Saturday, 02 December 2023
Email
Make My Homepage
RSS
Register
Munasabobin watan Safar Print E-mail
Written by administrator   
Tuesday, 10 December 2013 04:58

 Watan safar shine wata na biyu a jerin }idaya na watannin musulunci goma sha-biyu.Kuma wannan fili na munasabobi flili ne da yake bayanin muhimman abubuwan da suka auku a tarihi na watan da ake bayani akai,ko kuma wasu ayyuka da ake son aikatawa a cikin watan da dai sauransu.Wannan wata na safar wata ne wanda yake musibobi da balao’i  kan yawaita sauka a cikinsa,dalilin haka ko kamar yadda Allama Majlisi wato marubucin littafin Biharul-Anwar,yake cewa  a wani littafi na sa mai suna Zadul-Ma’ad,ta yiyu dalilin haka ya kasance ta fuskoki guda biyu.Na farko kasantuwar a cikin watan ne wafatin fiyayyen halitta Manzon Allah[SAAW].Na biyu:Kasantuwar  shi wannan wata na safar yana biye da watanni masu alfarma guda ukku  wato Zul-}ada,Zul-hajj da kuma watan Muharram  wa]anda aka haramta ya}i a cikin su,wato yanzu ke  nan kamar }ofar ya}i ta bu]e.Amma akwai addu’a ta neman tsari daga dukkan musibun da kan sauka a cikin watan safar,ga mai bu}atar  ganin wannan addu’a yana iya duba littafin mafatihul-Jinan,babi na biyu fasali na takwas,ita wannan addu’a kamar yadda bayanin ta yazo shine ana son biyata sau goma ko wace rana,wato tun daga farkon watan ke  nan har ya zuwa }arshensa.Haka nan baya ga wannan addu’a akwai wata ita ma ta neman tsarine daga saukar musibobi da bala’oi,ita addu’ar tana sashen Ba}iyatus-salihat,a babi na biyar,to a babin sai mutum ya duba munajati na is-tiaza,wato cikin munajatin nan goma da aka samo daga Imam Jawad[AS].A ta}aice dai wannan wata na safar wata ne da ake son mutum ya yawaita addu’oi na neman tsari a cikinsa.

