Friday, 24 May 2024
Email
Make My Homepage
RSS
Register
ASHURA A MAHANGAR AHLUL-BAIT [AS] DA AHLUS- SUNNAH. Print E-mail
Written by administrator   
Sunday, 20 October 2013 11:41

 Da farko dai   watan  muharram, da waki’ar Ashura ta auku,wata ne na juyayi da ba}in ciki dama kuka,a mahanga ta Ahlul bait,tun daga farkon watan har }arshen sa.kuma ko da a munasabobi na wiladar Aimma in mutum ya bincika zai ga babu wani imami daga cikin Aimma wanda wiladar sa tazo a cikin watan muharram,wato akasin kamar yadda a shi kuma watan shaaban babu wani Imami daga cikin Aimma wanda wafatin sa yazo aciki.sai dai wiladar su.                                                                                       Misali a cikin watan shaaban ne aka haifi Imam Husain,Imam Zainul Abidin,Imam Mahdi,Kuma tun bayan aukuwar wannan wa}i’a ta karbala,yau shekara sama da dubu da ]ari ukku da saba’in, mabiya Ahlul-bait duk shekara,suke raya wannan rana ta ashura da juyayi da zaman makoki da dai sauran su.Kuma masu tafi da iko na bani umayya a lokacin,wato wa]anda suka aukar da wannan wa}i’a ta ashura,suka yi iya iyawar su,domin su binne wannan al’amari na Ashura,ta hanyar }ago hadisai dabam- dabam,aka jingina su ga Manzon Allah,aka kuma gina mutane a kai,har ta kai ranar da wannan wa}i’a ta Ashura ta auku aka gina mutane,akan ranar farin ciki da kuma yelwa ta ma iyali,a wannan nahiya tamu watan muharram har la}abi ake yi masa da watan cika-ciki.Haka nan a watan akwai wani wasa da ake yi wai wasan Shara da dai wa]ansu abubuwa da ake acikin watan na al’adu dabam-dabam,kuma hadisai da aka }ago da nufin turbu]e al-amarin Ashura,an }ago su ta fuskoki daban-daban ne,alal misali hadisan da suka zo cewa WAI a ranar ashura Allah ya halicci sama da }asa, a ranar ashura  aka halicci duwatsu, a ranar ashura aka halicci koguna,a ranar ahura aka halicci  al-janna da wuta,a ranar ashura aka halicci Annabi Adam da Hawwa’u,a ranar ashura aka tseratar da Annabi Ibrahim daga wuta,a ranar ashura aka halakar da Fir’auna.Ta fuskacin bayin Allah da aka Haifa a ranar,aka }ago hadisai  cewa wai a ranar Ashura aka haifi Annabi Ibrahim da Annabi Isa,wani abin mamaki ma da yazo a hadisin shine cewa wai  ranar ashura aka haifi Manzon Allah.mutum na iya duba littafin TANBIHUL-GAFILIN na abu Lais Samar-}andi al-hanafi.a babin falalar ranar Ashura,zai ga wannan hadisin da ya kawo wa]annan abubuwan da aka ambata dama wa]anda ba a ambata ba.Wani abin mamaki ma hatta ranar ashurar,sai da aka kawo zantuka akai,wai wace rana ce,wasu suka ce ranar tara ce,wasu kuma wai ranar sha-]aya,mafi yawan su suka ce ranar goma ce. Wanda ko a hankal ce  adadin goma ace wai a samu sa~ani akai,duk dai wannan saboda }o}arin jirkita ranar wannan wa}i’a ne, kuma }ago hadisi da yi masa isnadi a jingina shi gaManzon Allah ba ba}on abu bane a daular bani umayya.Wuce nan ma ta kai ga a lokacin har }ir-}irar sahabi akeyi,wato a }ago suna ye da sunan cewa sahabbai ne, bayan haka kuma a }ir}iri matanin hadisi,ajingina masu ace sunji daga Manzon Allah.A saboda haka nema wani malami na madrasah ]in Ahlul bait,a wannan zamani da muke ciki,yayi zuzzurfan bahasi,a littafan Ahlu-sunna,kan irin wa]annan sahabbai da aka }ir}ira,daga }arshe yayi littafi mai juz’i biyu.To a binciken da yayi ya gano sahabbai ]ai-]ai har ]ari da hamsin.Shi yasa littafin yasa mai suna,KHAMSUNA-WA-MI’ATU SAHABIY-MUK-TALA{,ma’ana sahabbai ]ari da hamsin }ir -}irarru.Sunan malamin Allama sayyid Murtadha al-askariy.kuma duk wanda ya san shi,ko ya karanci littafan sa.zai san cewa shi }wararre ne,a wannan fanni na bincike, musammam kan abubuwan da aka yi sa~ani tsakanin sunna da shia.Hatta abunda wasu malaman sunna suka tafi akai na cewa wai asalin shia daga Abdullahi ibn Saba ne, yayi bincike akan sa,shima }ir }irarre mutum ne,sakamakon bincike nan sa,yai littafi shima juz’i biyu,Sunan littafin ABDULLAHI IBN SABASaboda haka ba abin mamaki bane.wa]annan hadisai da aka }ir}ira,aka jingina ma ranar ashura.A ka kuma gina mutane a kai,har ta kai ma suna ganin wa]annan abubuwa a matsayin addini,akasin haka kuma na nuna juyayi da  ba}in ciki,ba addini ba.

