Ahlul-Bayt [AS] a mahangar Sunna da Shi’a. |
![]() |
![]() |
Written by administrator | |||
Tuesday, 11 March 2014 05:29 | |||
Wannan maudu’i na Ahlul-bayt a mahangar sunna da shi’a maudi’i ne wanda ke da gayar muhimmanci,musamman idan mutum yayi la’akari da yadda mahanga ta banbanta tsakanin wa]annan makarantu guda biyu wato na shi’a da sunna dangane da Ahlul-bayt[AS] duk da cewa al-amarin Ahlul-bayt mutum zai iya tabbatar da shi a cikin littafan Ahlus-sunna ta fuskoki dabam-dabam.Shi yasa masu fada da mabiya Ahlul-bayt[AS] wato ‘yan shi’a,ya kamata su tambayi kansu cewa mi yasa ake samun ]an Ahlus-sunna yake komawa ]an shi’a?akasin da wuya kaga ]an shi’a ya koma Ahlus-sunna.Amsa anan itace saboda }arfin hujjojin da ‘yan shi’a suke dashi a cikin fitattun littafan Ahlus-sunna na hadisai da kuma tarihi,wato wa]anda suke tabbatar da cewa abun da suke akai cewa shine dai-dai,shi yasa zaka ga koda wane lokaci ]an shi’a sai dai ya kafa ma ]an sunna hujja a littafan sunnan,sai kaga ]an sunnan abun ya bashi mamaki yanzu a cikin littafanmu akwai wannan abu,to anan sai kaga cewa in dai ba ta’assubanci a cikin zuciyar mutum sai kaga mutum ya sallama.Anan bari aba da misali guda ]aya da Hadisi-Sa}alain wato hadisin da Manzon Allah[S] yace;Ya barmana abubuwa guda biyu wa]anda idan muka bisu ba zamu ~ace ba,wa]anda sune Al}ur’ani mai girma da kuma Ahlul-bayt[AS] wanda akan wannan asasi ne ‘yan shi’a suke ri}o da Ahlul-bayt.Wanda wannan hadisi gashi nan a littafai hadisai dabam-dabam na Ahlus-sunna,in ma mutum bai da manyan littafai na hadisi kamar su Sahihu Muslim to yana iya duba cikin littafin hadisi na Riyadus-salihin zai ga hadisin,wato dai hadisi ne sahihi a wajen Ahlus-sunna,amma a aikace in muka dubi Ahlus-sunna ko muka tambaya yaya ri}on su da Ahlul-bayt in ka kwatanta da yadda ‘yan shi’a suka ri}e su?Bama haka ba hatta hadisin a wajen Ahlua-sunna kamar ba}o ne,domin an gina mutane akan hadisin da yazo cewa Manzon Allah[S] yace na bar maku abubuwa guda biyu littafin Allah da sunna ta,wanda wannan hadisi in mutum yabi diddiginsa a fitattun littafan hadisai na Ahlus-sunna kamar Buhari da Muslim zai ga basu kawo shi ba,in da wannan hadisi yazo shine a cikin Muwa]]a Malik,kuma hadisin yazo a matsayin hadisi “Mursal”hadisi mursal shine hadisin da tabi’i yace Manzon Allah yace kaza,domin a hadisin Malik yace labari ya same ni cewa Manzon Allah yace;Na barmaku al-amura biyu baza ku ~ace ba matu}ar kuka yi ri}o dasu littafin Allah da kuma sunnar Annabinsa.”Ga mai son ganin hidisin ya duba cikin muwa]]a malik a Kitabul-jami’i wato a juz’i na biyu to a cikin kitabul jami’i ]in ya duba babin da ke Magana kan }addara abin mamaki a ciki aka saka hadisin.To mutum ya kwatanta shi da wanda yazo cikin littafin hadisi na Riyadus-salihin,a babin dake bayanin girmama Ahlu baitin Manzon Allah,wato hadisin da aka samo daga sahabin Manzon Allah mai suna Zaid ]an Ar}am wanda yace:Na barmaku abubuwa guda biyu wa]anda idan kuka yi ri}o da su baza ku ~ace ba,littafin Allah da kuma Ahlu-baitina.Idan mutum ya duba hadisin zai ga a }arshensa an sa “Rawahu Muslim”To tambaya anan idan hadisai biyu suka zo ]aya sahihi ]aya kuma mursal to wanne za a ]auka?Kuma wannan hadisi ya nuna mana cewa dole sai an ri}e wa]annan abubuwa guda biyu za a amintu daga ~acewa,amma matu}ar aka ri}e ]aya aka bar ]aya to dole za a ~ace.Shi yasa a wannan lokaci sai kaga abubuwa da yawa na ‘yan shi’a yana ba wasu daga cikin Ahlus sunna