            Wasu ayyukan da ake son aikatawa a cikin wannan wata na safar.Kamar yadda yazo a littafai musamman na Addu’oi,cewa ko wane wata yana da ayyuka kala biyu,akwai ayyuka na  “Am” akwai kuma ayyuka na “khas” Ayyuka na am sune ayyukan da ake son aikata su a ko wane wata cikin wa]annan watanni 12 na musulunci.Saboda haka akwai wasu ayyuka na ibadodi wa]anda ana son mutum ya maimaita su ko wane wata,irin wa]annan ayyuka ana ce masu ayyuka na shahariyya wato na wata-wata.Ayyuka na ibadodi kamar 1-Sallah.2-Addu’a.3-Azumi.4-Karatun wasu surori na Al-}ur’ani..Ga bayanin su 1-Sallah: Ana son daren farko na ko wane wata idan ya kama,mutum yayi sallah raka’a biyu,ko wace raka’a bayan fatiha mutum zai biya suratul-An’am,ko da ma bai haddace ta  ba yana iya biya ta  da Al-}ur’ani.Haka nan kuma a ranar farko na ko wane wata shima mutum zai yi sallah raka,a biyu,raka’ar farko bayan fatiha mutum zai biya {ul-huwallahu 30,raka’a ta biyu bayan fatiha mutum zai biya Inna-anzal-nahu 30,bayan ya sallame akwai wata addu’a da zai biya,ga mai bu}atar ganin wannan addu’a da wa]annan salloli da aka ambata ya duba littafin Mafatihul-jinan Babi na biyu fasali na 11.To idan mutum yayi wannan sallar ta daren farkon da kuma ranar farkon ba zai sake maimaitata ba sai kuma wani sabon watan,misali ace yayi ta watan safar to yanzu kuma sai daren farko da ranar farko na watan Rabi’ul-Awwal  zai sake yinta,bayan haka sai wata na gaba har dai shekara ta zagayo,ya kuma sake maimaita haka.2-Addu’a:Akwai addu’oi da aka  ruwaito daga Imam Ali[AS]wanda ake son biyawa tun daga 1 ga wata har ya zuwa 30 ga wata,ga mai son ganin wa]annan addu’oi  yana iya duba littafin Dhi-yaus-salihin,shafi na 380.Saboda haka ana son mutum ya kasance ko wace rana ya biya addu’ar ranar,wato dai tun daga farkon watan har }arshensa,ta yadda dai ko da ace mutum bai samu biya ta jiya ba to sai ya biya ta,bayan haka kuma sai ya biya ta ranar.Haka nan baya ga wannan addu’a,akwai kuma wata addu’a da ake son biyawa a daren farko na ko wane wata,wannan addu’ar ana ce mata addu’ar ganin sabon wata,ita ma mutum na iya duba ta a Dhiyaus-salihin shafi na378.3-Azumi: Ana son yin azumi na wata-wata guda ukku,yadda ake yin wannan azumin ko shine mutum zai azumci alhamis ta farkon goman farko na wata da kuma larabar farko ta goma na biyu,da kuma alhamis ]in }arshe ta goman }arshe na wata. Ko kuma azumin ranakun 13,14,15 na ko wane wata.ko mutum ya ]auki guda biyun ya lizimci aikata su, ko kuma ya lizimci ]aya daga ciki,dukkansu dai sun zo a ruwayoyi na hadisai.Amma na farkon shine wanda Manzon Allah[SAAW] ya bar duniya akai.4-Karatun wasu surorin Al-}ur’ani,akwai wasu surori da ake son karanta su ko wane wata sune: Suratul-A’araf,Suratul-Anfal,Suratu-Tauba,Suratu-Yunus da kuma Suratu-Nahal.Sai dai a lura in son samu ne ya kasance karanta wa]annan surori ya zamanto bai da Ala}a da saukar Al kur’ani da mutum yake a cikin kwanukan wata.wato ma’ana ya karanta surorin dabam.Wannan ke  nan bayani a ta}aice na bayanin ayyukan wata na  “Am” sai kuma ayyukan wata na khas:Sune ayyukan da wata ya ke~anta da su.A wannan wata na safar ayyukan da suke cikinsa sune:Akwai wata sallah da ake son yi a ranar 3 ga wata,ga mai bu}atar ganin yadda ake sallar yana iya duba mafatihul-jinan Babi na biyu fasali na 8.Haka nan kuma daga cikin ayyukan watan Safar akwai Ziyarar 40 ta Imam Husain[AS] wadda wannan shine babban aiki da ke cikin wannan watan.Ranar 40 ]in shahadar Imam Husaini[AS] rana  ce wadda take da muhimmanci musamman ga mabiya Ahlul-bayt[AS] Yama zo a hadisi cewa ziyarar Imam Husaini[AS] a ranar daga kusa ko nesa yana daga cikin Alamomin mumini,wato kamar yadda aka ruwaito daga Imam Hassan Al-askari[AS] yace: “Alamomin mu’umini[wato ]an shi’a]guda biyar ne.1-Yin sallah raka’a 51 ko wace rana.2-Ziyarar 40 na Imam Husain[AS].3-Sa zobe a hannun dama.4-Sa goshi a }asa wato ta’afir.5-Bayyana karatun basmala a sallah wato bisimillahi.To ita wannan ziyara ta 40,imma ta kasance daga kusane ko nesa.abin da ake nufi daga kusa shine idan mutum yana da dama da kuma ikon zuwa karbala to haka aka fi so.in kuma mutum bai da wannan damar da ikon sai yayi ziyarar daga nesa,wato daga garin da yake.Ga mai bu}atar ganin yadda ake wannan ziyara ta 40,yana iya duba littafin mafatihul-jinan Babi na ukku fasali na bakwai,mutum zai ga ziyarar can wajen }arshen fasalin.

