Saturday, 02 December 2023
Email
Make My Homepage
RSS
Register
ASALIN SHI’A DA ABUBUWAN DA AKA JINGINA MATA. Print E-mail
Written by administrator   
Sunday, 20 October 2013 11:43

 Asalin kafuwar shi’a da abubuwan da aka jingina mata yana ]aya daga cikin ababen da Malamai dabam-dabam na shi’a,suka yi rubuce-rubuce da bayanai dabam-dabam akai,saboda haka akwai littafai masu yawa a wannan fagen.Da yake ]aya daga cikin hanyoyin da ma}iya Shi’a suka dunga bi duk tsawon Tarihi na wannan al-umma,shine }ir}irar }aryaryaki da jingina su ga ‘yan shi’a da nufin su bi ce hasken Ahlul-bait[AS]da kuma shafa masu ba}in fenti wanda haka zai sa gaba da }iyayya garesu,domin haka ya ba da dama da kuma ya nayi na zubar da jinanansu da kuma ~ata dukiyoyinsu.Mutum ya binciki Tarihi zai ga haka,kuma ko da ma mutum bai binciki Tarihi ba,To ya dubi wannan zamani da yake ciki,zai ga abubuwa dabam-dabam na cutarwa da musgunawa da ake fuskantar dasu ga mabiya Ahlul-bait,a kuma sassan duniya dabam-dabam.Kasantuwar sabon salon da ma}iya suka fito dashi yanzu na amfani da wa]ansu da sunan cewa su wai ‘yan shi’a ne,su na amfani da abubuwan da aka }ir}ira aka jingina ma ‘yan shi’a,suna tabbatar dasu da bakunansu da kuma ayyukan su,suna yin haka ne kasantuwar yadda suka ga fahimta ta Ahlul-bayt[AS] tana da]a ya]uwa da kuma ci gaba a sassan duniya dabam-dabam.Saboda haka masu wannan aiki suna iya bada }o}ari da himma suga ina zasu kai,amma abun da muke da ya}ini dashi,shine cewa suna ~ata lokaci ne kuma ba zasu yi nasara ba,domin wannan zamani da muke ciki ko }arni da muke ciki zamanine ko }arni na Ahlul-bayt.Yazo akan cewa daga cikin alamomin bayyanar Imam Mahdi[AF] kafin bayyanar sa fahimta ta Ahlul-bayt[AS] zata watsu a bayan }asa.Kuma mu duba muyi tunani yau sama da shekara dubu da ]ari hu]u ana fa]a da shi’a, amma an kasa kau da ita da mabiyanta,to idan fa]a da ita alokacin da ba a yayinta, ba a iya kau da ita ba,to ina ga fa]a da ita lokacin da ake yayin ta,shi yasa a wannan zamanin idan ka kaga mutum na fa]a da shi’a to ka tausaya masa.Kuma mutum ya binciki Tarihi ya gani yaya }arshen masu fa]a da ita yake kasancewa,suna kyakkyawan }arshe ko mummunan }arshe ne,kuma mi yake samun su tun anan duniya.in ma baka san na tarihi ba to ka duba na zamanin ka,mi ya same su kuma ya }arshen su ya kasance.in mutum ya bincika ko ya duba zai ga yadda Allah ma]aukaki yayi dasu tun ma anan duniya kafin ranar }iyama.wannan darasi ne babba ga masu tunani da kuma tsokaci.Bayan wannan shinfi]a wannan rubutu Insha-Allah zai gudana kan wa]annan ababe sune.

1-      Asalin kafuwar shi’a.

2-      Abubuwan da aka jingina ma shi’a.

3-      Jarabawowi da ‘yan shi’a suka fuskanta kuma suke fuskanta tsawon Tarihi.

4-      Siffofi da ]abi’u na ‘yan shi’a.

