TAMBIHI
Wannan shafi na tambihi na maraba da ziyartarsa.
GABATARWA.
Da sunan Allah mai Rahma mai jin }ai, dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah{T} ubangijin talikai,tsira da amincin Allah su tabbata ga fiyayyen halitta kuma cikamakon Annabawa,Annabi Muhammad da kuma alayensa tsarkaka.
Bayan haka wannan shafi na Tambihi, rubuce rubuce ne da suka gabata a filin tambihi na jaridar Almizan. Filine da ake gabatar da Darussa na wasu fannoni na ilimin Addinin Musulunci, kamar ilimin Akla},Fi}hu,Hadisi,Tarihi da kuma rayuwar Manzon Allah [SAAW] da Ahlul-Bayt [AS] da dai sauran Maudu’oi dabam-dabam. Saboda bu}ata da wasu sashen ‘yan uwa suka yi, na cewa rubutuk-tukan da ake gabatarwa da kuma wa]anda suka gabata a tattara su a bu]e masu shafi a Internet, domin tunatarwa da kuma amfanuwa ga sauran mutane.Akan asasin haka aka bu]e wannan shafi Kuma a halin yanzu yana da ~angarori guda bakwai sune:
1- DARUSSA DAGA RAYUWAR MANZON ALLAH {S.A.A.W} DA KUMA AHLUL-BAYT {AS}
2- DARUSSAN AKHLA{.
3- DARUSSAN FI{HU.
4- DARUSSAN HADISI.
5- DARUSSA DAGA MAUDU ‘AI DABAM-DABAM.
6- DARUSSA DAGA MAHANGAR SUNNA DA SHI’A.
7- DARUSSA DAGA MUNASABOBI NA WATANNIN MUSULINCI.
Kuma Insha Allah za’a dunga samun }ari a wa]annan ~angarori guda bakwa lokaci bayan lokaci.Da fatan abubuwan da zamu karanta, Allah {T} ya amfanar damu,ya kuma bamu ikon aiki dasu. Allah {T} yasa su kasance haske gare mu duniya da lahira. Allah {T} ya kiyayemu kada su kasance duhu da nauyi akan mu gobe }iyamah.
MUHAMMAD SULAIMAN KADUNA.
WAS-SALATU WAS-SALAMU ALA MUHAMMADIN WA ALIHI[ [AYYIBINA[ [AHIRIN. |
|