sha’awa,wanda har malamansu sukan fa]i haka,misali kaji sunce ‘yan shi’a suna da jagoranci kuma suna biyayya ga jagorancin suna da tsari da kyakkyawan mu’amala da dai sauransu,to tambaya anan shine mi ye sirrin haka?amsa itace sakamakon ri}on sune da wa]annan abubuwa guda biyu wato Al}ur’ani da kuma Ahlul baiti[AS]Kuma zamu ga cewa hatta ma}iya na musulunci da musulmi basu iya amfani da ‘yan shi’a wajen cutar da ‘yan’uwansu musulmi,saboda me?saboda ba kara zube suke ba.A wannan maudu’i, bayani zai gudana insha-Allah akan wa]annan ababe1-Su waye ake nufi da Ahlul-bayt?.2-Son Ahlul bayt[AS].3-Kiyayya da Ahlul-bayt[AS].4-Hada tsakanin sonsu da kuma son makiyansu.5-Jahiltarsu da kuma tarihinsu.6-Ha}}o}in Ahlul-bayt.7- Makomar duniya Ahlul bayti ne. 1- Su waye ake nufi da Ahlul- bayt[AS]:Anan idan mutum yayi bincike a littafan shi’a da sunna zai ga cewa akwai banbancin fahimta ko mahanga akan su waye ake nufi da Ahlul-bayt[AS]?amma kuma duk da haka ‘yan shi’a akan fahimtar da suka tafi akai na wadanda ake nufi da Ahlul bait, zasu iya tabbatar da su waye ake nufi da Ahlul bayt a littafan Ahlus sunna.Domin idan mutum ya duba littafan Ahlus-sunna zai ga akwai fassarori dabam-dabam na su waye ake nufi da Ahlul-bayt[AS]?Amma ga fassarori guda biyar ana su mahangar.A-Abinda ake nufi da Ahlul-bayt sune matayen Manzon Allah[S].Wanda ya tafi akan wannan fahimta kuma ya yayata shine wani mutum da ake cema Ikrama wato maulan ibn Abbas,wanda gabaninsa ba wanda ya tafi akan wannan tafsiri sai shi,sai kuma mu}atil da yabi wannan ra’ayi nasa.saboda haka wadanda suka zo daga baya musamman malaman tafsiri kamar su [abari da sauransu to daga wajen ikrama da mu}atil suka ]auko.To tambaya wanene Ikrama da kuma Mu}atil?domin amsar wannan tambaya sai mutum ya koma a cikin wani littafi na sunna mai suna “Mizanul Iitidal” na Zahabi wanda yana cikin fitattun malaman Ahlus sunna,ya siffantasu da cewa da yawa daga cikin malaman Rijal basu amsar maganarsu wato ana tuhumtarsu da }arya a maganganunsu.B-Fassara ta biyu akan su waye ake nufi da Ahlul bayt a mahangar Ahlus sunna shine cewa:Ahlul bayt sune wa]anda aka haramta masu amsar sadaka daga cikin makusantar Manzon Allah na jini kamar su Alu-Abbas.Alu-A}il,Alu-Ja’afar da kuma Alu-Ali.Wannan Magana an ruwaito tane daga sahabin Manzon Allah Zaidu ]an Ar}am,Saboda haka hadisi ne “Mau}ufi”Hadisi mau}ufi shine hadisin da ya tsaya ga sahabi wato bai ce Manzon Allah yace ba.In mutum ya duba wancan hadisin da aka ce akwai shi cikin littafin Riyadus salihin a babin girmama Ahlu baytin Manzon Allah da kuma bayanin falalarsu,zai ga cewa daga cikin wa]anda suke zaune lokacin da sahabi Zaidu ]an Ar}am ke fa]a masu dangane da hadisi sa}alain,to ya tambaye shi cewa “Su waye Ahlu baitinsa ya Zaidu,shin matansa basu daga cikin Ahlu baitinsa,yace matansa suna daga cikin Ahlu baytinsa,?”sai ya ce masa amma “Ahlu baytinsa sune wa]anda aka haramta ma sadaka a bayansa,Alu-A}ilu,Alu Ja’afar,Alu-Abbas.”C-Fassara ta ukku akan su waye Ahlul bayt a mahangar Ahlus sunna shine cewa:Ahlul bayt sune As-habul- kisa’i[wato Sayyida Fadima,Ali,Hasan da Husain]da kuma matayen Manzon Allah[S] to wannan tafsiri na ukku shine wanda mafi yawan malaman Ahlus sunna suka tafi akai.D- Fassara ta hu]u akan su waye ake nufi da Ahlul bayt a mahangar Ahlus sunna shine cewa:Ahlul bayt sune Ashabul-kisa’i kawai ba tare da wasu ba,wato Manzon Allah da Ali da Fa]ima da Hasan da Husain[AS]sai dai wannan wasu