Darussa daga rayuwar Ummul A’imma, Fa]ima(AS) 2 |
Written by administrator | |||
Sunday, 20 October 2013 11:14 | |||
Bayan komawar Sayyida Fatima (AS) Madina, ta ci gaba da zama gaban Mahaifinta, a shekara ta biyu bayan hijira, a watan Rajab, (a wata ruwaya kuma watan Zulhijja), Manzon Allah (S) ya ]aura mata aure da Imam Ali (AS). Ga mai son }arin bayanin yadda auren ya gudana da sadakin auren da ma Sahabban da suka nemi aurenta da amsar da Manzon Allah (S) ya ba su, na cewa yana jiran umurnin Allah (T) ne, yana iya komawa ga littafan tarihi. Misali, FA[IMATUZ-ZAHRA, MINAL MAHDI ILAL LAHDI, na Shaikh Muhammad Kazim, ko kuma littafin FATIMATUZ-ZAHRA (AS) BAHJATU {ALBIL MUSTAFA (S), na Shaikh Ahmad Al-Hamdaniy da dai sauran littafai. Bayan wannan ]aurin auren mai albarka, Sayyida Fatima (AS) ta yi inti}ali daga gidan Nubuwwa zuwa gidan Imamanci. Allah (T) ya sanya wa wannan auren albarka mai yawa, don ta hanyarsu ne zuriyar Manzon Allah (S) ta wanzu zuwa yau ]in nan. Kuma za ta ci gaba da wanzuwa har zuwa tashin }iyama. Akwai wani Hadisi da ya zo daga Manzon Allah (S) da yake cewa; “Allah (T) ya sanya zuriyar kowane Annabi a tsatsonsa, amma ya sanya zuriyata a tsatson Ali (AS).” Sayyida Fatima (AS) ta haifi ’ya’ya guda biyar, maza uku, mata biyu, dukkansu Manzon Allah (S) ne ya sa masu suna. Na farko kamar yadda aka sani Imam Hasan (AS), na biyu Imam Husain (AS, ta uku ita ce Sayyida Zainab (AS), ta hu]u ita ce Sayyada Ummul Khulsum (AS), na biyar shi ne Muhsin (AS). Duk da shi ya zo a kan cewa ta yi ~arinsa ne, sakamakon wa]ansu al’amura da suka wakana marasa da]in ji da karantawa bayan rasuwar Manzon Allah (S). Bayanin haka zai zo insha Allah nan gaba. Ta yiwu a nan mutum ya kawo ishkal ]in cewa, an ce Manzon Allah (S) ne ya sanya masu sunaye, alhalin Muhsin a bayan wafatin Manzon Allah (S) ne aka yi ~arinsa. Amsa a nan ita ce dama tun gabanin wafatin Manzon Allah (S) ya shaida wa Sayyida Fatima (AS) abin da ke cikinta cewa, namiji ne kuma ya sanya masa suna Muhsin. Ya zo daga Imam Ali (AS) yana cewa; “Ku sanya wa yaranku suna tun gabanin haihuwarsu. In ba ku san abin da yake cikin ba, namiji ne ko mace, to ku sanya masu sunayen da suke ]aukar namiji da mace, (ko kuma misali mutum ya ayyana cewa in mace ce, kaza, in kuma namiji ne, kaza). Domin ~arinku, idan suka ha]u da ku ranar }iyama ba a sa masu suna ba, shi ~arin zai ce me ya sa ba ka sa min suna ba, alhali Manzon Allah (S) ya sanya wa Muhsin suna tun kafin a haife shi?” Sayyida Fatima (AS) ta rayu tare da Imam Ali (AS) rayuwa ]ayyiba, wacce take babban darasi ga ma’aurata. Alal misali ya zo a kan cewa Imam Ali (AS) yana cewa; “Tun da muke da Fatima ba ta ta~a ~ata min rai ko ta sa~a min a wani al’amari ba. Na kasance in na dube ta duk ba}in ciki da damuwa da yake tattare da ni