husain sai aka ga yayi kuka shigen yadda yayi a rana ta farko.Da aka tambaye shi kan kukan sai ya ba da amsa kamar yadda ya bayar a rana ta farko.Daga cikin abin da Imam Husain ya ke~anta da shi,shine bai ta~a shan mama[nono]na wata mace ba ko kuma na Sayyida Fatima[AS],kamar yadda Kulaini ya ruwaito a cikin littafin Kafi,juz’i na 1 shafi na 386 wato babin da yake Magana kan wiladar Imam Husain[AS].An samo daga Imam Sadik[AS] yace: “Imam Husain bai sha mama na wata mata ko kuma na Fatima ba.Ya kasance akan kawo shi wajen Manzon Allah[S] ya sa babban yatsansa a cikin bakin sa,sai ya tsotsa daga gareshi.Hakan ya kan isheshi kwana biyu,kwana ukku.Nan kuma wasu sassa ne na rayuwar Imam Husain[AS].1-Haihuwarsa:An haife shi a madina 3 ga watan Shaaban.2-Shekarunsa:Imam Husain[AS] ya rayu a duniya shekaru 57 ne.3-Muddan Imamancinsa:Shekaru goma ne.3-‘Ya’yansa:Imam Husain[AS] ya kasance yana da ‘ya’ya bakwai maza4 mata 3.Mazan sune,Imam Zainul-Abidin,Aliyyul Akbar,Jaafar da kuma Abdulla,Aliyyul Akbar da Abdullah sun yi shahada a karbala,ya Aba Abdullah da ake yi masa kinaya da shi ana nufin wannan Abdullah.Matan sune,Sukaina,Fatima da kuma Ru}ayya.4-Shahadarsa:Yayi shahada a ranar jumma’a a wata ruwaya ranar asabar 10 ga watan Muharram shekara ta 61 bayan hijira.Kuma yazo a ruwayoyi na hadisai cewa a ranar da yayi shahada ne Imam Mahdi[AF] zai bayyana wato a ranar asabar ko jumma’a 10 ga muharram a shekarar da Allah ta’ala shine masani a kai.5-{abarinsa:Yana a karbala ne tare da wa]anda suka yi shahada tare da shi. 1-Haihuwarsa:An haifi Abul-Fadhal Abbas a Madina,ranar 4 ga watan Shaaban,shekara ta 26 bayan hijira.A cikin ‘ya’yan Imam Ali[AS] maza, to baya ga Imam Hassan da Imam Husain to ba wanda ya kai shi daraja.Kuma Abul Fadhal Abbas tanadi ne na musamman da Imam Ali[AS] ya yi ma Imam Husain[AS] domin wa}i’ar Karbala.2-Nasabarsa:Sunan mahaifiyarsa Fa]ima ‘yar Hizam,idan mutum ya bibiyi tarihinta zai ga cewa baiwar Allah ce mai gayar biyayya da kuma girmamawa ga Ahlul baiti,alal misali lokacin da tazo gidan Imam Ali wato bayan auransu tace tana son idan Imam Ali zai kirata,ka da ya kirata da sunanta wato Fatima, saboda girmamawa ga Sayyida Fa]ima kuma ka da haka ya dun ga sosa ran su Imam Hassan,Imam Husain,Zainab wato saboda tunawa da mahaifiyarsu.To a lokacin shine Imam Ali yake ce mata Ummu banin,domin daga baya ta haifi ‘ya’ya maza guda hu]u.Wannan kuma in muka duba zamu ga cewa wata karama ce daga cikin karamomin Imam Ali[AS].Haka nan kuma wa]annan ‘ya’ya na ta tayi masu kashedi da cewa kada wani daga cikinsu ta ji ya kira sunan Imam Hassan da Husain sai dai su ce shugaba na.kuma dukkansu wadannan ‘ya’ya na ta sun yi shahada ne a wa}i’ar Karbala.Ga sunayen ‘ya’yan nata da kuma shekarun da ko wannensu yayi a duniya:Sayyid Abbas 34,Abdullah 25,Usman 21 sai kuma Ja’afar 19.Kuma dukkan wa]annan ‘ya’ya na ta sun yi shahada ne a karbala.Lokacin da labari yazo madina dangane da abubuwan da suka faru a karbala,abin da ya damu ummul banin shine Imam Husain,domin wanda yazo da maganar tana tambayarsa dangane da mi ya samu Husain sai yake ce mata an kashe maki ]anki wane da wane,tace Husaini fa sai yace shima an kashe shi jin haka sai ta fashe da