Tuesday, 23 July 2024
Email
Make My Homepage
RSS
Register
Darussa daga rayuwar Ummul A’imma Fatima (AS) 1 Print E-mail
Written by administrator   
Sunday, 20 October 2013 11:21

 Kasantuwar watan Jimada Sani 3 gare shi ne wafati ko shahadar Ummul A’imma, wato Sayyada Zahra (AS), amma wannan a ruwayar da ta fi shahara, domin akwai ruwayoyi da suka zo akasin haka, rubutu ko bayani dangane da tarihi ko rayuwar Sayyada Fatima (AS), wani fage ne mai fa]in gaske, wanda ba za a iya cimma ma}urarsa ba, domin idan mutum ya yi bincike zai ga cewa a tarihin wannan al’umma, ko ma tarihin ]an’adam ba}i ]aya a ~angaren mataye, ba a samu wacce Malamai daban-daban suka yi rubuce-rubuce na littafai dangane da tarihi da kuma rayuwarta ba, kamar Sayyida Fatima (AS).

Alal misali, akwai littafi mai suna ‘FA[IMATUZ-ZAHRA-BAHJATU-{AL-BIL-MUSTAFA (S)’ na  Shaikh Ahmad Al-Hamdaniy, wanda in mutum ya duba littafin zai ga akwai fasali da Malamin ya ke~ance, ya kawo sunayen  littafai na Malamai daban-daban na wa]annan Makarantu guda biyu, wato Shi’a da Sunna, musamman ma na Shi’a da suka yi rubutu dangane da Sayyida Fatima (AS). Misali tarihin da kuma rayuwar ta, ko kuma wani ~angare na rayuwarta,misali iliminta  ko kuma wa}i’a da ta auku, wadda take da ala}a da rayuwarta,misali al’amarin fadak  to ire-iren wa]annan rubuce-rubucen a fasalin Malamin ya kawo sunayen littafai ]ai-]ai har guda 246 wa]anda aka buga. Sannan kuma ya kawo sunayen littafai guda 44 wa]anda ba a buga ba. Ga mai bu}atar ganin sunayen wa]annan littafai yana iya komawa ga littafin da aka ambata a sama, fasali na 40 shafi na 679, zai ga sunayen wa]annan littafai da Malaman da suka rubuta su, da ma inda aka wallafa su.

Sayyada Fatima (AS) kyauta ce ta musamman da Allah (T) ya ba Manzonsa (S), wadda ta hanyarta ne zuriyyarsa suka wanzu, wanda ko a yau akwai su da dama, wato zuriyyar Manzon Allah (S) a kuma sassan duniya daban-daban akwai su. Na ji wani Malami a cikin jawabinsa yana cewa, a yanzu a }iyasi, a}alla akwai jikokin Manzon Allah (S) a sassa daban-daban na duniya sama da miliyan 50. Har ila yau akwai sashen Malaman Tafsiri da suka tafi a kan cewa ayoyin da suka zo a cikin Suratul-Kausar sun ba da  tafsirin Kausar da cewa ana nufin Sayyada Fatima (AS), da dai sauran zantuka na Malaman Tafsiri a kan ma’anar Kausar. Ga mai bu}atar ganin wa]annan zantuka ]in yana iya komawa ga Tafsirin Almizan na Allama Sayyid [aba-[aba’i, juz’i na 20.

Idan mutum ya bi ruwayoyin da suka zo na Hadisai dangane da Asbabun-Nuzul na Surar, zai ga cewa ta sauka ne a kan Mushirikan Makka kamar Abu Jahal da Walid ]an Mugira da dai sauransu, wa]anda suke sukar Manzon Allah (S) lokacin da ’ya’yansa Al}asim da Abdullah (AS) suka rasu, sai suna siffanta shi da cewa shi ‘Abtar’ ne Wal iya Zubillah, wato ma’ana wanda bai da tsatso a bayansa, shi ne wa]annan Ayoyin na Suratul Kausar suka sauka.

