Saturday, 02 December 2023
Email
Make My Homepage
RSS
Register
Munasabobin watan Rajab. Print E-mail
Written by administrator   
Friday, 02 May 2014 07:25

 Watan Rajab shine wata na bakwai a jerin }idaya na watannin musulunci 12.Kuma wata ne da yake da munasabobi masu yawa a cikinsa,idan mutum yayi bincike zai ga babu wani wata da yake da munasabobi masu yawa kamar watan Rajab,wato dai kamar yadda babu wani wata da yake da ayyuka na ibadodi kamar watan Ramadan.Haka nan kuma akwai ayyuka na ibadodi masu yawa da suka zo a cikin watan,ayyuka na ibadodi da suka zo cikin watan Rajab sun kasu kashi biyu akwai ayyuka na Amma wato wa]anda ake son aikata su tun daga farkon watan har zuwa }arshen sa.Akwai kuma ayyuka na khassa wato ayyukan da ake aikatawa a muhimman darare ko ranaku na watan misali daren farko da kuma ranar farko na watan,ko kuma daren 15 da kuma ranar 15 ga watan ko kuma daren 27 da kuma ranar 27 ga watan.Ga mai bu}atar ganin wa]annan ayyuka na Amma da khassa na watan Rajab yana iya duba mafatihul jinan babi na biyu fasali na ]aya.Har wala-yau akwai falaloli da darajoji da suka zo a ruwayoyi na hadisai dangane da watan,haka nan kuma watan Rajab yana daga cikin watanni guda 4 masu daraja wanda aka hana zaluntar kai a ciki,saboda haka yana da gayar muhimmanci mutum yaga cewa bai zalunci kansa ba a cikin wannan wata na Rajab ta hanyar aikata zunubi ko kuma rashin aikata ayyuka na ]a’a da ibadodi.                                           

1-      Munasabobin watan Rajab 

1-      Haihuwar  Imam Muhammad al-Ba}ir[AS] 1 Ga Watan Rajab.

2-      Shahadar Imam Ali al-Hadi[AS]   3 Ga Watan Rajab.

3-      Haihuwar Imam Muhammad al-Jawad  10 Ga Watan Rajab

4-      Haihuwar Imam Ali ibn Abi Talib  13 Ga Watan Rajab.

5-      Wafatin Sayyida Zainab[AS] 15 Ga Watan Rajab

6-      Shahadar Imam musa al-Kazim  25 Ga Watan Rajab.

7-      Wafatin Sayyidina Abu Talib 26 Ga watan Rajab,shekara 10 bayan aiko Manzon Allah[S]

8-      Wafatin Ummul Muminin Khadija 29 Ga watan Rajab,shekara 10bayan aiko Manzo Allah.

9-      Yaumul-Mab’as[ranar da aka aiko Manzon Allah SAAW da sa}o] 27 Ga Watan Rajab.

Wani tambihi anan shine tsakanin rasuwar Abu [alib da Sayyida Khadija kwana 3 ne,a wata ruwaya kwana 35.

Wa]annan sune wasu daga cikin muhimmam munasabobi da suka auku a watan Rajab. A yanzu Insha-Allah za a ]an yi bayani a kan ko wace munasaba amma a ta}aice.

1-      Haihuwar Imam Muhammad al-Ba}ir[AS] An haife shi a Madina,ranar Jumma’a 1 ga watan Rajab  shekara ta 57 bayan Hijira.Kuma shine Imam na biyar a jerin }idaya na Imamai 12.

2-      Nasabarsa:Sunan Mahaifiyarsa Fa]ima ‘yar Imam Hassan,yazo a kan cewa shine ka]ai ya ha]a irin wannan nasaba,wato cewa Mahaifinsa shine Imam Sajjad ]an Imam Husain[AS] mahaifiyarsa kuma Fadima ‘yar Imam Hassan[AS].

3-      Nash’a ]insa:Imam Ba}ir ya tashi a Madina,gaban mahaifinsa da kuma kakansa,ya rayu tare da kakansa Imam Husain[AS] shekara 4.Saboda haka wa}i’ar karbala tare dashi akayi wato lokacin yana da shekara 4 a duniya.Ya kuma rayu tare da mahaifinsa shekara 25.