            Sai kuma wasu abubuwa na tarihi da suka auku a cikin watan,a ]aya ga watan ne a fa]in wasu malamai aka isa da kan Imam Husain[AS] Dimash}a wato shekara ta 61 bayan hijira.Haka nan kuma a ]aya ga watan safar shekara ta 37 bayan hijira aka fara ya}in Siffin.Haka nan kuma a ]aya ga watan ne shekara ta 121 bayan hijira Zaid ]an Imam Zainul-Abidin[AS] yayi shahada.A bakwai ga watan safar shekara ta 50 bayan hijira shahadar Imam Hassan[AS] amma a wata ruwaya 28 ne.Har wala yau a bakwai ga watan safar shekara ta 128 bayan hijira aka haifi Imam Kazim[AS].Saboda haka a wannan rana ta bakwai ga watan safar munasabar  wilada da wafati na Aimma[AS] sun ha]u.Ranar 20 ga watan safar itace ranar cikar Imam Husain kwanaki 40 da shahadarsa.Haka nan a wannan rana ta 20 itace ranar da sahabin Manzon Allah[SAAW] mai suna Jabir ]an Abdullahi Al-ansariy[RA] ya ziyarci Imam Husai[AS] a karbala,shine farkon wanda ya fara ziyararsa,kuma wannan sahabi Allah ta’ala yayi masa yawancin rai har zuwa zamanin Imam Bakir[AS]. daman Manzon Allah[SAAW] ya barmar wasiyyar cewa ya isar da sallamar shi ga Imam Bakir[AS] ikon Allah kuma yaga Imam Bakir[AS] ya kuma isar da wannan sallama gareshi.Haka nan dai a wannan rana ta 20 ga watan safar a wata ruwaya su sayyida Zainab[AS] suka isa madina wato bayan tasowar su daga Sham.Saboda haka ta wata fuska rana ce ta juyayi da  bakin-ciki dama kuka,domin mutum yayi tunani su sayyida zainab[AS] sun bar madina da Imam Husain da  su wane da wane amma yau gashi sun dawo madina ba tare dasu ba wato duk an karkashe su a karbala,shi yasa yazo akan cewa da  su Zainab[AS] suka iso madina in da ta fara zuwa shine masallacin Manzon Allah[SAAW] tana zuwa ta dafa kofar masallacin ta face da kuka tace, “ Ya kakana ina mi}a maka ta’aziyyar ]an uwana Husain.”mu duba fa mu gani wa]annan mataye bayin Allah kowa daga cikinsu ya koma gida ba na shi,wato babu wanda ba’a kashe masa nasa ba,a wasu ruwayoyi yazo akan cewa hatta gidajensu bayan wa}i’ar karbala Yazidu[LA] ya bada umarnin a rusa su.Yazo akan cewa abubuwan da suka auku a karbala samun cikakken bayani na wasu abubuwa sai idan Imam Mahdi[AS] ya bayyana za a ji su.Haka nan a 28 ga wannan wata na safar  ranar Litinin shekara ta 11 bayan hijira,wafatin shugaban halittu baki ]aya kuma cikamakin Annabawa Manzon Allah[SAAW].Haka nan kuma a ranar }arshe na wannan wata na safar ne shahadar Imam Rida[AS]shekara ta 203 bayan hijira,Amma a ruwayar da tafi shahara itace cewa shahadarsa ta kasance 23 ga watan Zul-}ada ne.

            Wasu sashe na rayuwar Imam Hassan[AS]

1-      Haihuwarsa: An haife shi ranar talata 15 ga watan Ramadan,shekara ta 3 bayan hijira.