ka]an ne daga cikin malaman Ahlus sunna suka tafi akai.Kuma wannan fassara tayi muwafa}a da abun da shi’a suka tafi akai.To idan muka juya ta mahangar ‘yan shi’a akan su waye ake nufi da Ahlul bayt zamu ga fassara guda suke da ita akai.wato Ahlul bayt sune Ashabul-kisa’i da kuma Aimma tara da suka zo bayan Imam Husaini,kuma zasu iya kawo hujjojin haka a littafan Ahlus sunna,na Tafsirai da Hadisai da sauransu.Misali mutum ya duba cikin littafin tafsirin Suyu]i mai suna “Durrul-Mansur”a tafsirin ayar Innama yuridullahu liyuzhiba ankumur rijsa Ahlal bayti…….ya kawo cewa ummul muminina ummu Salma tace,a gida na wannan ayar ta sauka,sai nace ya Manzon Allah ni bani daga cikin Ahlul baiti?sai Manzon Allah yace mata kina akan alhairi,kina daga cikin matan Manzon Allah,a wani hadisi da suyu]i ya kawo a dai tafsirin wannan ayar,hadisin an samo shi daga Abi –Saidul kudri yace Manzon Allah yace;Wannan ayar ta sauka kan mutane biyar,Ni,Ali,Fa]ima,Hasan,Husain.A kuma tafsirin ibn Kasir shima ya fitar da wannan hadisi amma ta wata fuska cewa Aisha matar Manzon Allah tace wata rana naga Manzon Allah ya kira Ali da Fa]ima da Hasan da Husain,sai ya lullu~e su da mayafi yana cewa,ya ubangiji wa]annan sune Ahlu baitina.Sai Aisha tace sai naje kusa da su nace ya Manzon Allah,ni bana daga cikin Ahlu baitinka?sai Manzon Allah yace matsa,amma kina akan alhairi.Haka nan kuma a cikin sahihu Muslim a babin dake bayani dangane da falalolin Ahlu baytin Manzon Allah,ya kawo hadisi wanda aka samo daga Aisha tace;Wata rana Manzon Allah ya fita da mayafi sai Hasan yazo sai ya shigar da shi cikin mayafin,saannan Husaini yazo shima ya shigar dashi,saannan Fa]ima tazo ita ma ya shigar da ita,saannan Ali yazo shima ya shigar dashi,bayan haka sai ya karanta wannan aya ta Innama yuridullahu………A ta}aice dai akwai hadisai kusan goma da suka zo a littafan Ahlus sunna da ke nuna cewa Ahlul bayt sune Wa]anda shi’a suka tafi akai amma saboda gudun tsawaitawa baza a iya kawo su ba.Haka nan kuma idan mutum ya dubi siya}in wannan aya a mahanga ta fannin Nahawu zai ga cewa Dhama’ir ]in da aka yi amfani da shi muzakkar ne ba muannas ba,dalilin kawo wannan domin akwai malaman Ahlus sunna da suke kawo hujja da wannan aya akan cewa tana nufin matan Manzon Allah ne,A ta}aice akwai bahasi mai yawa a wannan aya ]in kuma ta fuskoki dabam dabam,domin hatta isma da ‘yan shi’a suke jin gina ma imamansu to ]aya daga cikin hujjojinsu akwai ita wannan aya ta “Ta]hir”. 2- Son Ahlul-bayt[AS]:Son Ahlul-baiti wajibine daga cikin wajibobi na Addini,kuma yana da falaloli masu yawan gaske ta fuskoki masu yawa wato a addinin mutum da duniyarsa da kuma lahirarsa.Haka nan son Ahlul-bayt[AS] shine lada ko sakamako da Manzon Allah[S] ya bu}aci wannan al’umma tasa da tayi masa a matsayin isar da sa}on da yayi,wato kamar yadda Allah ta’ala yake fa]i a cikin Al}ur’ani mai girma a suratu shura ayata 23, “Kace ban tambaye ku wata lada ba face so ga ma’abuta kusanci.”Wannan kalma ta {urba,shima in mutum yayi bincike a littafan Ahlus sunna musamman ma na tafsirai zai ga akwai fassarori dabam dabam,domin wani abin mamaki shine duk wani abun da ya shafi Ahlul bayt a littafan sunna sai kaga an bashi fassarori dabam dabam,to a irin wa]annan fassarori sai kaga wata fassarar tayi muwafa}a da abin da shi’a suka tafi akai,saboda haka sai haka ya zama makami na hujja a hannun ]an shi’a da zai kafa ta ga waninsa.shi yasa sai kaga so da yawa ]an shi’a bai da bu}atar kawo