kuka.3- La}ubbansa:Sayyid Abul Abbas yana da la}ubba masu yawa.Ana ce masa {amaru bani Hashim wato saboda gayar ken halitta da Allah ya yi masa.Ana kuma ce masa babul-Hawa’ij wato saboda duk wanda ya yi tawassuli da shi tare da iklasi ga ko wace bu}ata tasa to Allah ta’ala zai biya masa bu}atarsa.Ana kuma ce masa Hamilu-liwa’i domin a ranar Ashura shine Imam Husain ya ba tuta.4-Nash’a]insa:Sayyid Abul-Fadhal Abbas ya tashi a madina,ya kuma rayu tare da mahaifinsa shekaru 14,tare kuma da Imam Hassan[AS]shekara 24,tare kuma da Imam Husain[AS] shekaru 34.Abul Fadhal Abbas ya kasance ko da wane lokaci yana tare da Imam Husain[AS]5-Shekarunsa:Ya rayu a duniya shekaru 34 ne.6-‘Ya’yansa:Yana da yara biyu maza sune Fadhal da kuma {asim,wato shi yasa ake yi masa kinaya da Abul Fadhal.[an sa {asim yayi shahada ne a karbala.7-Wafatinsa:Yayi shahada ne ranar 10 ga watan muharram shekara ta 61 bayan hijira.8-{abarinsa: yana a karbala ne wato kusa da na Imam Husain[AS]. 1-Haihuwarsa:An haifi Imam Zainul Abidin a madina ranar jumma’a 5 ga watan shaaban shekara ta 38 bayan hijira.2-Nasabarsa:Sunan mahaifiyarsa Maryam a wata ruwaya Fa]ima,asalinta ba farisa ce wato mutuniyar Iran,kuma ita ]iya ce ga sarkin Iran na lokacin mai suna Yazdajir,.kafin zuwansu madina ta yi mafarki da Manzon Allah[S] da kuma Sayyida Zahra[AS].3-Nash’a]insa:Imam Zainul Abidin ya tashi a madina,bayan haihuwarsa Allah ta’ala ya yi ma mahaifiyarsa rasuwa kuma shi ka]ai ne a wajen mahaifiyarsa.ya rayu tare da kakansa Imam Ali shekara biyu,tare kuma da Amminsa Imam Hasan shekaru 12,tare kuma da mahaifinsa Imam Husain shekaru 23.Ya kuma rayu bayan shahadar mahaifinsa shekaru 34 ne.4-Shekarunsa:Imam Zainul Abidin[AS]ya rayu a duniya shekaru 57 ne.5-La}ubbansa:Imam Zainul Abidin yana da la}ubba masu yawa,amma la}ubbansa da suka fi fice sune Sajjad wato saboda yawan sujudarsa.Zainul Abidin wato saboda yawan ibadarsa.kuma ana yi masa kinaya da Abu Muhammad.6-Muddan Imamancinsa:Shekaru 34 ne.7-‘Ya’yansa:Imam Zainul Abidin ya kasance yana da ‘ya’ya 15 maza 11,mata hu]u.8-Wafatinsa:Ya rasu ranar 25 ga watan muharram shekara ta 95 bayan hijira.9-{abarinsa:Yana a madina ne wato a ma}abartar Ba}i’a. 1-Haihuwarsa:An haifi Imam Mahdi[AF] a garin samarra wato a Irak ranar Jumma’a 15 ga watan Shaaban shekara ta 255 bayan hijira.2-Nasabarsa:Sunan mahaifiyarsa Narjis,nasabarta na tu}ewa ne ga wasiyyin Annabi Isa wato Sham’un.Sunan mahaifinsa Imam Hasan Al-askari[AS].3- Nash’a]insa:Imam Mahdi ya rayu tare da mahaifinsa shekaru biyar,bayan rasuwar mahaifinsa ya shiga gaiba }arama ana ce mata gaiba ta farko,tsawon shekarun wannan gaiba ta farko shine shekaru 69.Bayan haka kuma ya shiga gaiba babba ana ce mata gaiba ta biyu.Tambaya anan minene banbanci tsakanin gaibar farko da ta biyu?Banbancin shine a ta farko akwai wasu bayin Allah ko jakadu guda hu]u da yake da ala}a da su,wa]anda ta hanyarsu yake ba da umarni ko hani zuwa ga shi’arsa ko kuma su idan suna da tambayoyi ko wasu matsaloli su kan gabatar ta hanyar wa]annan jakadu,sai dai nan a lura wa]annan jakadu ba sun kasance a lokaci guda bane a’a sun kasance ne ]aya bayan ]aya.To a gaiba ta biyu babu wa]annan jakadu sai abun da ake ce ma nuwwab amma wa]ancan kuma nuwwab