Wa]annan Ayoyi na wannan Sura guda uku ne, ita ce mafi gajartar Sura a cikin Surorin Al}ur’ani. In muka duba Aya ta }arshe cikin Surar, Allah (T) yana cewa, “Lallai mai aibantaka shi ne Abtar.” Mu duba mu gani a yau wa za ka gani, ko ya ce shi jikan Abu Jahal ne, ko jikan Wali ]an Mugira ne? Babu. Sai dai jikokinsu a munanan ayyukansu, amma ba a jini ba. Amma jikokin Manzon Allah (S) fa,ga sunan  a sassa daban-daban na duniya,a wa]ansu wajaje  ma saboda girmamawa gare shi suna da alama ko la}abi daga gani ko ka ji, ka san wannan jikan Manzon Allah (S) ne, misali alamar ba}in rawani, ko ba}ar hula, ko sa alama koriya, da dai makamantansu. Ko amsa la}abin Sayyid, ko Sharifi da dai makamantansu, ya danganta daga nahiya zuwa nahiya.

Haka nan kuma Sayyida Fatima (AS) kyauta ce ta musamman da Allah (T) ya bai wa wannan al’umma ta Manzon Allah (S), domin A’imma na Ahlul Baiti (AS) wa]anda Manzon Allah (S) ya bar wa wannan al’umma a matsayin Khalifofi a bayansa, kuma in an bi su ba za a ~ace ba. To dukkansu  in ka ]ebe Imam Ali (AS), sun kasance ’ya’ya da jikokin Sayyida  Fatima (AS) kuma idan mutum ya bibiyi tarihin wannan al’umma ta Manzon Allah (S) zai ga cewa gudummuwar da zuriyyar Sayyida Fatima (AS) suka bayar wajen raya wannan addinin na Musulunci da kuma kare shi, ya fi na kowa, kuma wannan a dukkan fagage na addini zai ga sun ba da gudummuwa fiye da kowa.

Alal misali, a fagen ilimi ne, a fagen gwagwarmaya ne, a fagen suluki zuwa ga Allah (T)ne. kuma a wannan zamanin mutum ya duba ya gani zai ga haka. Misali a Iran, Sayyid Imam Khumaini, a Ira}I, Sayyid Shahid Muhammad Ba}ir Sadr, Ayyatullahi Sayyid Ku’i, a Labanon, Sayyid Shahid Abbas Musawi, ga Sayyid Nasrullah. Mu ma a wannan nahiyar tamu Alhamdulillah ga Sayyid Ibraheem Zakzaky (H). Mu duba irin gudummuwar da ya bayar kuma yake kan bayarwa wajen raya wannan addinin da kuma kare shi,a wannan }asa da muke ciki. Shi ya sa in mutum ya yi bincike zai ga akwai Hadisai masu yawa da suka zo, da suke nuna muhimmancin girmama zuriyar Manzon Allah (S) da kuma kyautata masu.

Ga wasu daga ciki 1. An samo daga Imam Ali (AS) ya ce Manzon Allah (S) ya ce; “Mutum hu]u ni zan cece su gobe }iyama, mai girmama zuriyyata, mai biya masu bu}atunsu, mai kai-koma cikin al’amuransu a lokacin tsananinsu, mai son su da zuciyarsa da kuma harshensa”.

2. An samo daga Imam Sadi} (AS) ya ce Manzon Allah (S) ya ce; “Wallahi ba zan yi ceto ga duk wanda ya cutar da zuriyya ta ba”.

3. Manzon Allah[S] ya ce; “Cetona ya tabbata ga duk wanda ya taimaki Zuriyyata da hannunsa da harshensa da kuma dukiyarsa”.

4. Manzon Allah (S) ya ce; “Ku so Zuriyyata kuma ko girmamasu”.

5. An samo daga Imam Ridha (AS) ya ce; “Dubi zuwa ga zuriyata ibada ce, (shi wanda ya ruwaito wannan Hadisi ya ce wa Imam Ridha (AS) dubi zuwa ga A’imma daga cikin zuriyar ko kuma dubi zuwa ga Zuriyar Annabi? Imam Ridha (AS) ya ce masa a’a, dubi zuwa ga dukkan zuriyyar Manzon Allah (S) ibada ce, amma matu}ar su ba su bar tafarkinmu ba. Kuma ba su caku]a da sa~o ba.” Da dai Hadisai masu yawa a kan haka. Wanda ba za a iya kawo su ba saboda gudun tsawaitawa.