5-      Nasiha ga masu fa]a da }iyayya da shi’a

1-      Asalin kafuwar shi’a:Wannan wani abune da aka samu sa~ani tsakanin Malaman shi’a da Malaman sunnah akai,Malaman shi’a sun tafi akan cewa shi’a ta kafune tun lokacin Manzon Allah[S]kamar yadda zamu ga haka nan gaba a cikin wannan rubutu tare kuma da hujjar haka a littaffan Ahlus-sunna.Amma su kuma Malaman sunna sun ce ta kafune bayan rasuwar Manzon Allah[S]Bayan haka kuma suka sa~a a tsakaninsu kan lokacin da ta kafu ]in.Ga zantuka 4 da suka yi akan haka.1-Shi’a ta kafune a lokacin al-amarin sa}ifa.wato lokacin da wasu daga cikin sahabbai suka ha]u a sa}ifa da nufin za~en khalifa,bayan da suka gama aka samu wasu daga cikin sahabbai suka }i yin Bai’a ga khalifan da aka za~a,suka tsaya }yam akan cewa lalle khalifan cin Manzon Allah na Imam Ali ne,kasantuwar tun Manzon Allah yana duniya ya bayyana Imam Ali a matsayin khalifa a bayansa,ya bayyana haka Rasmiyyan wato officiarly a ranar Ghadir khum.2-Shi’a ta kafune a lokacin ya}in Jamal.Wato ya}in da akayi tsakanin Imam Ali da kuma sashen wasu daga cikin sahabbai }ar}ashin jagorancin Aisha matar Manzon Allah[S]. To wai anan aka samu  kafuwar shi’a.wato wadanda suka kasance tare da Imam Ali[AS]3-Shi’a ta kafune a lokacin ya}in Siffin.wato ya}in da akayi tsakanin Imam Ali da kuma Mu’awiya.To shima wai anan aka samu kafuwar shi’a wato wa]anda suka kasance tare da Imam Ali.4-Shi’a ta kafune bayan wa}i’ar Karbala.A ta}aice dai wa]annan lokuta guda hu]u,wato lokacin sa}ifa,lokacin ya}in Jamal,lokacin ya}in Siffin da kuma lokacin bayan wa}i’ar karbala,ba sune lokacin asalin kafuwar shi’a ba,face dai ace lokutane da suka taimaka wajen ya]uwar shi’a,da kuma fitar da matsayar su a fili.Domin idan muka duba ma’anar shi’a a is]ilahance ba a luggace ba,kamar yadda malamai na shi’a da sunna suka yi bayani, ma’anarta na nufin wa]anda suka bi Imam Ali suka taimaka masa,suka kuma ]auke shi a matsayin cewa shine khalifa bayan Manzon Allah mubasharatan.Wa]annan sune fitattun zantukan Malaman Ahlus-sunna  kan Asalin kafuwar shi’a,Amma akwai wa]ansu zantuka ]in sai dai basu kai wa]annan shahara ba.To yanzu bari muyi dubi a asalin kafuwar shi’a,a wajen su ‘yan shi’ar.Kamar yadda aka ambata a baya cewa asalin shi’a ta kafune tun lokacin Manzon Allah,kai hatta wannan kalma ta shi’a,daga wajen Manzon Allah[S] aka ji,kuma Al-hamdu lillah za a iya tabbatar da haka a littafan Ahlus-sunna ba wai na shi’a ba.Ga wasu daga cikin littafan.1-[abari cikin tafsirinsa mai suna Jami’ul- Bayan,yace:Ibn Humaid ya gaya mana daga Abu al-jarud daga Muhammad ]an Ali cewa,yayin da aka karanta wannan ayata, “Lalle wa]anda suka yi imani,kuma suka aikata ayyukan }warai,wa]annan sune mafifita alherin halitta.