Darussa daga rayuwar Manzon Allah (S) 2 |
Written by administrator | |||
Sunday, 20 October 2013 11:26 | |||
Kasantuwar wannan wata da muke ciki, wato na Rabi’ul Awwal, wata ne na wiladar Manzon Allah da kuma Imam Sadiq (AS). Kamar yadda ya zo a tarihi a ruwayar Iyalan Gidan Manzon Allah (S), an haifi Manzon Allah (S) ne a lokacin fitowar Alfijir ranar Juma’a 17 ga Rabi’ul Awwal a shekarar da ake wa la}abi da shekarar Giwa. Amma a ruwayar Ahlus Sunna sun tafi a kan ranar Litinin 12 ga watan Rabi’ul Awwal ne. Wanda a nan mutum in ya auna da hankalinsa, a ce an samu sa~ani na haihuwar wani Malami sai ’ya’yansa da jikokinsa suka ce an haife shi ne a ranar kaza, ]alibansa su kuma suka ce an haife shi rana kaza.to a hankalce wane ya kamata mutum ya bi? Kuma kamar yadda aka sani ne, an haifi Manzon Allah (S) a Makka. Kuma gidan da aka haifi Manzon Allah(S) a ciki, daga baya an gina Masallaci a cikinsa. Kuma Musulmi na zuwa suna yin Salla a cikinsa da kuma neman tabarruki. Kuma wannan abu ya kasance har ya zuwa shekara ta 1926 milidiyyah lokacin da Wahabiyawa suka rusa Masallacin da kuma gidan, wato a }o}arinsu na hana mutane zuwa wannan gida mai albarka domin neman tabarruki. Da kuma kau da duk wani abu da ke tuna wa mutane tarihin addinin Musulunci. Manzon Allah (S) an haife shi ne bayan wata biyu da rasuwar Mahaifinsa, wato Abdullahi [an Abdulmutallib. Abin da ya faru shi ne lokacin da Aminatu Bin Wahab, wato Mahaifiyar Manzon Allah (S) ta ]auki cikinsa da wata bakwai, sai Kakansa Abdulmu]allib ya tafi Madina shi da Mahaifin Manzon Allah (S) saboda su sayo kayan walimar haihuwar wannan ciki mai albarka. Bayan isar su Madina ba da da]ewa ba sai Mahaifin Manzon Allah (S) ya kamu da rashin lafiya, bayan jinya ta kwanaki 15, Allah (T) ya yi masa rasuwa, aka bizne shi a Madina. Bayan haihuwarsa (S) da shekara shida, Allah (T) ya yi wa Mahaifiyarsa rasuwa. Haka nan bayan haihuwarsa da shekara takwas da kuma kwana saba’in, Allah (T) ya yi wa Kakansa rasuwa. A lokacin haihuwar Manzon Allah (S) ayoyi da yawa sun bayyana, alal misali ya zo a kan cewa a daren haihuwar, baki ]ayan duniya ta cika da haske, wanda saboda haka Iblis (LA) ya yi kururuwa, ya yi yekuwa ga Shai]anu ’yan uwansa a kan su taru. Bayan da suka gan shi a firgice suka ce masa me ya firgitar da kai ya Shugabanmu? Sai ya ce masu; “Kaiconku! Ba ku ga canji a sama da }asa a wannan dare ba? Tabbas wani abu babba ya faru a doron }asa. Saboda haka ku je ku bincika menene ya faru?” Suka watsu a bayan }asa suka dawo suke ce masa ba su ga komai ba. Sai Iblis ]in ya ce masu bari ya je ya bincika da kansa. Sai ya gewaya a sassan duniya daban-daban har ya iso Makka, sai ya samu zagaye take da Mala’iku, ya nemi ya shiga aka hana shi, sai ya koma tsuntsu da nufin ya shiga, sai Mala’ika Jibril ya ce masa ana ganin ka (LA), sai Iblis ]in ya ce, tambaya ]aya zan yi maka Jibril. Sai ya ce wai me ya faru ne a wannan daren? Sai Mala’ika Jibril ya ce masa an haifi Muhammad (S). Sai Iblis ya ce; “Ina da rabo gare shi?” Ya ce masa, a’a. Ya ce; “Al’ummarsa fa?” Ya ce, na’am. Ya ce; “To na yarda”. Haka nan an samu daga Imam Ali (AS) ya