hujja cikin littafansa,sai dai yace ka duba cikin littafi kaza,}ila ma mutumin na da littafin a gida.To a wannan kalma ta illar mawaddata fil }urba akwai fassarori hu]u da suka yi akai sune:1-{urba anan wai yana nufin Manzon Allah,wai saboda kusancin da yake dashi ga }uraishawa na jini.2-{urba anan wai na nufin makusantan wa]anda ake Magana da su.3-{urba anan wai na nufin }urbani ga Allah,amma ita wannan fassara ta nawasib ce wato saboda }iyayyarsu ga Ahlul bayti.4-{urba anan yana nufin Ahlul bayt.Kuma wannan fassara tayi muwafa}a da abin da shi’a suka tafi akai,kuma zasu iya kafa hujjar haka a littafan Ahlus sunna,misali mutum ya duba cikin littafin “Fadha’ilus-sahaba na Ahmad ibn Hanbal akwai hadisi da ya kawo a ciki wanda aka samo daga Abdullahi ]an Abbas yace lokacin da wannan aya ta sauka ta “{ul-la-as-alukum-alaihi-ajran-illar-mawaddata-fil- }urba”muka ce ya Manzon Allah su waye wa]annan makusanta naka wa]anda aka wajabta mu so su?sai yace Ali,Fa]ima,da kuma ‘ya’yansu.Haka nan a wani hadisi Manzon Allah[S]yace; “Allah ta’ala yasa lada ta gare ku shine ku so Ahlu baitina,kuma zan tambaye ku dangane da su ranar }iyama.Bayan haka kuma akwai hadisai masu yawa da suka zo dangane da falalar son Ahlul bayti,ga wasu daga ciki,Manzon Allah[S] yace; “Duk wanda ya mutu akan son Ahlul bayti ya mutu shahidi.Duk wanda ya mutu akan son Ahlul bayti ya mutu a wanda aka gafarta masa.Duk wanda ya mutu akan son Ahlul bayti ya mutu a mai tuba.Duk wanda ya mutu akan son Ahlul bayti ya mutu mumini mai cikakken imani.Duk wanda ya mutu akan son Ahlul bayti mala’kan mutuwa zai masa bushara da gidan Aljanna.Duk wanda ya mutu akan son Ahlul bayti za a bu]e masa }ofofi biyu zuwa ga Aljanna a cikin kabarinsa.Duk wanda ya mutu akan son Ahlul bayti Allah ta’ala zai sanya kabarinsa ya zama maziyartar mala ‘ikun rahama.Wannan hadisi da yawa wasu daga cikin malaman Ahlus sunna sun fitar das hi cikin littafan su kamar su {ur’]abi cikin tafsirinsa na Al-jami’u da kuma Zama kashari a littafinsa mai suna Kash-shaf.Haka nan a wani hadisi da [abrani ya kawo,Manzon Allah yace; “Ku lizimci son mu Ahlul bayti,domin duk wanda ya ha]u da Allah yana son mu to zai shi ga Aljanna da cetonmu.”Haka nan kuma a wani hadisi da [abranin ya kawo daga Abdullahi ]an Abbas yace:Manzon Allah yace; “Bawa ba zai gushe ba ranar }iyama har sai a tambaye shi abubuwa hu]u,yadda ya }arar da rayuwarsa,yadda ya tsofar da jikinsa,yadda ya samu dukiyarsa da kuma yadda ya kashe ta,Da kuma son mu Ahlul bayti.”Wannan hadisi ya nuna mana cewa gobe }iyama za a tambayi ko wannen mu dangane da son sa ga Ahlul bayti.Saboda haka akwai hadisai masu yawa da suke bayanin falalar son Ahlul bayti amma saboda gudun tsawaitawa za a ta}aita da wa]annan. 3- {iyayya da Ahlu bayti:Abin mamaki a wannan alumma ta Manzon Allah an samu wasu mutane wanda A}idarsu itace gaba da }iyayya ga Ahlu bayti,wa]annan mutane ana kiransu “Nawasib”kuma abun mamaki har yanzu akwai su.domin duk wanda yayi karatu a wajensu zaka ga tasirin gubar haka a zantukansa da kuuma ayyukansa,alal misali zaka ga duk wani abun da ya shafi Ahlul bayti bai ganin darajarsa ko kuma kaga yana da zafin }iyayya da gaba ga masu ri}o da Ahlul bayti,kai hatta ma Aimma na Ahlul bayti zaka ga bai ganin darajarsu ko kuma ya fa]i abun da bai dace ba dangane dasu.Alal misali ire-iren wanda suka shawo wannan gubar akwai wanda ke cewa kuna damun mutane an kashe Husain to “so what dun an kashe shi”Haka nan na