Watan Jimadal-ula yana daga cikin watannin da babu munasabobi masu yawa a ciki wato kamar watan Rabius-sani.A farkon watan wato daren farko ko ranar farko akwai wata addu’a da ake son karantawa,ga mai bu}atar ganin ta yana iya duba littafin I}bal na sayyid ibn [awus.Wato wannan baya ga ayyukan da ake yi a ko wane farkon wata na watannin musulunci,wa]anda wa]annan ayyuka sun ha]a da addu’oi da salloli wato na daren farko da kuma ranar farko,ga mai bu}atar ganin su yana iya duba littafin mafatihul jinan babi na biyu fasali na sha-]aya.Munasabar farko na wannan wata na Jimadal-ula itace haihuwar Sayyida Zainab[AS] domin an haife ta 5 ga wannan wata.Idan mutum ya karanci tarihi da kuma rayuwar sayyida Zainab[AS] zai ga cewa ta fuskanci jarabawowi masu yawan gaske,ta kuma fuskoki dabam-dabam,yazo a tarihin ta cewa lokacin da aka haife ta,aka je aka shaida ma Manzon Allah[S] bayan da ya iso gidan sayyida Fa]ima[AS] ya ]auki wannan ‘ya mai albarka sai aka ga yana kuka,shine Sayyida Fa]ima take tambayar sa dangane wannan kuka nasa? Sai Manzon Allah yace ina kuka ne saboda jarabawowin da wannan yarinya zata fuskanta a rayuwarta! Idan mutum zai yi tunani zai ga cewa Sayyida Zainab ko da ace ba wata jarabawa da ta fuskanta a rayuwarta,to kasantuwar ta ga rasuwar Manzon Allah[S] da na Sayyida Fa]ima[AS] da kuma shahadar Imam Ali[AS] da na Imam Hasan[AS] da kuma na Imam Husain[AS] to wannan ya isa ya zama jarabawa babba a tarihin rayuwar ta,wanda in mutum ya duba zai ga cewa ba kawai taga rasuwar su bane, a’a taga dukkan jarabawar da ko wane daga cikin Wa]annan bayin Allah da aka ambata ya fuskanta a }arshen rayuwarsa.Misali taga yadda aka kai hari a gidan mahaifiyar ta da nufin za a }ona gidan,taga yadda aka sari mahaifinta da takobi wanda yayi sanadiyyar shahadar sa,taga yadda guba tayi ma ]an’uwanta Imam Hasan[AS],taga kuma yadda aka Sassari ]an’wanta Imam Husain[AS].
Sa’annan idan muka juya ga jarabawowin da ita }ashin kanta ta fuskanta a tarihin rayuwar ta zamu ga suna da yawa,amma wa]anda suka fi fice a cikin wa]annan jarabawowin sune:Wa}i’ar karbala musamman ma abubuwan da suka biyo bayan wa}i’ar karbala,domin idan mutum ya bibiyi tarihin abubuwan da suka faru bayan wa}i’ar Karbala,zai ga cewa idan an kasa jarabawowin da suka auku to Sayyida Zainab ita ta fuskanci mafi yawan jarabawowin.Wata jarabawa kuma da ta fuskanta a }arshen rayuwar ta shine korar ta daga madina,wato bayan dawowar su madina daga wa}i’ar karbala,kasantuwar yadda Sayyida Zainab ke bayanin abubuwan da suka auku a karbala,sai gwamnan Yazidu dake madina ya aika masa cewa in dai yana da bu}atar madina to ya kori Zainab daga cikin ta,ile ko Yazidu ya aiko akan cewa dole ta bar madina,lokacin Sayyida Zainab tace ba in da zata je sai duk abun da zai faru ya faru,jin haka aka ce wasu mataye daga cikin bani Hashim suka zo wajen ta suka nuna mata tayi hijira ta bar madinar,domin suka ce mata yazidu zai iya yin kome akan haka,zai ma iya maimaita wata karbala a madina,to shine Sayyida Zainab tayi hijira zuwa misra ta bar madina.Mu duba mu gani irin wannan jarabawa madina mahaifarta ne kuma birnin kakanta,anan ta taso kuma ta rayu amma ga shi a }arshen rayuwarta an tilasta mata barin garin,kuma wani abun ban mamaki hatta misirar da ta koma yazidun bai }yale ta ba,domin shi so yake ta kulle baki ta dena Magana kan wa}i’ar karbala,kuma idan mutum ya duba tarihin sayyida Zainab zai ga cewa ta rasu a sham ne domin kabarinta a yanzu yana }asar sham ne, to zai iya yuwuwa yazidun ne yasa a dawo da ita sham,domin a lokacin nan ne cibiyar mulkin sa take.Bayan haka nan wasu sassa ne na rayuwar ta a ta}aice:
1- Wiladar ta:An haife ta a madina,5 ga watan jimada-ula,shekara ta biyar bayan hijira.
