Wannan wata na Jimada Sani shine wata na shida a jerin }idaya na watannin musulunci goma sha-biyu,shima kamar watanni biyu da suka gabace shi baya da munasabobi da kuma ayyuka na ibadodi masu yawa a cikin sa,babban munasabar dake cikin wannan wata shine wilada da kuma wafati na Sayyida Fa]ima[AS].Daga cikin ayyuka na wannan watan akwai wata addu’a da ake son karanta ta a ranar farko na watan ga mai bu}atar ganinta yana iya duba littafin I}bal na Sayyid ibn [awus.Haka nan kuma akwai wata sallah mai raka’a hu]u,ga mai bu}atar ganin sallar da kuma surorin da ake karantawa a cikin ta yana iya duba littafin mafatihul jinan babi na biyu fasali na goma,wannan sallah bata da wani ayyanan nan lokaci na yin ta a cikin watan,saboda haka mutum zai iya yin ta ko da wane lokaci a cikin watan ko da ko ranar }arshe ce ta watan.
A ukku ga wannan wata ne a wata ruwaya wafatin Sayyida Zahra[AS] da yake akwai ruwayoyi dabam-dabam akai.Akan asasin wannan ruwaya ta ukku ga wata ya kasance kenan tsakanin rasuwar Manzon Allah[S] da kuma rasuwar ta kwanaki 95 ne,kuma gab da Manzon Allah[S] zai bar duniya yayi ma Sayyida Zahra[AS] albishir da cewa ita ce farkon wadda zata riske shi daga cikin Ahlul bayt[AS] wato kamar yadda yazo a wani hadisi da Shaikh [usiy ya ruwaito daga Abdullahi ]an Abbas yace:Lokacin da Manzon Allah zai rasu,sai yai kuka wadda har ta kai gemunsa ya ji}e da hawaye,sai aka ce ya Manzon Allah mi yasa kake kuka? Sai Manzon Allah yace ina kuka ne domin zuriyyita da kuma abubuwan da masharratan al-umma ta zasu yi masu a baya na,kamar ina ganin ‘yata Fa]ima an zalunce ta a bayana,tana kira ya babana ba wani wanda zai taimaka mata cikin al-ummata.Sai Fa]ima taji wannan bayani na Manzon Allah sai tai kuka,sai Manzon Allah yace mata kada kiyi kuka yake ‘yata,sai Fa]ima tace ba ina kuka bane saboda abin da za a yi mani a bayan ka bane,ina kuka ne saboda rabuwa da kai ya Manzon Allah,to shine Manzon Allah yace mata ina yi maki al-bishir ya ‘yar Muhammad kece farkon wadda zaki same ni daga cikin Ahlu baitina”.Haka kuma abun ya faru domin idan mutum ya duba tarihi zai ga cewa Sayyida Zahra[AS] itace farkon wadda ta fara rasuwa daga cikin Ahlul bayt[AS]bayan Manzon Allah[S].Sayyida Fadimatu Zahra[AS] ta fuskanci jarabawowi masu yawa bayan rasuwar Manzon Allah[S]akwai ma in da take cewa ta fuskanci musibobi wanda da za a zuba ma ranaku su da sun zama darare.Babbar jarabawar farko da ta fuskanta itace wafatin Manzon Allah[S]idan mutum ya duba tarihin ta zai ga cewa tun bayan da Manzon Allah ya rasu to babu wata rana wadda Sayyida Zahra[AS] bata yi kuka ba saboda tunawa da kuma shau}in ta ga Manzon Allah[S].Jarabawa ta biyu da ta fuskanta itace kai hari gidanta da nufin za a }ona gidan,mu duba irin wannan gida mai albarka wanda yazo akan cewa kusan kullum Manzon Allah yakan je gidan,kai hatta ma idan Manzon Allah yayi tafiya ya dawo kafin ya wuce gidan sa sai yaje gidan Sayyida Fa]ima,amma abun mamaki Mnzon Allah ya bar duniya ko kwana bakwai ba ayi ba da rasuwarsa sai ga wasu daga cikin ‘yan al-ummarsa zasu }ona gidan Inna lillahi-wa inna ilaihi-rajiun,abun mamaki wanda ya jagoranci wannan zuga na }ona wannan gida mai albarka,wani yake ce masa a hanya akwai fa Fa]ima cikin gidan,ba abun da ya fito bakin sa face cewa ko ma waye ke gidan! Ya jama’ar musulmi mu duba fa mu gani wa]anda suka fi kowa daraja a doron }asa baya ga Manzon Allah an je za a }ona su da kuma gidansu,domin da aka zo }ofar gidan ana ta hayaniya akan dole sai Imam Ali ya fito yayi bai’a, in ko ba haka wanda ya jagoranci abun yace a }ona gidan da wa]anda suke ciki.Ana cikin