Thursday, 19 September 2024
Email
Make My Homepage
RSS
Register
Darussa daga rayuwar Manzon Allah (S) 3 Print E-mail
Written by administrator   
Sunday, 20 October 2013 11:24

 Kasantuwar ba mu jima da fita daga wata mai albarka ba, wato watan Maulidin Manzon Allah (S), kuma a darussa daga rayuwar Manzon Allah (S) da ya gabata, in za a iya tunawa mun tsaya ne a bayani dangane da Akhlak ]in Manzon Allah (S), wanda muka kakkawo bayani kan kyautarsa a ta}aice da bayani a kan ha}urinsa da kuma afuwarsa, shi ma a ta}aice. A nan muka tsaya.

C. TAUSAYINSA: Manzon Allah (S) ya kasance mai yawan tausayi ga mutane da kuma wannan al’umma tasa, musamman ma ga Muminai, kamar yadda Allah (T) yake fa]i a cikin littafinsa cewa; “Shi (wato Manzon Allah (AS) ga Muminai mai tausayi ne mai jin }ai.” Tausayi ga mutane ta fuskoki guda biyu. Fuska ta farko tausayinsa a fagen Addini. Fuska ta biyu tausayinsa a fagen duniya. Idan mutum ya bibiyi rayuwar Manzon Allah (S) zai ga misali na irin wannan tausayi nasa ga mutane, musamman ma tausayinsa a fagen Addininsu, tunda shi yana da ala}a da makomarsu ta lahira. Misali lokacin da ya tafi da’awa a [a’ifa, dattawan [a’ifa suka sa matasansu suka jejjefi Manzon Allah (S) da duwatsu. Haka suka aiwatar da wannan mummunan aiki, har suka yi masa jina-jina. Shi ne Mala’ika mai kula da duwatsu ya same shi, ya ce ya ba shi umurnin ya yi masu ruwan duwatsu. Shi ne Manzon Allah (S) ya ce masa; “A’a, ina fatan ko su ba su musulunta ba, to a zuriyarsu a samu wa]anda za su musulunta, su bauta wa Allah shi ka]ai ba tare sun ha]a shi da wani ba.” A wata ruwayar kuma Manzon Allah (S) ya ce wata}ila su tuba, daga baya su musulunta.

Haka nan a ya}in Uhudu bayan abubuwan da suka faru, sun faru, wanda daga ciki akwai ji ma Manzon Allah (S) da aka yi a kansa da fuskarsa da kuma ha}orinsa, wanda wannan abu ya jawo }unci sosai a zukatan wasu daga cikin Sahabbansa; shi ne suka ce wa Manzon Allah (S) ya yi addu’a a kan su, wato su ma}iyan da suka yi wannan mummunan aiki, shi ne Manzon Allah (S) ya yi addu’a, amma akasin yadda su wa]anda suka bu}aci addu’ar. A tunaninsu sai Manzon Allah (S) ya ce; “Ya Ubangijina! Ka shiryar da su don su mutane ne da su ba su sani ba.”

Mu duba irin wannan tausayi na Manzon Allah (S) a wannan wa}i’ar ta Uhud da kuma [a’ifa, kuma akwai misalan irin haka da yawa a tarihin rayuwarsa. Kuma daga cikin tausayinsa ga wannan al’umma tasa, akwai lokacin da yake cewa ba domin kada ya matsa wa al’ummarsa ba, da ya umurce su da yin aswaki a kowace Alwala. Haka nan ya kasance mai tausayawa ga iyalinsa. Kamar yadda ]aya daga cikin masu yi masa hidima yake cewa; “Ban ta~a ganin, wani wanda yake da gayar tausayawa ga iyalinsa kamar Manzon Allah (S) ba” Wannan kenan a ta}aice dangane da tausayinsa.

