Wednesday, 24 April 2024
Email
Make My Homepage
RSS
Register
Munasabobin watan Rabi’ul Awwal Print E-mail
Written by administrator   
Monday, 06 January 2014 21:20

 Watan Rabiul- Awwal shine wata na ukku a jerin lissafi na watannin musulunci goma sha biyu.Kuma wannan wata na Rabiul-Awwal wata ne mai albarka kuma mai gayar daraja kasantuwar a cikinsa ne aka haifi shugaban halittu baki ]aya wato Manzon Allah[SAAW].kuma abubuwan da suka faru a tarihi a watan Rabiul Awwal suna da yawa,ga wasu daga cikinsu.A daren 1 ga wannan wata ne Manzon Allah[SAAW] yayi hijira daga Makka zuwa Madina. Haka nan a wannan dare ne Imam Ali[AS] ya kwana a shinfi]ar Manzon Allah[SAAW] wato bayan fitar shi zuwa madina.A ranar jumma’a takwas ga wannan wata ne shekara ta 260 bayan hijira,wafatin Imam Hassan Al-askari[AS] wato mahaifin Imam Mahdi[AF]Dalilin wafatin nasa shine,guba da aka sa masa a abinci,wanda khalifan Abbasawa na lokacin da ake kira Mu’utamad,ya bada umarnin ayi haka.Kuma idan muka duba tarihin Aimma[AS] zamu ga cewa baki ]ayansu wato tun daga Imam Ali[AS] zuwa Imam Hasan al-askari[AS] daga wanda aka kashe da takobi kamar Imam Ali[AS] da kuma Imam Husain[AS] sai kuma wanda aka sama guba,kamar yadda  aka yi ma Imam Hassan[AS] da Imam Ali Zainul Abidin[AS] da kuma sauran Imamai[AS] da suka biyo baya har ya zuwa Imam Hassan al-askari[AS]Yama zo akan cewa Imam Mahdi[AS] idan ya bayyana ,bayan addini ya kafu a duniya baki daya,bayan wasu shekaru wanda an sassa~a kan adadin wa]annan shekarun,daga }arshe zai yi shahada ne.Wato kamar dai yadda yazo daga Imam Hassan[AS] yace, “Babu wani daga cikinmu[wato Aimma A.S] face wanda aka kashe,ko kuma aka sama guba.”Saboda haka Imam Hasan al-askari[AS] yayi shahada ne.Kuma A wannan rana ta jumma’a  takwas ga watan Rbiul-Awwal shekara ta 260 bayan hijira  imamanci ya dawo ga Imam Mahdi[AF] kuma tun lokacin har ya zuwa yau ]inmu duk acikin imamancinsa ake,shi yasa daga cikin la}ubbansa ana ce masa maabucin zamani.A ranar goma ga wannan wata na Rabiul Awwal auren Manzon Allah[SAAW] da kuma sayyida khadija.A ranar 12 ga watan Rabiul-Awwal Manzon Allah[SAAW] ya isa Madina wato bayan hijirarsa daga makka.A ranar 14 ga watan Rabiul-Awwal Yazidu[LA] ya mutu,lokacin hijira na da shekara 64,kuma ya mutu yana da shekaru 37 ne a duniya,ya kuma yi shekara ukku da wata tara ne akan mulki.To mu duba fa mu gani ‘yan shekarun da yayi a duniya,da kuma gajerin mulkin da yayi,wato in ka kwatanta da na babansa Mua’wiya wanda yayi shekaru 40 akan mulki,shekaru 20 yana gomna,shekaru 20 kuma yana wai khalifa.Cikin shekarunnan ukku da wata tara mu duba irin ~arna da zalunci da Yazidu yayi wanda a tarihi ba wai na wannan al’umma ta Manzon Allah ba,a’a a tarihin ]an Adam baki ]aya,babu wani wanda yayi irin wannan ~arna da zalunci kamar sa.Wannan ]an mulkin da yayi shekarar farko ya aukar da wa}i’ar karbala,shekara ta biyu ya aika da maya}a zuwa madina,wanda