4-      La}ubbansa da Kinayarsa:Imam Ba}ir yana da la}ubba masu yawa,amma wa]anda suka fi fice sune Al-Ba}ir da kuma “SHABIH”ana ce masa haka ne saboda yayi kama da Manzon Allah[SAAW] so sai.Ana kuma yi masa kinaya da Abu Ja’afar.

5-      Shekarunsa:Imam Ba}ir[AS] ya rayu a duniya shekaru 57.

6-      Muddan Imamancinsa:Shekaru 19.

7-      ‘ya’yansa:Imam Bakir[AS] yana da ‘ya’ya bakwai,maza biyar,mata biyu.

8-      Wafatinsa:Ya rasu ranar litinin 7 ga watan Zul-hijja shekara ta 114 bayan Hijira.

9-      {abarinsa:}abarinsa yana Madina ne wato a Ba}i’a.

Shahadar  Imam Ali al-Hadi[AS]

1-      Wiladarsa:Imam Ali al-Hadi[AS]shine Imam na goma a jerin }idaya na Imamai 12.An haife shi a wani gari kusa da Madina a  na ce masa Sarya,a ran 15 ga watan Zul-hijja.shekara ta 212 bayan Hijira.

2-      Nasabarsa:Sunan mahaifiyarsa Sumanatu,amma an fi saninta da Sayyida,kuma ana yi mata kinaya da Ummul-Fadhal.kuma yazo a tarihinta cewa ta kasance mai yawan ibada,musamman ma ta ~angaren azumi.kuma ta kasance mai ta}awa da kuma zuhudu wato gudun duniya.Sunan mahaifinsa Imam Jawad[AS]

3-      Nash’a ]insa:Imam Ali al-Hadi[AS]ya tashi a madina,ya rayu a cikinta shekaru 22,ya kuma rayu tare da mahaifinsa shekara 8.{arshen rayuwarsa ta kasance a Ira} ne,domin ya zauna a cikinta shekaru 20.

4-      La}ubbansa da kinayarsa:Imam Ali al-Hadi[AS] ya kasance yana da la}ubba masu yawa,amma wa]annan biyun su suka fi fice.wato Al-Hadi da kuma Anna}iy.Haka nan anai masa kinaya da Abul-Hassanus-salis.

5-      Shekarunsa:Ya rayu a duniya shekaru 42.

6-      Muddan Imamancinsa:shekaru 33,a wata ruwaya 34.

7-      ‘ya’yansa:Yana da ‘ya’ya 5,maza 4.mace 1.

8-      Wafatinsa:Ya rasu ranar litinin 3 ga watan Rajab shekara ta 254 bayan hijira,ya rasu ne sakamakon guba da khalifan Abbasawa mai suna Mu’utazz yasa masa.

9-      {abarinsa:}abarinsa yana samarra,a }asar Ira} kusa dashi akwai }abarin ]ansa Imam Hassan al-askari[AS].

Haihuwar Imam Muhammad Al-Jawad[AS]

1-      Wiladarsa:An haifi Imam Jawad[AS] a madina,ranar 10 ga watanRajab shekara ta 195 bayan hijira.Kuma shine Imam na 9 a jerin }idaya na Imamai 12.

2-      Nasabarsa:Sunan mahaifiyarsa Sabika.sunan mahaifinsa Imam Ali- Arrida[AS]

3-      Nash’a ]insa:Ya tashi a madina,ya rayu tare da mahaifinsa shekara 18.Amma }arshen rayuwarsa ta kasance a Ira} ne.

4-      La}ubbansa da kuma kinayarsa:Yana da la}ubba masu yawa,amma wa]anda suka fi fice sune Al-Jawwad da kuma Atta}iy.Kuma anai masa kinaya da Abu Ja’afarus-sani.kuma yazo akan cewa Imam Ridha[AS] saboda Ta’aziminsa bai ambatonsa da sunansa sai dai da wannan kinaya ta Abu Ja’afar.