wannan hayaniya sai aka samu wani daga cikin wa]annan maharan ya ta}ar-}are ya tokari }ofar gidan da }afar sa,a lokacin kuma sayyida tana bayan }ofar ne tana Magana da su tana ce masu yanzu baza ku bar mu ba da halin da muke ciki na rasuwar Manzon Allah,to ana cikin haka ne da aka tokaro }ofar sai ya ha]a ta da Katanga kasantuwar tana bayan }ofa, anan ne tayi ~arin cikin Muhsin kuma wani daga cikin }ashin }irjinta ya karye, innalillahi-wa inna ilaihi rajiun,bayan haka aka zo aka tungumi Imam Ali aka fita dashi da nufin za a kai shi wajen wai khalifa akan yayi bai’a,haka sayyida Zahra ta biyo su,tasha gabansu to anan ne suka dunga yi mata bulala akan taba da hanya,kama kama dai har aka isa masallaci, nan ma taje tayi masu Magana da kuma garga]i, bayan haka ta wuce }abarin Manzon Allah tai kuka mai yawa ta shaida ma Manzon Allah ga halin da suke ciki,nan ma cikin masallacin da aka zo da Imam Ali ana ta hayaniya suna ce masa dole yayi bai’a,yace in ban yi bafa suka ce zamu kashe ka.to shine suka kama hannun Imam Ali da nufin su ]ora akan wanda suka za~a khalifa sai Imam Ali ya dun}ule hannunsa sai suka yi }o}arin su bu]e hannun suka kasa,sai shi khalifan ya ]auki hannunsa ya ]ora kan na Imam Ali.To daga nan Malaman Ahlus sunna suka tafi akan wai Ali yayi bai’a ga khalifan da aka za~a.Kuma wani abun lura anan shine Imam Ali ba wai ba zai iya fuskantar wa]annan mutanan bane tun da suka faro wannan abu na kai hari gidansa,abune wanda Manzon Allah tun kafin ya bar duniya ya fa]a masa ga abubuwan da zasu faru amma yace masa ya daure,saboda haka Imam Ali yayi aiki ne da wasiyyar da Manzon Allah yayi masa,wani misali da yake nuna cewa ba wai ba zai iya fuskantar su bane shine lokacin da suka yi nufin tone }abarin Sayyida Fa]ima,ya sawo kayan ya}i da kuma takobin da yake zuwa ya}i da ita yace masu kuzo kuyi ku gani sai suka zuba a guje.Kuma wa]annan abubuwan da suka faru na kai hari gidan Sayyida Fa]ima wani abune wanda bawai kawai littafan shi’a suka kawo ba,a’a har da littafai dabam dabam na Ahlus sunna sun tabbatar da haka saboda haka ba mai inkarin wannan wa}i’a face wanda ta’assubanci ya rufe masa zuciya ko kuma jahili da ya jahilci wannan wa}i’a.Wata jarabawa ta ukku da Sayyida Zahra[AS] ta fuskanta shine na al-amarin gadonta:Aka ce wai bata da gadon mahaifinta abun mamaki har aka kawo mata wani hadisi na cewa Manzon Allah yace Mu Annabawa ba a gadon mu,abun da muka bari sadaka ne.To mutum yaje yayi bincike kan wannan hadisin yabi diddigin isnadin sa zai ga cewa baki ]aya isnadinsa yana tu}ewa ga sahabi guda ]aya ne,wato a cikin sahabbai baki ]aya shi yaji wannan hadisi daga Manzon Allah.wanda wannan abu ko da ban mamaki,to haka dai shi wanda aka za~a a matsayin khalifa ya kafa hujja da wannan hadisi cewa shi yaji haka daga Manzon Allah,shine Sayyida Zahra ta kafa mashi hujjoji da ayoyi na Al-}ur’ani wa]anda suke nuna gadon ‘ya’yan Annabawa ga mahaifansu,duk da haka dai ba a bata gadon ba.Wata jarabawa ta hu]u da ta fuskanta shine al-amarin Fadak:Wannan shima abubuwan da suka faru akansa yana da ban mamaki, a ce mai matsayi ta ko wace fuska kamar Sayyida Zahra tayi Magana a ce ba a yarda ba sai ta kawo shaida,domin ta shaida masu cewa Fadak Manzon Allah[S] tun yana raye ya bata shi, amma suka ce basu yarda da wannan maganar ta ba sai ta kawo shaida, alhali ko daga cikin sunayenta akwai Siddi}a,to sai tace Imam Ali shine shaidanta suka ce basu yarda ba ai mijin tane,tace to ga Hassan da Husain suma shaida ne suka ce ai ‘ya’yan tane,a ta}aice duk shaidun da ta kawo basu amsa ba,saboda haka suka }wace mata Fadak.Haka ya ci gaba