wa]annan maya}a nasa suka yi ~arna da zalunci da kuma keta darajar masallacin ManzonAllah kai har da ma }abarin Manzan Allah.shekaru ta ukku ya }ona ka’aba,.To amma abun mamaki a wannan zamani namu an samu wasu da suke }o}arin wanke Yazidu,wai ba shi yasa aka kashe Imam Husain ba, ibn Ziyad ne,to tambayoyi anan sune:Wane mataki ya ]auka kan ibn Ziyad ]in a matsayinsa na shugabansa? Kuma waye ya ba da umarnin akai hari a madina da makka bayan wa}i’ar karbala? Kuma kawukan wa]anda aka kashe a karbala daga }arshe ina aka kai su? Kuma mi ya faru da aka kai su?Saboda haka masu wa]annan maganganu na jahilci da ta’assubanci ga ‘yan shi’a, sai  su fara da  fitattun malaman Ahlus sunna irin su Ahmad ibn Hambal,ibn Jauziy,Suyu]i da dai sauransu wa]anda suka tabbatar da abubuwan da Yazidu yayi suka kuma tsine masa.wani abun dariya da yazo daga ibn Kasir kan wannan al’amari na kashe Imam Husain da kuma lokacin da aka kai kan Imamu Husaini gabansa,to wa}en da Yazidu yayi na cewa Bani Hashim sun wasa da mulki babu wani wahayi daya sauka ……..shine ibn kasir yake cewa wannan Magana in dai Yazidu ya fa]e ta to Allah ya tsine masa,in kuma wani ne ya }aga ya jingina masa to Allah ya tsine ma wanda ya jingina masa.Kai bama maganar tsinewa ba akwai malaman Ahlus sunna da suka kafirta yazidu,mutum ya duba littafin ibn Hajar mai suna Sawa’i}ul muhuri}a,zai ga ya kawo bayanin cewa ibn Jauziy ya kafirta shi.Akwai ma littafin da ibn Jauziy ya rubuta mai suna, “Arradi alal muta’assibil anid almani’i an la’ani yazid.”wato ma’ana Raddi ga mai tsatsauran ta’asubanci mai hana a tsine ma yazidu.Wani lokaci in shaAllah za a yi rubutu mai taken, “Yazidu a littafan Ahlus sunna.”Wanda za a kawo bayanai na malaman Ahlus sunna dangane da Yazidu.Saboda haka masu }o}arin su wanke Yazidu sai su ba da amsoshin wa]annan abebe da suka zo a littafansu dangane da Yazidu,kuma tun da suna tare da yazidu,kuma suna son sa har suna ba shi yardar Allah, to Allah ya ta  da su tare da Yazidun,ya kai  su makomar da  ya kai yazidu gobe }iyama.Mutum ya binciki tarihi zai ga a duniyance yadda }arshen Yazidu ya kasance,wanda hatta kabarinsa daga baya bola ya zama wato wajen zuba shara.Amma mu duba }abarin ]an yazidun mai suna Mu’awiya ]an yazidu  har yanzu kabarinsa na nan,mabiya Ahlul baiti suna ziyartar kabarin.domin matar Yazidu da kuma ]ansa mu’awiya abun mamaki ‘yan shi’a ne wato mabiya Ahlul bayt.shi yasa bayan mutuwar yazidu wannan ]a nasa mu’awiya shi ya gaje shi,amma kwanaki 40 yayi akan mulki ya sauka don }ashin kansa,bayan yayi wata hu]uba wadda a ciki ya nuna cewa wannan al’amari ba a gidansu yake ba,a bani Hashim ne.ya kuma soki kakansa  Mu’awiya ]an Abu sufyan na fa]a da yayi da Imam Ali,bayan haka ya bayyana cewa ya sauka daga khilafancin.Daga baya yazo a tarihi cewa wasu daga cikin bani umayya suka sa masa guba wadda tayi sanadiyyar  rasuwarsa,kamar dai yadda suka yima Umar ]an Abdul Aziz.

