Monday, 20 January 2025
Email
Make My Homepage
RSS
Register
Munasabobin watan Rabius-sani Print E-mail
Written by administrator   
Wednesday, 05 February 2014 20:44

 Watan Rabius-sani shine wata na hu]u a jerin }idaya na watannin musulunci guda goma sha-biyu.Akwai addu’a da ake son biya ta a farkon watan ga mai bu}atar ganin ta yana iya duba littafin I}bal na Sayyid ibn [awus.Haka nan kuma ana son yin azumin ranar goma ga watan.Wannan wata na Rabius-sani yana ]aya daga cikin watannin da babu munasabobi masu yawa a cikinsa.Babbar munasabar dake cikinsa itace ta haihuwar Imam Hassan Al-askari[AS] shine Imami na goma sha-]aya a jerin Imamai 12,wato wa]anda Manzon Allah[SAAW] ya bar ma wannan al-umma tasa da su kasance khalifofi a bayansa.Idan mutum ya bibiyi tarihin Aimma na Ahlul bayt[AS] zai ga cewa ko wane Imami da irin jarrabawar da ya  fuskanta daga masu tafi da iko na zamaninsa.Domin jarabawowi da Aimma[AS] suka fuskanta za a iya kasa su gida biyu,akwai jarabawowi  da dukkansu sun fuskanci irin ta,misali kamar na amshe tafida iko na khalifanci a hannunsu.Akwai kuma jarabawowin da ko wane Imami ya ke~anta da ita a zamaninsa.To idan mutum yayi bincike dangane da tarihi da kuma rayuwar Imam Hasan al-askari[AS] zai ga cewa babbar jarabawar da ya fuskanta daga masu tafida iko na zamaninsa itace jarabawar sa ido,wato masu leken asiri gare shi da kuma wa]anda yake mu’amala da su da nufin tattara bayanai domin gabatar da shi ga masu tafi da iko.Domin a lokacin mujarradin ala}antuwa da Imam Hasan Al-askari yana iya kai wa  ga a kai mutum kurkuku,ko kuma a yanke ma mutum hukuncin kisa.Akwai ma lokacin da Imam Hasan alaskari[AS] yake ce ma mabiyansa,ko a hanya wani ya ha]u dashi a cikinsu kada yayi mai sallama ko kuma ya nuna ya san shi,kai ta kai ma yake ce ma wani na kusa dashi ko dai ya ~oye ala}ar dake tsakaninsu ko kuma ya fuskanci hukuncin kisa.Kai hatta tsare-tsaren da aka yi ma Imam Hasan al-askari[AS] a kurkuku sai  da aka ha]a shi da ‘yan le}en asiri da sunan cewa suma fursuna ne,nan ko a ~oye masu sa ido ne akan sa.Baya ga irin wannan jarabawa da Imam Hasan al-askari[AS] ya fuskanta tasa masa ido.Wata jarabawa kuma da ya  fuskanta ta fuskacin masu tafi da iko na zamaninsa itace na binciken iyalinsa,wato a lokacin abun da suka yi shine,suka ]auki mata }wararru wajen sanin cikin ‘ya mace,to lokaci bayan lokaci sai  su dun ga sa su suna duba iyalin Imam Hasan al-askari[AS] ko da akwai mai ciki acikin su,to tambaya anan miya sa suka ]auki wannan mataki akansa na binciken iyalinsa? Amsa anan itace su masu tafi da iko na zamaninsa suna da masaniya cewa shine Imami na sha-]aya,saboda haka shine zai haifi Imami na shabiyu wato Imam Mahdi[as],kuma bayan haka suna da masaniya a hadisai da suka zo daga Manzon Allah yace Imami na sha-biyu shine zai kau da zalunci da azzalumai a doron }asa,bayan haka ya shinfi]a a dalci a duniya.To saboda haka shine suke bincike cikin