da zama a hannun masu iko har ya zuwa zamanin Umar ]an Abdul-Aziz shine ya mai da shi ga jikokin Fa]ima,a lokacin sai ya mi}a shi ga Imam Ba}ir[AS].Wata jarabawa ta biyar da Sayyida Zahra[AS] ta fuskanta akwai tunani da juyayi na irin jarabawa da Imam Ali[AS] zai fuskanta a bayanta,domin gab da zata rasu sai aka ga tana kuka,Imam Ali ya tambaye ta mi yasa take kuka? tace masa tana kuka ne saboda abubuwan da zasu faru dashi a bayanta.A ta}aice dai akwai jarabawowi masu yawan gaske da Sayyida Fa]ima ta fuskanta bayan rasuwar Manzon Allah wa]anda ba za a iya kawo su ba saboda gudun tsawaitawa,alal misali }oce khalifanci daga hannun Imam Ali[AS]wanda idan mutum ya duba tarihi zai ga cewa a lokacin Sayyida Zahra[AS] tayi iya duk abun da zata iyayi na tunasar da sahabbai da kuma dawo da su kan wasiyyar da Manzon Allah yayi a ghadir kum,akan haka ta shiga lungu-lungu sa}o-sa}o na madina tana yi masu Magana abun mamaki wasu ma ce mata suka yi sun manta.Saboda haka daga abubuwan da aka yi ma Sayyida Fa]ima da kuma }wace khalifanci da aka yi mutum zai fahimci sirrin dake cikin hadisin nan da yazo cikin muwa]]a Malik na cewa bayan da aka yi janaizar sahabban da suka yi shahada a ya}in uhudu sai Manzon Allah yace wa]annan sune zan yi ma shaida gobe }iyama,sai Abubakar yace mufa sai Manzon Allah yace ban san mi za kuyi a bayana ba,mai son ganin wannan hadisi ya duba cikin littafin Muwa]]a Malik a kitabul-jihad a fasalin dake Magana kan shuhada’u fi sabilillahi.Kuma ma ko da ace mutum ya jahilci wa]annan abubuwan da suka auku a tarihi,ko kuma ya sani amma saboda ta’assubanci yana ganin kamar ba haka bane to ya tambayi kansa hadisai nawa ya sani na Sayyida Fa]ima ko kuma na ‘ya’yanta,akwai ma wani daga cikin fitattun Malaman Ahlus sunna da yake cewa kwata-kwata hadisan da aka samo daga wajen sayyida Fa]ima ba su wuce goma ba,to saboda Allah mutum ya auna da hankalinsa ace ta rayu da Manzon Allah shekaru kusan 20 amma kuma ace wai hadisai 10 kawai taji daga wajen sa anya? Kuma in mutum ya lura da kyau a zantuka da kuma koyarwa na sashen wasu daga cikin Malaman Ahlus sunna da wuya kaji ambaton Ahlul bayti a bakunan su,wato ke nan za a amshi hadisai daga kowa amma ban da ‘ya’yan Manzon Allah da kuma jikokinsa,saboda haka wannan kawai idan mutum yayi tunani ya isa ya nuna masa cewa lalle wasu abubuwa sun faru ga Ahlu baytin Manzon Allah[SAAW.
Haka kuma a ranar litinin ukku ga watan jimada sani shekara ta 1232 bayan hijira shehu Usman [an fodiyo ya rasu a sokoto.wato rasuwar sa tayi muwafa}a da ranar rasuwar Sayyida Fa]ima[AS].Kamar yadda ]an sa Muhammadu Bello rasuwarsa tayi muwafa}a da ranar shahadar Imam Musa al-kazim[AS] domin Muhammadu Bello ya rasu ne a ranar 25 ga watan Rajab shekara ta 1253.Insha-Allah wani lokaci a munasabar Shehu Usman [an fodiyo na haihuwarsa ko rasuwarsa za a rubutu dangane da tarihinsa da kuma Darussa daga rayuwarsa,nan wasu sassa ne na rayuwarsa a ta}aice.1-Haihuwarsa:An haifi shehu Usman [an fodiyo ranar lahadi }arshen watan safar shekara ta 1168 bayan hijira a wani gari da ake ce masa Maratta,a halin yanzu garin na cikin }asar Nijar ne.2-Nasabarsa:Sunan mahaifinsa Muhammad fodiyo,sunan mahaifiyarsa Hawwa’u.3- Shekarunsa:Shehu Usman ya rayu a duniya shekaru 63 ne.4-Muddan da yayi bayan tabbatar addini:Shehu Usman ya rayu bayan tajdidin addini shekaru 13 da wata bakwai.5- ‘Ya’yansa:yana da ‘ya’ya 17 maza 9 mata 8,amma a wani waje an nuna yana da wasu ‘ya’ya baya ga wa]annan.6-Wafatinsa:Shehu Usman ya rasu ranar litinin 3 ga watan jimada sani shekara ta 1232 bayan hijira.7-{abarinsa:Yana cikin garin sokato.