D. TAWALI’UNSA: Manzon Allah (S) ya kasance mai gayar }as}antar da kai. Ya zo a tarihinsa, saboda gayar Tawali’unsa. Mafi yawan lokuta shi yake yi wa kansa hidima, kuma yakan taimaka wa iyalinsa a ayyuka na yau da kullum na cikin gida. Akwai ma wani Sahabinsa da yake cewa, sun je kasuwa tare da Manzon Allah (S), sai ya yi sayayya, sai ya yi nufin ya ri}e abin da ya saya ]in, sai Manzon Allah (S) ya ce, a’a sai dai ya ri}e da kansa. Har yake ce masa ma’abocin abu shi ya fi cancanta da ya ]auki abinsa. Haka nan ya zo a kan cewa, akwai lokacin da ya ziyarci Sahabinsa mai suna Sa’ad [an Ubada. Da zai koma sai ya kawo dabba domin Manzon Allah (S) ya hau, sai ya ha]a shi da ]ansa mai suna {ais domin ya raka shi. Sai Manzon Allah ya hau dabbar ya ce wa {ais ]in ya hawo. Sai {ais ]in ya ce, a’a. Sai Manzon Allah (S) ya ce masa ko dai ya hawo, ko ya koma. Wato saboda Manzon Allah (S) bai son ya kasance shi yana tafiya kan dabba alhali shi kuma {ais yana bin sa a }asa. Wannan shi ma ya nuna tawali’u na Manzon Allah (S).

Akwai ma wani lokacin da suna tafiya da Abdullahi [an Abbas, sai ya kasance yana tafiya a bayansa, sai Manzon Allah (S) ya ce masa ya zo daura da shi, sai abin ya yi wa Abdullahi [an Abbas nauyi, amma kasantuwar ya ga haka Manzon Allah (S) yake so, sai ya zo daura da shi ]in suka ci gaba da tafiya, wanda shi ma wannan yana alamta tawali’un Manzon Allah( S).

Akwai lokacin da ya yi tafiya shi da wasu Sahabbansa, sai suka bu}atu da su yanka dabba, sai wani cikinsu ya ce shi zai yanka dabbar, wani ya ce shi zai jeme, wani kuma ya ce shi zai daddatsa ta, sai Manzon Allah (S) ya ce; “Ni kuma zan nemo itacen da za a dafa”. Mu duba tawali’u na Manzon Allah (S). Akwai misalai da dama na tawali’unsa ta fuskoki daban-daban.

E. KUNYARSA: Manzon Allah (S) ya kasance mai gayar kunya. Saboda gayar kunyarsa sau da yawa akan yi masa abu ko abubuwa na cutarwa, amma sai ya kau da kai, kamar yadda Allah (T) ya yi masa shaida a cikin littafinsa. “Lallai ne wannan yana cutar da Annabi, amma yana jin kunyar ku”.

Ya kasance saboda kunyarsa, ko da bai son abu ne sai dai a gane a fuskarsa. Haka nan ya zo a kan cewa saboda kunyarsa bai dawwamar da dubinsa a fuskar wani. Haka nan ya kasance idan fa]in wani abu gatsai yana da matsala, to yakan yi wa abin kinaya, wato domin sakayawa. Kuma ya kasance saboda kunyarsa idan aka fa]a masa wani ya yi abu da bai dace ba, in zai yi magana a kai bai cewa, me ya sa wane yake kaza? Ko yake cewa kaza? Sai dai ya ce me ya sa wa]ansu mutane suke aikata kaza? Ko suke cewa kaza?

F. AMANARSA: Manzon Allah (S) ya kasance tun yana Makka gabanin aiko masa da sa}o, jama’a kan kawo masa ajiyar kayyayakinsu gare shi. Shi ya sa lokacin da zai yi Hijira zuwa Madina, cikin abubuwan da ya umurci Imam Ali (AS) da yi, baya ga kwanciya a shimfi]arsa, shi ne na ba shi amanonin jama’a da suka kawo masa a kan ya mai da masu. A lokacin har la}abi suka yi masa da Muhammad Amintacce.

Akwai lokacin da Manzon Allah (S) yake cewa; “Wallahi lallai ni Amintacce ne a sama kuma amintacce a }asa”. Kuma ya kasance saboda Amanarsa da kuma gaskiyarsa, ba kawai jama’a na kawo masa ajiyar kaya ba ne, a’a, har }ararraki sukan kawo masa. Ko kuma al’amari ya taso, amma jama’a sai su duba menene matsayinsa? Sai su tsaya a kai. Wannan ma fa tun gabanin aiko masa da sa}o.