iyalinsa lokaci bayan lokaci ko akwai mai ciki da niyyar in ta haihu in ]a namiji ne su kashe shi.To ta Allah bata su ba,a irin wannan yana yi ne aka haifi Imam Mahdi[AS]bayan haihuwarsa ma har ya shekara biyar tare da mahaifinsa.ya zamanto da daukar cikinsa da haihuwarsa dama tasowarsa duk suka ~oyu masu.Mu duba wata jarabawa da Imam Mahdi[AS] ya ke~anta da ita,wato na cewa shine Imamin da tun kafin a haife shi ana nemansa a kashe.Domin yazo akan cewa wa]anda suka san haihuwar Imam Mahdi[AS] a lokacin sune wa]anda suke da gayar kusanci ga Imam Hasan Al-askari[AS] don ko  abin a}i}a na sunansa wato dabbar da ake yanka ma abin haihuwa ranar suna,Imam Hasan Al-askari[AS] ya bayar ne aka je wani waje aka saya aka yanka wato ba a gidansa ba.Mu duba irin wa]annan jarabawowi da Imam Hasan Al-askari ya fuskanta.Shi yasa idan mutum ya yi bincike dangane wajajen da aka haifi Imamai,mutum zai ga cewa Imamai dukkansu in ka cire Imam Mahdi[AS]wanda aka Haifa a samarra wato a }asar Ira}i,dukkansu daga wa]anda aka Haifa a madina sai kuma a makka.misali Imam Ali[AS] shi a makka aka haife shi,Sauran Imamai tun daga Imam Hassan[AS] har ya zuwa Imam Hasan al-askari[AS] duk a madina aka haife su,a cikinsu Imam Kazim[AS] ne yazo akan cewa an haife shi a wani waje da ake ce ma Abwa yana tsakanin Makka da Madina ne.Amma mu duba in da aka haifi Imam Mahdi[AS] wato ne sa da Madina da kuma Makka.Wanda wannan kawai in mutum yayi tunani zai fahimci lalle wani abu ya faru.Shi yasa in mutum ya dubi in da aka je Imam Hasan Al-askari[AS]zai ga cewa a sansani ne na maya}a wato a wannan zamani namu kamar ace barikin soja,duk dai saboda wannan manufar ce.Saboda haka Imam Hasan Al-askari yayi wata irin rayuwar ce wadda ta sha ban-ban in ka kwatanta da rayuwar sauran Aimma da suka gabace shi,wato ya rayu ne a barikin soja.Wanda ko mu a wnnan zamanin mutum yayi tunani ace ga Malami na Addini kuma yana da mabiya,amma ace masu tafi da iko su ]auke shi su kai  shi barikin soja shi da iyalansa akan dole su zauna anan wajen.Shi yasa in mutum yayi bincike dangane da ala}ar Imam Hasan Al-askari da shi’arsa wato mabiyansa a lokacin zai ga cewa a mafi yawan lokuta ala}a  cet a rubutu,wato su rubuto da tambayoyi ko neman wasu bayanai ko }arin haske kan wani abu,shi kuma ya mayar masu da amsa ta hanyar rubutuwa,aba wani amintaccen hannu ya kai masu.Kuma wani abin ba}in ciki da ban mamaki har yanzu wannan waje yana da matsala,wato wajen ziyara domin idan mutum ya  dubi Aimma[AS] da kaburburansu  ke cikin Ira}i zai ga cewa babu wanda wani lokacin ake samun matsalar zuwa ziyararsa kamar kabarin Imam Hasan Al-askari[AS] wanda yake tare yake da na Imam Ali-Alhadi[AS] wato mahaifinsa.Daga }arshe a nan insha-Allah za a kawo wasu misalai na irin rubuce -rubuce da Imam Hasan Al-askari[AS] ya aika ma mabiyansa a lokacin.Wannan wasiyyarsa ne da ya aika ma mabiyansa a lokacin. “Inai maku wasiyya da kuji tsoron