ce lokacin da aka haifi Manzon Allah (S) duk wani gunki da yake cikin Ka’aba sai da ya sunkuyar da fuskarsa ta tokari }asa. Kuma aka yi ta jin sauti daga sama yana cewa; “Gaskiya ta bayyana! {arya ta }are!!” A ta}aice dai duk wani abin da ake bauta wa ba Allah (T) ba, sai da aka ga Aya ta bayyana gare shi sakamakon haihuwar Manzon Allah (S). Misali, masu bautar wuta a Farisa aka ga wutar ta bice. Da dai makamantansu. Haka nan Mahaifiyar Manzon Allah (S) ta ce lokacin da ta haifi Manzon Allah (S)sai taji sauti na magana ana ce mata ‘lallai kin haifi Shugaban mutane, ki sa masa suna Muhammad’. Da dai ayoyi da dama da suka bayyana. Ga mai bu}atar }arin bayani a kai yana iya duba littafin Muntahal-Amal juzi na ]aya na Shaikh Abbas Al}ummi. Kuma in mutum ya bibiyi tarihin Manzon Allah (S) tun daga wiladarsa har ya zuwa wafatinsa zai ga ayoyi daban-daban da suka bayyana daga gare shi. Alal misali ya zo a kan cewa tun tasowarsa, wato gabanin aiko masa da sa}o, ko tafiya yake duwatsu da itatuwa da sauran halittu na Allah (T) sukan yi masa sallama, suna cewa Amincin Allah ya tabbata a gare ka ya Manzon Allah (S). Haka nan in yana tafiya gira-gizai kan yi masa inuwa. Shi ya sa in mutum ya duba mu’ujizozin da Allah ya bai wa Manzanninsa, to baki ]ayansu Allah (T) ya tara ya bai wa Manzonsa (S) da kuma }ari a kai. Insha Allah (T) in bayani ya zo a kan mu’ujizozinsa, za a kawo misassali a kai. Kuma da mutum zai tambaya a halittar Allah (T) baki ]aya wace halitta ce Allah (T) ya fara halitta. Amsa ita ce ruhin Manzon Allah (S), kamar yadda wani daga cikin Sahabban Manzon Allah (S),mai suna Jabir [an Abdullahi Al’ansari ya tambaya, ya ce; “Ya Manzon Allah (S)! Wane abu ne Allah (T) ya fara halitta?” Manzon Allah (S) ya ce masa; “Ya Jabir! Farkon abin da Allah ya soma halitta shi ne hasken Annabinku, kuma Allah (T) ya yi halitta baki ]aya ne. saboda Manzon Allah (S). Ta yiwu mutum ya ce hatta Aljannah da wuta? Amsa eh! Ya yi Aljannah ne saboda ya sa masoyan Manzon Allah (S), kamar yadda ya yi wuta saboda ya sa ma}iyan Manzon Allah (S). A ta}aice dai sanin Manzon Allah(S) da kuma matsayinsa wani abu ne wanda yake kamar yadda Manzon Allah (S) ya ce wa Imam Ali (AS); “Ba wanda ya sanni face Allah (T) da kuma kai”. Sani a nan, wato na Malakut ]in Manzon Allah (S), wato ha}i}aninsa da kuma matsayinsa a ba]inance. Sai kuma wasu darussa daga rayuwar Manzon Allah (S) domin rayuwar Manzon Allah (S) baki ]ayanta darussa ne, saboda haka babu wata halitta da Allah (T) ya halitta mai kamala kamar kamalar Manzon Allah (S), domin yana da kamala ta kowace fuska. Saboda haka a dukkan janibobi na rayuwarsa, misali A}la} ]insa, Ibadarsa, Jarumtakarsa, Iliminsa, Zuhudunsa, Mu’amalarsa. Da dai sauran ~angarori. Ba wai kawai a zamaninsa ya fi kowa ba ne, a’a, ’ya’yan Adam baki ]aya ba wanda ya kai shi ballantana ya fi shi. Ga misalan wasu daga cikin ~angarorin rayuwarsa mai albarka. 