Akwai ma lokacin da sa~ani ya auku tsakanin {uraishawa yayin ginin Ka’aba, wanda zai sa Hajarul-Aswad, suka ce to duk wanda ya fara shigowa, to shi ne zai yi mana hukunci. Ikon Allah! Sai ga Manzon Allah (S) ya shigo, duk baki ]ayansu suka ce “mun yarda da duk hukuncin da ya yanke.” Shi ne Manzon Allah (S) ya ce masu, to ga yadda za a yi. Nan take kuwa suka amince da wannan hukuncin na Manzon Allah (S).

G. GASKIYARSA: A wannan fagen hatta ma}iyansa sun yi masa shaida a kai. Akwai ma lokacin da Abu Jahal yake ce wa Manzon Allah (S); “Mu ba mu }aryataka ba, amma abin da ka zo da shi, shi ne muke }aryatawa”. Haka nan ya zo a kan cewa a ya}in Badar, akwai wani da ya ha]u da Abu Jahal ya ke~ance da shi ya ce masa; “Ka gani ba kowa daga ni sai kai, ka fa]a min gaskiya”. Muhammad mai gaskiya ne.Sai ya ce; “Muhammad mai gaskiya ne domin bai ta~a yin }arya ba”. Haka nan Hira} ]an Sarkin Rum ya tambayi Abu Sufyan; “Shin kun kasance kuna tuhumar sa da }arya gabanin ya fa]i abin da ya fa]i?” Ya ce; “A’a”.

H. CIKA AL{AWARINSA: Manzon Allah (S) ya kasance mai gayar cika al}awari. Akwai lokacin da suka yi al}awari da wani, sai da ya kwana uku yana jiran sa. Sai bayan kwana ukun mutumin ya tuna ai ko sun yi al}awari da Manzon Allah (S). Ko da ya zo wajen da suka yi al}awarin, sai ya samu Manzon Allah (S) a wajen yana jiran sa. Wannan al’amarin ya auku tun a Makka ne, wato gabanin aiko masa da sa}o. Shi ne har Manzon Allah (S) yake ce masa; “Ka wahal da ni, tun kwana uku ina nan ina jiran ka”.

Mu duba irin wannan gayar tsarewa da kuma kiyaye al}awari na Manzon Allah (S). Irin wa]annan ]abi’u na Manzon Allah (S) daban-daban da ake gabatarwa, Amanarsa, Gaskiyarsa, Al}awarinsa, Kyautarsa, Tawali’unsa, Ha}urinsa da dai sauran su, yana da muhimmanci su kasance madubi gare mu da za mu dubi kawukanmu da su, mu ga ya muke wajen ]abi’antuwa da su da kuma siffanta da su. Shi ya sa watan Maulidin wata ne na muhasaba a matsayinmu na ]ai-]aiku, da kuma al’ummance, watau kowannen mu ya samu lokaci a cikin watan ya zauna shi ka]ai ya yi wa kansa hisabi. Ya tambayi kansa ya yake wajen koyi da kuma siffantuwa da Manzon Allah (S) wajen ]abi’unsa da ayyukansa da kuma zantukansa.

Haka nan kuma ya tambayi kansa ya yake wajen aikatawa da kuma siffantuwa da sa}on da Manzon Allah (S) ya zo da shi, wato Al}ur’ani mai girma? Wato ya yake wajen aikata Al}ur’ani? Wato ala}arsa da Al}ur’ani ta wajen mujarradin karanta shi, haddarsa da kuma sanin iliminsa? Misali ilimin Tajwidi, ilimin Nasik da Mansuk, ilimin Asbabun Nuzul da dai makamantansu na ilimomin Al}ur’ani. Ya kasance ya ha]a wa]annan tare da aikata shi Al}ur’anin? Shi ya sa idan mutum na karatun Al}ur’ani ana son ya dinga lura da umurce-umurcen da yake karantawa, ya umartu da su?