ta~a jin wani malami ]an }asar Yaman yana cewa lokacin yana karatu a jami’a ya kasance yana tunanin ina ma dai da an kashe Imam Ali tun a ya}in badar,domin yace yadda aka gina su,an nuna masu cewa duk wa]annan rigingimu da suka auku tsakanin sahabbai Imam Ali ya haifar dasu.To mu duba wannan abu saboda Allah,amma Alhamdu lillahi wannan Malami yanzu ya fahimci gaskiyar lamari ya zama ]an shi’a.Kuma duk wanda yayi karatu ya kuma cire ta’assubanci a zuciyarsa gane wa]anda suka haifar da wannan matsala ta cusa }iyayya da gaba ga Ahlul bayti da kuma wa]anda suka yi ri}o da su bai da wuya,ashe a cikin khalifofin bani umayya ba akwai wanda ya assasa kuma ya sunna zagi da la’anta ga Imam Ali ba da Ahlul bayti,haka kuma ya cutar da gallaza ma wa]anda suka bi Ahlul bayti.Wani lokaci in naji masu cewa shi’a na zagin sahabbai sai in ji mamakin abun a zuciya ta,in ce in zagi ne ai an san wanda ya sunnata zagin sahabbai,insha-Allah wani lokaci za a yi rubutu mai taken Sahabbai a mahagar shi’a da sunna to za a fito da wa]annan abubuwa a fili. Kuma kamar yadda hadisai dabam dabam suka zo dake bayanin falalar son Ahlul bayti,to haka nan akwai hadisai da suka zo dangane mummunan sakamako ga mai }iyayya ga Ahlul bayti,ga misalan wasu daga ciki:Hakim ya fitar da hadisi a cikin Mustad-rak ]in shi cewa Manzon Allah yace: “Ina rantsuwa da wanda raina yake hannunsa babu wani da zai yi }iyayya da mu Ahlul bayti face Allah sai ya shigar da shi wuta.”Haka nan a wani hadisi Manzon Allah yace; “Ba mai son Ali face mu’umini,ba mai }insa face munafiki.”Wani hadisi da Tirmizi ya fitar makamancin wannan Manzon Allah yace; “Munafiki ba zai so Ali ba,mu’umini kuma ba zai }ishi ba.”Haka nan a wani hadisi Manzon Allah yace: “Duk wanda ya mutu akan }in Ahlul bayti ba zai sha}i }anshin Aljanna ba.”Da dai hadisai masu yawa da ke nuna mummunan sakamako na mai }iyayya ga Ahlul bayt[AS] ta wannan fuska ne idan mutum yaga masu fa]a ko }iyayya da gaba da ‘yan shi’a sai ya tausaya masu,domin ba wani laifi ‘yan shi’a suka yi ba face domin sun ri}e Ahlul bayti,wanda suma masu }iyayya da gaba dasu wajibine su ri}e su.Domin fa]a da ‘yan shi’a fa]a ne da Ahlul bayti,fa]a da Ahlul bayti kuma fa]a ne da Manzon Allah,fa]a da Manzon Allah kuma fa]a ne da Allah ta’ala,saboda haka mutum yayi hattara,kada ya jefa kan sa cikin halaka sakamakon jahilci ko ta’assubanci,saboda zai fi ma mutum sau}i yaje ma Allah ta’ala gobe }iyama da fahimta ta addini ko da jabu ce ko,amma yana da ya}ini kan abun da yake akai,ba tare da yayi fa]a da fahimtar wasu ba.Sai ya zamo al’amarinsa naga Allah,amma ace mutum yazo ya rayu a duniya akan jabun fahimta ta addini,a lokaci guda kuma yana fa]a da wa]anda suke kan sahihiyar fahimta ta addini,ya mutu a haka to al-amarinsa zai kasance da ban tsoro. 4- Ha]a tsakanin son su da kuma son ma}iyansu:Wannan abun mamaki zaka same shi tsakankanin ‘yan’uwan mu musulmi Ahlus sunna,wato zaka samu mutum yana son Ahlul bayt kuma a lokaci guda yana son ma}iyansu,ko ka samu yana girmama su a lokaci guda kuma yana girmama ma}iyansu,ko kuma sun yi ya}i tsakaninsu amma kuma a lokaci guda dukkansu masu gaskiya ne,wanda wannan ko a hankalce ya sa~a a ce mutane biyu sun fa]a amma kuma wai dukkansu suna da gaskiya,saboda haka dole ne a samu wanda yake da gaskiya a kuma samu wanda bai da gaskiya,misali a nan shine ya}in Siffin wato ya}in da ya gudana tsakanin Imam Ali da kuma Mu’awiya,kai hatta ma wa}i’ar karbala akwai wa]anda