yakan gushe”. Kuma ya ci gaba da cewa; “Wallahi tun da muke da ita ban ta~a ~ata mata ta rai ba, ko in tilasta ta a kan wani al’amari ba, har Allah (T) ya amshe ta.” Haka nan ita ma Sayyida Fatima (AS) a wasiyyarta take ce masa; “Tun da muke da kai ban ta~a sa~a maka ba.” Ta yo masa wasiyya da wasu al’amura, sannan ta ce masa, Allah (T) ya saka masa da alheri. Akwai wani abu da ya ta~a faruwa. Wata rana Imam Ali (AS) ya wayi gari yana jin yunwa, sai ya ce; “Ya Fatima (AS)! Akwai wani abu a wajenki na abinci?” Sai ta ce; “A’a. Ina ranstuwa da wanda ya girmama Babana da Annabta, ya kuma girmama ka da Wasicci, ba abin da na wayi gari da shi na abinci.” Ta ce; “Babu wani abinci gare mu tun kwananki biyu, face abin da na ]an fifita ka da shi a kaina da kuma wa]annan ’ya’yan namu, Hasan da Husain (AS).” Sai Imam Ali (AS) ya ce mata; “Ya Fatima (AS)! Me ya sa ba ki sanar da ni ba domin in nemo wani abu?” Sai ta ce; “Ya baban Hassan! Ina jin kunyar Ubangijina in kallafa maka abin da ba ka da iko da shi.” Akwai ire-iren wa]annan abubuwa wa]anda suke nuna yadda Sayyida Fatima (AS) ta rayu tare da Imam Ali (AS), wa]anda ba za a iya kawo su ba, saboda gudun tsawaitawa. Amma abin ba}in ciki sa~anin wasu zantuka wa]anda aka }ir}ira aka jingina su ga Imam Ali (AS) da kuma Sayyida Fatima (AS), domin ~ata shaksiyarsu. Wa]anda akan ci karo da su jifa-jifa a cikin littafai. Ga misalin guda biyu daga ciki. Na farko, wai sa~ani ya ta~a aukuwa tsakanin Imam Ali (AS) da Sayyida Fatima (AS), sai da Manzon Allah (S) ya yi sulhu tsakaninsu. Wai da ya je gidan ma ya samu Imam Ali yana barci a gaban }ofar gidan, shi ne wai Manzon Allah (S) ya zauna yana share masa tur~aya, yana ce masa; “Ka tashi ya Abut-Turab!” Sannan ya kama hannunsa ya shigar da shi wajen Fatima (AS) ya sasanta su. Shaikh Sadu} a cikin littafinsa na Ilal da ya kawo wannan labarin, shi ne ya ce; “Wannan labarin a wajena ba abin dogaro ba ne, kuma ban yarda a kan cewa dalilin haka ne ake ce wa Imam Ali (AS) Abut Turab ba”. Ya ci gaba da cewa; “Domin Imam Ali (AS) da Sayyida Fatima (AS) ba zai yiwu ka ce sa’insa ya auku tsakaninsu ba, wanda zai kai ga Manzon Allah (S) ya yi sulhu a tsakaninsu. Domin Imam Ali (AS) shi ne Shugaban Wasiyyai, ita kuma ita ce Shugabar mataye baki ]aya. Kuma sun kasance masu koyi da Manzon Allah (S) wajen kyawawan ]abi’unsa”. Kuma bayan haka muna da i’iti}adin cewa su Ma’asumai ne. Wani misali da Imam Khumaini ya bayar cewa; “Da Allah (T) zai tara Annabawansa baki ]aya tun daga kanAnnabi Adam har zuwa Manzon Allah (S) a unguwa ]aya, ya tambaya, za a samu sa~ani tsakanin su? Amsa ya ce; “A’a saboda kowannensu, zuciyarsa a tsarkake take, kuma Allah (T) yake nufi.” Abu na biyu shi ne abin da ya zo a wasu littafai cewa, wai Imam Ali (AS) ya nemi auren ]iyar Abu Jahal, sai