[suratul bayyina ayata 7] Sai Annabi[S] yace wa Ali, “Kai ne ya Ali da ‘yan shi’anka.” 2-Ibn Asakir ya ruwaito daga Jabir ]an Abdullahi al-ansari[RA] cewa: mun kasance wajen Manzon Allah[S]sai Ali yazo, sai Manzon Allah[S] yace, “Na rantse da wanda raina yake hannun sa,wannan[ya nuna Ali] da ‘yan shi’arsa sune masu samun rabo ranar }iyamah,sai kuma ya karanto wannan aya ta suratul Bayyina.”wato wadda aka kawo asama.3-Al-shabalanji cikin littafinsa Nurul-Absar,lokacin da yake Magana kan matsayin Imam Ali,ya kawo wani Hadisi daga ]an Abbas dake cewa, “Lokacin da aka saukar da ayar,lalle ne wa]anda suka yi imani,kuma suka aikata ayyukan }warai,wa]annan sune mafifita alherin halitta.Manzon Allah ya gaya wa Ali cewa:Kai da shi’arka zaku zo ranar }iyama kuna yardaddu.”4-Ibn Hajar al-Haisami cikin littafinsa Al-sawa’i}al-muhri}a,yace: “Ibn Abbas na cewa,lokacin da aka saukar da wannan aya wato ta suratul bayyina,Manzon Allah yace wa Ali:Kai da Shi’arka zaku zo ranar }iyama kuna yardaddu…..har daga }arshe ma shi Ibn Hajar yana cewa wannan Hadisi ingantacce ne.5- Haka nan Suyu]i shima ya fitar da haka a cikin Tafsirinsa na Durrun-Mansur.A ta}aice dai akwai malaman Ahlus sunna masu yawa da suka ruwaito wannan bayani kan wannan aya ta suratul bayyina,wannan ne ma yasa a tun lokacin Manzon Allah[S] ake kiran wasu daga cikin Sahabban Manzon Allah da sunan ‘yan Shi’ar Ali.Ga sunayen wasu daga cikinsu.Ammar ibn Yasir[RA]Salman Al farisi[RA]Abu zarr al-gifari[RA] Mikdad ibn Aswad[RA] Huzaifa ibn Yaman[RA] Abu ayyub al-ansari[RA]Bilal al-Habashi[RA] Jabir ibn Abdullahi al-ansari.[RA] Da dai sauran wasu sahabbai wanda ba za a iya kawo sunayensu duka ba saboda gudun tsawaitawa.Daga abubuwan da aka kawo cikin wa]annan littafai na malaman Ahlus sunna,ya nuna cewa shi’a ta kasance tun lokacin Manzon Allah ne,ba kamar yadda malaman  sunna ]in suka ce ta kasance ne bayan rasuwar Manzon Allah.

2-      Abubuwan da aka jingina ma ‘yan Shi’a:Akwai ababe da yawa da aka }ir}ira aka jingina ma ‘yan shi’a da nufin ~ata sunan su ko kuma da nufin sa }iyayyarsu a zukatan sauran musulmi,ko kuma da nufin samun kafa ta zubar da jinanansu da kuma ~ata dukiyoyin su,da kuma babbar manufarsu wadda itace hana mutane fahimtar Ahlul Bayt[AS] da bice haskensu..Wa]annan }age-}age sun yo asali tun lokacin daular Bani Umayya ne,kuma duk wanda yasan Tarihin Bani umayya,ya san cewa sun ginu kan }iyayya da Ahlul Bayt.Saboda haka wasu }aryayakin anyi yayinsu a Tarihi sun mutu,wasu kuma sun wanzu har yanzu,Ga misalan wasu daga ciki,wanda har yanzu ana yawo dasu.1-Wai yan shi’a suna da wani Al-}ur’ani sa~anin wanda yake hannun musulmi, wanda ga mai hankali da tunani in mutumin da,an fa]a masa ya yarda to mutumin wannan zamanin bai kamata ace ya yarda ba,saboda yadda duniya ta zama tamkar }auye ]aya kuma kayyakin sadarwa da na bincike ga sunan birjik,saboda haka cikin sau}i mutum zai iya bincikawa ya gano abin da ake fa]i ga ‘yan shi’ar nan haka ne? Makamancin haka ya ta~a ha]a ni da wani musulmi ]an wata }ungiya,muna tattaunawa kan irin wa]annan abubuwa da aka jingina ma shi’a,sai yace ai ‘yan shi’a suna da wani Al-}ur’ani,sai nace masa ba gaskiya bane.sai yace man haka abin yake,a ciki ma akwai wata sura wai suratul-Wilaya.To a lokacin akwai Alkur’ani tare da ni kuma bugun Iran.Sai na mi}a masa,nace ya duba bugun ina ne? ya duba yace man bugun Iran.Sai na ce ya nuna man suratul Wilaya a ciki.Ya duba,ya duba,jerin surorin.ya bu]e shafuffukan Alkur’anin,ni dai ina kallonsa.Sai can bayan ]an lokaci sai ya mi}o man Alkur’anin yace bai gani ba.Amma abun mamaki duk da haka yace an ce suna da suratul