Allah,da kuma yin tsen-tseni a cikin addinin ku,da kuma yin mujahada domin neman yardar Allah,da kuma gaskiya wajen Magana,da kuma kiyaye amana ga duk wanda ya baku amanar.da kuma tsawaita sujuda,da kuma kyakkyawan makwabtaka,kuyi sallah a wajajensu[wato kinaya na yin sallah a masallatan Ahlus sunna] ku halarci jana’izar su,kuje gaida marar lafiyarsu,ku basu ha}}o}in su.domin idan ]ayanku yayi tsen-tseni a addininsa,yayi gaskiya a maganarsa,ya ri}e amanar da aka bashi,ya kuma kyautata ]abi’arsa da mutane za a ce wannan ]an shi’a ne,wannan kuma sai ya faranta mini rai.Kuji tsoron Allah,ku kasance masu kyautatawa kada ku kasance masu munanawa.kuyi abun da zai sa a somu,ku kuji abinda zai sa a }imu,domin duk wani kyakkyawan abun da aka jingina mana to mu ma’abuta wannan abun ne,abun kuma da aka jingina mana mummuna to mu ba ma’abuta wannan abun bane.Muna da ha}}i a cikin littafin Allah,da kuma kusanci ga Manzon Allah,da kuma tsarkaka daga wajen Allah[wato Allah ta’ala ya tsarkake su Aimma na Ahlul bayt] ba wanda zai yi da’awar haka baya ga mu face ma}aryaci.Ku yawaita zikirin Allah,ku yawaita tunanin mutuwa,ku kuma yawaita karatun Al}ur’ani,ku kuma yawaita salati ga Manzon Allah,domin ko wane salati ga Manzon Allah yana da lada goma.Ku kiyaye wannan wasiyya da nayi maku.Allah ta’ala ya tsare ku,ina kuma mi }a sallama ta gareku”.Haka nan idan kuma muka duba wata wasiyyarsa da ya rubuta ma wani Malami daga cikin mabiyansa mai suna Aliyu ]an Husaini ]an Babawaihi al-}ummiy wato mahaifin sheikh Sadu},ga wasiyyar “Inai maka wasiyya daka ji tsoron Allah,ka kuma tsai da sallah,ka kuma ba  da zakka,domin ba a kar~ar sallar wanda bai ba da  zakka.Inai maka wasiyya da yafe ma laifin da aka yi maka,da kuma ha]iye fushi, da sadar da zumunci,da kuma taimaka ma ‘yan’uwa,da kuma kai komo wajen biyan bu}atunsu cikin sau}i da tsanani,da kuma yin ha}uri ga wanda yayi maka abin da bai dace ba,da kuma neman ilimin addini,da kuma sabati a cikin al-amura,da kuma yawaita karatun Al-}ur’ani,da kuma kyautata ]abi’a,da kuma umarni da kyakkyawa da kuma hani ga mummuna,da kuma nisantar alfasha baki ]ayanta.Ina horonka da sallar dare[wato sallar tahajjud]domin Manzon Allah yayi ma Imam Ali[AS] wasiyya da cewa: Ya Ali ina horonka da sallar dare,ina horon ka da sallar dare,ina horonka da sallar dare,duk wanda yake wala}anta sallar dare to baya daga cikin mu.Kuma kayi aiki da wannan wasiyyar tawa,kuma ka umarci dukkan shi’ata da wannan wasiyya da nayi maka na suma su aikata ta.Na kuma umarce ka da yin dauriya da kuma jiran faraj,domin Manzon Allah yace: Mafificin ayyukan al-ummata shine jiran faraj,kuma shi’ata ba zasu gushe cikin damuwa da ba}in ciki ba har sai ]ana ya bayyana, wanda Manzon Allah yayi albishir dashi cewa zai cika duniya da adalci kamar yadda ta cika da zalunci.Saboda haka ka daure,kuma ka umarci dukkan shi’ata da su daure,lalle }asa ta Allah ce,kuma zai gadar da ita ga bayinsa,kuma