Bayani kan sallar khusufin rana ko wata |
Written by administrator | |||
Monday, 30 December 2013 04:36 | |||
A wannan darasi bayani zai gudana insha-Allah dai dai gwargwadon iko akan sallar ayoyi wato misali sallar khusufin wata ko rana.Saboda haka bayanai zasu kasance akan wa]annan ababe kamar haka: 1-Wa]anne Abubuwane suke sabbaba yin ta? 2- Hukuncin yin ta wajibine ko mustahabbi? 5- Yadda ake yin sallar khusufi:Yadda ake yin sallar khusufin wata ko rana shine,da farko dai sallar raka’a biyu ce ko wace raka’a ruku’u biyar mutum zai yi,wato raka’a biyun ke nan suna da ruku’u goma.kuma akwai hanyoyi biyu da ake yin wannan sallah:Hanya ta farko mai tsawo hanya ta biyu gajera.Ta farkon itace,bayan mutum yayi niyyar yin sallar khusufin sai yayi kabbarar harama,bayan haka sai ya karanta fatiha,bayan haka kuma sai ya karanta sura misali ya karanta }ul-huwallahu ko inna anzal-nahu idan ya kammala karatun surar sai yayi ruku’u,to bayan ya taso daga ruku’u ya mi}e tsaye ba sujuda zai wuce ba a’a zai sake karanta fatiha ne da sura,bayan ya kammala karatun surar sai ya sake yin ruku’u,bayan ya taso daga ruku’in sai ya sake karanta fatiha da sura bayan haka ya sake yin ruku’u,idan ya taso daga ruku’uin sai ya sake karanta fatiha da sura,bayan haka kuma ya sake yin ruku’u,idan ya taso daga ruku’in ya sake karanta fatiha da sura bayan haka kuma sai yayi ruku’u,to idan ya taso daga ruku’in to yanzu zai tafi ga sujuda ne,idan mutum ya lissafa wa]annan ruku’u a wannan raka’ar guda ]aya zai ga mutum yayi ruku’u biyar ke nan.To bayan mutum ya kammala sujuda biyu sai ya mi}e tsaye wato zuwa raka’a ta biyu ya sake karanta fatiha da sura,bayan haka sai yayi ruku’u,to shigen haka zai yi kamar yadda yayi a raka’ar farko,bayan yayi ruku’u na biyar sai tafi ga sujuda bayan ya kammala sujuda guda biyu sai yayi tashahhud wato tahiya bayan ya kammala sai yayi sallama,shi ke nan ya gama.
Hanya ta biyu na yadda ake sallar khusufi shine,maimakon mutum ya karanta fatiha da sura a ko wane ]agowa daga ruku’u to sai ya karanta sura ]aya a kowace raka’a ta hanyar kakkasa surar misali:bayan yayi niyyar yin sallar khusufi sai yayi kabbarar harama bayan haka sai ya karanta fatiha,bayan fatiha misali sai ya ]auki suratul-}adr wato inna anzal nahu akan ita zai karanta,saboda haka bayan fatiha sai ya karanta aya ]aya,sai ya tafi ruku’u,bayan ya ]ago daga rukun sai ya sake karanta aya,wani tambihi anan shine ba zai karanta fatiha ba, haka nan a ]agowa ruku’i na ukku da na hu]u da na biyar,wato dai duka ba zai karanta fatiha ba zai wadatu da wadda yayi tun farko.bayan ya taso a ruku’u na biyar sai ya tafi sujuda,bayan ya taso daga sujuda biyu ya mi}e tsaye sai ya karanci fatiha bayan haka sai yayi shigen yadda yayi a raka’ar farko da surar da ya karanta ko wata sura ta dabam,bayan ya ]ago a ruku’u na biyar sai ya wuce sujuda,idan ya kammala sujuda biyu sai yayi tashahud yayi sallama.idan aka lura a wannan mutum ya karanta fatiha biyu da kuma sura biyu sa~anin waccan hanya ta farko da aka soma bayani wanda a cikin ta mutum zai karanta fatiha }afa goma da kuma sura goma.Wata mas’ala kuma itace a irin wannan sallah yaya mutum zai yi }unuti a cikinsu,to a nan akwai zantuka ukku wato kamar yadda Imam khumaini yayi bayani a cikin littafin Tahrirul-wasila,zance na farko shine yayi }unuti gabanin ruku’insa na 2 da na 4 da na 6 da na 8 da kuma na 10. Idan muka duba a wannan zance zamu ga mutum zai yi }unuti biyar ke nan.zan ce na biyu kuma shine cewa zai yi }unuti biyu ne na farko gabanin ruku’u na biyar,na biyu kuma gabanin ruku’u na goma.zan ce na ukku shine yin }unuti ]aya wato yayi shi gabanin zuwa ruku’u na goma.To a nan duk wanda mutum yayi cikin ]ayan ukkun nan yayi.kuma shi }unutin a matsayin mustahabbi yake,saboda haka da zai kasance bai yi }unutin ba sallar shi tayi.amma fa ya rasa ladar wannan mustahabbi.
6- Za a iya yin ta a jama’a wato jam’i:Yazo akan cewa mustahabbi nema ayi ta a jama’a,saboda haka idan a cikin jam’i yayi to anan liman zai ]auke masa karatu wato na fatiha da sura amma ban da sauran ayyuka wato kamar tasbihi cikin ruku’u da sujuda ko kuma }unuti.ke nan a sallar khusufi mutum na da za~i ko yayi shi ka]ai ko kuma yayi ta cikin jam’i ko da ko shi da iyalinsa ne.
|