wilaya.Sai na ce masa ai gashi kai baka gani ba.Ka ce ne ance.Masu yawo da irin wa]annan }ir}irarrun abubuwa da aka jingina ma shi’a,da zasu yi abu ]aya da sun samu waraka daga wannan guba da aka zuba cikin }wa}walensu,shine su dun ga duba littafan ‘yan shi’a,kan abun da aka jin gina masu,suga su mi suka ce kan abun.misali na wannan Magana na wai suna da wani Alkur’ani.Malaman Shi’a magabata da na yanzu duk sun yi rubuce-rubuce da bayanai akai,misali daga malamai magabata akwai Shaikh Sadu} wanda ya rasu a shekara ta 381 bayan Hijira,ga abin da yake cewa kan wannan abu,a littafinsa mai suna A}a’idu- shi’a, “Iiti}adin da muke dashi dangane da Alkur’ani,wanda Allah ya saukar ga Annabinsa Muhammad,shine wanda yake hannun mutane,ba ragi ba }ari,duk wanda ya jingina mana wani abu ba haka ba,to ma}aryacine.”A kuma malamai na wannan zamanin mutum na iya duba littafin A}a’idul-Imamiyya na sheikh Muzaffar.kuma mai irin wannan tunani ko fahimta ya zai yi da fa]in Allah ma]aukaki da yake cewa, “Lalle mu muka saukar da Ambato wato Alkur’ani  kuma mune masu kare shi.”An ya idan mutum ya fahimci ma’anar wannan aya zai iya yarda da cewa wai wasu suna da wani Alkur’ani.kuma tabbas masu irin wannan fahimtar da akwai shi ]in,to da duk hanyar da zasu bi domin su same shi,da sun bi don su same shi,musamman ma saboda su buga shi su ya]a, kuma an sha yi masu kira akan haka,cewa ina yake mu ma muna so mu ganshi.2-Daga cikin abubuwan da aka jinginawa ‘yan shi’a akwai cewa,Wai ‘yan shi’a suna da I’iti}adin Mala’ika Jibril yayi kuskure,wai lokacin da Allah ta’ala ya bashi sa}o zuwa ga Imam Ali sai yayi kuskure ya ba ma Annabi  Muhammad,mu duba irin wannan }arya tsagwaronta.ko da yake masu ya]a irin wa]annan ababe basu ]auki yima ]an shi’a }arya ba abakin kome,akwai ma wani da yake ce man ya ta~a jin wani wai malami daga cikin masu yawo da wa]annan }aryaryakin,yana cewa kayi }arya ga ]an shi’a domin a}ishi ya halatta,har yana cewa wai wannan hadisi ne daga Manzon Allah.kuma wannan }arya da suke fa]i na kuskuren mala’ika,to a hankalce mutum ya tambayi kansa,ko da mutum ]an’uwansa ba wai mala’ika ba wanda yake ma’asumi,sai ka bashi sa}o ya kai ma ]an shekara 10,amma da yaje sai ya kasa ban-bance shi da ]an shekara 40,maimakon yaba ]an shekara 10 sai yaba ]an shekara 40.kuma ya ci gaba da yin wannan kuskuren har tsawon shekaru 23,duk bai gane kuskure yake yi ba.Wannan kenan ga ]an Adam fa,to ina ga abin da yake sa}o ne daga masanin gaibi kuma mahallicin kowa da komi,kuma ta hanyar mala’ikansa,zuwa ga fiyayyen halitta baki ]aya? Ai ya kamata mutum ya auna da hankalinsa,ballantana kuma  abune sananne a nassin Alkur’ani cewa Mala’iku ma’asumai ne,wato basu kuskure,basu mantuwa,basa kuma sa~a ma Allah Ta’ala kan  abun da ya umarce su.3-Daga cikin abubuwan da aka jingina ma ‘yan shi’a,akwai cewa wai suna zagin sahabbai:Wannan abu yana da ban mamaki,akwai wani ]an’uwana na jini ya ta~a tambayata kan wannan abu,wai da gaske ne ‘yan shi’a suna zagin sahabbai,nace masa yadda kaji haka muma haka muke ji,na tambaye shi zagi addini ne ko idan kayi shi zai }ara maka Imani? Yace man A’a.na ce masa kuma ko a al’ada mai zagi kamilin mutum ne yace