Ranar 20 ga wannan wata na jimada sani aka haifi Sayyida Fa]imatuz-zahra[AS].Akwai wasu ayyuka na ibadodi da ake son aikatawa a ranar, daga cikin wa]annan ayyuka akwai yin azumi a ranar da kuma yawaita kyaututtuka da sadakoki musamman ga muminai.Haka nan kuma daga cikin ayyukan wannan rana ta wiladar Sayyida Zahra akwai yin ziyara gare ta,ga mai bu}atar ganin wannan ziyara yana iya duba mafatihul jinan babi na ukku fasali na ukku,da dai sauran ayyuka na ibadodi.Nan kuma wasu sassa ne na rayuwar Sayyida Zahra[AS].1-Haihuwarta:An haifi Sayyida Fa]ima[AS]a makka ranar jumma 20 ga watan jimada sani shekara ta biyar bayan aiko wa Manzon Allah da sa}o.Nasabarta:Kamar yadda aka sani mahaifin ta Manzon Allah[S]mahaifiyarta kuma Sayyida Khadija.Wani tambihi anan shine,Malaman madrsah ]in Ahlul bayt sun tafi akan cewa ‘ya’ya Manzon Allah baki ]aya an haife sune gabanin aiko masa da sa}o ne in banda Sayyida Fa]ima da kuma Ibrahim ]an Mariya wato su bayan aiko masa da sa}o ne aka haife su.3-Nash’a]inta:Sayyida Fa]ima ta tashi a makka,tana da shekara biyar mahaifiyarta ta rasu,tana da shekara takwas lokacin da aka yi hijira zuwa madina,bayan komawa madina anan ta rayu a kuma nan ta rasu.4-La}ubbanta da kuma kinayarta:Daga cikin la}ubbanta akwai Ma’asuma,Mazluma,Karima,Sabira da dai sauransu.Haka nan kuma tana da kinaya masu yawa amma wa]anda suka fi shahara sune Ummul-Aimma da kuma Ummu Abiha.5-Shekarunta: Sayyida Zahra[AS] ta rayu a duniya shekaru 18 a wata ruwaya shekaru 23 ne.6- ‘ya’yanta:Tana da ‘ya’ya biyar maza ukku mata biyu.7-Wafatinta:Akwai ruwayoyi kusan goma akai amma ruwayar da tafi shahara kuma wadda mai littafin mafatihul jinan ya tafi akai itace ukku ga watan jimada sani shekara ta 11 bayan hijira.8-Kabarinta:Shima wannan akwai sa~ani na ainihin in da }abarinta yake amma akwai zantuka ukku akai,wasu sun ce a Ba}i’a yake,wasu sun ce }abarinta yana tsakanin kabarin Manzon Allah da minbarinsa,wasu sun ce }abarinta yana cikin ]akinta.In sha-Allah idan Imam Mahdi[AF] ya bayyana ainihin in da }abarinta yake zai bayyana.
Haka nan kuma a makamanciyar wannan rana ta 20 ga wata na jimada sani shekara ta 1320 bayan hijira aka haifi Imam Khumaini.Nan kuma wasu sassa ne na rayuwarsa a ta}aice.1-Nasabarsa:Sunansa Ruhullah,Sunan mahaifinsa Ayatullahi Sayyid Mustafha,sunan mahaifiyarsa Sayyida Hajar ita kuma’yar Ayatullahi Mirza Ahmad, wato Imam Khumaini mahaifansa duka sadat ne,nasabarsa tana tu}ewa ga Imam Musa Al-kazim shi yasa ake masa la}abi da Al-musawi.Yana da wata biyar a duniya mahaifinsa ya rasu ta hanyar shahada domin an kashe shine,yana kuma da shekaru 15 a duniya mahaifiyarsa ta rasu.2-Shekarunsa: Ya rayu a duniya shekaru 93 ne.3-Muddan da ya rayu bayan juyin musulunci:kusan shekaru 10 ne ya rayu.4-‘Ya’yansa:yana da ‘ya’ya biyar maza biyu mata ukku.5- Wafatinsa:ya rasu ranar sati 3 ga watan june 1989,amma a lissafin watanni na musulunci ya rasu ne a 28 ga watan Shawwal 1409 ne.6-{abarinsa:Yana a Tehran ne wato babban birnin }asar Iran.
|