labarin haka ya kai ga Fatima (AS) sai ta kai }arar sa ga Manzon Allah (AS), wai sai Manzon Allah (S) ya hau kan mumbari ya yi hu]uba, ya nuna haka ba zai yiwu ba, ya kuma ce; “Duk wanda ya cutar da Fatima ya cutar da ni, wanda kuma ya cutar da ni, to ya cutar da Allah (T)”. A wannan labarin Shaikh [usiy, yana cewa; “Wannan labarin ~atacce ne, kuma }ir}irarre, asalinsa daga wani mutum ne da ake ce wa Karabisi-Albagdadiy, ya ce ya yi haka ne domin suka ga Imam Ali (AS)”. Da daidai ire-iren wa]annan abubuwa wa]anda mafi yawansu an }ir}ire su ne a zamanin Bani Umayyah. Irin wa]annan }ir}ire-}ir}ire da kuma }aryayyaki ba su ta}aita ga A’imma na Ahlul Baiti ba (AS), har da mabiyansu ma an yi. Ga misalin biyu shi ma daga ciki. Wai cewa ’yan Shi’a suna da i’iti}adin Mala’ika Jibril ya yi kuskure, wai lokacin da Allah (T) ya ba shi sa}o zuwa ga Ali (AS) sai ya yi kuskure ya ba Muhammad (S). Wannan }arya ce tsagwaronta. Wadda aka }ir}ira aka jingina wa mabiya Madrasa ]in Ahlul Baiti (AS) da nufin ~ata sunansu da kuma sa }iyayyarsu a zukatan Musulmi da kuma nufin ya zama hanyar da za a zubar da jininsu da kuma ~ata dukiyoyinsu. Wanda ko da a hankalce mutum ya tambayi kansa, ko da mutum ]an uwansa ba wai Mala’ika wanda yake Ma’asumi ba, wato ba ya kuskure, misali, sai ka ba wa wani mutum sa}o ya kai wa ]an shekara 10, amma da ya je sai ya kasa bambance shi da ]an shekara 40, maimakon ya ba ]an shekara 10 ]in, sai ya bai wa ]an shekara 40, kuma ya ci gaba da wannan kuskure har tsawon shekara 23 duk bai gane kuskure yake yi ba.Domin a lokacin Imam Ali[as] yana da shekaru kusan goma ne.Manzon Allah[S] kuma yana da shekaru 40.Wannan ke nan ga ]an’adam fa. To ina ga abin da yake sa}o ne daga masanin gaibi, kuma mahaliccin kowa da komai, ta hanyar Mala’ikansa, zuwa ga Fiyayyen halitta baki ]aya? Ai ya kamata mutum ya auna ko da da hankalinsa, ballantana kuma abu ne sananne a ‘nassin Al}ur’ani’ cewa Mala’iku Ma’asumai ne, wato ba su kuskure ba su mantuwa, ba su kuma sa~a wa Allah (T) kan abin da ya umurce su. Misali na biyu, wai ’yan Shi’a suna da wani Al}ur’ani sa~anin wanda yake hannun Musulmi. Wanda wannan in za a iya fa]a wa mutumin zamanin da ya yarda, mutumin wannan zamanin shi yana da hanyoyin da zai iya binciken wannan abu cikin sau}i. Saboda duniyar ta ]unkule ta zama kamar }auye guda. Hanyoyin sadarwa da kuma mu’amala da juna suna da sau}i, ba kamar zamanin da ba. Saboda haka cikin sau}i za ka iya bincike in kana so, kan wani abu da aka jingina wa wasu Musulmi. Makamancin haka ya ta~a ha]a ni da wani Musulmi ]an wata }ungiya, muna tattaunawa kan irin wa]annan abubuwa da aka jingina wa Shi’a, sai ya ce min ai ’yan Shi’a suna da wani Al}ur’ani. Sai na ce masa ba gaskiya ba ne. Sai ya ce min haka abin yake, a ciki ma akwai wata sura, wai Suratul