Darussa 12 daga rayuwar Imam Ali {AS} |
Written by administrator | |||
Sunday, 20 October 2013 11:11 | |||
.
Rubutu ko bayani dangane da tarihi da kuma Darussa daga rayuwar Imam Ali[AS] wani fage ne mai fa]in gaske.Saboda idan mutum yayi bincike zai ga cewa sahabban Manzon Allah[S] baki ]aya,ba a samu wani sahabi,wanda malamai na wa]annan makarantu guda biyu wato sunnah da shi’a,da suka yi rubuce-rubuce na tarihi da kuma bayanin darajojinsa,kamar yadda suka yi ga Imam Ali[AS] ba,duk ko da matakai da ma}iya Ahlul bayt suka ]auka na ~oye darajojin Imam Ali[AS].Domin idan mutum ya bibiyi tarihi zai ga cewa babu Imami daga cikin Imamai 12 da ya samu }iyayya da gaba daga ma}iya Ahlul bayt kamar Imam Ali[AS],an yi lokacin da masoyan Imam Ali suna ~oye darajojinsa da kuma matsayinsa saboda tsoro,ma}iyansa kuma sune ~oye wa]annan darajoji saboda hassada da kuma }iyayya.Kai bama fa]in darajojinsa ba,mujarradin ambaton sunansa zai iya zama fitina ga mutum,shi yasa a lokacin Bani Umayya da kuma Banul-Abbas masu ruwaito Hadisai sukan sakaya sunansa,saboda abun da ka iya faruwa a kansu,wato sai su ce daga baban Hasan,ko baban Zainab,wani lokaci ma suce daga wani mutum.Amma duk da irin wa]annan matakai darajojin Imam Ali[AS] basu ~oyu ba ga wannan al’umma.Akwai ma fa]in Ahmad ibn Hambal da yake cewa, “Babu wani daga cikin sahabban Manzon Allah wanda darajojinsa suka zo,kamar yadda suka zo ga Imam Ali.” Mai bu}atar ganin wannan yana iya duba littafin Suyu]i mai suna Tarikhul-Khulafa,a fasalin da yake bayanin Imam Ali.Haka nan yazo a cikin lttafin Tazkhiratul-Kawwas,Abdullahi ]an Abbas yana cewa: “Da ace itatuwa baki ]aya za a maida su al}aluma,koguna su zama tawada,mutane da aljannu su zama marubuta,to ba za su iya }ididdige darajojin Imam Ali ba.” Haka nan akwai wata daraja wadda Imam Ali ya ke~anta da ita a tarihin ]an Adam baki ]aya,wannan khususiyya ko itace haihuwarsa da aka yi a cikin ka’aba,wanda wannan ba wai malaman shi’a ba,a’a hatta malaman Ahlus-sunna sun tabbatar da haka,alal misali mutum na iya duba littafin Nurul-Absaar na Shaikh Shablanji wanda yana ]aya daga cikin malaman Ahlus sunna,to a cikin littafin idan mutum ya duba,a in da yake bayani kan darajojin Imam Ali zai ga ya kawo cewa an haife shi a cikin ka’aba,kuma ba a ta~a haihuwar wani a cikin ka’aba gabaninsa ba sai shi.Kuma sanin mu ne cewa tarihi bai rubuta an haifi wani a cikin ka’aba ba a bayansa.Haka nan Imam Ali shine farkon wanda ya amsa sa}on da Manzon Allah ya zo dashi,shine kuma farkon wanda yayi sallah tare da Manzon Allah.Haka nan a cikin sahabbai shine ya ke~anta da wannan la}abi na ‘Karramallahu Wajhahu” wato kamar yadda malaman Ahlus sunna suke ce mashi.Kuma ya zo akan cewa Manzon Allah bai ta~a shugabantar da wani a kansa ba,in mutum ya yi bincike zai ga haka.Haka nan Manzon Allah ya ke~ance shi da ‘yan uwantaka gareshi,bayan da ya koma Madina,wato lokacin da ya ha]a ‘yan uwantaka tsakanin Muhajirin da kuma Ansaar. Idan kuma muka juya ga wasu Hadisai da suka zo dangane da Imam Ali, zamu ga suna da yawa,ga wasu daga ciki:Manzon Allah[S] yace ma Ammar ]an Yasir[RA]: “Ya Ammar biyayya ga Ali,biyayya ce gare ni,biyayya gare ni,biyayya ce ga Allah Ta’ala.Ya Ammar idan mutane baki ]aya suka bi wata hanya,Aliy shi kuma ya bi wata hanya to kabi hanyar da Ali ya bi,ka bar mutanen.”Haka nan kuma daga Abu Zar[RA] yace Manzon Allah[S] yace: “Duk wanda yake son Ali ha}i}a yana sona,duk wanda