suke }o}arin su wanke wa]anda suka aukar da ita,har ma suna basu yardar Allah.To wannan shine ha]a son su da kuma na ma}iyansu wanda yin haka ya sa~a ma hankali da kuma addini.Saboda haka dole ne dangane da al-amarin Ahlul bayt mutum yayi abun da ake ce ma “Bara’a da Wula’a” Wato mutum ya barranta daga ma}iyansu ya kuma mi}a wilaya gare su.Domin yin haka shi ya dace da hankali da kuma shari’a.Saboda in ba haka ba to ya za a yi da wa]annan hadisai masu yawa da suka zo dangane da falalar son Ahlul bayti da kuma mummunan sakamako na }insu.Amma idan mutum ya dubi tsakankanin mabiya Ahlul bayti sai ga akasin haka wato suna nuna soyayyarsu ga Ahlul bayti kuma suna nuna }iyayyarsu ga ma}iyansu misali suna nuna son su ga Imam Husaini,a lokaci guda kuma suna nuna }iyayyar su ga Yazidu. 5- Jahiltarsu da kuma tarihinsu:Haka wannan shima yna daga cikin abubuwan da mutum zai gani tsakankanin Ahlus sunna,wato mutum zai ga mafi yawansu sun jahilci tarihin Ahlul bayti,kai bama tarihin rayuwarsu ba hatta sunayensu mutum zai ga sun jahilta ko ka samu mutum bai ta~a ji ba,ta wani ]an’uwa da aka Haifa masa ]a namiji sai ]an’uwan ya sa masa suna Kazim sai baban ]an’uwan da yaji sunan yace masa wannan wane suna ne Kazim,ga sunaye nan masu kyau ba ka sa masa ba sai wannan suna,to mu duba fa mu gani hatta sunayen su an jahilta to ina ga kuma tarihinsu,to ballantana kuma aje ga sanin falalolinsu da kuma matsayinsu.Kuma wannan fa bai ta}aita ga amawan Ahlus sunna ba a’a hatta ga Malamansu zaka samu cewa sun jahilci tarihin Ahlul bayti,misali kana iya jin malami ya biya hadisin da yazo daga Manzon Allah cewa; “Duk wanda ya mutu bai san Imamin zamaninsa ba to ya mutu mutuwar jahiliyya.”to da mutum zai tambaye shi yace Allah gafarta Malam wanene Imamin wannan zamanin? zai ce maka shima bai sani ba.Kai hatta wa}i’oi da suka auku a tarihi sai kaga wasu malaman sunna sun jahilce su,Alal misali akwai wani malami dana ]an bashi labari kusan shekaru ishirin da suka wuce dangane abubuwan da suka auku a karbala ga Imam Husaini wanda hat ta kai ga daga }arshe aka kashe shi,yace waya yi sanadiyyar haka nace Yazidu,yace wanene Yazidu,nace Yazidu ]an Mu’awiya yace Mu’awiya sahabi nace shifa,to shine ya kama fa]in inna nillahi-wa-inna-ilaihi-raji’un,kuma abun mamaki wannan malamin ana ]aukar karatuttuka a wajensa,misali a fannin fi}hu tun daga }awa’idi har muktasar,haka nan lugga har ya zuwa littafin mu}ama ana yi wajensa.A ta}aice dai abinda ya shafi fannin tarihi to da yawa tsakankanin ‘yan sunna zaka ga an jahilta,wani lokaci zaka ga ba wai tarihi na Ahlul bayti ba a’a hatta na sunnar ma An jahilta.Kuma duk wanda yayi karatun Zaure zai tabbatar maka da haka cewa fannin ilimin tarihi yana daga cikin fannonin ilimin da ba a karatunsa.Amma in da mutum zai dubi tsakankanin mabiya Ahlul bayti zai ga Akasin haka,wato zai ga cewa sun san tarihin Ahlul bayti da wa}i’oin da suka auku a wannan al’umma ta Manzon Allah da ma tarihin wa]anda suka aukar da wa}i’oin.A ta}aice dai zaka samu ]an shi’a zai yi baka tarihin abubuwan da suka auku tun daga bayan wafatin Manzon Allah da kuma daulolin da akayi tiryan-tiryan kai wani ma zai iya dire maka har ya zuwa wannan zamanin. 