A ranar jumma’a 17 ga wannan wata na Rabiul Awwal haihuwar fiyayyen halitta wato Manzon Allah[S] wannan akan asasin madrasah ]in Ahlul bait[AS] amma a madrasah ta Ahlus sunnah sun tafi akan cewa ranar litinin 12 ga watan Rabiul Awwal.Har wala yau,a shigen wannan rana ta jumma’a 17 gareshi shekara ta 83 bayan hijira. aka haifi Imam Ja’afarus Sadik[AS] A madina,kuma daga wannan suna nasa mai albarka ake kiran mabiya Ahlul bayt[AS] a ta fuskacin mazhaba da ‘yan mazhabar Ja’afariyya.Imam Ja’afarus sadik[AS] yana da wasu abubuwan da ya ke~anta dasu in ka kwatanta da sauran Aimma na Ahlul bayt,misali ya rayu rayuwar mai tsawo domin duk Aimma 12 wato idan ka cire Imam Mahdi[AF],to Aimman da suka gabace shi da kuma wa]anda suka biyo bayansa,ya fisu tsawon rayuwar,saboda ya koma ga ta’ala yana da shekaru 65 a wata ruwayar 68.Haka nan kuma a lokacin Imamancin sane daular Bani umayya ta kife,daular Bani Abbas ta hau.Bayan haka kuma ya samu yanayi da kuma dama ta koyarwa fiye da sauran Aimma da suka zo bayansa.Domin a lokacin a madina kawai yana da masu ]aukar karatu a wajensa sama da mutum dubu hu]u wa]anda suke mabiya Ahlul bayt ban da wa]anda suke kan wasu mazhabobi ko A}idoji dabam dabam,idan mutum ya binciki tarihi zai ga cewa hatta Abu Hanifa da kuma Anas ]an malik wato shugaban mazhabar Hanafiyya da kuma malikiyya da dai wasu daga cikin fitattun malaman Ahlus sunna duk sun yi karatu a wajensa .A ranar 26 ga wannan wata na Rabiul Awwal shekara ta 41 bayan hijira sulhun Imam Hasan[AS] da Mu’awiya ya kasance.

Ayyukan da ake son aikatawa a cikin watan Rabiul Awwal:Ko wane wata daga cikin wa]annan watanni 12 na musulunci yana da ayyuka iri biyu,Ayyuka na “Amma” da kuma ayyuka na “khassa” Ayyuka na amma sune wanda suke ko wane wata ake maimaita su,mai son ganin irin wa]annan ayyuka na amma yana iya duba mafatihul jinan babi na biyu fasali na sha-]aya.Saboda haka ayyukan da za a kawo nan ayyuka na khassa ne wato sun ke~anta da watan Rabiul-Awwal.A ranar 12 ga watan rabiul Awwal akwai sallah raka’a biyu da ake son yi,a raka’a ta farko bayan fatiha mutum zai karanta }ulya ayyuhal kafirun sau ukku.A raka’a ta biyu kuma bayan fatiha }ulhullahu }afa ukku.A ranar 17 kuma ga watan Rabiul Awwal akwai ayyuka kamar haka:1-Wanka.2-Azumi.3-Ziyarar Manzon Allah[SAAW] daga kusa ko nesa.4-Ziyarar Imam Ali[AS]5- Sallah raka’a biyu a farkon yinin ko wace raka’a bayan fatiha mutum zai karanta Inna Anzalnahu 10 da kuma }ulhuwallahu 10.6-Biya wata addu’a mai mafatihu bai kawo taba,mutum na iya duba ta a Zadul Ma’ad na Allama majlisi ko kuma littafin I}bal na sayyid ibn [awus.7- Girmama wannan rana ta 17,da kuma yin kyaututtuka a cikin ta,da dai sauran ayyuka na alheri.Mai son ganin wa]annan ayyuka na khassa na watan Rabiul Awwal yana iya duba mafatihu  babi na biyu fasali na tara.