Wilayah. To a lokacin akwai Al}ur’ani tare da ni bugun Iran. Sai na mi}a masa na ce ya duba bugun ina ne? Ya duba ya ce bugun Iran ne. Sai na ce ya nuna min Suratul Wilaya a ciki. Ya duba ya duba, jerin surorin, ya bu]e shafuffukan Al}ur’anin, ya ce bai gani ba. Amma abin mamaki duk da haka ya ce ai an ce suna da Suratul Wilayah. Sai na ce masa amma ga shi ai kai ba ka gani ba. Ka ce ne an ce, har a lokacin nake ]an yi masa bayani cewa in za ka hukunta mutum, to za ka hukunta shi ne da abin da ka ji, ko ka gani, ba abin da aka fa]a maka ba dangane da shi. Na da]a masa da cewa babban abin da yake cutar da Musulmin da suke da ire-iren wa]annan ra’ayoyi ga ’yan Shi’a shi ne, suna samun ’yan kutaibat, wato }ananan littafai wa]anda ma}iya Shi’a suka rubuta, maimakon su samu littafan da su ’yan Shi’ar suka rubuta da kansu, su karanta. Sa~anin yadda muke a nan, da mutum zai je }asashen Shi’a zai ga akasin haka, wato mutum zai ga Malamansu suna da littafan Ahlus Sunnah, da littafan Shi’a. Mu ko a nan da kuma sauran }asashen Ahlus Sunnah. Za ka ga mafi yawansu ba su da litttafan Shi’a, ko da ka samu, galibi za ka ga littafai ne da ma}iya Shi’a suka rubuta, su suke karantawa, suke kuma kafa hujja da su. Saboda haka akwai bu}atar yin tunani a kan wannan abu da kuma gyara a kai. Musamman idan muka yi la’akari da yadda ma}iya addinin Musulunci da Musulmi suka tasa al’ummar Musulmi gaba, ba tare da tantancewa kai ]an Sunan ne ko Shi’a ba. Wannan ke nan dai a ta}aice.Kuma mutum ya auna da hankalin sa yau da ace ‘yan shia,suna da wani Al’}urani,to da wannan zamanin da muke ciki,wanda yake da kayan buge-buge na littafai masu yawa,to da masu ya]a irin wa]annan }aryaryaki da sun buga su,sun ya]a a duniya.Bayan haka kuma mu duba fa]in Allah[T] mu muka saukar da Al-}ur’ani,mune kuma masu kare shi,To mai irin wannan tunani yaya zai da wannan ayar? Sayyida Fatima (AS) ta rasu ran 3 ga watan Jimada Sani, shekara ta 11 bayan hijira, amma wannan a kan nassin ruwayar da ta fi shahara, domin akwai ruwayoyi akasin haka. A kan asasin wannan ruwaya tsakanin wafatinta da wafatin Manzon Allah (S) wata uku ne da kwana biyar. Wa]annan watanni uku da kuma kwana biyar na }arshen rayuwarta, ta fuskanci jarabawowi a cikinsu, fiye da dukkan jarabawowin da ta fuskanta a tarihin rayuwarta. Wanda insha Allah in an zo bayani dangane da jarabawowinta za a kawo wasu daga ciki. Haka nan akwai sa~ani na Malamai a kan ainihin inda }abarinta yake. Akwai zantuka uku; wasu Malaman sun ce }abarinta a ba}i’a yake, wato kusa da }aburburan Imamai hu]u (AS) da ke wajen. Wasu kuma sun ce }abarinta yana tsakanin }abarin Manzon Allah (S) da kuma mumbarinsa. Wasu kuma sun ce a cikin ]akinta }abarinta yake. Sanin ainihin inda wannan }abarin nata yake ga mutane, insha Allah, sai dai Imam Mahdi (AF) ya bayyana. Shi ne zai fa]i ainihin inda }abarin nata yake, kuma ~oyuwar }abarin ta ga mutane, tare da irin wa]annan darajoji da kuma matsayinta a hankalce zai nuna wa mutum cewa, lallai wani abu ya faru. Kuma ga dukkan alamu marasa da]i ne. Ga mai bu}atar ganin wa]annan ababe, yana iya komawa ga littafan tarihi, misali littafin Muntahal-Amal na Shaikh Abbas {ummy da dai makamantansu. Sai kuma wasu darussa daga ~angarori na rayuwarta domin su kasance darasi da za mu darastu da su, wato ta hanyar }o}arin aikatawa daidai gwargwadon ikonmu. 1. IBADARTA: Sayyida Fatima (AS) ta kasance mai yawan ibada. Akwai wata magana ta Hasanul Basari yana cewa; “Babu wani a wannan al’umma wanda yake ya kai Fatima (AS) ibada, ta kasance tana tsayuwa wajen Salla, har }afafuwanta su kumbura.” Imam Hasan (AS) yana cewa Mahaifiyata Fatima (AS) ta kasance mai yawan ibada. Akwai lokacin da yake cewa; “Na ga Mahaifiyata Fatima (AS) ta tsaya a wajen ibadarta a daren Juma’a, ba ta gushe ba tana ruku’u tana sujuda har gari ya waye, bayan haka sai in ji tana addu’o’i ga Muminai maza da Muminai mata, tana ambatonsu da sunayensu, amma ita ba ta yi wa kanta addu’a ba, sai nace mata ya mahaifiyata mai ya sa ba ki yi wa kanki addu’a , kamar yadda na ji kina wa wasu? Sai ta ce ya ]ana « makwabci sannan gida ». Kuma ya zo cewa ta kasance idan tana ibada a ]akinta, haske yakan bayyana ya haskaka birnin Madina baki ]aya, nan ne ma wannan suna nata na Zahra ya yo asali. Shi ya sa a lokacin da an ga haske ya haskaka ko’ina, idan aka zo aka duba, sai a ga Sayyida Fatima (AS) take ibada. Kuma wannan haske kamar yadda ya zo a Hadisi, ba wai kawai ga mutanen }asa ba, har Mala’iku a sama suna ganin wannan hasken. Manzon Allah (S) ya ce; “ Duk lokacin da Fatima ta tsaya a wajen ibadarta, haskenta yakan bayyana ga Mala’ikun sama, kamar yadda hasken taurari ke bayyana ga wa]anda suke doron }asa. A lokacin Allah (T) ya ce wa Mala’ikunsa; “Ya ku Mala’ikuna! Ku duba baiwata Fatima, Shugabar bayina mata, ta tsayu gaba gare ni. Ga~u~~anta na makyarkyata saboda tsorona, ta halarto da zuciyarta ga ibadata. Ina shaida maku na amintar da Shi’arta daga wuta”. Kuma ya zo a tarihinta cewa kwanaki 10 na }arshen watan Ramadan ta kasance ba ta barci a cikinsu da daddare. Takan raya dararen ne da ibadodi, kuma takan kwa]aitar da wa]anda ke gidanta da raya dararen. Ya zo cewa a daren 23 na watan Ramadan ba ta barin kowa ya yi barci a gidanta, wato saboda muhimmacin daren da kuma falalolinsa sai dai su raya shi da ibadodi. A kan haka ne ma takan ]auki matakai tun a cikin yini na wa]anda ke gidan nata, na sa su su yi barci da rana da kuma }aranta abinci a lokacin bu]e baki, duk dai saboda su sami sau}i da kuma }arfin raya daren 23 ]in. Takan ce; “Marar sa’a shi ne wanda bai samu alherin daren