yake sona ha}i}a yana son Allah,duk wanda yake }in Ali ha}i}a yana }ina,wanda yake }ina ha}i}a yana }in Allah.” A wata ruwaya daga Ummu Salma[RA] t ace na ji Manzon Allah yana cewa: “Duk wanda ya zagi Ali ha}i}a ya zage ni,duk wanda ya cutar da Ali ha}i}a ya cutar da ni.”Akwai ma lokacin da Ummu Salma ta kafa hujja ga su Mu’awiya da wannan hadisi,lokacin da suka sunnata zagin Imam Ali,tace masu zagin Ali da kuke yi to ku sani kuna zagin Manzon Allah ne.Masu cewa ana zagin sahabbai da sun karanci tarihi sosai,da zasu fahimci cewa Mu’awiya shine ya assasa zagin sahabbai a wannan al’umma kuma ya gina mutane akai.A wani hadisi Manzon Allah yace: “Ba mai son ka ya Ali face mumini,ba mai }inka face munafiki.” Wani sahabi da ake ce ma Abi Sa’idil Khudri ya ce mun kasance muna gane munafikai ta hanyar }iyayyarsu ga Ali.Haka nan idan muka juya zuwa ga ayoyi na Al}ur’ani mai girma da suka sauka masu ala}a da Imam Ali suma zamu ga suna da yawa,akwai ma fa]in Abdullahi ]an Abbas yace babu wani wanda ayoyi na littafin Allah suka sauka dangane da shi kamar yadda suka sauka dangane da Ali.Ga mai bu}atar ganin wa]annan ayoyi dabam-dabam yana iya samun wani littafi mai suna “Aliyun Fil Kitaabi was Sunnah juz’i na ]aya.Ya duba zai ga wa]annan ayoyi a kuma ruwayoyi na Ahlus Sunnah. A ta}aice dai falaloli da kuma darajojin Imam Ali[AS] suna da yawa wanda za a iya siffatansu da cewa la tu’addu wala tuhsa.Ko da ma ace ba ayoyi ko hadisai da suka zo da darajojinsa to kasantuwarsa miji ga shugaban mataye kuma ‘yar Manzon Allah ko kuma kasantuwarsa wanda ya tashi a gidan Manzon Allah to sun isa su zamo darajoji gareshi.Ballantana kuma idan muka juya a mahangan Urafa wato arifai ga matsayin Imam Ali,zamu ga cewa suna siffanta shi a matsayin Mu’ujiza na Manzon Allah[S],wanda sanin Malakut ]in Imam Ali[AS] wato ba]ininsa sai Allah Ta’ala da kuma Manzon Allah[S] HAIHUWAR IMAM ALI[AS] An haifi Imam Ali[AS] a makka ranar Jumma’a 13 ga watan Rajab,shekaru talatin bayan Aamul fil,wato shekarar giwa.Lokacin haihuwar Imam Ali[AS] akwai ayoyi da suka kasance,wanda mutane su ka yi ta mamaki,alal misali akwai wani mutum da ake ce masa ibn {a’anab ya ce: “Na kasance ina zaune tare da Abbas ]an Abdul-Mu]allib tare kuma da wasu daga cikin Banu Hashim kusa da Ka’aba,sai ga Fatima ‘yar Asad tana tahowa[wato mahaifiyar Imam Ali] a lokacin tana da cikinsa wata tara,na}uda ta kamata.Sai suka ji tana cewa: “Ya Ubangijina,ni na na yi imani da kai,da kuma abinda ya zo daga wajenka ta hanyar Manzanninka da kuma littafanka,kuma ni ina mai gasgatawa da zantukan kakana Ibrahim[AS].Ina ro}on ka da ha}}in wannan ]aki da wanda ya ginashi,da kuma wannan abin da yake cikin cikina,ka sau}a}e min wannan haihuwa.Sai ibn {a’anab ya ce sai muka ga Ka’aba ta bu]e, sai Fatima bint Asad ta shiga ciki,ta faku daga ganinmu.Bayan haka in da ya bu]e na Ka’abar sai ya rufe da iznin Allah,muka yi muka yi mu bu]e,domin sashen matayenmu su taimaka mata,amma }ofar Ka’aba ba ta bu]u ba.Sai muka fahimci cewa to wannan wani al’amari daga wajen Allah Ta’ala.Bayan kwana hu]u sai ga shi ta fito ]auke da Ali a hannunta.” Ya zo akan cewa lokacin da ta yi nufin fita sai ta ji sautin Magana cewa: “Ya Fatima ki sa masa suna Ali.” Wa]annan kwanaki hu]u da tayi cikin Ka’aba yazo akan cewa ‘ya’yan itace na Aljanna ake kawo mata.Da dai sauran ayoyi da suka bayyana a lokacin haihuwarsa.Mahaifiyar Imam Ali[AS] ta rayu har ya zuwa hijirar Manzon