1. AKHLA{ [INSA: A kyautar sa; Manzon Allah (S) ya kasance mai yawan kyauta. Saboda ma gayar kyautarsa ba a ta~a tambayarsa wani abu ya ce babu ba. Ga misali na kyautarsa. An ruwaito cewa wata rana Manzon Allah (S) ya je wajen mai sai da tufafi ya sai riga ta Dirhami hu]u, bayan ya dawo ya sa rigar ya fito daga gida, sai wani daga cikin Sahabbansa na Ansar ya ce; “Ya Manzon Allah (S)! Ina son ka ban riga”. Sai Manzon Allah ya tu~e wannan rigar ya ba shi. Sai ya sake komawa ga mai sai da tufafin domin sayen wata rigar, ita ma Dirhami hu]u, sai ku]insa ya rage Dirhami biyu, a kan hanyarsa ta dawowa sai ya ha]u da wata kuyanga tana kuka a hanya, sai Manzon Allah (S) ya tambaye ta; “Lafiya kike kuka?” Ta ce; “Ya Manzon Allah (S)! An aike ni ne da Dirhami biyu domin in sayo gari sai ku]in suka fa]i”. Sai Manzon Allah(S) ya ba ta sauran Dirhami biyun da yake da shi. Sai ta ce; “Ina gudun in na koma za a dake ni”. Sai Manzon Allah (S) ya raka ta har gidansu. Da suka isa gidan, sai ya yi sallama, sai mutanen gidan suka fahimci wannan sautin Manzon Allah ne, sai suka yi shiru ba su amsa ba har sai da Manzon Allah ya yi sallama ]aya, biyu, uku, a ta ukun sai suka amsa. Sai Manzon Allah (S) ya ce masu; “Ba ku ji sallama ta ta farko ba ne?” Sai suka ce; “Mun ji. Muna so ne ka }ara mana aminci (domin mai sallama yana cewa ne amincin Allah ya tabbata a gare ku.) Saboda kwa]ayin wannan Addu’a ta aminci daga Manzon Allah (S) sai suka yi shiru, domin Manzon Allah (S) ya }ara”. Bayan sun amsa sallamar, sai suka ce; “Iyayenmu su zama fansa gare ka ya Manzon Allah (S) me ke tafe da kai?” Manzon Allah(S) ya ce masu wannan Kuyangar taku ce ke gudun kada ku dake ta. Nan take mai Kuyangar ya ce ya ’yanta ta saboda Allah. Sakamakon rako ta da ka yi ya Manzon Allah (S). Haka nan ya zo a kan cewa an ta~a ba shi kyautar tufafi, bayan ya sa su, sai wani daga cikin Sahabbansa ya ce ya Manzon Allah (S) wannan tufafin na da kyau. Aka ce sai Manzon Allah (S) ya je ya tu~e tufafin ya ba shi, kuma a lokacin an ce yana bu}atarsu sosai. Haka nan ya zo a kan cewa an ta~a kawo masa dukiya daga Bahrain, sai ya ce wa Sahabbansa, su juye dukiyar, suka juye. Haka ya dinga raba wa Sahabbansa, har ta }are shi bai ]auki komai ba. Manzon Allah (S) saboda gayar kyautarsa idan aka zo aka tambaye shi abu ko da bai da shi, yakan ce a je wajen wane a amsa ba shi, zai bayar daga baya. Ko kuma ya turo mai bu}atar ga inda yake ganin zai samu biyan bu}atar. Alal misali akwai wani abu makamancin haka da ya faru. An ruwaito daga Jabir ]an Abdullahi Al’ansari ya ce; “Mun yi Sallar Asar tare da Manzon Allah (S), bayan Salla muna zaune tare da Manzon Allah (S), sai ga wani Dattijo ya zo ya je wajen Manzon Allah (S) yake yi masa bayanin halin da yake ciki na }unci na rayuwa na rashin abinci da tufafi da kuma ku]i, sai Manzon Allah ya ce masa; “Ga shi kuwa ba ni da wani abu da zan ba ka”. Amma da yake mai nuni ga alheri tamkar wanda ya aikata ne. Sai ya ce masa; “Ka tafi gidan Fatima”. Wannan Dattijo sai ya kama hanya zuwa gidan Sayyida Fatima (AS) da ya je gidan ya yi sallama. Bayan haka ya shida wa Sayyida Fatima (AS) ga halin da yake ciki na bai da abinci da tufafi da kuma ku]i. A lokacin ya zo a kan cewa Sayyida Fatima (AS) ita ma ba ta da shi, saboda haka sai ta je ta ]auko shimfi]ar da Hasan da Husain ke kwana, ta ce ga shi ya je ya