6- Ha}}o}in Ahlul bayti:Akwai ha}}o}i da Ahlul bayti suke da shi ga dukkan musulmi baki ]aya kasantuwar sune wa]anda Manzon Allah ya barma wannan al’umma tasa da suyi ri}o da su a bayansa,saboda haka wa]annan ha}}o}i sun shafi ko wane musulmi musammam ma ga wa]anda suka yi ri}o da su,kuma wa]annan ha}}o}i suna da yawa saboda haka nan wasu ne daga ciki:1-Saninsu:Sanin Imaman Ahlul bayti a matsayin su na khalifofin Manzon Allah yana da gayar muhimmanci,domin rashin saninsu yana iya janyo ma mutum yayi mutuwar jahiliyya kamar dai yadda yazo a hadisin da aka kawo.Kuma kasantuwar ba suyi khalifanci ba a zahirance wato ba su tafi da iko ba,bai tada su daga matsayinsu na khalifofin Manzon Allah ba,domin so da yawa wasu malaman Ahlus sunna suna kafa hujja da cewa kuna cewa sune khalifofin Manzon Allah to sun tafi da iko ne?Saboda haka mu wajen mu duk da basu tafi da iko ba,suna dai nan a matsayinsu da Allah ta’ala ya basu na khalifanci.Misali kamar yadda Allah ta’ala ya aiko da Annabawa to akwai annabin da yazo har ya gama rayuwarsa da kuma kiran da yayi amma ba wanda yayi imani da shi,to tambaya wannan ya ta da shi daga matsayin Annabi? Amsa a’a,to haka nan shima imamanci ko khalifanci don wasu basu yarda ba to bai tada su a matsayin su na imamai ba ko khalifofi da Allah ta’ala ya za~a,domin mu wajenmu kamar yadda ba mutane suke za~ar Annabi ba to haka nan khalifan Manzon Allah,Allah ta’ala ne yake za~a.Saboda haka sanin Aimma na Ahlul bayt wani abune mai muhimmancin gaske,domin idan mutum ya mutu bayan an sa shi cikin kabari to bayan an tambaye shi waye ubangijinsa?waye Annabinsa? Bayan haka kuma sai a tambayi mutum waye Imaminsa?haka nan ranar }iyama za a tambayi mutum dangane da Ahlul bayti kamar dai yadda yazo a hadisin da ya gabata.2-Daga cikin ha}}o}in Ahlul bayti akwai yi masu biyayya,wato mutum ya aikata umarce-umarcensu ya kuma nisanci abubuwan da suka hana,wato dai kamar yadda yazo a hadisi daga Imam Ba}ir[AS]yace; “Bayan mutum ya san Imaminsa to yai masa biyayya.”3-Daga cikin ha}}o}in Ahlul bayti akwai ziyararsu:Wato kamar yadda yazo a hadisi da aka samo daga Imam Sadik[AS] yace; “Wanda ya ziyarce su to yana da lada kamar wanda ya ziyarci Manzon Allah.”Kuma ziyarar Ahlul bayti ta kasu kashi biyu,akwai ziyara ta kusa akwai kuma ziyara ta nesa,ziyara ta kusa itace ziyararsu a kaburburansu,ziyara ta kuma nesa itace itace mutum ya ziyarce su daga garin d a yake.Kuma abubuwan da ake karantawa idan an ziyarce su a kusa ko nesa Alhamdu lillahi duk sun zo Alittafan Addu’oi da kuma na ziyara.Kai akwai ma ziyarar su ta ranakun mako wanda yake da muhimmanci ko wannen mu ya lizimta ma kansa karanta ta ko wace rana,ga mai bu}atar ganin wa]annan ziyarori na ko wane imami da kuma ranakun yi,yana iya duba littafin mafatihul jinan babi na ]aya fasali na biyar.4-Daga cikin ha}}o}in da Ahlul bayti da suke da shi akwai ha}}in khumusi,bayani dangane da khumusi sanka-sanka wani abune da ya shafi fannin fi}hu,saboda haka a darasin fi}hu wani lokaci in sha Allah bayani zai gudana akai.5-Daga cikin ha}}o}in da Ahlul bayti suke da shi akwai kyautatawa ga zuriyyarsu.Yazo a hadisi Manzon Allah yace: “Mutum hu]u ni zan cecesu ranar }iyama,mai kyautata ma zuriyyata bayana,da mai biya masu bu}atunsu,da mai kai komo ga al-amuransu lokacin da suka shiga cikin tsanani da kuma mai son su a zuciyarsa da kuma harshensa.”Haka nan kuma a wani hadisi Manzon Allah yace; “Wallahi ba zan ceci duk wanda ya cutar da zuriyya ta ba.”Saboda haka son zuriyyar Ahlul bayti da kuma girmama su da kuma kyautata masu wani abune wanda yake da gayar muhimmanci a addinin mutum da duniyarsa da kuma lahirarsa.6-Daga cikin ha}}o}in Ahlul bayti akwai kiyaye munasabobi na wiladarsu wato haihuwarsu