Haka nan idan aka duba zuwa ga darajoji da kuma matsayi na Sayyida Fatima (AS), za mu ga akwai Hadisai da dama da suka zo a kan haka. Akwai ma sashen Malamai da suka rubuta littafai hususan kan matsayinta da kuma darajojinta. Misali ga biyu daga cikin littafan. 1. Fada’iluz-Zahra (AS) na [abrasi, 2.Fada’ilu Fa]imatiz-zahra (AS) na Hakim Annaisaburi, da dai sauran su. Amma ga wasu Hadisai da suka zo dangane da darajojinta da kuma matsayinta. Manzon Allah (S) ya ce, “Fa]ima Shugabar mataye ce baki ]aya.” Sai aka tambaye shi Maryam ’yar Imran fa? Sai ya ce, “Ita Shugabar Mata ce, amma na zamaninta.” Haka nan ya zo cikin littafin Kanzul Ummal da kuma Mizanul i’itidal, daga Manzon Allah (S) ya ce; “Farkon wanda zai soma shiga Aljannah Fa]ima ce.”

Haka nan ya zo a kan cewa Fatima (AS) ita ce Shugabar matayen Aljannah. Haka nan ya zo dai a cikin wa]annan littafai da aka ambata, Manzon Allah (S) ya ce, Allah (T) yana fushi da fushin Fatima (AS) yana yarda da yardarta. A wani Hadisi kuma Manzon Allah (S) ya ce; “Duk wanda yake son Fatima (AS) ha}i}a yana so na, duk wanda ya fusata ta ha}i}a ya fusata ni.”

A wani Hadisi kuma, Manzon Allah (S) ya ce; “Da a ce kyau mutum ne, to da Fatima ce.” Da dai sauran Hadisai masu yawa a kan fada’il ]inta. Kai ko dama a ce babu Hadisai da suke bayani dangane da matsayinta, kasantuwarta ’ya ga Fiyayyen Halitta, mata ga Imam Ali (AS) Uwa ga Imam Hasan da Husain (AS) ya isa ya zame mata babbar daraja da kuma matsayi, ballantana kuma ga ‘nusus’ a kan haka, wato Hadisai da wasu ayoyi.

Da mutum ya duba da kyau zai ga cewa komai na Sayyida Fa]ima (AS) tun daga wiladarta zuwa wafatinta ‘SAMAWIY’ ne. Wato ko dai daga sama ya zo, ko aka aiko da shi, ko kuma aka yo wahayinsa. Ga misalai; Ya zo a Hadisai cewa ‘Nu]fa’ wanda ya kasance sabab na ]aukar cikin Fatima (AS) ya kasance ne daga ’ya’yan itace da Manzon Allah (S) ya ci a Aljanna, wa]anda suka kar~i haihuwarta daga Aljanna suka zo, su ne Mahaifiyar Annabi Isa (AS), wato Maryam ’yar Imran, ’yar uwar Annabi Musa (AS), Kulsum, Asiya ’yar Muzahim wadda Fir’auna ya kashe, da kuma Saratu matar Annabi Ibrahim (AS). Ga mai bu}atar }arin bayani ko ganin haka. Ya duba littafin Muntahal Amal juz’i na ]aya na Shaikh Abbas Al}ummy, wato marubucin Littafin Mafatihul Jinan.

Shi ma wannan suna nata, FATIMA, saukakke ne daga sama, wato an yo wahayi ne a sa mata wannan suna. Haka nan kuma ]aurin aurenta sai da aka yi a sama, sannan aka yi a }asa Likafaninta daga Aljannah yake. Da dai sauran ababe nata samawiyya. Ya ma zo daga Ma’asumai (AS) cewa; “Talauci ba ya shiga gidan da yake akwai mai suna Fatima (AS)”. Akwai Hadisi da ya zo daga Imam Sadi} (AS) da ke nuni dangane da girmama sunan, da kuma girmama wadda aka sa wa sunan. A ta}aice dai darajoji da falaloli na Sayyida Fatima (AS) suna da yawan gaske