man a’a.Nace masa kuma ga ]ana wane lokacin yana da shekara 14,nace masa tun da nike dashi ban ta~a zaginsa ba,A ta}aice dai nace masa,ba wai zagin musulmi ba ballantana sahabi, ko zagin wanda ba musulmi ba,ba addini bane,domin Allah yana cewa, “Kada ku zagi wa]anda suke kiran koma bayan Allah…”Ta yiyu waninsu yace ai alokacin ashura muna jin kuna la’anta,mai wannan tunanin ya duba littafan wasu daga cikin fitattun malaman sunna kamar Suyy]i zai ga haka,wato suma sunyi la’anta ga wa]anda suka yi aikin da kuma wa]anda suka goya masu baya.Kuma batun al-amarin Sahabbai ga duk wanda ya bu]e tunaninsa ya karanci littafan shi’a,zai ga matsaya da matsayin da suka basu shine matsaya da matsayin da Al}ur’ani da Hadisan Manzon Allah[S]suka basu,ba kamar yadda matsaya da matsayin da Ahlus sunna suka basu ba,wato na jingina masu adala gabaki ]ayansu,shi yasa ko wajen gabatarwa zaka ji suna cewa wa- As-habihi-Ajma’in,to idan mutum yace haka ayoyi irin na suratul Munafi}un,ko suratul Ahzab ko suratu Tauba ko ayoyi irin su Ya’ayyuhallazin Amanu-inja’akum fasi}un bina-bain…duk ya zai yi dasu,wato in ka tafi akan Ajma’in.Kuma mu duba ayar da suke yawan kawowa ta }arshen suratul Fathi, “Muhammandur rasulullah wallazina ma’ahu……”To mutum ya duba cikon ayar mi Allah yace, “Wa adallahullazina amanu wa Amilus salihati MINHUM magfiratan wa ajran Azima.”mahallish-shahid anan shine Minhum,ga wanda yasan }a’idodi na luggar Arabiyya ya san in akace ‘min’ yana nufin tab’ib wato sashe ba duka ba.Amma idan mutum ya koma ga malaman shi’a zai ga sun kasa sahabbai gida hu]u.1-Wa]anda suka yi imani da Manzon Allah kuma suka bishi sau da }afa ba tare da sa~a masa ba,a umarninsa da kuma haninsa ba.2-Wa]anda suka yi imani da Manzon Allah,amma binsu ga Manzon Allah bai zamo sau da }afa ba,wato wani lokaci zai iya bada umarni su sa~a,misali lokacin da yace akawo man takarda in rubuta abun da in anbi ba za a ~ace ba,to a lokacin kamar yadda wasu suka sani,sai sahabbai suka sa~a tsakaninsu wasu suna akawo takardar wasu kuma na cewa kada a kawo, littafin Allah ya ishemu daga }arshe Manzon Allah yace su tashi su bashi waje,wannan abu yana cikin littafin Buhari,wani misali kuma ranar Uhud Manzon Allah ya aje wasu a bayan dutsen uhud yace masu duk yadda ta kaya kada su bar wajen,amma daga }arshe mi ya faru,cikinsu wasu suka bi umarnin wasu kuma suka sa~a,akwai misalan irin wannan da yawa.3-Wa]anda tun asali basu yi imani da Manzon Allah ba a zukatansu sai a fatar baki kawai,kamar fa]in Allah Ta’ala a farkon suratul munafi}un, “Idan munafukai suka je maka suka ce,mun shaida kai lalle Manzon Allah ne,kuma Allah yana sane lalle kai Manzon sane.kuma lalle Allah yana shada cewa,lalle munafukan ma}aryatane.”da dai ayoyi dabam-dabam a kuma wajaje dabam dabam na Al}ur’ani da suka yi Magana kan munafukai,kuma kowa yasan munafukai a cikin musulmi suke.4-Wa]anda suka yi imani da Manzon Allah kuma suna da ala}a dashi ta jini,wato sahabbaine kuma ‘yanuwansa na jini.To saboda Allah  wannan ko a hankalce bai fi kama da hankali ba,to ballantana a shari’ance,haka abun yake.Saboda haka in mutum bai sani ba ya sani. Ba sahabbai matsayin da ya sa~a ma Al}ur’ani da