Wasu sashe na rayuwar Imam Sadi}[AS]

1-     Haihuwarsa:An haife shi ranar jumma’a 17 ga watan Rabiul Awwal shekara ta 83 bayan hijira.

2-     Nasabarsa:Mahaifinsa Imam Muhammad Al-bakir[AS]Mahaifiyarsa Fatimatu ‘yar {asim.

3-     Nash’a ]insa:Imam Sadi}[AS] ya tashi a madina ya rayu a madina ya kuma rasu a cikinta.

4-     La}ubbansa:Yana da la}ubba da yawa amma wanda yafi shahara shine Sadi},kuma ana yi masa kinaya da Abu Abdullah.

5-     Shekarunsa:Ya rayu shekaru 65 a duniya a wani }aulin ma 68.

6-     Muddan Imamancinsa:Shekaru 34.

7-     ‘Ya’yansa:Yana da ‘ya’ya 10.maza 7,mata 3.

8-     Wafatinsa:Ya rasu ranar 25 ga watan shawwal shekara ta 148 bayan Hijira.

9-     {abarinsa:Yana a madina ne a ma}abartar Ba}i’a.

Wasu sashe na rayuwar Imam Hassan al-askari[AS]

1-     Haihuwarsa:An haife shi a madina ranar litinin 8 ga watan Rabius Sani shekara ta 232.

2-     Nasabarsa:Mahaifinsa Imam Ali al-hadi[AS] sunan mahaifiyarsa Salil.

3-     Nash’a ]insa: An haife shi a madina,yana da shekaru 4 da watanni suka koma Ira}i shi da mahaifinsa,saboda haka a Ira}i ne yayi sauran rayuwarsa har yayi shahada.khalifan Abbasawa a lokacin mai suna Mutawakkil shi yayi sanadiyyar komawar tasu.wanda shi mutawakil malaman tarihi suna kwatanta shi da yazidu.domin a zamaninsa ya gallaza ma masu ziyarar Imam Husaini[AS] ta fuskoki dabam-dabam,domin a lokacinsa ne yasa dokar duk wanda aka kama ya ziyarci Imam Husain da a yanke masa hannu,in ya sake a yanke daya hannun,in ya sake a yanke masa }afa,haka yai tayi da yaga duk wannan matakin bai yi ba shine ya ]auki matakin shafe kabarin Imam Husain ta hanyar  abkar da ambaliya ta ruwa da gangan,ta Allah ba tashi ba shima wannan bai yi ba,a ta}aice dai a zamaninsa ya gallaza ma mabiya Ahlul bait ba ka]an ba.Daga }arshe ma ]ansa ne ya kashe shi saboda zagin da yake ma Imam Ali[AS] da kuma Sayyida Fatima[AS]. Imam Hassan al-askari[AS] ya rayu  tare  da mahaifinsa shekaru 22.

4-     La}ubbansa:yana da la}ubba masu yawa amma wanda yafi shahara shine al-askari.wannan la}abi ya samo asali ne daga unguwar da ya zauna da yake sansani ne na maya}a,a wannan zamani namu kamar ace barikin soja.

5-     Shekarunsa:Ya rayu a duniya shekaru 28.

6-     Muddan Imamancinsa:Shekaru shidda ne.

7-     ‘Ya’yansa:]a ]aya shine Imam Mahdi[AS]

8-     Wafatinsa: Ya rasu ranar Jumma’a 8 ga watan Rabiul Awwal shekara ta 260 bayan hijira.

9-     Kabarinsa:Yana a Samarra ne wato a }asar Ira} tare da na mahaifinsa Imam Ali al-hadi[AS].

 

 
Home Munasabobi Munasabobin watan Rabi’ul Awwal
Copyright © 2024. www.tambihin.net. Designed by KH