2-      Nasabarsa:Mahaifinsa Imam Ali[AS] mahaifiyarsa Sayyida Fatima[AS]kakansa ta wajen mahaifiya Manzon Allah[SAAW].kakansa ta wajen mahaifi Abu Dalib.kakarsa ta wajen mahaifiya Sayyida Khadija.kakarsa ta wajen mahaifi Fadimatu ‘yar Asad.

3-      Nash’a ]insa:Imam Hassan[AS]kamar yadda aka haife shi a madina anan ya rayu kuma ya rasu,face kusan shekaru shidda da yayi a kufa,lokacin da Imam Ali[AS] yana zaune a kufa.Bayan shahadar Imam Ali[AS] da wata shidda Imam Hassan[AS] ya bar kufa ya dawo madina.Ya rayu tare da kakansa wato Manzon Allah[SAAW] shekaru bakwai da watanni.Ya rayu tare da Mahaifinsa Imam Ali[AS] shekaru 37.Bayan shahadar Imam Ali[AS] ya rayu shekaru 10.Imam Hassan[AS] ya halarci duk ya}o}in da Imam Ali[AS] yayi wato ya}in Jamal,siffin da kuma ya}in Nahrawan.

4-      La}ubbansa: Yana da la}ubba masu yawa amma wanda yafi fice shine  “Assib]i” kuma anai masa kinaya da Abu Muhammad wannan kinaya yazo akan cewa Manzon Allah ne yasa masa ita.

5-      Shekarunsa: Imam Hassan[AS] ya rayu a duniya shekaru 47.

6-      Muddan Imamancinsa: Shekaru 10 ne.

7-      ‘Ya’yansa:Imam Hassan[AS] yana ‘ya’ya 15,maza 8,mata 7.

8-      Wafatinsa: Imam Hassan[AS] ya rasu ranar Alhamis 7 ga watan safar a wata ruwaya kuma 28,shekara ta 50 bayan hijira.

9-      Kabarinsa: Yana madina ne a Ba}i’a,kusa da kabarin kakarsa Fatima ‘yar Asad wato mahaifiyar Imam Ali[AS].

Wasu sashe na rayuwar fiyayyen halitta Manzon Allah[SAAW]

1-      Haihuwarsa: An haifi  Manzon Allah[SAAW] a makka ranar jumma’a 17 ga watan Rabi’ul Awwal,amma a ruwaya ta Ahlus-sunna ranar litinin 12 ga watan Rabi’ul Awwal, a shekarar da aka fi sani da shekarar giwaye

2-      Nasabars:Mahaifiyarsa,Aminatu ‘yar Wahab.Mahaifinsa Abdullahi ]an Abdul-Mu]allib.

3-      Nash’a ]insa:Manzon Allah ya tashi a  makka,ya rayu a makka shekaru 53,wato kafin ya koma madina,bayan ya koma madina ya rayu a cikinta shekaru 10.Saboda haka Manzon Allah[SAAW] ya rayu a wa]annan garuruwa biyu wato makka da madina.

4-      La}ubbansa: Manzon Allah yana da sunaye da la}ubba da kinaya  masu yawa fiye da kowane ]an Adam.Amma kinayarsa da tafi shahara itace Abul-{asim.

5-      Shekarunsa:Manzon Allah ya rayu shekaru 63 ne a duniya.

6-      Muddan manzancinsa: shekaru 23 ne.

7-      ‘Ya’yansa: Akwai sa~anin ruwayoyi akai tsakanin Malaman sunna da shi’a akai,amma abinda yafi shahara shine cewa yana da ‘ya’ya bakwai maza 3,mata 4.

8-      Wafatinsa: Manzon Allah[SAAW] ya rasu ranar litinin 28 ga watan safar,amma a ruwaya ta Ahlus sunna sun tafi akan cewa  22 ga watan Rabi’ul Awwal.shekara ta 11 bayan hijira.

9-      Kabarinsa:Yana madina ne wato a cikin masallacinsa.

 
Home Munasabobi Munasabobin watan Safar
Copyright © 2023. www.tambihin.net. Designed by KH