            Kuma mu ]auka wa]annan hadisai  da aka jingina ma ranar Ashura,ba }ir}irarru bane,to  mutum ya auna da hankalin sa,ace ranar da akayi ma gidan Manzon Allah irin wannan aika-aika,ta zamo ranar farin ciki da kuma yelwata ma iyali!Anya mutum ko kunya ba zai ji ba, na,  Manzon Allah,gobe }iyama,kuma da wacce fuska zai dube shi gobe }iyama.Domin in mutum bai sani ba ya sani,su jagororin da suka jagoran ci wannan mummunan aika-aika,sun yi da nufin ]aukar fansa na iyayen su  da kakanin su da  aka kashe a ya}o}in da Manzon Allah yayi,Misali ya}in badar da makaman tansu.Kuma koda ma a al’ada, wato a rayuwar yau da kullum,idan ba}in ciki da farin ciki suka ha]u,to akan ]auki ba}in ciki a bar farin ciki,misali mutum nada mata sai ta haihu ko kuma a ranar sunan haihuwar,Allah yayi ma mahaifin sa ko mahaifiyar sa rasuwa.To tambaya yanzu mi zai rinjaya a zuciyar sa,murnan haihuwa ko juyayin rasuwa,tabbas juyayin rasuwa zai rinjaya,wani misali kuma ace ]aurin aure da rasuwa suka ha]u,kuma haka ai ya sha aukuwa tsakan-kanin mutane,za ayi ]aurin aure mutuwa ta bijiro kaga an ]aga shi.kuma  ballantana wanda akayi ma wannan abu matsayin sa, ga musulmi ya wuce uwa ko uba.Imam Husain fa,wanda koda ba nassi na hadisai da suka nuna matsayin sa,to kasantuwar sa ]a ga Sayyida Fa]ima da Imam Ali kuma jika ga manzon Allah to wannan ka]ai ya ishe shi matsayi.To ballan tana ga mabiya Ahlul bait,suna da I iti}adin cewa shi, Ma’asum ne,]an Ma’asum,jikan Ma’asum,baban Ma’asumai.Bayan wannan shinfi]a insha Allah wannan rubuta zai gudana kan wa]annan ababe.

1-Falalar juyayi da kuka saboda wa}i’ar Ashura.              

2-Halin da Al umma Manzon Allah[s] take ciki, gabanin wak’ ar ashura.

3-Sabab din da suka aukar da wakiar Ashura.

4-Natijojin da suka biyo bayan wakiar Ashura.

5-Wannan wa}i’ar ta Ashura ita zata kasance sabab na dawowar addini.

6-Godiya ga Allah kan ni’imar da yayi mana.

