Darussa 12 daga rayuwar Imam Husain (AS) 1 |
Written by administrator | |||
Saturday, 19 October 2013 14:10 | |||
Kasantuwar wannan watan da muke ciki, wato Muharram a cikinsa ne, 10 ga shi, shahadar Imam Husain (AS). Shahadar tasa ta kasance ranar Juma’a, a wata ruwaya ranar Asabar shekara ta 61 bayan hijira. Kuma shahadar tasa ta kasance kamar yadda aka sani a Karbala. Tsakanin isar sa Karbala da shahadarsa, kwanaki takwas ne. Domin ya isa Karbala 2 ga watan Muharram, kuma kabarinsa yana Karbala ]in ne tare da wa]anda suka yi shahada da shi. Kuma lokacin da ya yi shahada yana da shekara 57 a duniya. Kuma wannan wata na Muharram, kamar yadda aka sani shi ne na farko a cikin }idaya na watannin Musulunci 12, kuma yana daga cikin watanni guda hu]u masu alfarma da daraja da kuma matsayi a wajen Allah (T), wanda ma saboda daraja da matsayin wa]annan watanni guda hu]u ne Allah (T) ya yi hani ga zaluntar kai a cikinsa, kamar yadda ya zo a cikin Al}ur’ani mai girma a cikin Suratul Taubah Aya ta 36. Kai hatta ma lokacin Jahiliyyah sun kasance suna girmama wa]annan watanni ta fuskoki daban-daban. Alal misali Shaikh Sadu} ya ruwaito a cikin littafinsa da ake ce wa Amaly daga Ibrahim ]an Abi Mahmoud ya ce Imam Ridah ya ce; “Watan Muharram wata ne wanda mutanen jahiliyya suka haramta zalunci da kuma ya}i a cikinsa saboda darajarsa, amma mu aka halasta jininmu a cikinsa, aka keta mutuncinmu a cikinsa, aka ribace matayenmu da ’ya’yanmu a cikinsa, aka kunna wuta a hemominmu, aka kwashe abin da yake ciki na kayayyakin mu, ba a kiyaye alfarmar Manzon Allah (S) a cikin al’amarinmu ba”. Haka nan kuma wannan wata ne na juyayi da ba}in ciki da ma kuka ga Ahlul Bait (AS) da kuma wa]anda suka yi ri}o da su, kamar yadda ya zo daga Imam Ridah (AS) ya ce; “Babana wato Imam Kazim(AS) ya kasance idan watan Muharram ya shiga ba a ganin dariya a fuskarsa, har ya zuwa 10 ga watan. A ranar 10 ga watan, wato ranar Ashura, takan kasance ranar ba}in ciki da kuka gare shi, kuma yakan ce wannan ita ce ranar da aka kashe Imam Husain (AS)”. Saboda haka wannan wata, wata ne wanda tun daga farkonsa har }ashensa, wata ne na juyayi da ba}in ciki da kuka. Wanda baya ga al’amarin Ashura da ya auku a cikin watan, har ila yau a cikin wannan wata ne wafatin Imam Ali Zainul Abidin (AS), wanda kamar yadda aka sani ]a ne ga Imam Husain (SA). Kuma daga cikin khususiyya ta wannan wata na Muharram shi ne wata ne na wafati, wato babu wani daga cikin A’imma na Ahlul Bait (AS) da aka haifa a cikinsa, wato akasin watan Sha’aban, wanda shi ma daga cikin khususiyya ]insa, shi ne wata ne na wilada, wato babu wani daga cikin A’imma ]in Ahlul Baiti (AS) da rasuwarsa ta kasance a ciki. sauran watanni 10 kuma. In mutum ya bibiya zai ga cewa, kowane wata a cikinsa akwai wilada da wafati na wani daga cikin A’imma na Ahlul Baiti (AS). Misali a nan shi ne, watan da ke gaban wannan wata, wato Safar, a cikinsa akwai wiladar Imam Kazim (AS) da kuma wafatin Imam Hasan (AS). Haka nan watan Rabi’ul Awwal a cikinsa akwai wiladar Imam Sadi} (AS) da kuma wafatin Imam Askari. Shi wannan wata na Muharrram babu wata wilada ta Ma’asumi da ya zo a cikinsa, shi ya sa mabiya