ba.” Sayyida Fatima (AS) ta kasance mai yawan karatun Al}ur’ani. Ta kasance ko ayyukan yau da kullum na gida take yi tana yi tana karatun Alkur’ani ne. Haka kuma Fatima (AS) ta kasance mai yawan addu’o’i. Akwai ma wasu Malamai na Madrasah ]in Ahlul Baiti (AS) da suka tattara wasu daga cikin addu’o’inta suka mai da su littafi. Misali Sahifatuz Zahra, wadda Shaikh Jawad {ayyumiy ya wallafa.Haka nan ta kasance sa’ar }arshe ta kowace ranar Juma’a takan lizimci addu’o’i a lokacin, wato gab da rana za ta fa]i. Ya zo a Hadisi cewa sa’ar }arshe ta ranar Juma’a yana daga cikin lokuta da Allah (T) kan amshi addu’o’i. Haka nan idan mutum ya duba zai ga cewa, wasu ibadodi masu yawa daga wajenta aka samo. Kyakkyawan misali tasbihohin da muke yi bayan Salla, wato Allahu Akbar, Alhamdulillah da Subhanallah. Asalinsu daga wajenta aka samo. Akwai Sallolin da aka samo daga wajenta, mutum na iya duba Mafatihul Jinan in yana bu}ata. Har ila yau Sayyida Fatima (AS) ta kasance mai yawan Azumi. A ta}aice dai Sayyida Fatima (AS) a fagen ibada ta kai mustawa-aliya ta kowacce fuska. 2. ILIMINTA: Duk da ]imbin ilimin da Sayyida Fatima (AS) take da shi da kuma yawan Hadisai da ta ji daga mahaifinta. Amma abin ba}in ciki ka]an ne }warai suka zo a littafan Hadisai na Madrash ]in Ahlus Sunnah, har ma akwai wata magana ta Suyu]i,da yake cewa baki ]aya abin da Fatima (AS) ta ruwaito na Hadisai, ba su kai Hadisai 10 ba. Wanda ko a hankali mutum ya tambayi kansa, a ce tana gaban Manzon Allah (S) shekara takwas a Makka tana tare da shi a Madina sama da shekara 10, amma duk tsawon wa]annan shekaru 18 Hadisai 10 kawai ta ji. Anya ba dai akwai wani abu a }asa ba? Alhali ko in da mutum zai koma ga littafan Hadisai na Ahlul Baiti (AS) zai ga akasin haka. Wato zai samu Hadisai da dama wa]anda aka ruwaito daga Sayyida Fatima (AS). Ko da a ce mutum bai san komai ba a Hadisan da aka ruwaito daga Sayyida Fatima (AS), amma ya karanci hu]ubobin da ta yi guda biyu gabanin rasuwarta. [aya wadda ta yi a masallacin Manzon Allah (S) ga Sahabban Manzon Allah (S) kan abin da ya shafi khalifanci da kuma Fadak. Ta biyu hu]ubar da ta yi wa matayen Sahabbai a gidanta. In mutum ya karanta wa]annan hu]ubobi zai ga cewa baya ga uslubin bayani, zai ga sun }unshi fasaha da kuma balaga, wanda suke nuna cewa lallai Sayyida Fatima (AS) a fagen ilimi, shi ma ta kai mustawa-aliya. Da yake kamar yadda aka ambata a baya cewa abubuwa da yawa nata sun ~oyu, musamman a duniyar Sunnah, amma a duniyar Ahlul Baiti (AS) al’amuran ta ba su ~oye ba, kamar hasken rana suke. Sayyida Fatima (AS) ta kasance takan karantar da matayen Sahabbai kuma wani lokaci in suna da tambayoyi sukan zo kai tsaye ko su aiko. Misali, akwai wata Dattijiwa da ta aiko ’yarta zuwa ga Fatima (AS) kan wasu tambayoyi na Salla. Ta zo ta tambayi