Haka nan hane-hanen da mutum yake karantawa ya hanu? {issoshin da yake karantawa na Annabawa ya darastu da darussan da ke ciki. Ayoyi na tsoratarwa da yake karantawa,ya tsoratu dasu, na kwa]aitarwa ya kwa]aitu da su? Wato ya kasance yana karanta Al}ur’ani karatu mai ruhi, ba karatu na gafala ba. Wato majarradin karatun lafuzzan ba tare da tunanin wa]annan abubuwa da kuma halartar da zuciya ba. Domin kamar yadda akwai ruhin Azumi, da kuma ruhin Salla, to akwai kuma ruhin karatun Al}ur’ani, wa]anda abubuwan da ake ambata suna daga cikin ruhin karatun Al}ur’ani, wanda in babu su, zai kasance kamar jiki ne babu ruhi.

Muhasabar da mutum zai yi wa kansa, sa’annan ya tambayi kansa ya yake wajen koyi da siffantuwa na ]abi’o’i da ayyuka da kuma zantuka na wa]anda Manzon Allah (S) ya bar wa wannan al’umma nasa su yi ri}o da su a bayansa, wato Ahlul Baiti (AS). Wato kada ya zamanto mutum ala}arsa da Imamai na Ahlul Baiti (AS) mujarradin i’iti}adi na Imamancinsa, wato Khalifancinsu ga Manzon Allah (S), ya zamanto abin ya wuce nan, ya kasance yana mai koyi da siffata da kuma bin su sau da }afa daidai gwargwadon ikonsa.

Idan mutum ya bibiyi zantuka na Imaman Ahlul Baiti (AS) zai ga cewa wannan shi ne babban abin da suka bu}ata daga mabiyansu. Haka nan duk dai a wannan hisabi mutum ya tambayi kansa, ya yake wajen Manzon Allah (S)? Ya kuma Manzon Allah (S) yake wajensa? Tunani a kan wannan yana da gayar muhimmanci, domin ala}antuwa da Manzon Allah (S) a wannan gida na duniya mutum ne yake gina shi. Saboda haka idan mutum ya kasance yana raye, to dama ce babba gare shi na kyautata koyinsa da Manzon Allah (S), domin mutum na mutuwa, dama ta }are. Saboda haka yake da muhimmanci yin  tunani kan ya mutum yake wajen Manzon Allah (S)? Wannan ko ta yin la’akari da kuma tunani na ayyukansa da ake kai wa Manzon Allah (S). Domin kamar yadda ya zo a ruwayoyi na Hadisai, ayyukan da mutane suke aikatawa a matsayi na ]ai-]ai akan kai wa Manzon Allah (S) ayyukan. Wa]ansu su faranta masa rai, ayyukan wasu kuma su ba}anta masa rai. Akwai ma lokacin da Imam Sadi} (AS) yake ce wa mabiyinsa; “Ku daina munana wa Manzon Allah (S). Sai ya ga duk hankalinsu ya tashi. Har wasu suka tambaya, ta yaya muke munana wa Manzon Allah (S)? Imam Sadi} (AS) ya ce masu; “Ba ku san ayyukanku ba ana kai wa Manzon Allah (S)? Wasu ayyukan su faranta masa rai, wasu kuma su ba}anta masa rai”.

Saboda haka kenan ayyukan mutum da ake kai wa Manzon Allah (S) idan kyakkyawa ne, zai kasance kenan za su dinga faranta wa Manzon Allah (S) rai. Wannan kuma shi zai sa ya kasance,  Manzon Allah (S) ya zamto yana son mutum. Kamar yadda ya zo a Hadisi daga Manzon Allah (S) ya ce; “Wanda na fi so daga cikinku, wanda kuma ya fi kowa kusa da ni gobe }iyama shi ne wanda ya fi ku kyawawan ]abi’u”. Kowannen mu yana son ya kasance kusa da Manzon Allah (S) a gidan Aljannah, to wannan duk ya ta’alla}a ne da yadda mutum yake  wajen Manzon Allah (S) a wannan gida na duniya. Idan kuma akasin kyawawan ayyuka na mutum ne ake kai wa Manzon Allah (S), wato munana zai kasance ke nan za su dinga ba}anta wa Manzon Allah (S) rai, kuma haka zai kasance daga cikin dalilin da Manzon Allah (S) zai zamto bai son mutum. Wannan ke nan ta fuskacin ya kake a wajen Manzon Allah (S).