2- Nasabar ta:Sunan Mahaifinta Imam Ali[AS] sunan mahaifiyar ta Sayyida Fa]ima[AS] itace ta ukku a wajen mahaifiyar ta,wato baya ga Imam Hasan da Imam Husain sai ita,bayan ta kuma sai ummu-khul-sum,sai kuma Muhsin,a wajen mahaifin ta itace ‘ya mace ta farko gare shi domin Imam Ali yana da ‘ya’ya mata 14,to sayyida Zainab itace ta farkon su.
3- Nash’a ]inta:Sayyida Zainab ta tashi a madina,kuma ta rayu tare da kakanta wato Manzon Allah da kuma mahaifiyar ta kusan shekaru shidda.Tare kuma da Imam Ali shekaru 35.Tare kuma da Imam Hasan shekaru 45.Tare kuma da Imam Husain shekaru 55 ne.
4-‘Ya’yanta:Sayyida Zainab[AS] tana ‘ya’ya guda biyar,maza 4 da kuma mace ]aya,ga sunayen ‘ya’yan:Ali,Aun,Muhammad,Abbas,Ummu-khul-sum,biyu daga cikin ‘ya’yanta sun yi shahada a karbala wato Muhammad da Aun,da kuma mijin ‘yar ta wato ummu khul sum sunan sa {asim ]an Muhammad ]an Ja’afar.Saboda haka lokacin da aka yi wa}i’ar karbala Sayyida Zainab tana matsayin dattijiwa ne,domin a lokacin ta doshi shekaru 60 a duniya,tanan mutum zai fahimci gayar bushewar zuciya da kuma rashin kunya na ibn Ziyad da kuma Yazidu na irin maganganu na rashin ladabi da suka yi ma Zainab lokacin da aka kai ta fadar su wato a kufa da sham,saboda a Haifa ta haife su,domin a lokacin Yazidu da ibn Ziyad ba wanda ya kai shekaru 40 a cikin su,dukkan su suna 30 da wani abu ne.
5-Wafatin ta:Sayyida Zainab[AS] ta rasu ranar lahadi 15 ga watan Rajab shekara ta 62 bayan hijira a wata ruwaya shekara ta 65 bayan hijira.6-Shekarun ta:Sayyida Zainab ta bar duniya tana da shekaru 60,ba mamaki mutum yaci karo da wata ruwaya akasin haka.7-Kabarin ta: kabarin ta yana sham ne wannan shi yafi shahara musamman ga mabiya Ahlul bayti,amma akwai wa]anda suka tafi akan cewa kabarin ta yana misra ne.
A goma ga wannan watan ne shekara ta 36 bayan hijira a kayi ya}in Jamal,wato ya}i ne da ya gudana tsakanin Imam Ali da kuma su [alha ]an Ubaidullahi da Zubairu ]an Awwam da kuma Aisha,wanda daga }arshe Imam Ali ne ya samu nasara akan su.Haka nan a ranakun 13,14,15 a wata ruwaya cewa a ]ayan wa]annan kwanakin ne wafatin sayyida Fa]ima[AS] shi yasa mabiya Ahlul bayt a sassan duniya dabam-dabam su kan yi zaman makokinta a wa]annan ranakun,amma akwai ruwayoyi da suka zo akasin haka,kamar ruwayar 3 ga watan jimada sani da dai sauransu.