sunnar Manzon Allah Bani umayyane suka assasashi kuma suka gina mutane akai,wato saboda }iyayyar su da Ahlul Bayt.Domin wata gaba ce da suke da ita ga Bani Hashim tun a lokacin Jahiliyya,kuma in mutum ya dubi jagororin da suka ya}i wannan addini zai ga sune,misali Abu sufyan ya ya}i Manzon Allah[S]. Mu’awiya ya ya}i Imm Ali,Yazidu[LA] ya ya}i Imam Husain.Kai hatta zagin sahabbai da wasu ke jingina ma shi’a,su binciki Tarihi suga waye ya assasashi,Mu’awiyane ya assasa,misali bashi ya sunnata zagin Imam Ali ba kuma ya gina mutane akai a kuma cikin masallatai,zuwanUmar ]an Abdul Aziz ya hana,har ya maye dai dai inda ake zagi da la’anta ga Imam Ali da Ayar,Inna llaha ya’amuru bli adli wal ihsan….wanda har yanzu a masallatan jumma’a,a }arshen hu]uba limamai kan karanta ta.kuma in mutum yayi bincike zai ga Banu umayya sun }agi abubuwa da yawa sun sa cikin addini,misali Azanus-sani wanda mai Risala yake cewa Ahadasahu banu umayya,wato su suka }age shi.Shi yasa idan mutum ya dubi madrasa ]in Ahlus sunna da kyau zai ga tana da ~angarori biyu na koyarwa,koyarwar sahabbai da kuma koyarwar Bani umayya,kuma ko yanzu a aikace kana iya ganin tasirin karantarwa guda biyu,a ~angarorin Ahlus sunna,zaka samu wasunsu duk abin da ya shafi Ahlul bayt suna son shi kuma suna girmama shi,wasu kaga akasin haka.Saboda haka lalle mutum yayi hankali kai ba bani umayya ba ajini,amma a aiki ya zamo kana cikinsu,wanda zai iya janyo maka gobe }iyama ka tashi tare dasu.saboda haka abun bana wasa bane,abu ne wanda yake da ala}a da addinin mutum da kuma lahirarsa,shi yasa ko a lokacin sahabbai sun yi inkarin abubuwa da daman na bani umayya,mutum ya binciki littafai musamman na Tarihi zai gani.Kuma wani abin mamaki masu cewa ana zagin sahabbai,zaka ga ma}iya addini sun ta~a shaksiyyar Manzon Allah,misali ~atanci gareshi ko zagi,ba zaka ga sunyi wani kata~us ba,sai kaga wa]anda suka ce basu yarda da Manzon ba,su zasu fito suyi muzaharori akan basu yarda ba.misali abinda ya auku a watannin baya na ~atanci ga Manzon Allah,]aya daga cikin masallatai na }ungiya wani ya mi}e daga cikinsu yace,shifa ya lura  al-amarinsu na bu}atar gyara,munce ana zagin sahabbai,amma yanzu gashi an zagi Manzon Allah bamu fito mun nuna fushinmu ba akai.amma ga wa]anda muke ce masu suna zagin sahabbai su sun fito sun nuna fushinsu,har yake ce masu shin Manzon Allah bai fi sahabbai daraja bane?   4- Daga cikin abubuwan da aka jingina ma Shi’a akwai cewa, wai suna tuhumar Aisha matar Manzon Allah,wannan abu ya na gayar ban mamaki,domin babu wani malami daga cikin malaman shi’a magabata da na yanzu,da suka tafi akan haka,in kuma mutum yana ganin ba haka bane,ga littaffan Tafsirai nan na malaman shi’a ya bincike a suratun nur ya gani,daga }arshe zata bayyana masa akan cewa,duk ruwayoyin da suka zo akan wannan abu ruwayoyi ne na Ahlus sunna, ba na shi’a ba,amma kasantuwar mutane ba bincike suke ba a littafan shi’a. komi sai a }ir}ira a fa]i, su kuma yarda.Domin shi’a suna da Iiti}adin duk wani abu da zai ta~a shaksiyyar Manzon Allah a mutunce,to tsarkakke ne daga haka.Kuma irin wa]annan }aryaryaki da wasu suka }ago,wasu kuma suka gada suna ya]awa,suyi tunanin ha]uwar su