Ahlul Baiti (AS) a sassan duniya daban-daban suke raya wannan wata ta fuskoki daban-daban, musamman 10 na farko na watan ta hanyar zaman makoki da sa ba}a}en kaya, wanda wannan yana da asali. Kuma akwai Hadisai a kai da aka samo daga Imam Sadi} (AS). Imam Husain (AS) kamar yadda aka sani shi ne Imami na uku a jerin }idaya na Imamai 12. An haife shi a Madina ranar Alhamis 3 ga watan Sha’aban, a wata ruwaya 5 gare shi, shekara ta 4 bayan Hijira, kuma tsakanin haihuwarsa da Imam Hasan (AS) wata shida ne. Wannan ita ce ruwayar da ta fi shahara, domin akwai ruwayoyi da suka zo sa~anin haka. Kuma wata shida shi ne a}alla muddan ciki a shari’a. Ya zo a kan cewa a tarihi ba a haifi wani a wata shida ba face Annabi Yahya (AS) da kuma Imam Husain (AS). Saboda haka ba kamar yadda mutanenmu suka ]auka ko sawwala ba, cewa Imam Hasan (AS) da kuma Imam Husain (AS) sun kasance tagwaye ne, wato ’yan biyu wajen haihuwa. A’a tsakinsu akwai a}alla wata shida. Bayan da aka haifi Imam Husain (AS) aka je aka shaida wa Manzon Allah(S) sai ya zo wannan gida mai albarka yana murna da kuma farin ciki, ya ce wa Asma’u ’yar Uwais ta mi}o masa shi, Manzon Allah (S) ya }ar~e shi ya rungume shi, ya yi masa kiran Salla a kunensa na dama, sannan ya yi I}ama a kunnensa na hagu. Sai ya ]ora shi a kan cinyarsa mai albarka ya yi kuka, sai ita Asma’u ’yar Uwais ta ce; “Babana da Mamana sun kasance fansa gare ka ya Manzon Allah (S), wannan kukan fa?” Sai Manzon Allah(S) ya ce mata; “Ina kuka ne saboda abin da zai same shi a bayana, wa]ansu jama’a azzalumai za su kashe shi, ba za su samu ceto na ba”. Sannan ya ce wa Imam Ali (AS); “Ka sa masa suna ya baban Hasan!” Sai ya ce; “Ban kasance zan riga ka wajen sa masa suna ba”. Sai Manzon Allah (S) ya ce; “Ka sa masa suna Husain (AS)”. A rana ta bakwai da haihuwa, Manzon Allah ya sake zuwa wannan gidan mai albarka ya sa aka mi}o masa Imam Husain (AS) aka yi masa a}i}a, aski da dai makamantansu. Bayan haka ya zauna ya ]ora shi a kan cinyarsa mai albarka ya yi kuka kamar na ranar farko, da aka tambaye shi, ya ba da amsa kamar yadda ya bayar a ranar farko. Daga cikin khususiyyar Imam Husain (AS), wato abin da ya ke~anta da shi, bai ta~a shan mama na wata mace ba, ko kuma na Sayyida Fatima (AS) ba. Kamar yadda Kulaini ya ruwaito a cikin littafin Kafi juzu’i na 1, shafi na 386, wato babin da yake magana kan wiladar Imam Husain (AS). An samo daga Imam Sadi} (AS) ya ce; “Imam Husain (AS) bai sha mama na wata ba ko na Fatima (AS), ya kasance akan kawo shi wajen Manzon Allah (S) ya sa babban yatsansa cikin bakinsa sai ya tsotsa daga gare shi. Hakan yakan ishe shi kwana biyu ko kwana uku”. Saboda haka Imam Husain (AS) ya taso ne a gaban Manzon Allah (S), ya rayu tare da shi kimanin shekara bakwai. Bayan wafatin Manzon Allah (S), Imam Husain (AS) ya zauna gaban Mahaifinsa, wato Imam Ali (AS), ya rayu tare da shi kusan shekaru 30. Bayan Shahadar Imam Ali (AS) ya rayu tare da Imam Hasan (AS) kusan shekaru 10, bayan wafatin Imam Hasan (AS) Imamanci ya koma gare shi, muddan Imamancinsa su ne shekara 10 wato daga shekara 50 bayan hijira zuwa shekara 60 bayan hijira. Imam Husain (AS) ya kasance tare da shi