TARIHINTA

An haifi Sayyida Fatim a (AS) a Makka, ranar Juma’a 20 ga watan Jimada Sani, Shekara ta biyar, bayan aiko wa Manzon Allah (S) da sa}o. Akwai sashen Malamai da suka tafi a kan cewa she}ara biyu bayan bi’isa ne. Amma su Malaman Ahlus Sunna sun tafi a kan cewa she}ara biyar gabanin aiko Manzon Allah (S) ne aka haife ta. Sunan Mahaifiyarta, kamar yadda aka sani, Khadijah (AS). Tana da shekara biyar Allah (T) ya yi wa Mahaifiyarta rasuwa, domin ta rasu shekara 10 bayan bi’isa. Har ila yau a wannan shekarar ce Allah (T) ya yi wa Abu [alib (AS) rasuwa. Ya zo a kan cewa tsakanin rasuwar Khadija da Abu [alib (AS) kwana uku ne. Shi ya sa shekarar aka yi mata la}abi da shekarar ba}in ciki. Bayan rasuwarsu ne Manzon Allah (S) ya tafi [a’ifa domin isar da sa}o.

Wani ]an tambihi a nan shi ne, Malaman Madrasah ]in Ahlul Baiti (AS) sun tafi a kan cewa ’ya’yan Manzon Allah (S) baki ]aya an haife su ne gabanin aiko masa da sa}o, in ban da Sayyida Fatima (AS) da kuma Ibrahim ]an Mariya. Su bayan bi’isa ne aka haife su. Har ila yau akwai ayyukan da ake son aikatawa ranar wiladar Sayyida Fa]ima (AS), daga ciki akwai Azumi, wato ana son mutum ya yi Azumi a ranar domin godiya ga Allah (T) ga wannan babbar kyauta da ya bayar, da kuma yin Alhairai a ranar da sadakoki ga muminai da kuma yin ziyara ga Sayyida Fa]ima (AS). Yadda ziyarar take, mutum na iya komawa ga littafin Mafatihu. Har ila yau a irin wannan ranar ne ta haihuwar Sayyida Zahra (AS) aka haifi Imam Khumaini, an haife shi ne 20 ga watan Jimada Sani a she}ara ta 1321 bayan hijira.

Sayyida Fatima (AS) tana da sunaye da yawa da kuma la}ubba masu yawa. Imam Sadi} (AS) ya ce Fatima (AS) tana da sunaye tara a wajen Allah (T), su ne: Fatima, Siddi}a, Mubaraka, [ahira, Zakiyya, Radiyyah, Muhaddisa da kuma Zahra. A wata ruwaya, akwai Mardiyya, da kuma Batul. Daga kuma cikin la}ubbanta, akwai Ma’asumma, Karima, Shahida, Rashida, Sabira, Mu’azzama Mazluma da dai sauransu. Haka nan kuma tana da kinaya da yawa, amma wa]anda suka fi fice su ne: Ummul A’imma da kuma Ummu Abiha.

Ya zo a kan cewa Manzon Allah (S) ne ya yi mata kinaya da haka. Manzon Allah (S) ya kasance yana girmama Sayyida Fatima (AS) gayar girmamawa. Ya zo a kan cewa in ta zo wajen shi a gida yakan tashi, ya ce ta zauna inda yake zaune. Haka nan Manzon Allah (S) ya kasance idan zai yi tafiya, bayan ya bar gida, sai ya biya wajen Sayyida Fatima (AS) ya yi bankwana da ita, sannan ya tafi, in kuma ya dawo daga tafiyar, sai ya biyo gidan Fatima (AS), sannan ya wuce gida.