5-      Shekarunsa:Ya rayu a duniya shekaru 25.Wato shine mafi}arancin shekaru idan an kwatanta da Imaman da suka gabace shi da kuma wa]anda suka biyo bayansa.Kamar yadda Imam Sadi}[AS] shine mafi yawan shekaru,a cikin Aimma[AS] domin ya rasu yana da shekaru 65,a wata ruwaya 68.

6-      Muddan Imamancinsa:Shekaru 17 ne.

7-      ‘Ya’yansa:Yana da ‘ya’ya 4.maza biyu,mata biyu.

8-      Wafatinsa:Imam Jawad[AS] ya rasu ranar Asabar }arshen watan Zul-}ida,shekara ta 220 bayan Hijira.kuma ya rasu sakamakon guba da khalifan Abbasawa mai suna Mu’utasim yasa asa masa.wato kamar yadda aka sa guba ga Imaman da suka gabace shi da kuma wa]anda suka biyo bayansa,in ka ]ebe Imam Ali[AS] da kuma Imam Husain[AS] su da takobi ne aka aka kashe su.kamar dai yadda yazo daga Imam Sadik[AS] yace, “Babu wani daga cikinmu face wanda aka kashe da takobi ko aka sa mai guba.”

9-      Kabarinsa:}abarinsa yana a kazimiyyane wato a Ira}, kusa dana kakansa Imam Kazim[AS].

Haihuwar Imam Ali[AS]

1-      Wiladarsa:An haifi Imam Ali[AS] ranar Jumma’a 13 ga watan Rajab.wato bayan haihuwar Manzon Allah[SAAW] da shekaru 30.An haife shi a makka kuma a cikin ka’aba,wanda wannan wata khususiyyace ta Imam Ali[AS]domin ba’a ta~a haihuwar wani a cikin ka’aba in bashi ba.

2-      Nasabarsa:Sunan mahaifiyarsa Fa]ima ‘yar Asad,kuma ta rayu har zuwa lokacin da Manzon Allah[SAAW] yayi Hijira zuwa Madina,saboda haka da ita akayi wannan hijirar,Imam Ali nema ya jagoranci hijirar tasu.Sunan mahaifinsa Abdu Manaf,anai masa kinaya da Abu [alib,da yake shine babban ]ansa namiji,bayan shi sai A}il,sai Ja’afar,sai Imam Ali wato shine ]an autansu,kuma Ja’afar ]an Abu  [alib shine farkon shahidi a cikin Bani Hashim.

3-      Nash’a ]insa:Imam Ali[AS] ya tashi a makka,kuma a gidan Manzon Allah[SAAW] ya rayu tare da mahaifinsa kusan shekaru 20.Ya kuma rayu tare da Manzon Allah[SAAW] shekaru 33.}arshen rayuwarsa kuma yayi a kufa ne.

4-      La}ubbansa da Kinayarsa:Yana da la}ubba masu yawa,amma wa]anda suka fi shahara sune,Amiril-Mu’uminin,Murtadha, Haidar,Wasiyyi da dai sauransu.Haka nan kinayoyinsa suma suna da yawa,wa]anda suka fi fice sune,Abu-Turab,Abul-Hassan, Abu-sib-]ain.

5-      Shekarunsa:Ya rayu shekaru 63 a duniya.

6-      Muddan Imamancinsa:Shekaru 33.

7-      ‘Ya’yansa:Yana da ‘ya’ya 25,maza 11,mata 14.

8-      Wafatinsa:Yayi shahada 21 ga watan Ramadan shekara ta 40 bayan Hijira.

9-      {abarinsa:}abarinsa yana Birnin Najaf ne,wato a Ira}.

Sayyida Zainab[AS]

1-      Wiladarta:An haifi Sayyida Zainab[AS] a Madina 5 ga watan Jimadal ula,shekara ta biyar bayan Hijira.

2-      Nasabarta:Sunan mahaifinta Imam Ali[AS] mahaifiyarta kuma Sayyida Fatima[AS] kuma itace ta ukku,a wajen mahaifanta.wato baya ga Imam Hassan[AS]da kuma Imam Husain[AS]sai ita,bayanta kuma Ummu-khul-sum,sai kuma Muhusin.

3-      Nash’a ]inta:Ta rayu tare da mahaifiyarta da kuma kakanta wato Manzon Allah[SAAW] kusan shekaru shidda.Tare kuma da mahaifinta shekaru 35,tare kuma da Imam Hassan[AS]shekaru 45,tare kuma da Imam Husain[AS]shekaru 55.