aka yi ya}o}in Jamal da Siffin da kuma Naharwan, kuma wa]annan shekaru 10 na Imamancinsa sun kasance a Madina ne har ya zuwa 28 ga watan Rajab shekara ta 60 bayan hijira lokacin da ya bar Madina zuwa Makka. Daga nan kuma zuwa Karbala, shi ya sa al’amarin Ashura ba kamar yadda da yawa suka ]auka ko fahimta ba, na cewa wannan wani abu ne da ya faru a cikin kwanaki 10, ko ma yini guda, wato ]aya ga watan Muharrram zuwa 10 gare shi. A’a, wannan wani abu ne da in mutum ya bincika a cikin littafan tarihi zai ga cewa abu ne wanda aka kwashe kimanin wata shida, abubuwa daban-daban suna gudana, wato tun daga fitowar Imam Husain (AS) daga Madina zuwa Makka, daga nan kuma sai fitar sa daga Makka zuwa Karbala, wanda ko da a ce abin da ya auku a ranar Ashura bai auku ba, to abubuwan da suka faru tun daga fitowar sa Madina zuwa isar sa Karbala, sun isa su zama abin juyayi da kuka. Shi ya sa sanin abubuwan da suka faru gabanin Ashura yana da muhimmancin gaske. Wannan al’amari na wa}i’ar Ashura ya soma faruwa ne tun daga watan Rajab shekara ta 60 bayan Hijira, wato bayan mutuwar Mu’awiyya da kuma hawan Yazidu kan karagar mulki. Daga cikin abubuwan da Yazidu ya soma yi shi ne aikawa da wasi}a zuwa ga Gwamnan Madina na lokacin, wanda ake kira da Walid [an Utbah [an Abu Sufyan da umurnin cewa ya kama Imam Husain (AS) domin ya yi masa bai’a, idan ya }i, ya kashe shi ya aika masa da kansa. Lokacin da wannan sa}on ya zo ga Walid, sai ya kira Marwan yana neman shawara kan yadda zai ~ullo wa al’amarin. Sai Marwan ya ce masa; “Ni abin da nake gani, ka kira shi yanzu, ka umurce shi da yin bai’a, in ya yi shi kenan, in bai yi ba, sai ka kashe shi tun gabanin ya san cewa Mu’awiyya ya mutu”. Sai ya kar~i wannan shawara tasa, ya aika masa a wannan dare yana neman sa, ya aika wani da ake kira da Amru Ibn Usman, ya tafi ya same shi a masallacin Manzon Allah (S) ya shaida masa sa}on da ke tafe da shi. Shi ne har wani yake tambayar Imam Husain (AS) me yake gani ya sa ya aiko a wannan lokacin, alhali bai saba zama a lokacin ba? Imam Husain (AS) ya ba shi amsa da cewa; “Ina ganin Mu’awiyya ne ya mutu, don haka ya aiko min domin yin bai’a ga Yazidu”. A lokacin sai Imam Husain (AS) ya wuce gida ya tara mutum 30 daga mutanen gidansa da kuma bayinsa, ya umurci kowanensu da ya ]auki makami, ya kamo hanya da su zuwa fada, ya ce masu; “Idan kun ji na ]aukaka muryata, to ku shigo cikin fadar. Lokacin da Imam Husain (AS) ya shiga ga Walid, sai ya samu Marwan [an Hakam tare da shi. Bayan da Imam Husain (AS) ya zauna, sai Walid ya yi masa bayani dangane da mutuwar Mu’awiyya da kuma sa}on da Yazidu ya aiko na yi masa bai’a, sai Imam Husain (AS) ya ce, to ai wannan ba abu ba ne wanda ya kamata a ce an yi shi ~oye, a bayyane ya kamata a ce an yi shi, wato a bainar jama’a. Sai Walid ya ce lallai haka ne. Har ma ya ce yana iya tafiya, abin ya zamanto a gaban mutane ne aka yi. A lokacin sai Marwan [an Hakam ya bu]e baki ya ce wa Walid, “Wallahi idan Husain ya bar nan bai yi bai’a ba, to ba za ka ta~a samun iko a kansa ba. Har sai an yi kashe-kashe a tsakanin ku da shi. Saboda haka ka tsare shi kada ya fita har sai ya yi bai’a, ko kuma ka kashe