Sayyida Fatima (AS), ta ba ta amsa, ta sake wata tambayar ta ba ta amsa, haka-haka dai sai da ta yi tambayoyi 10, tana ba ta amsa a kai, sai ta ji kunyar ci gaba da tambayoyin. Ta ce ban son in matsa maki ya ’yar Manzon Allah (S). Shi ne Sayyida Fatima (AS) ta ce mata. Ba matsala in kina da wasu tambayoyi ki yi. Haka nan Sayyida Fatima (AS) ta kasance takan tura ’ya’yanta, wato Imam Hasan (AS) da kuma Imam Husain (AS) Majalisin Manzon Allah (S), in sun dawo takan tambaye su abubuwan da aka karantar. Da dai misalai da dama irin wa]annan na rayutuwar Sayyyida Zahra (AS) a fagen ilimi. 3. KUKANTA: Sayyida Fatima (AS) ta kasance mai yawan kuka saboda tsoron Allah (T) da kuma yawan kuka saboda rabuwa da Manzon Allah (S), wato bayan wafatinsa. Ya zo a kan cewa saboda yawan kuka na rabuwarta da Manzon Allah (S), sai da mutanen Madina suka damu a kan haka. Sai ya kasance takan fita ta je ma}abartar Shuhada, ta yi kuka, bayan wani lokaci sai ta dawo. Ya zo a Hadisi da aka samu daga Imam Sadi} (AS) ya ce; “Masu yawan kuka guda biyar ne, daga cikinsu ya ambaci Sayyida Fatima (AS). Wannan darasi ne babba gare mu, mu duba matsayi da kuma darajoji irin nata, da kuma cewa ita Ma’asumiya ce, amma yadda take yawan kuka saboda tsoron Allah (T) da kuma rabuwarta da Manzon Allah (S). Kuma shi kukan kamar yadda Malaman Irfani suka yi bayani, yana gudana a}alla ta fuskoki guda biyar. i. Kuka na tsoron Allah (T) ii. Kuka saboda shau}in saduwa da Allah (T) iii. Kuka saboda ba}in cikin abin da aka yi wa Manzon Allah (S) da kuma Ahlul Bait (AS) ]insa. Ko kuma shau}in son saduwa da su. iiiv. Kuka saboda zunubin da mutum ya aikata, v. Kuka na munajati da Allah (T). da yakan kasance ga wasu bayin Allah (T) lokacin munajatinsu da Allah (T). Yana da muhimmanci ga kowannenmu, cikin wa]annan nau’uka na kuka da ma wasu da ba a ambata ba,ya kasance mutum yana aikata su.musammam ma lokacin sallar Tahajjud ]insa.misalin nau’in kukan da ba a ambata ba shine, Imamin wannan zamanin ga shi yana raye muna raye, amma kuma ba mu ganin sa. Bayin Allah (T) da yawa suna kuka kan irin wannan rabuwa, wato rashin kasantuwa tare, in mutum ya duba wasu fa]arori a cikin du’a’u Nudba sun }unshi hakan, ya kasance mutum irin wa]annan kuka ko wani daga ciki yana yi a kullum,ko mako ko wata ta yadda dai kada mutum ya zamanto idanuwansa a bushe suke. Domin bushewar idanuwa yana alamta bushewar zuciya, bushewar zuciya kuma yana alamta yawan zunubi.Kuma kuka yana da falaloli masu yawan gaske a wannan addini na musulunci.Insha-Allah wani lokaci bayani zai gudana akai. Wasu ~angarori na rayuwar Sayyida Fatima (AS), kamar akhla} ]inta, mu’amalarta, zuhudunta, jarabawowinta da sauransu, in Allah ya kai mu wata munasabar wafatinta za a ]ora.
|
|||
Last Updated on Tuesday, 29 October 2013 19:44 |