Haka nan kuma a ranar 15 ga watan jimada ula ne shekara ta 38 bayan hijira aka kashe Muhammad ]an Abubakar,yana daga cikin shi’a ]in Imam Ali kuma yana daga cikin makusantarsa,a lokacin ma da aka kashe shi yana matsayin gwamnan Imam Ali a misra.Kuma kisan da aka yi masa kisa ne na ban mamaki da kuma rashin imani,yadda abun ya faru shine Mu’awiya ne ya aika da maya}a zuwa misra a lokacin,lokacin da maya}an suka isa misra aka fafata ya}i wanda daga }arshe ya kai ga wa]annan maya}a suka kama Muhammad ]an Abubukar,to kafin su kashe shi sai da suka tsare shi,suka bar shi da yunwa da }ishi har na kwanaki,bayan haka sai suka kashe shi bayan da suka kashe shi sai suka sare kansa bayan haka kuma suka }ona gawarsa,da labarin haka ya isa ga Mu’awiya an ce yayi farin ciki ba ka]an ba,wato jin cewa an kashe Muhammad ]an Abubakar,ga wanda ya san tarihin Mu’awiya da kuma tarihin irin mulkin da yayi ya san cewa akwai sahabbai da yawa da yasa aka kashe misali sahabin Manzon Allah Hujur ]an Adiyyi wanda kwanakin baya ‘yan tawayen siriya suka tone }abarin sa.Abun ka ga ]an’uwa an ce lokacin da labarin abun da ya faru na kashe Muhammad ]an Abubakar ya isa ga Aisha an ce tayi ba}in ciki ba ka]an ba,kuma wannan shi yayi sanadiyyar ~atawar ta da Mu’awiya,domin yazo akan cewa bayan faruwar wannan abu duk sallar da tayi sai tayi addu’a kan Mu’awiya da kuma Amru ]an As da yake shi ya jagoranci ya}in da aka yi a misra ]in wato a lokacin.Duk da cewa ga wanda ya bibiyi tarihi ya san cewa akwai banbancin ra’ayi tsakanin Aisha da kuma ]an uwan ta Muhammad misali a ya}in Jamal ya kasance a bayan Imam Ali ne ba a bayan ta ba,haka nan ]an shi Muhammad mai suna {asim yana daga ckin sahabban Imam Zainul Abidin,wato dai da Muhammad ]an Abubaka da kuma ]ansa {asim duk ‘yan shi’a ne,kuma {asim ]an Muhammad babban malami ne a lokacin, kuma shi ne baban mahaifiyar Imam Ja’afarus-sadi}[AS],kuma shi Muhammad ]an Abubukar a gidan Imam Ali ya tashi,da yake asali mahaifiyarsa mai suna Asma’u ‘yar Umais matar Ja’afar ]an Abu [alib ne,bayan shahadarsa sai Abubakar ya aure ta,ta Haifa masa wannan ]a Muhammad,to bayan rasuwarsa shine Imam Ali ya aure ta,lokacin Muhammad na }arami,dalilin tashin shi gidan Imam Ali ke nan.
Haka nan a wata ruwaya a 15 ga wannan wata ne aka haifi Imam Zainul Abidin[AS] wato a shekara ta 38 bayan hijira.amma a ruwayar da tafi shahara shine cewa an haife shi a 5 ga watan sha’aban ne. Amma anan tabarrukan ga wasu sassa na rayuwar sa a ta}aice.
1- Haihuwarsa:An haifi Imam Zainul Abidin a madina ranar jumma’a 5 ga watan sha’aban,a wata ruwaya 15 ga watan jimadal ula,shekara ta 38 bayan hijira.
2- Nasabarsa:Sunan mahaifiyar sa Maryam a wata ruwayar kuma Fa]ima,asalinta ba farisiya ce wato muniyar Iran,sunan mahaifinsa Imam Husain.
3- Nash’a ]insa:Imam Zainul Abidin[AS] kamar yadda aka haife shi a madina,to a madinar ya tashi,nan ya rayu,anan kuma ya rasu.lokacin da aka yi waki’ar karbala yana da shekaru 22 ne a duniya.
4- La}ubbansa:Imam Zainul Abidin yana da la}ubba masu yawa amma wa]anda suka fi shahara sune,Zainul Abidin da kuma Sajjad.Ana kuma yi masa kinaya da Abu Muhammad.
5- Shekarunsa:Imam Zainul Abidin ya rayu a duniya shekaru 57.
6- Muddan Imamancin sa:Muddan imamancin Imam Zainul Abidin shekaru 34 ne.
7- ‘Ya’yansa:Imam Zainul Abidin yana da ‘ya’ya 15,maza 11,mata 4.
8- Wafatin sa:Imam Zainul Abidin ya rasu ranar 25 ga watan Muharram,shekara ta 95 bayan hijira.
9- {abarin sa:}abarin sa yana madina ne,wato a ma}abartar Ba}i’a.
10- Kalifofin Umayyawa da yayi zamani da su:1-Yazidu ]an Mu’awiya.2-Mu’awiya ]an Yazidu.3-Marwan ]an Hakam.4-Abdul-Malik ]an Marwan.5-Walid ]an Abdul-Malik.
11- Wanda yayi sanadiyyar wafatin sa:Kamar yadda yazo a hadisi daga Imam Hasan[AS] yace, “Babu wani daga cikin mu [wato Aimma na Ahlul baiyti]face wanda za a kashe da takobi,ko kuma wanda za a sama guba.”Idan mutum ya bibiyi tarihin imamai dukkansu zai ga cewa daga wanda aka kashe da takobi kamar yadda aka yi ga Imam Ali[AS] da kuma Imam Husain[AS] sai kuma wa]anda aka sama guba wato kamar yadda aka yi ga Imam Hasan da kuma saurai Imamai.To Imam Zainul Abidin[AS] shima guba aka sa mashi ta hanyar umarnin khalifan Umayyawa mai suna Walid ]an Abdul-Malik.
|