kyakkyawan a}iba tana ga masu ta}awa.Sallama gareka da kuma dukkan shi’ata,wa has bunallahu wa ni’imal wakil.Wa]annan wasiyyoyi na Imam Hasan Al-askari yana da muhimmanci ga ko wannenmu yayi ma kansa muhasaba akai wato ya binciki kansa akan  ya siffata da wa]annan siffofi,in haka ne sai ya gode ma Allah ta’ala kan wannan ni’ima da yayi masa,in ko akasin haka ne to sai yayi mujahada wajen ganin cewa ya siffata da siffofin ko kuma wa]anda bai da su.Kuma ire-iren wa]annan rubuce-rubuce na Imam Hasan Al-askari zuwa ga shi’arsa suna da yawa ga mai bu}atar ganinsu yana iya duba littafi mai suna Aimmatuna juz’i na biyu.Yama zo a tarihinsa cewa ya rubuta tafsiri na Al-}ur’ani kuma wannan tafsiri nasa  har yanzu ana samunsa,sai dai ba cikakke bane wato na Al}ur’ani baki ]aya a’a wasu surorine.Kuma idan mutum yayi tunani na irin wannan yana yi da Imam Hassan Al-askari ya samu kansa abune na juyayi dama kuka akai.

            Nan kuma wasu hadisai ne da aka ruwaito daga wajensa:Imam Hasan Al-askari[AS] yace; “Fushi shine mabu]in dukkan sharri”.A wani hadisi kuma yace; “Babu wata jarrabawa face akwai hikimar Allah dake kewaye da ita.Imam Hasan Al-askari[AS] yace; “Yana daga cikin tawadiu yin sallama ga dukkan wanda ka gitta ma,da kuma zama a  koma bayan majlisi” wato wajen zama. A wani hadisin kuma yana cewa; “Duk wanda ya yarda da zama a koma bayan majilisi to Allah da Mala’ikunsa baza su gushe suna yi masa salati ba har sai ya bar wajen”. A wani hadisi kuma da aka samo daga gare shi[AS] yace; “Ibada ba itace yawan Azumi da sallah ba,ibada itace yawaita tunani dangane da Allah ta’ala”.Haka nan kuma Imam Hasan Al-askari[AS]yace; “Wanda yafi mutane tsentseni shine wanda ya tsaya gun shubuhat,wanda yafi kowa gudun duniya shine wanda ya guje ma haram,wanda kuma yafi kowa mujahada shine wanda ya bar zunubi”. A wani hadisin kuma yana cewa; “Duk babban da ya bar gaskiya sai ya }as-}anta,duk }aramin da ya ]auki gaskiya sai ya ]aukaka.A wani hadisin kuma yana cewa; “Duk wanda ya hau kan }arya to zata saukar dashi gidan nadama”.Da dai sauran hadisai masu yawa da aka ruwaito daga wajensa.Wani tambihi anan shine Imam Hasan Al-askari[AS] shine Imamin da aka ruwaito hadisai ka]an daga wajensa,abun da ko ya janyo wannan shine dalilan da akayi bayani a baya wato na shamakance shi daga jama’a,da kuma sa ido gareshi ga duk masu muamala dashi,Kamar yadda kuma Imam Sadi}[AS] shine Imamin da aka samu hadisai a wajen sa fiye da ko wane Imami,akwai ma lokacin da yake cewa: “Ku tambayeni tun gabanin in bar duniya domin babu wani wanda zai baku hadisi a bayana kamar yadda nike baku shi a yanzu”.Tabbas ko haka abun ya kasance domin a bayansa ba a samu wani Imami ba  da ya samu yanayi na koyar da ulum na Ahlul baiti ba kamarsa.Wannan ke nan a ta}aice dangane da munasabar dake cikin wannan wata,wato na haihuwar Imam Hasan Al-askari[AS].

 
Copyright © 2025. www.tambihin.net. Designed by KH