1-Falalar juyayi da kuka saboda wa}i’ar Ashura;Akwai hadisai masu yawan gaske  da suka zo daga Manzon Allah da kuma Aimma dangane da haka,ga wasu daga ciki,An samo daga Imam Ridha yace, “kuka domin Imam Husain yana kan kare zunubi”Har wala yau daga Imam Ridha yace, “Wanda yayi kuka saboda Imam Husain har hawaye suka zubo,Allah zai gafarta masa dukkan zunuban sa }arami da babba.”Haka nan yazo akan cewa akwai lokacin da aka ambaci Imam Husain[AS] gaban Imam Sadi}[AS]sai aka ga yayi kuka.yace Imam Husain yace, “Mumini ba zai ambace ni ba ko ya tuna dani face yayi kuka”Yazo a tarihin Imam Khumain cewa duk lokacin da aka ambaci Imam Husain a gaban sa,sai an ga hawaye ya zubo masa.Haka nan an samo daga Imam Sadi},[AS] “Nunfashin mai ba}in ciki saboda zalincin da aka yi mana tasbihi ne,juyayi domin mu Ibada ne,”Haka nan wani da ake cema Aba Ammar,ya shiga wajen Imam Sadi}[AS],sai yace masa ya Aba Ammar, kayi man wa}e na Imam Husain,da yake shi mawa}ine na Ahlul bait.Sai yai wa}en,Imam Sadi}[as] yai kuka,sai yace masa ya aba Ammar,wanda yayi wa}e saboda Imam Husain,har mutum 50,ko 30,ko 20,ko 10, suka yi kuka,to yana da Aljanna,Akwai shima wani mawa}in Ahlul bait mai suna Jaafar, ya je wajen Imam Sadi}[AS]sai yace masa, babu wani wanda zai yi wa}e kan Imam Husain yayi kuka,ko wasu suyi kuka face an gafar ta masa kuma al-janna ta wajaba gare shi.Haka nan daga Imam Ridha[AS] yace, “Duk wanda ranar ashura ta kasance ranar musibar sa,da ba}in cikin sa,da kukan sa,to Allah zai sanya masa ranar }iyama ta kasance ranar farin cikin sa da murnar sa,”da dai hadisai masu yawa makaman tan wa]annan da aka samo daga Aimma na Ahlul bait.Kuma tun gabanin aukuwar wannan wa}i’a ta ashura,Manzon Allah[S] yayi kuka a lokuta dabam-dabam a kuma wajaje dabam-dabam,akanta.kuma haka yazo a masadir naAhlus sunna da yawa,ga mai bu}atar ganin wa]annan masadir, yana iya duba littafi mai suna MA’ALIMU-MADRASATAIN,juz’i na ukku, na Sayyid Murtadha al-askari.Ga ]aya daga cikin hadisan daya kawo.Lokacin da Husain ya kai shekara biyu da haihuwa,Manzon Allah[S] ya fita wata tafiya,akan hanyar tafiyar sai aka ji Manzon Allah[S] yace inna-lillahi-wa inna-ilaihi rajiun,aka ga kuma yana kuka,aka tambaye shi dangane da haka,Yace Jibril ne yake fa]a man  wata }asa wadda ake cema karbala,za a kasha ]ana Husain a wajen,aka ce masa waye zai kasheshi ya Manzon Allah,yace wani mutumi da ake cema yazidu.lokacin da Manzon Allah[S] ya dawo daga tafiyar,yana cikin damuwa,ya hau mumbarin sa yai khu]uba kan wannan abu,Husain na gaban sa da kuma Hassan,Lokacin daya gama khu]ubar ya ]ora hannun daman sa akan Husain,ya ]aga kansa zuwa sama,yace, “Ya ubangiji ni Muhammad bawan kane kuma Annabin ka,wannan yana daga cikin za~a~~un zuriyyita,ya ubangiji Jibril ya fa]a man cewa wannan ]a nawa za a kashe shi,jin haka sai sahabban sa dake cikin masallacin suka fashe da kuka,Manzon Allah, yace masu  kuna kuka amma baza ku taimaka masa ba! Ya ubangiji ka ji~in ce shi ka taimaka masa,”Saboda haka  kukan  juyayin kashe Imam Husain[AS] Manzon Allah[S] yayi, kuma sahabban sa sunyi,wato ga wanda yake ganin cewa wai bidi’a ne.