sayar domin ya biya bu}atarsa. Sai Dattijon ya ce shi ba zai amsa ba, domin shi a tunaninsa abin ba zai yi }ima ba. Shi wannan Dattijo, kamar yadda ya zo a ruwaya, daga }auye ya zo. To kasantuwar ya raina wannan abin da aka ba shi, sai Sayyida Fatima (AS) ta shiga gida ta ]ebe abin wuyanta, wato sar}a, ta kawo masa. Sai ya amsa, bai tsaya ko’ina ba sai wajen Manzon Allah (S), ya same shi yana zaune tare da Sahabbai, ya ce; “Ya Manzon Allah (S)! Fatima (AS) ta ba ni wannan sar}ar a kan in sayar domin in biya bu}atuna”. Sai Manzon Allah (S) ya fashe da kuka, ya ce yaya ko ba za ka samu biyan bu}ata ba , alhali Fatima ’yar Muhammad Shugabar mataye ta ba ka. Sai Ammar ]an Yasir (RA) ya ce; “Ya Manzon Allah (S) ka ba ni izini in saye wannan abin wuyan”. Sai Manzon Allah (S) ya ce masa yana iya saye. Sai Ammar ya tambayi wannan Dattijon a kan nawa zai sayar masa da sa}ar? Sai ya ce masa; “Ni dai abin da nake bu}ata kayan abinci da tufa ko da kuwa ]aya ne, da kuma Dinare, shi ma ko da kuwa ]aya ne da zai kai ni garinmu”. Aka ce, sai Ammar ya ha]a masa kayayyakin abinci da kuma tufafi da kuma dabbar da zai hau zuwa garinsu, ya kuma ba shi ku]i Dinare 20. Bayan haka sai shi Dattijon ya zo wajen Manzon Allah (S), sai Manzon Allah (S) ya ce masa; “Ka samu abinci da tufan?” Sai Dattijon ya ce; “Ya Manzon Allah (S) ai ni na zama mawadaci”. Saboda farin ciki da jin da]i, kafin ya bar wajen zuwa }auyensu, ya yi addu’a, ya ce; “Ya Allah! Wanda babu wani abin bauta in ba shi ba, ka ba Fatima abin da ido bai ta~a gani ba, kuma kunne bai ta~a ji ba”. Bayan haka, Ammar ]an Yasir da ya sai wannan sar}a, ya sa mata turare na Almiski ya na]e ta a wani }yalle mai kyau ya ba Bawansa ya kai wa Manzon Allah (S). sar}ar da Bawan, duk ya ba shi. Daya isa wajen Manzon Allah (S) ya fa]a masa sa}on. Sai Manzon Allah (S) ya ce ya kai wa Fatima sar}ar da wannan Bawa. Ya je wajen Fatima (AS) ta amshi sar}ar, shi kuma Bawan, ta ’yanta shi. Lokacin da Manzon Allah (S) ya ji haka sai ya yi murmushi ya ce; “Wannan sar}a mai albarka ta biya bu}atar mabu}aci (wato Dattijo)ta ‘yanta bawa,ta kuma koma hannun mai ita. Duk da yake wannan }issa tana da tsawo, amma akwai darussa da yawa a cikinta, amma ba za a iya fitar da su ba saboda gudun tsawaitawa. Haka nan akwai misali da yawa a kyautar Manzon Allah (S), shi ma saboda gudun tsawaitawa ba za a iya ci gaba da kawowa ba. B. Ha}uri da kuma afuwarsa: Manzon Allah (S) ya kasance mai yawan ha}uri da kuma afuwa kan abubuwan da aka yi masa. Akwai Sahabinsa mai suna Anas [an Malik, ya ce ya yi wa Manzon Allah (S) hidima shekara 10; “Amma ko daidai da rana ]aya bai ta~a ce man tir ba. Ko kuma wani abu da na aikata ya ce man me ya sa ka aikata? Ko kuma wani abin da ban yi ba, ya ce me ya sa ba ka yi ba? Kuma bai ta~a zagina ba, ko dukana, ko kuma yi man tsawa ba, ko kuma ya gintse man fuska, ko kuma ya umurce ni in yi wani abu, sai na yi jinkiri wajen yin sa, ya yi min fa]a. Duk bai ta~a yi ba”. Wato wannan yana nuna gayar ha}uri na Manzon Allah (S), kuma mu duba irin cutarwar da gallazawa da mutanen Makka suka yi masa tsawon shekara 13 shi da wa]anda suka yi imani