shi”. Jin haka sai Imam Husain (AS) ya ce wa Marwan, “Ya kai [an Zar}a’u (sunan wata kakarsa ce ta wajen uba wanda a lokacin ta yi fice wajen fasi}anci), ta~ewa ta tabbata a gare ka, kai za ka ba da umurnin a kashe ni ko shi?” Sannan Imam Husain (AS) ya juyo ga Walid, wato shi Gwamnan Madina ]in, ya ce masa; “Mu ne Ahlul Baitin Manzon Allah (S), da mu Allah (T) ya bu]e, kuma da mu zai kulle. Yazid mutum ne fasi}i, mashayin giya mai kisan kai. Irina ba ya bai’a ga irinsa”. Sai Imam Husain (AS) ya fita. Wannan abu ya faru ne a daren Asabar 27 ga watan Rajab. A bayan fitar Imam Husain (AS) sai Marwan ya ce wa Walid, ba ka bi abin da na ce ba. Ya ce masa kaiconka! Ka yi nuni ne gare ni da abin da in na aikata zai tafi da addinina da kuma duniya ta”. Har yake ce masa; “Wallahi ba zan so in mallaki duniya da abin da ke cikinta baki ]aya ba a kan in kashe Husain (AS)”. Bayan lokaci ka]an da faruwar wannan al’amarin sai Yazid ya sauke Walid ya na]a wani Gwamna wanda ake ce wa Amru [an Sa’id. Kashegari, wato ranar Lahadi 28 ga watan Rajab, Imam Husain (AS) ya kama hanya zuwa Makka, a tare da shi akwai ’ya’yansa da iyalinsa da ’yan uwansa kamar su Zainab (AS) da kuma ’ya’yan ]an uwansa, Imam Hasan (AS) da dai sauran su. Amma kafin ya kama hanya sai da ya tafi kabarin Manzon Allah (S) da na Mahaifiyarsa wato Sayyida Fatima (SA), da na ]an uwansa, wato Imam Hasan (AS) ya yi bankwana da su. Lokacin da Ummu Salma (RA), wato ]aya daga cikin matan Manzon Allah (S) ta ga Imam Husain (AS) ya yi niyyar wannan tafiyar tasa, sai ta same shi ta ce masa; “Ya kai ]ana! Kada ka sa ni cikin damuwa, da wannan fita taka zuwa Ira}i, domin ni na ji Kakanka yana cewa za a kashe ]ana Husain (AS) a }asar Ira}i a wurin da ake ce wa Karbala”. Sai Imam Husain (AS) ya ba ta amsa da cewa; “Wallahi ni ma na san haka, cewa babu makawa sai an kashe ni, kuma na san ranar da za a kashe ni da wanda zai kashe ni da ma inda za a bizne ni. Na san kuma su waye za a kashe a mutanen gidana da ’yan uwana da kuma jama’ata. In ma kina so in nuna maki inda }abarina zai kasance sai in nuna maki”. Sai ya yi nuni zuwa wajajen Karbala ta hanyar kashafi, sai ga shi ta ga }abarinsa da sassanin maya}ansa da dai makamantansu. Ganin haka sai Ummu Salma ta yi kuka, kuka mai yawa, ta mi}a al’amarin ga Allah (T). Sai Imam Husain (AS) ya ci gaba da ce mata, Allah (T) ya so ya gan ni a wanda aka kashe aka kuma yanka. Kuma ya so ya ga iyalina da ’ya’yana da ’yan uwana ribatattu, wa]anda kuma aka zalunta suna neman taimako, amma ba wanda zai taimaka masu. Sai Ummu Salma ta ce masa akwai tur~aya wadda Kakanka ya ba ni ita, tana cikin kwalba, sai Imam Husain (AS) ya ]ibi wata tur~aya ya ba ta ya ce ta ha]a ta tare da wadda Manzon Allah (S) ya ba ta. A duk lokacin da ta ga ta koma jini, to ta tabbatar an kashe shi. A }arshe Imam Husain (AS) ya shaida mata cewa za su kashe shi, ko da bai fita zuwa Ira}i ba. Ikon Allah haka kuma abin ya faru, ranar da Imam Husain (AS) ya yi shahada, wato ranar Ashura, Ummu Salma (RA) ta ga wannan tur~ayar da ke cikin kwalba ta canza zuwa jini, ta fahimci lallai an kashe Imam Husain (AS), ta yi kuka, kuka mai yawa. Kafin Imam Husain (AS) ya fita Madina ya bu}aci a kawo masa tawada da takarda ya rubuta wasiyya, bayan da ya gama rubutawa ya na]e takardar ya mi}a wa ]an uwansa mai suna Muhammad [an Hannafiyyah, ]a ne ga Imam Ali (AS), ya kama hanya zuwa Makka, ya isa Makka daren Juma’a 3 ga watan Sha’aban, wato ranar ta yi mawafa}a da ranar haihuwarsa. Lokacin da labari ya bazu a cikin garin Makka da kuma wa]anda suka zo Umura, cewa Imam Husain (AS) ya zo Makka, sun yi farin ciki mai yawa. Saboda haka ne ma jama’a da dama suka ri}a zuwa wajensa safe da yamma. Imam Husain (AS), lokacin da yake zaune a Makka ya yi ta samun wasi}u daga mutanen Kufa. Abin da wasi}un suka }unsa shi ne, na bu}atuwar ya zo Kufa, domin su yi masa bai’a da kuma kasantuwa a bayansa ba bayan Yazidu ba, wanda kasantuwar haka yana Makka ]in sai ya aika ]an Amminsa, wato Musulim Bin A}il da ya je Kufa. Bayan da ya isa Kufa ya aika wa Imam Husain (AS) yadda ya ga al’amura, har ma cikin sa}on ya bu}aci Imam Husain (AS) da ya taso zuwa Kufa, Muslim [an A}il yana zaune a Kufa daga baya mutanen Kufa suka ba da baya, suka warware wannan bai’a da suka yi, wanda daga }arshe ma ta kai ma suka kashe shi, wanda kenan Muslim Bin A}il shi ne shahidin farko a wannan wa}i’ar ta Ashura. Imam Husain (AS) ya bar Makka da nufin kama hanya zuwa Kufa a ranar Tarwiyya, wato takwas ga watan Zulhijja, wanda kenan Imam Husain (AS) ya zauna a Makka kimanin watanni hu]u, har Imam Husain (AS) ya yi haramar aikin Hajji, sai ya kasance a ranar 8 ga watan Zulhijja, sabon Gwamnan Madina wanda Yazid ya na]a, wato Amru [an Sa’id ya iso Makka cikin jama’a masu yawa ya bayyana cewa ya zo aikin Hajji ne, amma ha}i}anin manufar zuwansa sa}o ne daga Yazid, cewa ya zo ya samu Imam Husain (AS) a Makka ya kama shi ko dai ya kashe shi, ko kuma ya kai shi Sham. Shi ma Imam Husain (AS) ya fahimci haka, saboda haka ne ya canza niyya daga Hajji zuwa Umra. Amma kafin wucewarsa ya yi wa jama’a hu]uba wanda ta }unshi bayanai dangane da abubuwan da za su faru gare shi da kuma wa]anda ke tare da shi. Bayan haka ya kama hanya zuwa Kufa. A kan hanyarsa ta zuwa Kufa labari ya zo na shahadar Muslim Bin A}il da kuma warware bai’a da mutanen Kufa suka yi, ya ci gaba da tafiya har lokacin da suka ha]u da Hur [an Yazid, wanda shi kuma Ibn Ziyad ne ya aiko shi a kan ya tare Imam Husain (AS). Imam Husain (AS) ya isa Karbala 2 ga watan Muharram shekara ta 61 bayan hijira wanda baki ]aya shi da iyalinsa da Sahabbansa ba su kai su ]ari ba, amma haka suka fuskanci maya}a wanda yawansu ya kai dubu 30. Wannan al’amari ya auku a ranar Ashura wato 10 ga watan Muharram shekara ta 61 bayan Hijira, wanda a wannan rana Imam Husain (AS) da kuma sama da bayin Allah (T) 70 da ke tare da shi, suka yi shahada. Ya ma zo a kan cewa lokacin da suka isa Karbala, duk da cewa Imam Husain (AS) ya sani, amma sai ya tambaya, ina ne nan? Sai aka ce masa Karbala, sai ya ce; “Wannan waje ne na ba}in ciki da kuma bala’i, nan ne za a zubar da jininmu, kuma a nan ne }aburburanmu suke. Ya ce haka Kakana, Manzon Allah (S) ya fa]a min. Daga }arshe sai darussa da za mu koya daga wannan wa}i’ar ta Ashura. Akwai darussa da dama da za mu koya daga wannan