2-Halin da Al-umma take ciki gabanin wa}i’ar Ashura;Idan mutum ya dubi halin da musulmi da musulunci suke ciki zai ga cewa,abin yana da ban mamaki da kuma ban takaici,dama ]aure kai.ace an wayi gari,mutum  irin yazidu[LA] ]an giya,mazinaci,azzalumi wai ya zama shugaba na khalifan cin Manzon Allah.kuma wannan abun nasa ba a ~oye ba,a’a abayyane,ya sha giya ya bugu kuma yazo yaja mutane sallah, kuma abishi a haka,akwai ma lokacin da yazo yaja mutane sallar asuba,yai raka’a shidda,ya juyo ya dubi mamu, yace masu ko kuna so in }ara maku,mu duba fa mu gani,kuma alokacin akwai sahabban Manzon Allah a raye,abin mamaki ma wasunsu sun yi masa bai,a.wanda ko a wannan zamanin mutum ya duba haka zai iya yiwuwa,ace za ayi sallah liman yazo a buge da mayen giya,yaja mutane sallah,wa ze bishi.amma a wancan lokacin saboda yadda aka gina mutane kan biyayya ga khalifa koda fajirine,fasi}i,sai su bishi.Shi yasa lokacin da yazidu ya aika ma Imam Husain ta hannun gomnan sa dake madina,akan yai masa bai’a,Imam Husain yace ba dai iri naba,}in yin wannan bai’a shi ya haifar da wa}i’ar Ashura,kuma wannan sadaukar war da yayi, ita ta ceci Musulunci da musulmi,kuma ta wanzar da  musulunci zuwa yau,domin a lokacin bawai musulmai kawai ba,a’a har musulunci na cikin hatsari,a hannun irin wa]annan khalifofi na bani-umayya,kuma har yau ]in mu akwai tasirin abubuwan da suka }aga suka sa cikin musulunci,suka kuma gina mutane akai,in mutum ya duba duniyar Ahlus sunna zai ga haka.Alal misali hadisai da suka zo da nunin yin biyayya ga ko wane shugaba koda ko fajiri ne,fasi}I,kamar wannan hadisin,wanda muslim ya ruwaito daga khuzaifa yace,Manzon Allah[S]yace, “Bayana za a samu wadansu shugabanni,basu shiryatuwa da shiriyi ta,basu sunnatuwa da sunna ta,sai ya tambaya yaya zan yi ya Manzon Allah[S]in na riski zamanin?sai yace masa,kaji  kayi biyayya ga shugaba,koda shugaban ya dake ka ya kwace maka dukiya,kaji kayi biyayya,”haka nan a wani hadisin shima wai daga Manzon Allah[S]yace,Wanda yaga wani abin}I daga shugaban sa to ya daure,domin duk wanda ya bar jama’a dai dai da ta}I ,ya mutu to ya mutu mutuwar jahiliyya,da dai hadisai irin wa]annan.To mutum ya kwatan taw a]annan hadisai da wani hadisi da aka samo daga Imam Husain[AS]yace yaji daga Manzon Allah[s]yace, “Duk wanda yaga shugaba ja’iri wanda yake halatta abin da Allah ya haram ta,yana sa~a ma sunnar manzon sa,yana zaluntar bayin Allah,bai yi inkari gare shi da aiki koda Magana,to Allah zai kai shi,inda ya kai shi,”mutum ya kwatanta wa]annan hadisai,yai ma kansa al}alanci.Daga cikin halin da al-ummar musulmi ke ciki gabanin wa}I’ar ashura,akwai zalunta da kuma cutarwa ga Ahlu baitin Manzon Allah[s] da kuma mabiyan su,zalunci na farko gare su shine }wace ha}}in tafida iko daga hannun su,bayan haka kuma aka dunga cutar dasu ta fuskoki dabam-dabam,mu duba Imam Hassan har bayan wafatin sa sai da aka cutar da shi, ta yin ruwan kibau a na’ashin gawar sa,saboda ya bu}aci a binne shi kusa da kakansa,haka bani umayya suka fito da makamai akan basu yarda ba,sai dai ayi ya}I,ganin haka Imam Husain yace a kai shi Ba}i’a,a binne,yama bar wasiyyar haka.kuma mu duba irin cutarwa da kuma gallazawa da aka yima mabiya Ahlul bait,a lokacin Maawiya,kisa ne,sawa a kurkuku,azabtarwa,da dai sauran su.