tare da shi. Haka nan bayan hijirarsa zuwa Madina, suka bi shi da ya}o}i daban-daban da kuma }ulle-}ulle da makirce-makirce daban-daban har ya zuwa shekara ta takwas bayan hijira. Lokacin da Allah ya ba shi nasara a kan su, ya tattara su Mushirikan Makka baki ]aya a waje guda ya ce masu; “Me za ku ce? Me kuma kuke tsammani zan yi maku?” Suka ce; “Ba mu tsammanin komai face alheri, domin kai mai karamci ne ]an mai karamci”. Ya ce masu; “To ku tafi na sake ku baki ]aya, kuma na yafe maku”. Mu duba irin wannan gayar ha}uri da Afuwa na Manzon Allah (S). A ce an kwashe shekaru ]ai-]ai har 21 ana cutar da kai, amma daga }arshe ka yi afuwa ga dukkan wannan cutarwar? Kuma ba wai kawai ya yi masu afuwa ba ne, kuma ya kyautata masu, domin bayan Fatahu Makka, ya}in da ya biyo baya shi ne ya}in Hunain, kuma an samu ganima a ya}in sosai. Ya zo a kan cewa wannan ganima mai yawa da aka samu, haka Manzon Allah (S) ya dunga raba ta ga wa]annan da ya saka, kuma ya yi masu afuwa. Wannan ya ba shi Ra}umi 100,200, Akuya 100,200 da dai sauran kayayyaki na ganima. Har ta kai wasu daga cikin Sahabbansa, Ansar suka ji }ai}ayin abin a zukatansu, suka koma gefe suka yi }us-}us cewa ga su, su sun taimaka masa, amma ga shi yana fifita mutanensa da ganima. Da Manzon Allah (S) ya ji haka shi ne ya tara Ansarawa baki-]aya ya yi masu jawabi, wanda ya ratsa zukatansu, su kai ta kuka, suka nemi afuwar }ai}ayin da wasu suka ji a zukatansu da kuma zantukan da wasu suka yi a kan haka. Daga cikin abin da Manzon Allah(S) ya ce masu a cikin jawabin, ashe bai fi maku ba ku tafi da Manzon Allah (S) (wato zuwa Madina), su kuma su tafi da Awaki da Ra}uma (wato zuwa Makka)”, Haka nan Manzon Allah (S) ya yi afuwa ga ]ai-]aikun mutanen da suka cutar da shi ko kuma suka nemi su kashe shi. Alal misali akwai wata Bayahudiya da ta sa masa guba a nama da nufin kashe shi, amma ya yi mata afuwa. Akwai kuma }issar wani mushiriki da ya zo a kan cewa Manzon Allah (S) ya zauna a }ar}ashin wata itaciya domin hutawa, sai ya rataye takobinsa. Sai wannan mushirikin ya lalla~a ya ]auki takobin ya ]aga sama zai sara. Ya ce wa Manzon Allah (S); “Wa zai kare ka daga gare ni?” Sai Manzon Allah (S) ya ce masa; “Allah (T)”. Nan take sai takobin ta fa]i daga hannun mutumin. Sai Manzon Allah (S) ya ]auki takobin ya ce masa; “Wa zai kare ka daga gare ni?” Mutumin ya ce; “Ka zama mai alherin ri}o”. Manzon Allah (S) ya ce masa za ka Musulunta ya ce, a’a. Sai ya ce; “Sai dai in yi maka al}awarin ba zan ya}e ka ba. Ko kuma in kasance cikin wa]anda za su ya}e ka ba”. Sai Manzon Allah (S) ya }yale shi ya tafi. Shi ne da ya koma gida yake ce wa abokansa, na zo maku daga mafi alherin mutane. Mu duba ita ma wannan afuwa ta Manzon Allah (S). Kuma Manzon Allah (S) ya kasance yana cewa; “ Ubangijina ya yi man wasiyya da abu bakwai. Ya yi min wasiyya da yin Iklasi ~oye da bayyane.in yi afuwa ga wanda ya zalunce ni.in ba wanda ya hana min.in sadar ga wanda ya yanke min. Shiruna ya zama tafakkur (wato tunani). Dubina ya zamo lura (wato ]aukar darasi)”. In sha Allah za a ]ora a kai a nan gaba.
|
|||
Last Updated on Tuesday, 29 October 2013 19:41 |