4-      ‘ya’yanta:Sayyida Zainab[AS]tana da ‘ya’ya guda biyar-maza 4,mace 1,sune Ali,Aun,Muhammad,Abbas da kuma Ummu-khul-sum.Biyu daga cikin ‘ya’yanta sun yi shahada a karbala sune Muhammad da kuma Aun.sai kuma mijin ‘yarta mai suna {asim ]an Muhammad ]an Ja’afar,shima a karbala yayi shahada.

5-      Shekarunta:Sayyida Zainab[AS]ta rayu kusan shekaru 60 a duniya.

6-      Wafatinta:Sayyida Zainab[AS] ta rasu ranar lahadi 15 ga watan Rajab,shekara ta 62 bayan Hijira,a wata ruwaya 65.

7-      {abarinta:Akwai sa~ani tsakanin malaman tarihi,na ainihin inda }abarinta yake,akwai zantuka ukku,wa]ansu sunce a Misra,wasu kuma suka ce a Madina,wasu kuma suka ce a sham,wannan shine wanda mabiya Ahlul-bait suka tafi akai.

Shahadar  Imam kazim[AS]

1-      Wiladarsa:An haifi Imam Kazim[AS] a wani gari da ake ce masa Abwa,yana tsakanin Makka da Madina ne.ranar lahadi 7 ga watan safar,shekara ta 128 bayan Hijira.Kuma shine Imam na bakwai a jerin }idaya na Imamai 12.

2-      Nasabarsa:sunan mahaifiyarsa Hamida,yazo a tarihinta cewa a fagen ilimi ta kai mustawa-aliya,har  ta kai Imam Sadi}[AS] yakan umarci mataye dasu koma wajenta dangane da hukunce-hukuncen addini.Akwai ma lokacin da yake cewa Hamida tsarkakkiya ce daga dukkan aibobi.sunan mahaifinsa Imam Sadik[AS].

3-      La}ubbansa da kuma kinayarsa:Ya kasance yana da la}ubba masu yawa,amma wa]anda suka fi fice sune Al-kazim da kuma Babul-Hawa’ij.Ana yi masa kinaya daAbu Ibrahim da kuma Abul-Hassan.

4-      Nash’a ]insa:ya tashi a madina,ya kuma rayu tare da mahaifinsa shekaru 20.}arshen rayuwarsa ya kasance a Ira} ne.

5-      Shekarunsa:Y a rayu shekaru 55 a duniya.

6-      Muddan Imamancinsa:shekaru 35.

7-      ‘Ya’yansa:yana da ‘ya’ya 36,maza 17,mata 19.Imam kazim[AS] shine mafi yawan ‘ya’ya idan an kwatanta da Imaman da suka gabace shi da kuma wanda suka zo bayansa.kamar yadda Imam Ridha[AS] da kuma Imam Askari[AS] sune mafi}arancin ‘ya’ya,domin ko wannensu yana da ]a ]aya ne.wato Imam Jawad[AS] da kuma Imam Mahdi[AF]

8-      Wafatinsa:Imam Kazim[AS]ya yasu ranar Jumma’a 25 ga watan Rajab,shekara ta 183 bayan Hijira,kuma ya rasu a kurkune,sakamakon guba da aka saka nasa.

9-      {abarinsa:}abarinsa yana kazimiyya ne a }asar Ira}.Wannan kenan a ta}aice dangane da munasaba ta Wilada ko wafati na Aimma na Ahlul-bait[AS] da suka kasance a watan Rajab.

Haka nan kuma a ranar Alhamis 25 ga watan Rajab  shekara ta 1253 Muhammadu Bello ]an Shehu Usman ]an Fodiyo ya rasu.Ya rasu yana da shekaru 58 a duniya,ya rasu a garin Wurno yanzu haka }abarin sa  ya na Wurne ne.Kuma  yayi shekaru 21 a shugabanci bayan Shehu Usman.

 

 
Home Munasabobi Munasabobin watan Rajab.
Copyright © 2023. www.tambihin.net. Designed by KH