Sayyida Zahra (AS) ta tashi a Makka, gaban Mahaifinta. Saboda haka dukkan tsangwama da wahalhalu da Manzon Allah (S) ya fuskanta daga ma}iya a Makka wajen isar da wannan sa}o, a gaban idonta suka wakana. Ya ma zo a tarihinta cewa, bayan rasuwar Mahaifiyarta Khadija (AS), idan Manzon Allah (S) ya fita yin da’awa, kuma ma}iya suka yi masa jina-jina, in har ya dawo gida, Sayyida Fatima (AS) ce ke wanke masa. Akwai lokacin da ya je Ka’aba yana Salla, bayan ya yi sujuda ma}iya suka ]auko tumbin dabba, wanda ya ru~e yana wari suka sa masa a baya. Sai aka je aka shaida wa Sayyida Zahra (AS) ita ta zo ta ]auke masa. Daga irin wa]annan ayyuka da take yi wa Manzon Allah (S), wasu Malamai suke ganin wannan kinaya da Manzon Allah (S) yake yi mata na Ummu Abiha ya samo asali. Haka wannan yanayi ya ci gaba da gudana har zuwa lokacin da Manzon Allah (S) ya yi hijira daga Makkah zuwa Madina.

Kafin hijirarsa, ya yi umurni ga Imam Ali (AS) da ya kwana a shimfi]arsa, da kuma mi}a masu ajiyoyi da amanonin kayyayakinsu. Bayan nan ya zo Madina ya same shi tare da iyalinsa. Haka kuma al’amarin ya auku bayan Imam Ali (AS) ya mi}a amanoni da kuma ajiyoyi na mutane, sai ya kama hanya zuwa Madina tare da wa]annan bayin Allah (T), su ne Sayyida Fatima (AS) da Fatima ’yar Asad, wato Mahaifiyar Imam Ali (AS), da Fatima ’yar Hamza, da kuma Fatima ’yar Zubair ]an Abdul Mu]allib, tare kuma da wasu mazaje guda biyu, su ne Ai’man da kuma wani da ake ce wa, Abu Wa}idil-laisi. Haka suka yi hijira daga Makka zuwa Madina, suka bar Makka da rana, ido na ganin ido suka kama hanya.

Bayan fitarsu, sai {uraishawa suka aiko maya}a takwas a kan su bi su da umurnin cewa su kashe Imam Ali (AS). Suka bi su, suka same su a wani waje da ake ce wa Dajanan. Da Imam Ali (AS) ya ga haka sai ya tsai da tafiyar, ya ce wa wa]annan mazaje guda biyu da ke tare da shi, wato Ai’man da Abu Wa}id, da su gurfanar da ra}uman da wa]annan bayin Allah (T) ke kai, ya sa a ]aure ra}uman. Bayan haka ya tafi wajen su ma}iyan da takobinsa, sa-in-sa ta magana ta gudana a tsakaninsu. Daga cikin abubuwan da suka ce wai shi da wa]annan bayin Allah (T) su koma Makka ]au’an ko karhan. Haka dai musayar maganganu suka gudana. Daga }arshe abin ma ya kai ga gumurzu. Tunda suka ga Imam Ali (AS) ya samu ]ayansu, wanda ya fi za}ewa, ya rafke shi, ya sassare shi da takobi, ganin haka sauran maya}an suka tarwatse suka gudu. Bayan haka sai su Imam Ali (AS) suka ci gaba da tafiya har suka iso Madina.

Ya zo a kan cewa lokacin da Manzon Allah (S) ya iso Madina, bai shiga Madina ba. Ya tsaya a wani waje ne da ake ce masa }uba, har a lokacin wasu suka ce masa ya shiga Madina mana, ya ce, ba zai shiga ba har sai ]an Amminsa da kuma ’yarsa sun iso, haka kuwa aka yi. Sai da suka iso, sannan Manzon Allah (S) ya shiga Madina. An ce lokacin da Imam Ali (AS) ya iso Madina }afafuwansa sun kukkumbura sun kuma tsattsage, saboda ya zo a }asa tun daga Makka har zuwa Madina, ba a kan dabba ba.

Insha Allah a kashi na biyu na darussa daga rayuwar Ummul A’imma, Fatima (AS) za a ]ora a kai. Wato rayuwar Sayyida Fatima (AS) bayan komawa Madina.

 

 

Last Updated on Tuesday, 29 October 2013 19:44
 
Home Tarihi Darussa daga rayuwar Ummul A’imma Fatima (AS) 1
Copyright © 2024. www.tambihin.net. Designed by KH