al’amari na Ashura. Amma ga guda biyu daga ciki. 1. MUHIMMANCIN KYAKKYWAN A{IBA: A cikin rayuwar mutum babu abin da ya fi muhimmaci a kan a}ibarsa, wato }arshensa. Shi ya sa da za a yi tambayar cewa, a cikin rayuwar mutum menene ya fi muhimmanci? Amsa ita ce yadda ya bar duniya a addinance, wa]anda suka yi wannan aika-aikar, inda mutum zai bi tarihin rayuwar wa]ansunsu abin zai ba shi mamaki. Domin wasunsu sun kasance tare da Imam Ali (AS) har ma sun yi ya}i a bayansa, amma yau ga shi sun dawo suna ya}ar ]ansa da mutanen gidansa, har ma daga }arshe suka karkashe su, tare da kuma sun san matsayinsu, ba wai sun jahilta ba ne. Saboda haka wannan akwai abin ban tsoro a ciki, a ce mutum ya zauna da Ma’asumi, ya rayu tare da shi har ya koma ga Allah (T), shi kuma daga baya ya zo ya canza. Allah ya yi mana kyakkyawar a}iba. 2. ILLAR SON DUNIYA DA ABIN DUNIYA: Da yawa daga cikin wa]anda suka yi wannan mummunan aiki, babban abin da ya kai su ga aikata wannan aiki shi ne tunanin abin da za a ba su na duniya. To, abin tambaya a nan, yau ina abin da aka ba su na duniyar yake? In ma an ba su kuma ina wa]anda suka ba su suke? Suna ina yau? Wanda su da abin da aka ba su ba su kai shekara 100 ba. Amma ga shi sun jefa kawukansu a wahala da azaba ta dindindin. 3. {ARANCIN ADADI BAI HANA FUSKANTAR MA{IYA: Idan mutum ya dubi adadin jama’ar da ke tare da Imam Husain (AS) ya kwatanta da adadin da ke gefen ma}iya, zai ga cewa bambancin ba ka]an bane, amma duk da }arancin adadi, haka Imam Husain (AS) da jama’arsa suka fuskanci wa]annan dubban ma}iya. Tabbas Imam Husain (AS) da jama’arsa su suka samu nasara a kan wa]annan ma}iya. Da yake nasara iri biyu ce, akwai babbar nasara wadda ita ce nasarar lahira, akwai kuma }aramar nasarar wadda ita ce nasarar duniya, ita kuma iri biyu ce, akwai ta zahiri wadda ita ce samun nasara kan ma}iyi, da kuma ta ba]ini wadda ita ce dakewa a kan gaskiya, wato tafarki har mutuwa ta zo a kashe mutum a kai, ko kuma samun galaba kan ma}iyi. 4. {IYASTA ABIN DA YA SAME SU GA MUTUM A KANSA: Duk lokacin da abu ya samu mutum a hanyar addini ko kuma saboda ri}onsa ga Ahlul Baiti (AS), to ya kwatanta wannan abin da ya same shi da abin da ya samu Imam Husain (AS) da Sahabbansa da kuma abubuwan da suka biyo bayan shahadarsu. Zai ga cewa abin ba zai kwatantu ba. Zai kuma ga cewa abin da ya same shi ko ka]an bai kai ]aya bisa goma ba in an kwatanta da abin da ya samu su Imam Husain (AS) ba. Wannan tunani sai ya sa ya ga rashin }imar abin da yake samunsa sakamakon bin sa ga tafarkin Allah (T) da kuma ri}o da Ahlul Bait (AS). 5. MUHIMMANCIN DAKEWA DA SADAUKAR DA KAI DOMIN [AUKAKA ADDINI DA KUMA WANZUWARSA: Dakewa da sadaukar da kai da Imam Husain (AS) ya yi tare da Sahabbansa shi ya wanzar da wannan addini zuwa yanzu. Domin da ba don wannan sadaukar da kai da kuma dakewa ba, da idan an ce yau babu addinin Musulunci, to ba za a yi musu ba. Saboda haka wannan darasi ne babba gare mu. Daga }arshe babu abin cewa face “Assalamu Alal Husain Wa’ala Aliyu Bin Husain Wa Ala Auladil Husain Wa Ala As’habil Husain. Ya Laitana Kunna Ma’akum Fanafuza fauzan Azima.”
|
|||
Last Updated on Tuesday, 29 October 2013 19:46 |