3-Sabab ]in da suka aukar da wa}i’ar Ashura.Akwai dalilai masu yawa da suka sabbaba wannan wa}I’ar ta Ashura.Amma dalili na asasi  day a sabbaba haka shine,rashi aiwatar da sa}on da Manzon Allah ya isar a  ranar ghadir,da anbi abunda ya fa]i, da haka bata faru ba,shi yasa akwai wata Magana ta Imam Husain[AS] da yake cewa,Tun a sa}ifa aka kashe shi.Dalili na ukku shine Hassada da }iyayya  wanda khususan Bani umayya suke dashi ga Bani Hashim,kuma wannan ya ]auko asali ne tun a lokacin jahiliyya,wato suna jin haushin daukakar su akan su,da Musulinca yazo sai hassadar da }iyayya suka da]a }aruwa,kasantuwar gashi yanzu manzo ya fito daga Bani Hashim.Dalili na ukku shine ]aukar fansa,na iyayen su da kakannin su da aka kasha a ya}o}in da Manzon Allah, yayi misali kamar ya}in Badar da makaman tansu,shi yasa lokacin da aka kawo kan Imam Husain gaban yazidu,yana murna yana wa}e yana cewa,ina ma dai kakannin sa suna nan suga ]aukar fansa da yayi,Domin su bani umayya su suka jagoranci fa]a da Manzon Allah, har zuwa lokacin da aka samu,iko akan su,wato a fat-hu makka,mutum yabi tarihin su zai ga haka,misali Abu Sufyan ya ya}I, Manzon Allah,]ansa Muawiya ya  ya}i Imam Ali da Imam Hassan,jikansa Yazidu ya ya}i Imam Husain.Yazo a tafsiri cewa Shajaratul-mal-una,bani ummayya ne.Kuma su wa]annan jagarorin bani umayya da aka ambata,in mutum yabi tarihin rayuwar su zai ga musulin cin su, na zahiri ne kawai,amma a ba]inance basu yarda dashi ba,domin zantikan su ya nuna haka,misali lokacin da yazidu yake wancan wa}en cikin abun da yake cewa,shine wai Bani hashim sunyi wasa da mulki ,ba wani wahayi daya sauka ba kuma littafin da aka saukar,a ta}aice dai wa]annan suna daga cikin sabubban da suka haifar da wannan wa}i’a ta karbala.                                   

4-Natijojin da suka biyo bayan wa}i’ar Ashura,Akwai natijoji masu yawa da suka biyo bayan wannan wa}i,ar,ga wasu daga ciki,ya farkar da al-ummar musulmi a lokacin,wanda wannan farkawa ta janyo tawaye  ga Yzidu da mutanen madina da makka,suka yi masa,wanda sanadiyyar wannan tawaye ya aiko maya}a daga sham zuwa madina da makka,mutum ya tambayi tarihi zai fa]a masa munanan ababen da wa]annan maya}a nasa suka yi a wa]annan birane masu tsarki.Daga cikin natijojin akwai cewa ya karya }ud-siyya,wato matsayi na irin wa]annan khalifofi  na bani umayya a zukatan musulmi,wato yadda da  suka ]auke su da matsayi,wa}I,ar sai ta wanke wannan a zukatan su.Daga cikin natijojin shine ya tona asirin irin wa]anan jagorori na bani umayya,cewa ashe addini ma basu yi imani das hi ba,kafirci ne a zukatan su,Akwai ma lokacin da Abu Sufyan ya samu wani khalifa, yace yayi abun daya ga dama, ba wata wuta ko aljanna.Daga cikin natijojin akwai cewa ya rayar da addini,ya kuma wanzar dashi.domin su bani umayya addinin suka so su kawar ko su jirkita shi su dawo da jahiliyya.da dai natijojomasu yawan gaske da suka biyo bayan wannan wa}i’a.                                                                                  