da Allah Ta’ala ranar }iyama da kuma irin nauyin zunuban da suka ]auka ma kawukansu,wato na wannan }azafi ga ‘yan shi’ar da suka wuce da  na wannan zamanin da kuma wa]anda zasu zo nan gaba.5-Daga cikin abubuwan da aka }ir}ira aka jingina ma shi’a,akwai cewa wai asalin shi’a daga Abdullahi ibn saba ne:Wannan shima }age ne,domin wasu daga cikin malaman Tarihi da masu bincike dabam-dabam sun tabbatar da cewa babu wani mutum mai suna Abdullahi ibn Saba,ma}iya shi’a ne suka }ir}iro wannan suna, don su katange su da kuma sa masu shamaki daga fahimtar gaskiya.Ga mai bu}atar ganin bincike da aka yi daga cikin littafan Ahlus suna wa]anda suka tabbatar da cewa wannan suna }ir}irarshi akayi,ya na iya duba littafi mai suna Abdullahi ibn Saba juz’i biyu ne. na Allama Murtadha al askari.Don duk wanda zai yi bincike a cikin littafan shi’a ko ya saurare su,zai ga irin }arfin hujjojin da suke akai,akan duk wani abu da aka jingina masu ko kuma wanda suke akai.kuma wani abun mamaki da kuma ban sha’awa shine duk abin da ‘yan shi’a suke akai,ya shafi A}ida ne ko wasu ababe na Fi}hu,to zasu iya tabbatar da hujjojunsu a littafan Ahlus sunna.misali mas’alar khalifanci ta Imamai 12,mutum ya duba Buhari da muslim zai ga hadisai masu nuni da haka,ko kuma al-amarin ha]a sallah da ‘yan shi’a kan yi.ko sujuda kan turba ko shafa akan }afafu da dai makamantansu,duk ire-are wa]annan ababe  mutum na iya tabbatar dasu a littafan sunna. Shi yasa shuk’ran la fak’ran sai dai kaga Ahlus sunna ya koma shi’a ba ]an shi’a ya koma sunna ba,kuma yadda malaman shi’a suka san littafan sunna,to ko ‘yan sunnar basu san su haka ba,ta yiyu wannan yayi ma wasu nauyi amma in mutum ya ]ebe son zuciya da ta’assubanci zai ga abun haka yake.Akwai wani Ayatullahi da muka ta~a ziyarta a birnin }um,yake cewa yana mamakin malaman Ahlus sunna,mu muna da littafansu amma su basu da littafanmu,yace duk abin da suke dashi muna da shi,amma abin da muke dashi basu dashi. Daga }arshe Nasiha ga masu fa]a da }iyayya da shi’a.Idan zaka hukumta mutum to zaka  hukumta shi da abun da kaji ko ka gani.ba abin da aka fa]a maka ba dangane da shi,domin babban abinda yake cutar da wa]annan sashen musulmi da suke da ire-ire wa]annan ra’ayoyi ga ‘yan shi’a shine, suna samun }ananan littafai wa]anda ma}iya shi’a suka rubuta,suna karanta su da kuma ya]a su,maimakon su sami littafan dasu ‘yan shi’a suka rubuta da kansu su karanta.sa~anin ko da mutum zai je }asashen ‘yan shi’a zai ga akasin haka,wato mutum zai ga malamansu suna da littafan ahlua sunna tare da na shi’a.Haka nan kuma masu ya]a irin wa]annan ababe  na sa~ani da rarraba tsakanin musulmi,su duba yadda ma}iya addini duk da sa~aninsu,amma suka dun}ule wajen fa]a da mulunci da musulmi ba tare da banbancewa ko kai ]an sunna ne ko ]an shi’a.Bayan haka kuma in a wajen ka mutum akan ~ata yake ko ka fitar dashi musulunci,shin }iyayya da fa]a dashi shi zai dawo dashi kan hanya.ko kuma uslubi na hikima da ilimi da kyakkyawan mu’amala.Wannan kenan dai baki ]aya a ta}aice.   

Last Updated on Tuesday, 29 October 2013 19:52
 
Home Shia/Sunnah ASALIN SHI’A DA ABUBUWAN DA AKA JINGINA MATA.
Copyright © 2023. www.tambihin.net. Designed by KH