da kuma wafatinsu wato rasuwarsu.Wato a mataki na ]ai-]ai ku da kuma na jama’a.Saboda haka yana da gayar muhimmanci ga ko wannen mu namiji ne ko mace ya zamanto yana kiyaye ko wace rana ta wilada ko wafati na Ahlul bayti,kuma sassau}ar hanya akan haka itace duk watan da ya kama na musulunci to mutum ya bincika domin yaga munasababin dake cikin watan,idan mutum ya lizimci haka to yau da gobe zai kai matsayin da ya kiyaye munabar ko wane Imami cikin Imamai.Domin kiyaye wa]annan munasabobi na Ma’asumin[AS]yana daga cikin alamomin son su.Yama zo a hadisi daga Imam Sadik[AS] yace; “Masoyanmu sune wa]anda suke farin ciki da farin cikinmu,suke kuma bakin ciki da bakin cikinmu.”Wannan ke nan a ta}aice na ha}}o}in Ahlul bayti. 7- Makomar duniya Ahlul baytine:Duk da cewa a tsawon tarihin wannan al-umma ta Manzon Allah[S] ba Ahlul bayti bane suka jagoran ce ta ba wato a matsayi na tafi da iko,amma yazo a hadisai masu yawa daga littafan sunna da shi’a cewa Manzon Allah[S] yace,ba za a yi tashin duniya ba har sai wani daga cikin Ahlu baytinsa ya shugabanci duniya baki daya,kuma zai cika duniya da adalci kamar yadda ta cika da zalunci.Wannan bawa na Allah ta’ala a ijma’in shi’a da sunna shine Imam Mahdi[AF] Saboda haka wannan wani rubutaccen abune kuma hukumtacce daga wajen Allah cewa haka sai ya tabbata.Kuma ga dukkan alamu ana kusa da bayyanarsa,saboda haka wannan }arni da muke ciki }arni ne na Ahlul bayti.Domin alamomin bayyanar Imam Mahdi sun kasu kashi kashi ukku sune:1-Akwai alamomin da zasu kasance gabanin bayyanarsa.2-Akwai alamomin da zasu kasance gab da ya bayyana.3-Akwai alamomin da zasu kasance idan ya bayyana.Idan mutum yayi bincike dangane da alamomi na farko zai ga cewa duk sun bayyana misali yawan fasadi,yawan zalunci,yawan kashe-kashe,lalacewar tattalin arziki na duniya domin shima yana cikin alamomin bayyanarsa,ya]uwar fahimta ta Ahlul bayti da dai ssauranu.To a yanzu alamomin da suke gudana alamomine da yazo akan cewa zasu kasance gab da ya bayyana ne.Shi yasa wa]annan ayoyi da ake ganin su a yanzu a sararin samaniya na sunayen Ahlul bayti ko ganin hoton surarsu a sama duk yana cikin alamomin da zasu auku gab da ya bayyana.Akwai wanda shima zai auku ba makawa shine na jin Magana daga sama,kuma wannan sautin Magana kowa dake duniya a lokacin sai yaji,abinda za a ji a sautin maganar shine cewa “Gaskiya tana ga Ahlu baytin Muhammad”Kuma duk wa]annan abubuwa na ayoyi suna nan cikin littafan hadisai na sunna da shi’a.In sha Allah in Allah ya kai mu a watan shaaban na bana za a yi rubutu mai taken “Kusantowar bayyanar Imam Mahdi” wanda a cikin sa za a kawo wa]annan hadisai.Amma yanzu ga Nassin hadisin da aka kawo na Magana da za a ji.An samo daga Imam Ali[AS] yace; “Idan mai kira yayi kira daga sama yana cewa lalle gaskiya tana ga Ahlu baytin Muhammad,to a lokacin Mahdi zai bayyana.”A wani hadisin yazo cewa ko wane harshe mutum ke Magana dashi sai yaji wannan Magana,kai hadisin ya nuna cewa hatta mai barci sai yaji,har yazo cewa za a wayi gari babu wani abun tattaunawa face wannan Magana da aka ji,wannan yace kaji,yace nima naji.Saboda haka kira anan musammam ga wadanda suke fada da shi’a da ku hutar da kanku,wannan shi’anci da kuke ganin yake tasowa a wannan kasa dama duniya baki daya yin Allah ta’ala ne,in kuma mutum yana ganin ba haka bane to ga fili ga mai doki.Saboda haka wannan haske na Ahlul bayti da yake dagowa tabbas muna da yakini sai ya mamaye duniya baki daya.
|