Sai ta fuskacin kuma ya Manzon Allah (S) yake a wajenka? Wannan ko mutum zai yi tunani, ya kuma dube shi ta fuskoki daban-daban. Alal misali yaya sanin sa ga Manzon Allah (S)? Yaya son sa ga Manzon Allah (S)? Yaya shau}insa ga Manzon Allah (S)? Yaya damuwarsa ga cutarwar da aka yi wa Manzon Allah(S)? Da dai sauran ala}o}in }albiyya (wato na zuciya) da Manzon Allah (S), to irin wa]annan ala}o}i na ba]ini, wato kamar son sa, girmama shi, shau}insa na zahiri da kuma ba]ini, wato kamar koyi da shi da kuma ]abi’antuwa da ]abi’o’insa, su ake so mutum ya gina kansa a kai domin ala}antuwarsa da Manzon Allah (S). Kuma irin wannan ala}a da Manzon Allah (S) ta zahiri da kuma ba]ini, mutum ya tambayi kansa, a wannan muhasaba da yake yi wa kansa, shin ya ci gaba ne, ko yana nan a inda yake? Ko kuma wa’iyazubillahi ya ci baya ne daga Maulidin bara zuwa Maulidin bana? In mutum ya binciki kansa, zai ga dai ba zai fita daga ]ayan ukun nan ba. Ko dai ya zamanto mai zaluntar kansa, wato ya ci baya ke nan, ko kuma mai ta}aitawa, wato yana nan inda yake bai ci gaba ba, ko kuma ya ci gaba, wato ya shiga cikin sabi}un, wanda haka ake so. Domin a fagen addini kullum ana son mutum ya dinga ci gaba ne, ba ci baya ba. Ko kuma ya tsaya bai gaba. Shi ya sa ya zo a Hadisi cewa a addini ana son mutum ya dinga duba wanda yake sama da shi, ba wanda yake }asa da shi ba. Saboda wannan shi zai sa mutum ya }ara }aimi akasin kuma a fagen duniya, shi kuma ana son mutum ya dinga duban wanda yake }asa da shi, ba sama da shi ba. Wannan kuma shi zai sa mutum ya dinga godiya ga abin da Allah (T) ya ba shi da kuma wadatuwa da shi. Wannan ke nan a ta}aice dangane da muhasaba a watan Maulidi.

Haka nan watan Maulidi wata ne na godiya ga Allah (T) na wannan babbar ni’ima da ya yi mana na sanya mu cikin ’yan wannan al’umma ta Manzon Allah (S) a kan sauran Annabawa. To, haka nan ya fifita wannan al’umma ta Manzon Allah (S) a kan sauran al’umma da suka shu]e. Ya ma zo a wasu ruwayoyi na Hadisai cewa wasu daga cikin Annabawan Allah (T) kuma Manzanninsa Ulul-Azim, sun yi fata da kuma burin ina ma da su ’yan al’ummar Manzon Allah (S) ne, wato saboda falaloli da kuma darajoji da suka gani na wannan al’umma a littafan da Allah(T) ya ba su kamar Attaura da makamantan su. Saboda haka idan watan ya kama gabanin ya }are, mutum ya samu wani lokaci ya yi salatus shukur ko kuma a}alla sujudus shukur domin godiya ga Allah (T) na wannan babbar ni’ima da ya yi masa na kasantar da shi ]an al’ummar Manzon Allah (S). Wannan ke nan dai a ta}aice. Insha Allah (T) sauran wasu daga cikin darrusa na rayuwar Manzon Allah, kamar ibadarsa da mu’amalarsa misali da iyalinsa, ma}wabtansa, ’yan uwansa na jini, da dai sauran ~angarori na mutane, Shaja’arsa, Zuhudunsa, Mu’ujizarsa da sauransu wajen cin abinci, barci, tafiya, zama, sa tufafi da dai makamantan su.

In Allah (T) ya kai mu wata munasabar za a ]ora a kai.

 

 

Last Updated on Tuesday, 29 October 2013 19:43
 
Home Tarihi Darussa daga rayuwar Manzon Allah (S) 3
Copyright © 2024. www.tambihin.net. Designed by KH