5-Wannan wa}I’a ta Ashura ita zata kasance sabab ]in tabbatar addini,a duniya baki ]aya,Akwai ruwayoyi da suka zo cewa Imam Mahdi zai bayyana ne ranar Ashura,ga wani hadisi  akan haka,An samo daga Imam Sadi}[AS] yace, “Mahdi zai bayyana ranar Ashura,ranar da aka kashe Husain”kuma koda ma ba hadisi akan haka,mutum ya duba wannan zamani namu,yadda ranar Ashura take kasancewa,a sassan duniya dabam-dabam,zai ga yadda mabiya Ahlul bait,a ranar suke cikin caji da }umaji na sadaukarwa,da jinin su da dukiyar su,nasu dana iyalin su,kuma ko wace shekara abin }aruwa ya keyi,mutum ya auna da tunanin sa,anya wannan rana ta ashura, wata rana ba zata canza tarihin duniya ba,Wani abun da zai ba wasu mamaki,Hatta juyin musulinci daya auku a Iran,Asasin sa ya faro ne daga ranar Ashura,Shi yasa wannan zamani da muke ciki zamani ne na Ahlul bait,wannan yasa mutum yake ganin kullum,sai da]a ri}o ake da Ahlul bait,shi yasa a wannan zamanin da ake ciki,in kaga mutum na fa]a da mabiya fahimta ta Ahlul bait,wato ‘yan shia ka tausaya masa,Domin idan har khalifofi na bani ummaya  da khalifofi na Abbasawa irin fa]an da suka yi da Ahlul bait da mabiyan su,basu sami nasara ba,na kauda suba,To ina ga wannan zamani na Ahlul baiti,saboda haka in kaga mutum na fa]a da shia,~ata lokacin sa kawai ya keyi,ko shi bai yiba to ‘ya’yan sa, ko jikokin sa sai sunyi,wato sai sun bi Ahlul bait,kuma ko a yanzu abun ya soma faruwa,da yawa yanzu zaka ga cewa,mutum ko ba akan fahimtar Ahlul bait ba yake,in ka shafa a cikin dangin sa na jini ta wajen uwa ko uba,sai ka samu akwai wanda ko wa]anda suke ri}o da Ahlul bait,saboda haka makomar duniya AHLUL BAIT ne,wannan wani hukum taccen abune da Allah ya hukum ta,lokaci ne kawai.

6-Godiya ga Allah kan ni’imar da yayi mana,na ni’imta mu dayayi na ri}o da Ahlul-bait,domin al-barkacin ri}o da sune,  muke ganin ranar Ashura a matsayin ranar ba}in ciki da juyayi,wato akasin yadda wasu musulmi suke ganin ta a matsayin ranar farin ciki da kuma yelwata ma iyali.kuma wa]anda suka tafi a kan wannan fahimta,abin tausayawa ne,domin in muka duba muma da haka muke,wato girman sunna ne,Allah[T] bisa  falalar sa ya shirya tar damu.saboda haka suma,      sai muyi masu fatan Allah ya shir ya tar dasu ga ri}o da Ahlul bait.Mu kuma Allah[T]ya rayar damu akai,ya tashe mu akai.ya kuma a zurta mu da ceton su.                                                                                                                                    

Last Updated on Tuesday, 29 October 2013 19:52
 
Home Shia/Sunnah ASHURA A MAHANGAR AHLUL-BAIT [AS] DA AHLUS- SUNNAH.
Copyright © 2024. www.tambihin.net. Designed by KH