khassa.4- La}ubbansa:Yana da la}ubba masu yawa daga cikin su akwaiAl- Mahdi,Al-{a’im,A-Muntazar,Sahibuz Zaman.Haka nan ana yi masa kinaya da Abul-{asim.5-Shekarunsa:A yanzu Imam Mahdi[AS] yana da shekara dubu ]aya da ]ari ]aya da tamanin wato 1180 a duniya,saboda haka a wannan al’umma ta Manzon Allah ba wanda ya kai shi yawan shekaru.Ta yiyu wani ya tambaya cewa mutum zai iya tsawon rai haka?Amsa na’am.Idan mutum ya duba tarihin wasu Annabawa da ma wa]anda ba Annabawa ba zai ga haka,misali Annabi Nuhu[AS]ya yi shekaru 2500 a duniya,ya shekara 850 gabanin aiko masa da sa}o,ya shekara 950 wajen isar da sa}o,ya kuma shekara 700 bayan halakar da mutanensa.Annabi Adam shi kuma ya shekara 930 a duniya,Annabi Idris 965,Annabi Hudu 962.Saboda haka wannan tsawon rai na Imam Mahdi ba wani ba}on abu bane a tarihin ]an Adam.Kai ko da ma ba a samu a cikin tarihi wani yayi tsawon rai irin haka ba,hujjar cewa Allah Ta’ala mai iko ne akan kome ya wadatar. Kasantuwar wannan wata na shaaban ne aka haifi malaminmu kuma jagoranmu a wannan gwagwarmaya ta tabbatar da addini,ga wasu sassa na rayuwarsa mai albarka.1-Haihuwarsa:An haifi Sayyid Zakzaky[H] ne a birnin Zariya ranar Talata 15 ga watan Shaaban shekara ta 1372 bayan hijira wanda ya dai dai da 5 ga watan May 1953 miladiyya.2-Nasabarsa:Sunan mahaifinsa Yaaqoub shi kuma ]an Aliyu ]an Tajuddin ]an limam Husain.Shi liman Husain wani malamine kuma bawan Allah da ya fito daga Mali yazo garin Sokoto a lokacin Shehu Usman ]an Fodiyo.Sunan mahaifiyarsa Hajiya Salihatu.3-Nash’a]insa:Sayyid Zakzaky[H]ya tashi a garin Zariya kuma ya taso mai ri}o da son addini,kuma ya kasance mai haza}a da basira tun tasowarsa, Yayi karatu a wajen malamai dabam-dabam a zariya da kano.3-La}ubbansa:Akwai Al-Zakzaky wanda yake nufin mutumin zazzau.Akwai kuma la}ubba da Shehu Usman ya ambace shi da shi misali Sharafud-din da kuma Ibrahimul Magribiy.4-Shekarunsa:Yanzu yana da shekaru 63 a duniya.5-‘Ya’yansa:Yana da ‘ya’ya 9 maza 7 mata biyu.6-Muddan da’awarsa:A yanzu haka Sayyid Zakzaky ya kwashe kusan shekaru 40 yana wannan kira domin tabbatar da addini a wannan }asa. Sai kuma abun da ya shafi ayyuka na ibadodi da ake son aikatawa cikin wannan wata na Shaaban.Ayyukan sun kasu kashi biyu,akwai ayyuka na amma wato sune ayyuka na ibadodi da ake son aikatawa a ko wace rana cikin watan Shaaban,akwai kuma ayyuka na khassa wato sune ayyukan da ake son aikatawa a wasu ranaku ko darare na cikin watan Shaaban,wannan ke nan a dun}ule amma a warware mutum na iya duba littafin mafatihul jinan ko Dhiya’us salihin da sauransu.Wani tambihi anan shine wannan wata da muka ciki na Shaaban wata ne na shiri da kuma yin shimfi]a ga babban ba}o da yake tafe wato watan Ramadan.Wato dai kamar yadda yake bisa al-ada in zaka yi babban ba}o to zaka yi shirya-shirye na zuwansa.To haka ya kamata mutum yayi kafin zuwan watan Ramadan ya kasance ya shirya kansa ta hanyar tazkiyyar naf’s ]insa wato tsarkake kansa zahiri da ba]ini,da kuma horas da kansa ga ayyuka na ibadodi dabam-dabam ta yadda jikinsa zai saba kafin shigar watan Ramadan,wato domin ya kasance mutum ya samu sau}in raya dararensa da kuma ranekunsa da ibadodi,haka nan kuma domin ya samu zau}i da halawar watan Ramadan.
|