Allah daga Makka zuwa Madina,ta yi hijira ta same shi a Madina,ya zo a tarihi cewa itace mace ta farko da ta taka da }afafuwanta ba tare da ta hau dabba ba tun daga Makka zuwa Madina a lokacin hijira.Kuma ta ba da gudunmawa sosai wajen kafuwa da kuma tabbatuwan wannan addini na Musulunci.Haka nan kuma akwai hadisai masu yawa da aka ruwaito daga wajenta,wa]anda ta ji daga Manzon Allah.Kuma ta kasance lokacin da take ri}on Manzon Allah ta kan fifita shi akan ‘ya’yanta baki ]aya.Lokacin da ta rasu Manzon Allah ya yi kuka mai yawa,kuma shi ya ji~inci dukkan al’amuranta na jana’iza,domin hatta likkafaninta Manzon Allah rigarsa ya bayar aka yi dashi.Haka nan a wajen yi mata sallah Manzon Allah kabbarori saba’in yayi,har Umar yake ce ma Manzon Allah kayi ma wannan matar abun da baka ta~a yi ma wani ba,sai Manzon Allah ya ce masa ita Uwa tace bayan mahaifiyata. Sunan mahaifin Imam Ali Abdu Manaf,amma ana yi masa kinaya da Abu [alib wato ]aya daga cikin ‘ya’yansa,da yake yana da ‘ya’ya bakwai ne,maza hu]u,mata ukku.Mazan sune:1-[alib wanda shine babban ]ansa.2- A}il.3-Ja’afar.4-Ali wato Imam Ali shine ]an autansu.Matan sune:1- Ummu Hani.2-Jumanatu.3-Wari]atu.Kuma Abu [alib ya ba da gudunmawa mai yawan gaske wajen kariya ga Manzon Allah a lokacin da yake isar da sa}o a makka.Idan mutum ya karanci tarihi zai ga duk wahalhalun da Manzo ya sha da wa]anda suka yi imani dashi,to da Abu [alib aka sha.Kyakkyawan misali anan shine tsare su da aka yi a wajen da ake ce ma Shi’ibi Abi [alib har na tsawon shekaru ukku,da kuma wasu dokoki da aka aza akansu na cewa ba zasu saya ba kuma ba za a sayar masu ba,ba zasu wajen wa]ansu ba,su kuma ba za a zo wajen su ba, da dai sauransu.Haka nan da }in mi}a Manzon Allah da Abu [alib yayi ga {uraishawa kamar yadda suka bu}ata,da kuma wasiyyar da yayi ga Bani Hashim gab da zai rasu,na cewa Banu Hashim su ci gaba da wannan kariya ga Manzo domin isar da wannan sa}on.Amma duk da haka mu duba yadda aka jirkita tarihi aka kuma gina mutane akai dangane da Abu [alib.Wa]annan abubuwa sun auku ne a lokacin daular Bani umayya da nufin wai ~ata shakhsiyyar Imam Ali.Saboda haka a lokacin suka }ir}iro hadisai wai yadda zai kasance cikin wuta,da kuma wasu ayoyi da aka canza asbabun nuzul ]insu wato dalilan saukarsu duk dai aka jingina ma Abu [alib.Wanda }ir}iro hadisai ta hanyar yi masu isnadi da kuma matani a jingina su ga Manzon Allah,ba wani ~oyayyen abu bane a lokacin Daular Bani umayya,duk wanda ya karanci fannin Ulumul-Hadis zai tabbatar da haka,wato akwai sashe na Hadisai maudu’ai wato }ir}irarru.A lokacin ya kai ga cewa ba wai hukuma ba hatta ‘yan kasuwa su kan sa a }ir}ira masu hadisi dangane da sana’arsu,akwai }issar wani mutum da ya kawo albasa a makka a lokacin,to sai albasar bata sayu ba,sai abun ya dame shi,sai wani yace masa kaje ayi maka hadisi akanta,sai ko ya tafi,shi mutumin dama yazo daga garin da ake ce ma Akka.Ga hadisin da akayi masa,An samo daga wane yace yaji Manzon Allah yace, “Duk wanda yaci albasar Akka a Makka yana da lada kaza” jin haka nan take mutane suka saye wannan albasa ta Akka.Mu duba fa mu gani yadda aka yi wasa da addini a wannan al’umma,kuma abin ba}in ciki aka gina mutane akai,wato suka rayu akai suka kuma mutu akai.Insha-Allah a darasi na gaba za a kawo Darussa daga rayuwar Imam Ali[AS] misali Ibadarsa,Akla} ]insa,iliminsa,shaja’arsa da dai sauransu. ]
|
|||
Last Updated on Wednesday, 14 October 2015 09:52 |